Skip to content
Part 23 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Baba Ladi ta kalle ni ta ce, “O’ oh maganar auren ne ta mayar da ke haka?”

Ko gidan Yaya Auwalun da nayi niyyar zuwa kasawa nayi. Aikin da na saba yi na gida kuwa Umma ko saurarona a kai ba ta yi ba.

Al’amuran baya sai suka fara dawo mun. “To shi kenan shi kuma wannan auren idan na yi shi menene zai zamo nashi matsalar? Don kuwa a yanzu sai na fahimci cewa babu wata mata da take zaune a dakin mijinta ba tare da ta yi hakuri da wasu matsaloli ba sai dai kawai na wasu yafi na wasu.
Haka nan na wasu yayi sanadin aurensu, yayin da na wasu kuma ake ta ci gaba da fafatawa.

Ba hakuri ko rashin hakuri ba ne yake kashewa mata aure, sai dai kawai kowacce mace da nata kaddarar.
Don kuwa sai kaga wata matar masifaffiya ta fitini kowa dangi da shi kanshi mijin ba dadinta ya ji ba. Amma auren na nan ana zaune a haka saboda kaddarar ta ba ta aure-aure ba ce.

Haka nan wasu matan kuma sai ka same su masu matukar hakuri, amma wasu ‘yan dalilai da ba su kai sun kawo ba sun zamo dalilin rabuwar nasu auren.

Ni kam a kafin zuwan wannan rana fatana daban, haka nan hankalina a kwance yake.

Haka nan na yi kyau na sake murjewa na zama cikakkiyar mace. Wanda kana ganina ka san ina da watacciyar nutsuwa da kwanciyar hankali.
To amma tunda Babana ya yi mun wannan maganar sai naji gabana ya fadi, don maganar aure a yanzu yana tsoratar da ni.

A take sai na fahimci dai wato ita ‘ya mace da zarar ta girma ta kai munzalin aure sai ta shiga cikin wani yanayi. Idan ta yi auren matsaloli idan bata yi ba ma hankalinta ba kwanciya yayi ba.

Don kuwa ita a lokacin burinta bai wuce na auren ba, haka nan mutanen gari ba barinta za su yi da zantuttuka ba.

Tsawon daren nan ban runtsa ba tunani kawai barkatai a cikin raina. Baba Ladi da ba ta barci mai nisa saboda kusur-kusur dinta da kuma sabo da tashin nafilar dare har tayi ta gama idona biyu, ban kuma tashi ba saboda ina hutun sallah.

Sai dai duk da haka kwana nayi addu’o’i cike da bakina da kuma zuciyata.

Ban samu na runtsa ba sai bayan da aka yi sallar asuba. Wajen karfe takwas da kwata na tashi na fito tsakar gida da nufin nayi wanka na kama ayyukana, sai na samu Umma ta gama.
Na nemi wuri na zauna ina karyawa ita kuma Umma tana tankade garin alkama da zata yi tuwo dashi sai kawai ga sallama.

“Wai ana sallama da Hauwa’u.” Cikin sauri na dago kai na kalli yaron, sannan na kalli Umma. Takadenta take yi ko kallona bata yi ba.

A wannan irin safiyar kuma kira haka ko karyawa ban yi ba. Sai dai duk da abinda na fada ban fasa tashi ba. Don kuwa ba sai an ce mun ga mai kiran ba, mutumin da Babana ya yi mun magana a kanshi ne.

After dress na dauko na dora a kan riga da wando na material da ke jikina na mutsuka hoda don ko hodar ban shafa ba da na fito wanka.

Na dosa hanyar fita kofar gida sai dai a daidai nan ne naji wani irin mummunan faduwar gaba take na fara jero addu’o’i ina maimaitawa. Ina kuma fata duk wanda zan gani yayi mun a cikin raina kada na samu matsala, ya kuma zamo mai alkhairi a gare ni. Don kuwa ba na fata a kan maganar aurena Babana ya sake bacin rai.

Na isa daidai inda yake tsaye ya jingina da mota. Daga bayanshi na fito. Don haka na dan kare mishi kallo. Dogo ne dan siriri yana kuma sanye da kaftani masu ruwan kasa.


“Salamu alaikum! “
Nayi mishi sallama daidai na karasa inda yake, me zan gani? Amsawar da zai yi tare da juyowa sai kawai muka yi ido hudu da malam Zakariyya.
Shi kanshi ya gane kaduwar da nayi da na ganshi. Murmushi ya yi abinda ban taba sanin ya iya ba.

“Malama Hauwa’u kina nan lafiya ko?” Kasa amsawa nayi saboda yanayin da na shiga. Haka nan ko gaishe shi na kasa yi.

“Nasan kin yi mamakin ganina ba kuma komai yasa nayi hakan ba sai dai don ganin da nayi miki na cikakkiyar ya mai tarbiyya. Wacce nasan a kowanne yanayi zata zamanto mai bin umurnin iyayenta.”

Ban tuntube ki na nemi ra’ayinki ba duk kuwa da cewa idan na bukaci hakan mai sauki ne a wurina, to sai na guji wasu abubuwa da ka iya biyo baya. Ina fata za ki gafarce ni.”
Ganin ban ce mishi komai ba, ba ni kuma da niyya, sai kawai ya ci gaba.
“Ina da mata da ‘ya’ya hudu, mata biyu maza biyu. Ina kuma fata zamu samu fahimtar juna ba tare da wata matsala ba? Zan ba ki dan lokaci domin ki yi shawara, don haka zan dawo a cikin sati mai kamawa.”

Na ce, “A’a ba ma sai nayi shawara ba.”
Ya gyara tsayuwarshi ya ce, “To menene ra’ayinki?” Na ce, “A gaskiya ni bani da niyyar yin aure a yanzu saboda karatu nake, duk kuma abinda zai shiga tsakanina da karatuna ba na son shi.”

Ya dan yi murmushi kadan ya ce, “A’a ke dai idan kina da wata matsalar kawai ki fadi, amma ba wannan ba don kuwa ni kema kin san ba zan hana ki karatu ba a matsayin da nake na malaminki, kuma nutsuwarki da na gani yasa nayi takakka na biyo ki.”

“To kuma kina ganin sai na hana ki ci gaba da karatu bayan a halin da muke ciki zaki je aji na uku ne.”

Na kawar da kaina gefe na ce, “kawai ra’ayina kenan, kuma ina fata maganar za ta tsaya a nan.”
Na yi mishi sallama na juya na shiga gida. Na zauna a kan katifata cikin daurewar kai.


To ban kullaci malam Zakariyya ba kan abubuwan da ya mun ba don kuwa ma sai na ce ban san abinda ya yi mun mai tsanani ba.


Tunda bai fadar da ni ba kamar yadda nayi zato ba daidai gwargwado, kuma abinda naci shi ya ba ni haka nan rashin mu’amallar shi da dalibai ba laifi ba ne. Don kuwa yana kare mutuncin shi ne. Daliban Jami’a wasu ko ba ka neme su ba su za su baka kansu, don shedananci.Ko kuma don suci sakamako mai kyau.

To amma kwata-kwata ni bana ra’ ayin shi. Ban san dalili ba yanayin shi na dakewa yana matukar fadar mun da gaba a duk sanda na ganshi kuma sai na tuna da Ishak saboda daurewar fuskar shi.

Mutane ne da basa murmushi sai da wani dalili. Sannan kuma sai kawai a ganni a aji na zama matar malam Zakariyya. Kai abin zai yi mun wuya tunanina daya kawai shi ne Babana, ga dukkan alama kuma ya yarda ya amince da shi.

Ga ni kuma abinda na gaya mishi a ranar ta nuna yarda ne da maganar.
Idan kuma har zan sallami malam Zakariyya to zan yi hakan ne cikin hikimar da wani abu ba zai shiga tsakanina da Babana ba.

Shiryawa nayi tsaf cikin kasaitacciyar kwalliya ta leshi coffee brown mai adon zare sky bluc da pink na yafa gyale pink na saka takalmi na pink na rike purse pink na yiwa umma sallama.

Gidan su Nasiba na tafi, kasancewar ko kwana hudu bamu yi da rabuwa ba, ya bata mamakin ganina.

Tana murmushi ke kuwa wannan irin cin kwalliya kamar sabuwar amarya?”
Na ce, “To wa ya sani ne.” Na labarta mata komai da yake faruwa, tun daga kirana da Babana yayi har zuwan malam Zakariyya da abinda na gaya mishi.

Ta dan yi shiru zuwa can ta ce, “To amma idan gaskiya zan gaya miki, to banga aibin malam Zakariyya ba. Mutum ne mai mutunci wanda babu wani mutum da ya taɓa bada labarin mummunan abinda yayi.

Sannan dan kankanin abinda yayi miki, kuma kema laifi kika yi mishi a matsayinshi na malami.

Kuma ko kina matar shi zai iya hukunta ki a makaranta don kuwa matsayinki na matarshi daban matsayinshi na malaminki daban.
Muna cikin wannan hirar ne aka yi sallama da Nasiba. Ta kalli Usman yaron Yayanta da yazo mata da sakon.
Ta tambaye shi wanda yake sallama da ita ya ce ban tambaya ba, bari na koma ya dawo ya ce wai in ji malaminku ne malamn Zakariyya.

Muka zubawa juna ido cikin mamaki ta ce, “lallai abin nayi ne. Bari na bude mishi dakin baki.”
Ta mike tsaye tana yafa gyalenta, na ce “To kada dai ki ce mishi ina nan, yauwa.”

Bata kulani ba wucewa tayi ta fita. Ni kuwa tashi nayi na shiga wurin Hajiya na zauna muna hirarmu, don kuwa mata ce me barkwanci.

Na kusa awa guda a zaune a dakin amma a raina ina mamakin dadewan Nasiba, sai gata ta shigo ta kalle ni.
“Dan zo mana baiwar Allah.”
Na mike na bita a tunanin da nake yi ma ya tafi, sai da muka fito ta ce ko kin gane ko, ina ganin ya kamata ku dan fahimci juna, don ni banga aibun shi ba. Sannan ma mutunne mai saukin kai ba yadda muke yi mishi gani ba a baya.”

Dan mintina talatin dinnan da kuka yi shi ne ki ka fahimci hakan?”

Ta ce, “A’a ba haka ba ne, amma to sai a ce boye hali yayi ya biyo ta inda ya bi don neman aurenki. Ke kin san kenan mutun ne mai mutunci.

Don kuwa da da wata manufa yake nemanki da ya dade da nunawa. Kada ki wulakanta shi idan kuma kin ga hakan bai yi miki ba shi ke nan. Yana jiranki a falo.”

Juyawa tayi ta bar ni a tsaye a wurin ta shige dakinta. Na shiga falon da ta sauke malam.

Ban samu daman daga ido na kalle shi ba, saboda zuba mun idanu da yayi yana kallona. Nabi kujerar da ke daf dani na zauna. Tun kan na gaishe shi ya ce.

“Ina fata shishshige miki da nake yi ba ya sawa kina kara tsanata?”
Nayi hanzarin dago kaina muka hada ido.

Ya ce, “Abinda na lura da shi kenan, bakya ra’ayina. To amma duk da haka ina so ki bani lokaci da zamu fahimci juna a tsakaninmu. Idan har na gane hakan ba mai yiwuwa ba ne. To ina tabbatar miki duk yadda na matsu da abin zan iya hakura. Amma a yanzu idan kika ƙi bani hadin kanki to ba ki yi mun adalci ba. Bai kamata na zauna ina gaya miki halin da nake ciki game dake bba Amma ina so ki san abin. ya kai makura ne yasa na kasa hakuri na kai ga yın magana.”

“A yanzu din nan da nake yi miki maganar nan shekaru bakwai ne da aurena da matata, amma tun bayan nan ban sake kallon wata na yi mata makamanciyar wannan magana da nake yi miki ba a yau. Ba ina yi miki maganar ba ne don ki ji tausayina ba, ni ba abin tausayi ba ne don zan iya shanyewa na hadiye na bar shi a zuciyata.”

“Tunda na dade ina shanyewa ba tare da wani ya fahimci komai a kai ba, to amma ina so na gamsar da zuciyata. Na san nayi mata adalci ban hanata abinda take so ba, sai bayan da na tabbatar yafi karfina.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mai Daki 22Mai Daki 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×