Skip to content
Part 25 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

“Hauwa’u.” Ya kara kirana. Shiru na sake yi, sai da ya kara daga murya na amsa tare da gyara zama ina kallon shi.

“Shiga daki ki kwanta.” Abinda nake ta jira kenan, don haka ban tsaya bata lokaci ba mike na nufi hanyar fita.

Ya ce, Ina za ki je? Na juyo ina kallonshi, “ga daki nan shiga ki kwanta.”

Wucewa nayi na shiga daya daga cikin dakunan kwanan shi biyu da ke falon.
Na gyara na kwanta sai dai ba barci nayi ba.

Haka nan sama-sama ina jiwo maganar ban dai san me suke yi ba.

An kusa awa guda sai naga shigowar shi ban dai motsa ba har da maganar da ya yi mun don ya gani ko nayi barci.

Washegari da asuba yana dawowa daga Sallah ya ce mu je naga kitchen da tun zuwa na ban taba lekawa ba.
Babba ne sosai don kuwa ya kai girman daki, haka nan zagaye yake da tiles kasa da jikin bango.

A gefen sink an saka kabinet bango zuwa bango ga gas cooker freezer da na’urorin girki.

Ya kalle ni “ina so ne za ki fara yin girki daga safiyar yau tunda kinga ai Amina tay miki na kwanakin ukun da ki ka yi har gashi ta yi na jiya ko?”
Na ce haka ne, don haka ina so ko shayi ne ki hada a sha da rana sai a yi abinci na ce “to.”

Kamar yadda ya fada hakan nayi sai dai na dada da soyayyen kwai tunda da biredi za a sha shayin.

Yana tsaye yana saka links din rigarshi ni kuma ina goge mishi takalman da zai sa maganar makarantata tana cina a rai.

Amma na gagara yi mishi maganar. Ya gama shirin shi zai tafi ya ce, “Ki yiwa Amina magana zata nuna miki komai na kayan amfani.”

Na ce, “To”. Har ya juya sai ya dawo “Kina da magana ne?” Kamar nayi shiru sai na kasa na ce “eh.”

Ya ce, “To menene?” Na ce, “Ta game da makarantana ne. Ya ce, Ban manta ba, sai dai na yi nufin kiyi sati biyu ne sai ranar Monday ki fara zuwa.”
Amma idan kinga hakan bai yi miki ba ki shirya gobe ki fara zuwa.

Na dawo dakin nashi nayi mishi kyakkyawan gyara na hada kayan wankin dakin.

Sannan na nufi kicin don nasan dakina baya bukatar gyara.

Sai da na gama gyaran kicin din sannan na fito na samu Amina a dakinta.

Tana can ciki, don haka a falo na tsaya na yi sallama. Ta fito cikin murmushi.
“A’a, Amarya ta fito ko ai Darling yayi mun magana kan ya kamata na huta haka kema ki shiga kicin din, shekaru bakwai ai ba wasa ba ne.”

“Kullum fa aikin kenan da safe kana kicin da rana haka da daddare kuma baka huta ba. Ai kin ga kwana biyu ai nima na dan samu barci. jiya har ce mun ya yi na kara dan nauyi alamar na yi kiba.”

Na ce, “Haka ne. Ya ce, Nazo wurin ki ki nuna mun abubuwan amfani.”

Ta fito ta shiga kicin din tana nuna mun inda abubuwan suke. Ta juya ta fita na kasa hassala komai don bacin rai.

Me take nufi da maganganun da tayi mun. Na dan kokarta na fara aikina.
Dafaduka nayi da taji hadin kayan lambu da karas da hanta, sannan nayi lemon ginger na hada duka na gama cikin kankanin lokaci.

Don haka nayi wanka na gyara jikina na kammala komai a wajen shi kamar yadda aka saba.

Ba a wani dade ba naji dawowarshi na mike na shiga falon, amma har Amina ta riga ni ta tsiyaya mishi lemon jinjar tana ba shi a kofi.

Raina ya sosu amma sai na shanye na karasa tare da yi mishi barka da zuwa.
Na gyara zama ina zuba mishi abincin na mika mishi ya karba ya fara ci, ita ma Aminan tana ci tana magana.

“Kaga cin abincin yan Jami’a, wannan hade-hade ai dole yayi dadi ko ya ki don kuwa zakin abinda ke ciki kawai ya isa.”

Kamar yadda ban ce ba haka shima ya gama cin abincin shi ya koma wurin aiki, nima na tattara wurin sannan na fito na samu yara sun dawo.

Na basu abincin sannan na dora na dare, Tuwo na yi miyar kuka.

Ana gobe zan koma makaranta. Malam ya zauna damu a falon shi “Amina Hauwa’u zata koma Makaranta gobe.
Don haka ina so ki rinka yin abincin rana kullum in yaso ita sai ta rinka yin na dare.

Bata musa ba haka nan ni ga wurina sauki na samu, don haka shiri sosai na yi.

Da sassafe muka fita tare zuwa Makaranta. Yan ajinmu kowa da abinda yake fada akan canzawar da nayi, ballantana Nasiba da ke ta bi na da kallo
Ta dai gaji ta ce, “Kai mu ma dai bari mu yi auren nan mu ji.” Na ce, “Kyaji dai da shi.”


Kullum da safe tare muke tafiya Makaranta mu kuma dawo tare. Idan muka dawo kuma to zan zo na samu Amina tayi abincinta na rana.

Don haka ni kuma idan na dan huta sai na shiga kicin na yi na dare.
Ban taba sawa Amina ido a kan harkarta da mijinta ba. Don kuwa ranar kwananta ina gama cin abincina nake tashi na tafi dakina nayi harkokin gabana.

Amma idan kwanana ne to sai ta kai sha dayan dare, idan ba ce mata ya yi zai kwanta ba.

Haka nan idan ranar kwananta ne ko da nake yin abincin dare to ita nake mikawa ba na cewa don nayi abincin sai na zuba mishi da hannuna.
Ita kuwa ko ni ce nayi abinci ranar kwanana to idan ban yi da gaske ba sai ta zuba ta mika mishi, tana tambayarshi abubuwan da yake so.
Na yi ta kokarin daurewa akan abin, amma ta kai ma daga shi har ita sun kure ni.

Don haka yau da na gama abinci kai musu na yi falon na baiwa kowa a gidan nashi na debo nawa na dawo dakina na zauna na ci na ƙoshi. Na dauko assignment din da nake dashi na fara yi.

Wajejen karfe tara sai gashi ya shigo dakin ya nemi wuri kusa da ni ya zauna.

Lafiya ki ka dawo nan?”
Na ce, “Lafiya kalau, ina dai da abin yi ne.”

Ya ce, “To ai da sai ki zo muje can ki yi abinda za ki yin.” Na ce, “Ai ina son nutsuwa ne sosai.”

“Kina so ki ce mun idan kina tare da ni ba bi da nutsuwa?
Na ce, “Ni fa ba haka nake nufi ba, amma ka duba ka gani fa lissafi ne kashi uku cikin hudun aikin.”

Haka dai ya hakura ya bar ni ya tafi.
Washegari kuwa na ci abinci a falo sai dai ban wani bata lokaci ba na mike na dawo dakina.

Ko da kwana ya juya kan Amina ma ban tsaya ba ina gama cin abinci nake dawowa dakina.

Idan ya tambaye ni na ce kasan jarrabawa ta kusa ina da bukatar samun lokaci don karatu.
Sai dai ban sani ba ko abin ya fara gundurar shi ne.

Da wurwuri na gama aikina na kammala komai a yadda muka saba na dauko nawa na dawo dakina na zauna.
Zan fara ci sai gashi ya shigo, “Tashi ki wuce mu je.” Na kalle shi sai dai ban mishi musu ba don banga alamar zan iya yin hakan ba saboda yanayin da na gani a tare dashi.

Muna shiga falon Amina tana zaune tayi baje-baje ta sheka kwalliya sai kyalli take yi.

Ta kalle ni tayi ‘yar dariya ta ce, “Hauwa ‘u kenan ‘yar lelen Darling to ke in banda abin ki, kin san darling ya saba cin abinci a nan don kin yi girki ki dauki naki ki tafi ai kin san ba zai sa ya ɗauki na shi ya biki ba takamar ke kika yi.”

Ban ce mata komai ba shima bai ce ba sai dai maganar ta kara ɓata mun rai.
“Nemi wuri ki zauna ban kuma yarda daga yau ki kara daukan abincinki ki tafi wani wuri ki ci ba.”

Ban wani ci abincin ba, shima kuma hirar yau ba wani sosai yake amsata ba tara da rabi nayi na mike da nufin zuwa na kwanta.

Ya ce, “Ina za ki?” Na ce “zan kwanta” ya ce “ga daki nan” na dan yi jim saboda ko kadan ba na jin dadin raina na ce “ina so ne na yi Assignment.”
Ya ce, “gobe ki yi.” Dawowa nayi na wuce shi na shiga dakin barcin shi na kwanta.

Bai shigo ba sai wajen goma da ashirin. Daidai inda nasa kaina a filo yazo ya tsaya ya kira sunana na amsa ya ce “tashi ki zauna.”

“Menene damuwarki? Ya tambaye ni bayan shima ya zauna a kan wani madaidaicin stool muna fuskantar juna.”

Na ce, “Babu.” Ya ce “akwai gaya mun kawa don na san kina da ita.” Nayi shiru ban ce komai ba.

“Haba Hauwa’u idan nayi miki wani abu ki fada mun don na gyara idan kuma wani ne sai na dauki matakin da ya dace akai amma idan ba ki fada mun ba wa za ki fada ma? Ba zamana kike yi ba. Ba zan so na rinka ganin ki cikin bacin rai ba abin kuma da ke faruwa kenan kwana biyun nan”.

Maganganun da yake yi mun su ne suka sani fara kuka saboda nauyin da kirjina ya yi mun.

Sai da na yi kukana na share hawaye sannan ya ce “ki yi hakuri amma ban san na bata miki rai haka ba.”
Ya mike ya dauko robar ruwan sanyi ya miko mun, ban musa bà na karba na kwalkwala na gyara zan kwanta tare da jan bargo zan kwanta.

Yana zaune a inda yake ya ce, “idan kika yi mun haka kin yi mun adalci?” A hankali na ce,
“Me na yi maka na rashin adalci?
Ya ce, “Ba ki sani ba? Ya ce, Yaushe rabonki da kwana a dakin nan? Kin kusa kwana goma.”

“Na kyale ki ne saboda ba na son takura miki, amma ke banga haka a tare da ke ba.”

“A yanzu kuma da na tirsasa ki kin ja bargo kin rufa. Tashi ki yi min bayanin abinda kike so zan yi miki, amma bana son ki rinka kokarin da ƙarfi sai kin tauye mun hakkina da ke kanki.”
Danne tawa damuwar nayi na biya mishi tashi bukatar.

Zazzabin da na tashi dashi ya yi dalilin da muka kusa makara.

Duk da ban tsaya yin wani abu ba baya ga shayin da na dafa.

Daidai lokacin da muka yi break sai ga wayar shi. Na kalli Nasiba na ce, “Ki raka ni ofishin malam yana kirana.”
Ta ce, A’a ke dai je ki nasan abinda kiran yake nufi, sai kuma kawai ya ganni sokai-sokai na rakaki.

Na juya na barta a friends joint na nufi ofishin shi. Na samu dalibai da yawa amma sai na nemi wuri na zauna a can gefe saboda sanin da nayi ofishin ba ya rabo da dalibai masu matsala.
Don shi ne Dean of students affairs, yana sallamar na ciki ya kira sakatariyar shi ya ce mata kada wani ya sake shigowa.

Sannan ya dawo ya ce “Yaya jikin naki?” Na ce da sauki. “To me zan kawo miki?” Na ce, “ruwa kawai”.

Ya miko mun ruwan sannan ya zauna a kan doguwar kujerar da nake zaune a kai ya mannu ya jikina. Na dan yi kokarin matsawa don kuwa kunyar Malam kan kama ni a irin wadannan lokutan.

Shima matsowa ya sake yi na dan yi murmushi ya ce, “A to kya yi dariya dai kema, me yasa ki ke guduna?”
A hankali nayi magana na ce, ”Ba na gudunka.

Ya ce, “Kina yi mana kodayake na fahimci laifi na yi miki shi yasa nake so ki gaya mun laifin.”

Na rasa yadda zan yi nayi mishi wata magana. “Ka da kiji kunyar gaya mun matsalarki.”

Ganewan da na yi ba zan iya kaucewa ba yasa na ce, “Ni dai kawai na fi so na rinka zama a dakina ne.”

Ya ce, “zan bar ki ki rinka zama a dakinki idan kin gaya mun dalili.” Na ce, “dalilin kenan saboda karatuna.”
Ya ce, “ban yarda ba, wannan ba dalili ba ne don haka ban yarda da zaman daki ba, tashi ki ba ni madara a fridge.”

Na mike na isa wurin fndge din na dauko hade da tumblan na tsiyaya na mika mishi, ya zuba mun ido yana kallona.

Na dan kawar da kaina gefe. Yasa hannu ya riko hannuna da kofin gaba daya ya kai bakin shi. Sai da ya shanye madarar sannan ya sake hannuna na ajiye kofin.

Ya ce, “ki koyi hidimar mijinki. Ki kula da abubuwan da yake so da dabi’unshi nunawa na kusa dake cewa abinda yake yi baya ba ki haushi. Don za ki yi wanda yafi haka. Kina da kyau kina da kuruciya, baya ga haka Allah yayi miki wasu baiwa da kema ba ki san da su ba. Uwa uba kuma mijinki yana sonki. Kada ki bar wa wata mijinki saboda zafin kishi.”

“Kuma don kina jin haushin wani abu ba zai sa na canza dabi’ata ta zama da ku ba a kullum.”

Dan Juyowa nayi na kalle shi saboda abubuwan da yake fada. Ya ce, “eh matsalarki kenan ko ba haka ba ne?”
Na ce, “Ni ba haka ba ne, na ce maka ba ni da matsala.” Ya dan yi dariya ya ce, To na ji ba ki da matsala.

Na mike da niyyar tafiya, don ganin lokaci ya kure na break din mu, na dauki tumblan da robar zan mayar, shima ya mike ya biyo ni.

Ina ajiyewa na juyo ya rike ni tare da mannani jikin bango yasa hannu ya zare hijabin da ke jikina.

Na dan fara kokarin yin magana amma bai bar ni ba. Na fara kokarin zamewa ya dauke ni ya ajiye ni a kan makeken teburin da ke tsakiyar office din.

Da kyar naja jikina na koma kan kujerar da na baro na kifa kaina. Na kasa komawa kusa da shi na dauki hijabina. Na kuma kasa kallon shi.
Ya taso ya zauna kusa da ni tare da jawo ni jikin shi nayi saurin cewa “zan koma aji fa.”

“Kuma…” Ya ce, “kuma me?”
Kunya tana da kyau a addini, amma taki ta yi yawa Hauwa’u, ki daure ki dan rage saboda ni ki taimake ni kema kuma ki taimaki kanki.

Da na dawo na zauna sai na fahimci gaskiya kawai ya gaya mun, kishi shi ne abinda yafi kuntata min.
Don haka ya zama dole nayi ko yi da shawarar da ya ba ni.

Shiri sosai nayi ranar da na karbi girkina na yi kayatacciyar kwalliya.
Na shiga dakin shi na fitar da duk wani abinda bai yi mun ba, na sake shimfidu na feshe shi da turare.

Ina kammala abinci kuwa na hada komai.

Na zauna zan fara zuba abinci sai Amina ta dauko plate din shi zata zuba mishi kamar yadda ta saba.

Na mika hannu da niyyar karba, ta kalle ni, “Ai zan zuba mishi ne, na ce eh na sani amma ci naki kawai na hutar da ke.”

Ta dan tabe baki tare da cewa, “ai shi kenan.”

Na zuba mishi na mika mishi, sannan na zuba mishi abin sha na ajiye a kusa da shi.

Sannan na zuba nawa na fara ci. Duk motsin da zai yi idona na kanshi na kankane, don haka yau ko doguwar hira ba ayi ba.

Tun ina yi ina dan jin kunyar abubuwa har na zake, sai kuma na gane da gaske abinda ya takura mun kenan.
Shirye-shiryen jarrabawarmu ya kankama gadan-gadan, don kuwa a gobe ne ma zamu fara.

Zama tsakanina da Amina ya canza gabadaya, don kuwa sai na gaisheta sau uku kafin ta amsa mun sau daya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mai Daki 24Mai Daki 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×