Hira sosai muka yi da Umma ina mata korafin ba a taba kawo min su Tasi'u ba. Tayi murmushi ta ce, "To sai ki gayawa Babanku tukunna. Na ce, "To." Babana ba karamin jin dadin ganina ya yi ba.
Yayi ta murmushi ba iyaka, yana ta dan yi mun tambayoyi ina ba shi amsa tare da jaddada tambaya daya da yake yi min. Babu matsala dai ko Hauwa'u? Na ce, "A'a babu." Ya ce, "To ki yi ta hakuri kin ji, shi zaman tare hakuri ake yi."
Na ce, "To Baba." Kamar na danne abinda ke damuna. . .