Skip to content
Part 5 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Hira sosai muka yi da Umma ina mata korafin ba a taba kawo min su Tasi’u ba. Tayi murmushi ta ce, “To sai ki gayawa Babanku tukunna. Na ce, “To.” Babana ba karamin jin dadin ganina ya yi ba.

Yayi ta murmushi ba iyaka, yana ta dan yi mun tambayoyi ina ba shi amsa tare da jaddada tambaya daya da yake yi min. Babu matsala dai ko Hauwa’u? Na ce, “A’a babu.” Ya ce, “To ki yi ta hakuri kin ji, shi zaman tare hakuri ake yi.”

Na ce, “To Baba.” Kamar na danne abinda ke damuna sai dai na kasa. Na ce
“Baba sai dai maganar Makarantata ne har yanzu shiru. Nayi mishi bayanin yadda muka yi da Ishak ya dan yi shiru zuwa can ya ce, “To babban al’amari a wurin mu ai shi ne ki zauna lafiya a dakin aurenki.

Kuma ga dukkan alamu kina da kwanciyar hankali. Ita maganar karatu tana zuwa ne daga baya.

Amma tunda dama can yasan da maganar ina ganin bari ni da kaina nayi mishi tuni muji abin da zai ce.”

Tun kan Ishak yazo daukana nayi wa Babana magana akan ina bukatar su Tasi’u su zo min kwana biyu, ya ce “To.”

Ba a wani dade ba rannan kawai da rana sai ga Yaya Auwalu da su Tasi’u da dan kayansu a kullin leda. Murnata bata boyuwa, na rasa inda zan ajiye su. Nan da nan na shiga kicin na fara ajiye musu dan abinda nake dashi. Muka yi hira da Yaya Auwalu sosai daga ni kuma ya yaba da inda nake don kuwa bai taba zuwa ba shima sai yau. Ya jima sosai kafin yayi mun sallama ya tafi, ya bar mun Tasi’u da Sadisu akan za su yi mun sati guda.

Muka wuni muna harkokinmu ba kadan ba cikin raha da jin dadi. Hindu kuma tazo ta debe su ta kai wa Mominsu suka gaisaa suka dawo tare da kaninta Abubakar.

Da daddare kuwa hira muka sha ba kadan ba, nayi dariyar abubuwan da suke bani labari har na gaji. Rabon da naji dadi irin a yau har na manta. Ba su yi barci da wuri ba saboda kallon da suke yi sai wajen karfe goma na dare kafin nan kuwa ni kaina na gaji.

Nayi wanka na gyara na hau gadona na kwanta, kan ka ce meye har nayi barci abinda ya hana ni jin dawowar Ishak don kuwa ban farka daga barci ba sai da naji kiran sallar Asubahi.

Da sassafe Ishak ya fita wanda shi ne dalilin da ya sa ban tuna gaya mishi zuwaan su Tasiu ba sai bayan tafiyarshi.

A yau mna wuni muka yi muna harkokinmu. Nayi mana abinci mai dadi dafadukar taliya da taji hanta ga kuma farfesun kayan ciki, don kuwa nasan babu abinda suke so irin taliyar.
Yau ma sai da muka yi hirarmu wajen karfe goma sannan na shinfide su a dayan dakin na gyara musu komai na fito na hau gadona ina tunani a raina irin kewar da zan ji ranar da su Tasi’u za su koma gida.

Idan da da hali da na roki Umma ko Babanmu su bar mun su Tasi’u. Kwanciyar nayi da nufin na yiwa Ishak maganar idan ya amince to, tunda muna da wadatar waje. Yau ma ban san sanda ya dawo ba saboda barci mai nauyi da ya dauke ni. Can cikin barcina naji kamar ana kirana.

Na bude ido cikin sauri saboda gane ba mafarki nake yi ba. Sadisu ne. Sai dai ba ni kadai ce na tashi ba har da Ishak.

“Menene ya faru Sadisu? Ya ce, “Aunty zan yi fitsari ne.” Na mike cikin sanyin jiki saboda irin kallon da Ishak yake yi mun, na dawo dakin da suke nasa shi a bayan gida yay.

Na sake shimfide shi ina kara jaddada musu in sun ji wata bukata ba sai sun tashe ni ba su shiga bandaki kawai su yi.

Na kuma gaya musu hakan tun kafin su kwanta amma kuma sha’ani irin na yaro.
Na shigo dakin, Ishak yana zaune a kan bakin gadon nayi nufin wucewa naje na kwanta, duk kuwa da sanin da nayi na cewa ni yake jira.
Sai, dai yanayin shi da ke sani cikin faduwar gaba. “Zo nan. Abinda yace mun kenan. Na nemi wuri a kasa na zauna. Me wadannan yaran suke yi mun a gida?

Lafazin da yayi amfani da shi yasa na rasa abunda zan ce, ko kuma ta inda zan fara. Cikin daga murya ya ce, “Ba ki ji abinda na ce ba ne ko ya ya? Na ce, “Eh naji, ba ka gane su ba ne? Su Tasi’une fa da Sadisu kannena.

“Hala kin ga alamar makanta ne a tare da ni ko? Nayi maza na ce “A’a ba haka ba ne.” Idan na ce zan tsaya fadin irin tashin hankalin da na gani ranar a tare da lshak to nayi karya. Duk kuwa da irin bayanan da nayi mishi wanda ko saurarona bai yi ba.

Maganar kuwa da muka wayi gari da ita ita ce, ta bai yarda su sake kwana mishi a gida ba, maza-maza na sa a mayar da su kwana biyun da suka yi ya isa haka.

Bai ci komai ba ya fita. Bai bani kudin motar mayar da su ba, duk kuwa da yasan banida ko asi.

Nayi iyakacin kokarina wajen juriya kada ‘yan yaran nan su fahimci wani abu. Tasi’u bai fi shekara shida ba, shi kuwa Sati yafi uku amma bai cika hudu ba. Yan kannena da nake da su amma wai Ishak ba zai iya mu’amalla da su ba.
To sai da wa? Ko da yake ni din ma da ya aura ga irin yadda yake tafiyar da ni. Sanin hakan da nayi bai hana ni bakin ciki mai yawa ba. Biye mishi zan yi?

Ko kuwa dai zan nemi mafita ne? Na gama ayyukana nayi lullubi tare da rufe gidan na shiga gidan su Hindu.

Mominsu tana daki nayi sallama na shiga, na bar su Tasi’u a wajen yara suna wasa. Ban boyewa Momi komai ba.

Ta tashi ta shiga daki ta dauko kudi masu yawa ta bani ta ce “Ki koma gida ida Hindu ta dawo zan turo miki ita sai ki bata ta mayar da su gida.

Kiyi hakuri, ki kuma yiwa mijinki iyakacin biyayyar da za ki iya idan har bata sabon Ubangiji ba ce.

Kada ki să damuwa a ranki ko kuma ki ce wai za ki yi fushi da shi kin ji ko?” Na ce “Eh.”

Na dawo gida na ci gaba da kwanciya, don kuwana rasa kuzari tunani iri-iri a cikin raina.
To da Ishak ya yi mun haka a kan kannena shi nashi ‘yan uwan baya tunanin za su iya zuwa ko kuwa idan suka zo ya ya yake so ayi?

Na sake yin shiru, to a zaman da nake yi ma zan iya cewa bai taba yi mun wata magana ta game da ‘yan uwanshi ba kamar yadda ban taba ganin wani yazo ya ce shi abokin shi ne ba.

Nayi saurin mikewa na zauna ina wasu yan tunane-tunane a raina, tambayoyi iri-iri da nake bukatar na samu amsarsu…

Sallamar Abubakar kanin Hindu ne ya katse mun tunanina. Ya miko inun bakar leda ya ce “Ga shi in ji Momi. Na karba ina dubawa.

Littattafai ne na Hausa da alama ta bani ne na samu na karanta ni ba ma’abociyar karatun ba ne, amma sai naga barı na ajiye kada ta ce na gwasaleta.

Na mike don samarwa kaina abinda zan ci tunda yamma ta fara yi. Chips kawai na soya da kwai naci na sha shayi akai sannan nayi sailar Magriba.

Ina idar da saliah sai kawa naji sallamar shigowar Ishak, mamaki ne yayi matukar kama ni, zan iya cewa tunda, aka yi aurenmu ya koma aiki bai taba dawowa kafin ayi saliar isha’i ba.

Asali na ya dawo karie tara yayi sauri. Na mike ina nade dardumar sallah tare da yi mishi sannu da zuwa, bai amsa ba don dama nasan hakan ne zai biyo baya.

Saboda zai yi mun abu wanda zai sani bakin ciki amma shi ne kuma mai yin fushi idan har ba hakuri na bashi ba, kuma to ba zai taba saukowa ba.

Sai dai a wannan tunda dai nasan ban yi mishi wani laiff ba, to nima ban shirya bada hakurin ba.

Na shiga kicin cikin sauri nayi mishi abinda zai ci, fried rice da farfesun danyen kifi wanda duka aikin bai dauke ni awa guda ba.

Na kawo na ajiye mishi. Sai dai ban ganshi a falon ba. Na shiga cikin dakin kwananmu nan ma hakan. buruntun da naji a daya dakin ne yasa ni lekawa.

Gyarawa yake yi yana kakkawar da wasu abubuwa duk da dai har da ba a wani amfani da daki banabarin shi da datti.

Ine tsaye ina kallon ‘irin gyaran da yake yi na shiga daki na dauko wani zanin gadon na shimfida akan gadon na sa tsintsiya na share dakin.

Bai ce mun kala ba ya shiga asalin dakinmu ya fara kwaso kayan shi yana maida su daya dakin.

Aikin da ya dauke shi har karfe goman dare, don kuwa tsinke nashi sai da ya dauke ya kai shi daya dakin, kuma ya gyare shi tsaf ina zaune a falo ina kallonshi.

Ya shiga bandaki yayi wanka ya hada tea yasha bai ko kalli abincin da na ajiye mishi ba ya shiga sabon dakinshi ya kwanta.

Ba sai na jira an yi mun wani bayani ba nima da kaina na fahimci abinda hakan yake nufi, nima sai na shiga tsohon dakinmu ko kuma na ce na asalin na kwanta.

Al’amarin Ishak ba na karewa ba ne, kuma na lura idan na ce zan zauna ina kwana ido biyu saboda bacin ran da yake sa ni to zan wahala ba kadan ba.

Kwana da kwanaki muna cikin wannan hali ya mayar da wancani dakin na shi nima kuina ga nawa.

Tsakanina da shi gaisuwa ce ta safe ta dare kuwa bana ma sanin sanda yake dawowa. Nayi iyakacin addu’o’in da zan yi a kan hakan ban ga canji ba.

Gyaran daki nake yi lokacin da na sake cin karo da littattafan Momi. Na bude daya na fara karantawa. Wunin ranar bata kare ba sai da na gama shi tas na dauko na biyun shima haka.

Cikin kankanin lokaci sai na koma wurin Momi neman kari. Kullum da safe idan na gama aikina na gida sai na zauna nayi ta karatuna bana tashi sai sallah ko cin abinci.
Sai ya zamana na koyi abubuwa in-iri wadanda wani bai taba zaunar da ni ya koya mun ba.

Abubuwa da suka danganci zama da miji, zama da mutane, girki, kula da kai, gyaran jiki, kai abubuwa daban-daban. Idan nazo wani wajen naji takaici, wani wajen nayi dariya, wani wajen naji tausayi, wani wajen kuwa naji kamar labarina ake bayarwa da’ Ishak.

Don haka ga abinda zan yi. Damuwata tayi matukar raguwa, na kuma yi niyyar yin amfani da shawarwarin da Marubuta suke bayarwa da suka danganci zama na aure na kuma zubar da na banza.

Tsawon sati biyun da muka yi a hakaa muka yi ta da Ishak gaisuwar safe, dn uwa da daddare kan ya dawo nayi barci.

Amma na kuduri aniyar gyaran aurena don na fahimci ba haka ake auren ba. Aure yana yin nasara ne idan har akwai kyakkyawar alaka ta addini da zamantakewa a tsakanin ma’aurata, uwa uba kuma soyayya ta gaskiya da take haifar da yafiya a kowanne lokaci.

Sannan Annabi (S.A.W) ba haka yayi zama da nashi iyalin ba, don kuwa babu wani mutum da zai nunawa matarshi kwatankwacin irin soyayyar da ya nuna ga iyalinshi.

Babu kyamata, babu hantara bare tsangwama a cikin al’amarin aure. Miji da mata (ma’aurata) duka su baiwa junansu lokaci na hira, kulawa, da tausayawa wacce suke haifar da karin soyayya da fahimta a tsakani.

Na jawo akwatin kananan kayana na bude ina dubawa tare da tunanin wacce zan yi amfani da ita. Duk da ina jin kunyar yin hakan amma idan har zai kawo mun gyara ga aurena to ki meye zan yi idan ba sabon Ubangiji ba ne.

Rigar bata wuce mun iya gwiwa ba, haka nan shara-shara ce don kuwa kusan koma nawa a bayyane yake. Na gyara gashin kaina wanda na wanke shi da man wanke gashi na (Trichup)na kuma shafe shi da kayan gyara iri-iri. Duk da ba wani tsawo ne da gashin nawa ba ya yi kyau ba kadan ba. Ga jikina da yayi luwai-luwai saboda jin dadi.

Maganar gaskiya ita ce Ishak ya wadata ni da abubuwan jin dadi da suka danganci abinci da na gyara. Sai dai a yanzu na fahimci ba su ba ne masu muhimmanci wanda bai bani ba shi ne komai, wato soyayyarsa da lokacinsa.

Na kuma kuduri aniyar nema ta hanyar da ta dace.

Na dawo falo na zauna na ci gaba da yan karance-karancena, don kada barci ya dauke ni.

Yau sha daya saura kwata ya dawo. A lokaci na dawowar Ishak kuwa to ya dawo da wuri. Ya shige dakinshi ban ce mishi komai ba kamar yadda bai kalle ni ba.

Gabana sai faduwa yake yi, kodai na kyale shi ne kawai? Kai a’a, na dauki abincin da na ajiye mishi wanda ni kaina rabon da nayi girkin gidan da shi har na manta saboda ba ya ci.
Nayi sallama a daidai. kofar dakin na shiga ba tare da na jira amsawar shi ba. Wanka yake yi, don haka na zaunaa bakin gadon ina jiran shi. Ya fito yana goge kanshi da karamin tawul nayi mishi sannu na kuma gabatar mishi da abinci.

Bai ce mun komai ba sai da ya zo zai kwanta. Ya ce, “Ni fa kwanciya zan yi ko za ki je dakinki ne?” Wani abu ne ya tokare ni a wuya, na mike na dawo dakina na kwanta.

Don takaici sai kawai na fashe da kuka. Me ke faruwa ne’? Shin fita hanyar Ishak zan yi ko ya ya? Abu daya ne ya sani na ji sanyi da naje debe kwanukan abincin da na kai mishi naga ya dan ci.

<< Mai Daki 4Mai Daki 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.