Skip to content
Part 27 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Bana shiga harkar Amina, amma ita sai ta shiga tawa. Har ya gama cin abincin bai sake cewa komai ba.

Na kuma san dama tayi mishi maganar ne don ta saka mishi damuwa a ranshi da zargi.

Wanda dama daga tambayar da yayi mun a ranar da abin ya faru.

Ganin da nayi hankalinshi yana wani wuri yasa na tattara abin da zan tattara na wuce shi naje na kwanta.

Washegarin da muka gama jarrabawa a gida na wuni. Ina zaune a gaban Baba Ladi don har yanzu tana nan bata tafi ba, tana yaba mun kyan da nayi.

Ta ce, “Gashi ba zama ki ke yi ba amma kwanciyar hankali sai dai ina ga ko za a karbar miki magani ne ‘yar nan? Na ce, A’a Baba Ladi lafiya kalau, ni kuwa na fada mata haka ne don na san matsalata ya kuma zamar mun dole na fuskanci Malam na yi mishi bayani.

Sai dai ta yaya? Tunanin da nake ta yi kenan. Ban koma ba sai da na jira dawowar babana na yi musu sallama bayan nayi musu Alherin da na riko musu.

A yanzu zamanmu da Amina ya canza.
Kasancewar mun gama jarrabawa ni ke yin Abincina na cikakken kwanaki biyu rana da dare.

Babu damar na fito tsakar gida zan yi wani abu ko zan shiga kicin sai ta fara zazzaga maganganun habaici iri-iri.

Ni kuma ban iya irin wadannan habaice-habaicen ba, don haka ba na kulata.

Abinda na sani shi ne, ba ta fito baro-baro ta ce dani take yi ba.

Duk da nasan dani din take yi, ni kuma ba na son rikici.

Rannan na kwana dakin Malam na fito da sassafe cikin kwalliya sosai don yin abin karyawa. Kamar yadda muke hutu suma malam Jami’a hutu suke yi.

Don haka shima Mallam baya zuwa aiki kullum, sai ya dauro.

Kokarinshi na ganin ya kammala karatun shi ne na Phd din da yake yi.

Hakan ne yasa na kuke nake shirya mishi gara iri-iri. Na shiga kicin na fara harhada abubuwan da zan yi amfani da su, sai ga Amina ta shigo.

Ta tsaya tana kare mun kallo, na ce mata ina kwana? Sai da ta tabe baki sannan ta ce, lafiya.

Wai Allah ya rufawa mutane asiri kwashen ragowar mutane Darling ya dauko in banda haka da ban san irin sanaben da aka yi mana a cikin gidan nan ba.

Duk da bata mun ran da maganar tayi ƙokari nayi na shanye amma sai na juyo na fuskanceta.

Nayi murmushi na ce, Amina kenan, ai ni ya kwaso ni yana da cikakken sanin cewa biyu sun aure ni kafin shi.

Amma duk da haka ya aura yake kuma ganin mutuncina da darajata da ta iyayena.

To amma ke fa? Matar da ya aura a zaton budurwa ya ganta a burme ga kuma tsaraba a sunke jagwalgwalon ‘yan birni?

Don haka duk abinda za ki gaya mun fade shi ba zan ji haushi ba.

Na juya na ci gaba da aikina, kirjina sai harbawa yake yi don naji zafin maganar da Amina tayi mun.

Ni kuma nasan na fada mata ne kawai don ramuwa ba wai don naji ba, asali ma ni ban san komai game da ita ba. Baya ga ‘yan uwanta da nake gani suna zuwa.

Ban san lokacin da ta bar wurin ba, na dai juyo ne ban ganta ba.

Na gama aikina na dauko a babban tray na shiga falo zan ajiye na sameta a falon tana zaune tana kukan sharbe shi kuma yana wasu bayanai da ban fahimta ba.

“Zo nan Hauwa’u”. Na dawo kan doguwar kujerar da yake na zauna na ce gani.

“Me ya hada ki da Amina ki ka gaggaya mata maganganun da kika yi mata?” Na kalle ta yadda ta dage take fyace majina da gefen rigar barcin ta.

Na ce, “ zo ne ta ce maka na gaya mata bakaken maganganu amma bata yi maka bayanin dalilin da yasa na gaya mata ba?”

Ke ba na son surutu, ki bani amsar tambayata kawai.

Nayi mishi bayanan komai da ya faru tun shigarta kicin samuna da tayi da kuma maganar da ta gaya mun.

Shiru ya yi, zuwa can ya ce “ni na sanki Amina na san kuma ba karya tayi miki ba, kin fada mata abinda ki ka fada wane hukunci ki ke so nayi mata bayan ke ce ki ka fara gaya mata bakar magana.”

“Duk lokacin da ɗayarku ta tsokani wata da magana ta rama kada mutum ya zo wurina don ya ji zafi. Ba na so, ya ya zan auro mata ki zo kina gaya mata irin wadannan maganganun, idan Bazawara na auro ta ina ruwanki, ina abinda ya shafe ki?”

“Ke na aurowa ita ballantana ki ce bata yi miki ba? Ai ni ki ka zaga ba ita ba.” Ya kalle ni.

“Tashi ki hada mun abinci.”

Na hada mishi abin karyawa na mika mishi na hada mishi ruwan lipton a wani kofin na ajiye mishi.

Bata nuna alamar ci ba don kuwa har yanzu zaune take tana kuka tana fyace majina.

Ya gama karyawa na mike na dawo wurina na kwanta don na dan samu barci sai dai hayani ya ce ta kaure tsakaninsu ba na jin abinda yake fada ita ce dai take bayanin ya wulakantata. Ya tona mata asiri a wajena, don haka ita ba za ta yarda ba.

Wasa gaske karamar magana sai ta zama babba, kafin yamma ina kicin sai ga iyayen Amina sun iso, Goggonta da kuma yar Aminan. Na shiga dakin Aminan inda suke na gaishe su, sannan na kai musu abin tabawa tunda ni ce a kicin, na dawo na ci gaba da harkokina.

Ba a jinma ba aka yi kirana a falo na shiga, gabadaya sun hallara. Na ce mishi, “Ga ni”

Tunda shi ne ya kira ni ya ce yi musu bayanin abinda ya faru dazu da safe.
Na yi bayanin komai suna salati suna salallami tare da tafa hannu, ita kuwa Amina Kuka take yi.

“Alhaji ka ci amanar son da yarinyar nan tayi maka.” Ya kalle ni “Tashi ki tafi.” Na mike zan tafi, Goggon Amina ta ce, “A’a ta tafi ina, ai gara ta zauna ayi da ita tunda ko ta tafi ma kawar da jiki ne kawai za a labarta mata komai.”

“Tunda ta kai ma sirrin dake tsakaninka da matarka dadadde ma bai tsira ba.” Ya kalle ni,
“Ina ce aiki kike yi? Na ce, eh. Ya ce “To je ki abinki”.

Na dawo kicin jikina a sanyaye magana na gayawa Amina don taji zafin ta gashi ta zama gagaruma.

To da alama dai kenan maganar da na fada mata gaskiya ce ko kuwa yaya? Ba su fito ba sai sallar Magariba.

Na kai musu abincin su dakin Amina, nima na shiga dakina don gabatar da sallah ta.

Mallam bai nuna min komai kan maganar tunda da ni da shi ne kawai muka san maganar bata taba shiga tsakaninmu ba.

Nayi ta ne kawai don na rama bakar maganar da ta yi mun, ita kuwa Amina tsakaninsu da Darling din nata ya ki dadi.

Don ta kafe akan cewa ya wulakantata a wurina, ya tona mata asiri.

Zama tsakanina da ita kuwa abin ba a cewa komai, don a yanzu ko na gaisheta bata amsawa.

Idan kuwa a wurin cin abinci muka gamu, to babu mai cewa kome, ya haɗa mu ya yi mana magana kan hakan, ta ce ita tsakaninta da ni babu zaman lafiya har abada.

Idan ba kwatar mata hakkinta yayi ba. Za kuma ta tabbatar na gane kurena. Ya ce to babu laifi, ke Hauwa’u na ce na’am, ya ce ke ce ƙarama don haka kada ki gajiya. Da gaisheta da kike yi kullum.

Don Allah baya son gaba ta wuce kwana uku, haka nan kada ki riketa da komai a cikin ranki kin gane ko? Na ce eh ta kalle ni taja tsaki ta tashi ta tafi.

Don haka ba na jin haushinta, ya’yanta kuwa ‘ya’yan mijina ne, ina da kyakkyawar alaka da su.

Ko da ba sa zaman gida saboda makaranta, duk lokacin da su kenan mu’amallar da ke tsakaninmu mai kyau ce.

A daidai wannan lokacin ne na fahimci ina da sabon shigar ciki, saboda kula da nayi ta hanyar yawaita yin gwajin do it yourself da nake yi.

Na same shi zaune yana duba takardun da yake rubutawa na kammala karatunshi na nemi wuri na zauna ina jiran ya gama.
Ya kalle ni, yaya dai amarya da magana ne.

Na dan yi murmushin jin sunan da ya kira ni, na ce “eh amma ai zan jira ka gama tukuna” ya ce, “A’a ke dai na tattara na ajiye kawai maganarki ai tafi wannan aikin tunda don ku ake yin shi.”

Matso nan ki zauna na karasa inda yake nuna mun na zauna sai dai na kasa yi mishi bayanin saboda zuba mun ido da yayi.

Ya dan yi murmushi ya ce, “Hauwa’u kenan, kin san wani abu? Na dan girgiza kai ya ce, Kunyarki tana ba ni sha’awa, tana kuma ƙara mun sonki da ganin martabarki a kullum.”

“Don kuwa nasan kunya aba ce da Allah yake yiwa salihan bayinshi.”

Cikin hikima ya saka ni nayi mishi bayanin komai, don haka take kawai sai ya kira likitan da yake mu’amala da shi ya ce, mu same shi a gida.

Ya rubuta gwaje-gwaje da kuma scarning, ba mu dawo gida ba sai da muka biya muka yi.

Kamar yadda aka taba yi mun bayani a baya, wannan ma haka ne, bambanci kawai shi ne wannan cewa yayi mahaifata bata da karfin rike nauyi mai yawa.

Don haka idan cikin ya kai wasu watanni za a daure bakinta, don haka zan rage ayyukan ƙarfi da kuma yawan zirga-zirga har zuwa lokacin da za a daure.

Muka dawo gida ya ce naje na kira mishi Amina. Nayi sallama a bakin kofar na shiga nayi mata bayanin kiran da yake mata, muka hadu a falon mata bayani a gajarce.

Sannan ya ce, Don haka yana so ta karɓar mun aiki har kafin na samu lafiya nayi kwari.
Tayi mishi wani irin kallo da ban taba ganin tayi mishi makamancin shi ba, sannan ta ce
“Zakari kenan lallai ka same ni a yadda kake so, na karbeta abinci fa ka ce?”

Ya ce. “Eh na wani dan lokaci ne kawai saboda lalurar da ke tare da ita.” Ta ce, “To ba zan iya ba ko cikinta ya zauna ko kada ya zauna wannan matsalarku ce ba tawa ba. A kan wannan ‘yar iskar karuwar da ka…”

“Ke!” Ya daka mata tsawa, take kuma da ni da ita muka zuba mishi ido.

Ni dai na dauka zai rufeta da duka ne saboda abinda na gani a cikin idonshi, itama kuma ba ta kara cewa komai ba.

Juyawa tayi ta fita. Shi kuma ya koma ya zauna sai da na bari zuciyarshi tayi sanyi sannan na ce “ni fa idan ka yarda ma zan iya yin girki tunda dai ba mai yawa ba ne.”

Ya ce, “A’a ki bari kawai nasan abinda zan yi.”
Da daddare Amina ba ta yi abinci ba, kamar yadda ta fada shi kuma ya ce bai yarda nayi ba.

Don haka takeaway yayi mana har da yaran gabadaya.

Washegari da safe da kanshi ya shiga kicin ya tafasa ruwan zafi ya hada tea ya baiwa yaranshi, sannan ya ajiye mun ya tasa ni a gaba.

Na ce, “da ka yarda da abinda nake gaya maka. Zan iya kananan aikace-aikace shima likitan ya gaya maka jijjiga jikina ne ba zan yi ba.”

Ya ce, “Ban yarda ba, idan kuma na gane kema ban isa na saki ko na hanaki ba zan san irin zaman da zan yi da ke.”

Wannan magana da yayi tasa jikina yayi sanyi, don haka ban sake yi mishi maganar ba.

Kwance kawai nake a dakina tunda yau Aminaa tarbi kicin din.

Waya muke yi da Nasiba kan batun aurenta wata mai zuwa, tare da yi mata bayanin halin da nake ciki.

Muna ‘yar hira kan shirye-shiryen bikin mallam ya shigo ya zauna a kusa da inda nasa kaina a kan gado yana jin hirar shakiyancin da Nasiba take yi.

Ya dan yi murmushi bayan na kashe wayar ya ce, Kawancenku da Nasiba dai akwai mamaki a ciki, don kuwa halayenku daban- daban.

Na gyara zamana a kan gadon ya miko mun ledar da ke rike a hannunshi tare da plate na bude rabin kaza ce sai wata hadaddiyar shinkafa a robar disposable.

Na mike tsaye ya ce, “ina zuwa?” Na ce zan zauko abu ne a fridge. Ya ce, zauna me za ki dauko? “Na ce ruwa.”

Ya isa fridge din ya miko mun robar ruwan Swan, gyara zama nayi sai da na kusa cinye abincin nan da rabin kazar sannan nasha ruwa, sannan ya fita.

Da daddare ma shigowa yayi ya ce “ko zamu je falo ne to idan za ki iya” na dan yi murmushi na ce, “Haba dai nan da falon kum bayan na ce maka gar nake jina.”

“Ka dai ki yarda ne in kuma aka ce haka zamu yi ta zama ai zaka wahala da yawa, ya ce “to ya na iya Hauwa’u?”

“Ina so naga dan da za ki haifo mun sannan ko ba don ni ba kema ai kina da hakkin na kula da ke, sannan na gamsar da kaina cewa ban kware ki ba. Don ina da wasu ‘ya’ya ke fa?”
Tausayinshi ya kama ni, lalurar da ta same ni a gidan wani shi kuma yana ta wahala da ita.

Muka shiga falon Amina ta sha kwalliya tana zaune ta gama abincin ta tunda girkinta ne.

Ban sani ba ko ganin Malam da tayi daga wurina ne ya ɓata mata rai?


Tunda ba ya shiga dakin wacce ba ita ce da girki ba, sai bisa lalura. To ita kuma bata dauke ni a matsayin mai lalura ba. Babu wanda ya ce wani abu a cikinmu har ita.

Na nemi wuri na zauna shi kuwa ya shiga uwar dakin shi. Ta mike ta bishi zuwa can ya sake fitowa tare da ita ya zauna a kan kujerar da ya saba zama.

Ta dauki plate dinshi ta zuba mishi abinci ta mika mishi, bai kalleta ba da remote a hannunshi yana kokarin kamo (BBC World).

Ta gaji ta ajiye a kasa ta zuba mishi ruwan lemo a kofi, ta debi nata taja gefe ta fara ci.

Ni dai dama a koshe nake don kuwa duk sanda ya fita zai shigo mun da wani abu. Babu wanda ya yi magana a cikinmu, don kuwa yanzu bama hira da Amina.

Hirar dai da shi ne, to shi kuma yau fuskar a daure take, don haka sai kawai na mike na dawo dakina, saboda hango abubuwan da ke shirin tashi da nake yi.

Malam ya daina cin abincin Amina kwata-kwata, ni kuwa kullum zai kawo mun na rana da na dare da safe kuwa hakura nake yi na sha tea a hankali kuma yana ta neman mai aiki har kuma an samu, sai dai aikace-aikacen gida ne kawai ban da girki.

Amina kuwa babu abinda bata yi ba amma ya ki yarda ya rinka cin abincin nata, wanda hakan ne yasa manyansu suka zo don yi musu sulhu.

An kuma bata rashin gaskiya, shi kuma an ba shi hakuri tare da jaddada wa Amina kan ya kamata ta gyara kan zamanta da mijinta shi kam ya kafe ya ce ba zai ci abincin ba sai na wartsake mun koma canje-canje yadda aka saba, amma yanzu tunda ya nemi alfarmar ta a farko taki to ba ya so ta rinka girkawa tana ci.

Bikin Nasiba yazo, har gida ta kawo wa malam wanda za ta aura suka kuma ba shi IV. Don haka shiri sosai muke yi na bikin, duk da dai a gida nake zaune amma komai da ni ake yi a waya.

Sanin da nayi malam ba zai bar ni zuwa walima a send forth ba yasa ban ma bata lokaci wajen tambaya ba, amma a yau daurin aure shiri nayi cikin wani irin leshi mai kyan gaske.

Ga wani irin annuri da ke fita a jikina na kwanciyar hankali da zama wuri daya, ga kuma kyan da yaron ciki ke sawa.

Don haka ko ban ce komai ba ma an san na hade kenan. Zama nayi a dakina ina jiran shigowar malam don mu tafi tare, tunda nasan zai halarci daurin auren, wanda za ayi karfe goma na safiya.

Ya shigo dakin cikin babbar riga ‘yar ciki da wando na asalin yadin voil fari tas da hular sh damanga itama fara.

Sai bakin takalmi sawu ciki da agogonshi da ya daura rolex mai bakar fata.

Ina murmushi ina kallonshi a yau kam annurinshi bai sa na kasa kallonshi ba, dogon mutum sosai dan siriri ba can ba baya cikin bakake baya cikin farare.

Na sha rokonshi ya bar kasumbar shi da kullum yake kankarewa amma sai yayi murmushi kawai ya gyara dan gashin bakin da ta zagaye labban bakinshi na sama.

“Na dai yi kyau kenan” Na sake fadada murmushina na ce, ba kadan ba, ya ce to “ zan tafi.” Na mike ina gyara gyalena, ya ce ina za ki? Na kalle shi na ce, gidan bikin mana. Ya ce, a’a ni ba mu yi haka da ke ba, gabana ya fadi na ce, “Haba Mallam, bikin Nasiba ne fa kada kayi mun haka.”

Ya ce, “Zan yi miki fiye da haka don kuwa ba zaki je ba in dauke ki na kai ki gidan biki na ajiye ki na dawo, ke hankalinki daya kuwa?”

“Ba kya kallon halin da ki ke ciki ne? Duk yadda ki ke da Nasiba ba zai sa nayi gangancin da za ki yi mun asarar wannan cikin ba, gara ki san da haka.”

Juyawa ya yi ya fita ya bar ni a tsaye rike da gyalena a hannu, kukan da nayi ranar ba na wasa ba ne.

Ace yadda muke da Nasiba amma wai an hana ni zuwa bikinta? Ita ya ya zata dauki abin.

Wajen sallar azahar ya dawo yana kallona, ya ce kai Hauwa’u kenan kuka kika yi? Wasu hawayen suka zubo mun ya dan yi murmushi ya ce, “Gaskiya ban kyauta ba yi hakuri ki ci abincinki ya gyara zama ya bude abinda ya zo mun da shi.

Ya ce, “bude baki na ba ki da hannuna. Ban kalle shi ba. Ya ce, “Idan kina son na bar ki ki je gobe na dawo na samu kin cinye.” Ya tashi ya fita saboda kiran da aka yi mishi a waya.

Na dan wartsake saboda maganar da ya yi mun, don haka washegari ma da sassafe na shirya ban tsaya jiranshi ba, bin shi falon shi nayi na samu yana wanka.

Na shiga har cikin dakin na zauna a bakin gadon ya fito yana kallona, “kai Hauwa’u kina jin dadi fa, wannan kwalliyar duk ni aka yi wa ita” Na dan yi murmushi.

Ya jawo mai zai fara shafawa ya ce, “yanzu kinga in banda ba na son ki rinka wani motsi mai ƙarfi ai da sai na baki man nan ki shafa mun.”

Na kalle shi na ce, “Mallam yanzu man ma motsi ne mai karfi” ya ce, “eh mana ni inda zai yiwu ma ai da ko numfashin nan naki da karban miki nayi.”

To amma ina ba hali, ya mike ya dauko kaya yana sakawa, ni kuma ina kallon agogo saboda kaguwan da nayi shima ya kalli agogon ya ce, “Af, kina kallon agogo zan bata miki lokaci ko, yi hakuri bari na dan je nan kusa na dawo sai mu tafi.” Na ce, “To ko zaka sauke ni ne sai ka wuce daga can?” Ya ce, “Ki dai jira ni ba wani dadewa zan yi ba.”

Tun ina jiran Mallam a zaune har na gaji na kwanta barci ya dauke ni, ban farka ba sai wajen Azahar na dauki waya na kira shi bugu daya ya ɗauka. “Yaya amarya kin gaji da jira ko? kada ki damu gani nan. Ba shi ya dawo ba sai wajen karfe hudu da rabi.”

Ya shigo tamkar babu abinda ya faru, “Allah dai yasa kin yi tunanin hada tea kin sha tunda ban samu kawo miki abinci da wuri ba.”

Karo na farko da yayi magana ban kula shi ba ya ajiye abincin.

Wani irin lafiyayyen kifi da aka bude shi aka cire kayarshi, sannan aka gasa yayi kyau ya ajiye a gefena tare da robar ruwa.

“Ba na so kina shan zaki da yawa.” Ya yago kifin “Bude baki na baki.” Na kalle shi takaicina ya sake karuwa ganewan da nayi da saninshi yayi mun abinda yayin.

Na mike zan bar wurin, ya ce “zo nan. Ban kula shi ba na ci gaba da tafiya, zo nan Hauwa’u kada ki koyi dabi’ar da ba ta ki ba.”

Dawowa na zauna. hakuri. Kuka na kama yi saboda bacin rai, yau ne ranar karshe ta bikin Nasiba.

Kuka sosai nayi yana bani hakuri. “Tun jiya nayi mata bayanin ba za ki samu halarta ba ta kuma san ba haka kawai zan hana ki ba, ai tasan lalurarki.”

Na ce, “To ai da sai ka gaya mun ba ka sa ni na saka rai da zuwa ba,” ya ce, “To nayi kuskure ba kuma zan kara ba”. Ya sake miko min kifin. “Yi hakuri ki ci, don nasan kin huce.”


Cikina ya yi kwari har an saka mun robar an kuma dan rage min dokoki sai dai ba mai yawa ba, don haka Mallam ya kai ni gidan Nasiba nayi mata wuni zur.

Gidanta ita kadai, don mijin nata bai taba aure ba. Komai na gidan mai kyau. Na kuma kai mata gudunmawa ta duk da sanin da nayi Malam ya bata.

A gida kuma na fara yin abinci tare da taimakon Sahura mai aiki, sai dai lallabawa nake yi komai a hankali.

A lokacin ne kuma aka kawo Abulkhairi hutu. Na gayawa Mallam ina so naje gida ya ce, a’a a kawo shi nan.

Yaron ya girma sosai kamar shi ɗaya da Babanshi sai ko haskena da ya yi.

Kyauta sosai Mallam ya yi mishi wanda hakan yasa ni ƙara damka mishi zuciyata dungurungum dinta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mai Daki 26Mai Daki 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×