Skip to content
Part 6 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Yau ma shiri sosai nayi mishi ban damu da korata da yayi ba jiya, don kuwa gyara nake so. Kuma na kuduri aniyar yi ta kowacce hanya in dai ba fin karfina abin ya yi ba.

Ganin da nayi ya dan ci abincin yasa ni yin niyyar yi mishi wani abincin da nufin neman burge shi.

Sai dai kash! Ban ma san abincin da yake so ba. To amma na cire wannan tunanin a raina kawai nayi abincina mai kyau kuma na burgewa na dan hada mishi da kunun zaki.

Yau ma irin kwalliyar jiya nayi. Ban kuma yi barci ba har ya dawo. Dakin shi na bishi yana kokarin daure igiyar rigar barcinshi na ajiye tiren da ke dauke da food flask da sauran plate da cokula na. Juya na je na dauko Jug din da na ajiye na kunun zaki na dawo.

Ina shigowa ya ce, “Ki kwashe kwanukan nan ki fita da su ba zan ci abinci a wannan daren ba.” Raina bai baci ba, na ce “To ga kunun zaki mai sanyi ne sosai.” Na kalli yanayin shi yana daga kwance hakan ne yasa na jawo kofi na tsiyaya mishi kunun na mika mishi.

Kamar dai ba zai karba ba sai ya mike ya zauna ya karba ya kara miko mun kofin na kara, mishi na tashi da niyyar fitar da kwanukan abincin da ya ce ba zai ci ba.

Har na juya ya kira ni “Zo ki zuba mun kadan.” Na ce “To.” Kadan din na zuba mishi na kara mishi kunun zakin sannan na jira ya gama na kwashe kwanukan na fitar.

Ban koma dakin ba nawa na shiga nayi kwanciyata. Da sassafe ban koma barci ba sammako nayi na yi mishi abin karyawa cikin sauri na kawo mishi.

Har ya gama shiri lokacin da na shiga. Kwalliya sosai nayi ya kalle ni ya kalli tiren kayan karyawan. Na ce “Ko za ka karya ne kafin ka fita?”

Bai musa ba zama ya yi na zuba mishi ya karya har ya mike sai ya kalle ni
“Unguwa za ki je? Na ce, “A’a.” Ya ce, “Au to na dauka ko kin fara fita ne ba ki tambaye ni ba.”
Na ce, “A’a ba za a yi hakan ba.” Yau wuni nayi cikin jin dadi a raina. Wajen karfe uku da rabi yaron da ya saba aikowa da cefane yayi sallama.

Na zauna ina duba cefanen yadda ya saba kawowa ne bambanci kawai shi ne kafar Saniyan da na gani a ciki. Na dauko wayata duk da ban taba yin hakan ba, ban kuma san ya ya zai dauki hakan ba.

Tana yin kara ya dauka, “Lafiya? Tambayar tayi mun wani iri, amma sai na daure na ce “Dama zan tambaye ka ne, kafar Saniyar da na gani za ka ci abincin dare a gida ne?”

“Da can sauran cefanen da ake kawowa tambaya ki ke yi?” Na ce, “Aa.” Ban saurari jin karashen maganar ba na kashe wayar saboda abinda naji a cikin zuciyata na tamkar ina kokarin cusa kaina da yawa a wajen Ishak.
Na hada kayan kawai na sanya kowanne a mazauninshi na kuma wanke kafar da niyyar yin miyar ganda da ita.

Sai da na hada komai sannan na dora tuwon shinkafa. Na gyara kicin din na kammala komai a mazauninshi. Na dawo daki nan ma na kara kikkintsa abubuwan da suke bukatar kintsi.

Sai da na gama ayyukan abinci sannan na shiryawa Ishak nashi abincin a inda na saba, tare da sauran kunun zakin jiya wanda ya kara jika.

Yayi dadi ba kadan ba. Na shiga wanka na hado da alwala nayi sallar Magriba sannan na zauna domin nayi shafa.

Yau ana idar da sallar Isha’i kawai sai ga Ishak shi kanshi ya gane nayi mamakin hakan, sai da ya gama shirinshi kafin ya fito ya zauna a falon.

“Kawo mun abincin nan wurin”. Na shiga dakinshi inda na ajiye abincin nashi na fito dashi na zuba. Ba karamin abinci yaci ba, don kuwa miyar tayi dadi ba kadan ba.

Na gama kwashe kwanukan sannan na dawo ina kallon tashar da ya kamo ta Aljazeera yana sauraron labarai.

Sai wajen karfe goma sannan na mikKe
don kwanciya. A raina nasan idan na ce zan jira Ishak ban san lokacin da zai kwanta ba.
Haka nan kwanakin da nayi ina zaman jiran dawowarshi sun sa barci ya kama ni da yawa. Na gama shirina na zauna a bakin gado ina addu’o’ina da na saba yi na kullum kafin kwanciya, sai ya shigo.

“Zo mana.” Na mike na bishi ba zai yiwu na ce Ishak yana neman mata ba don kuwa ban gani da ido ba bani kuma da wanda zai fada mun.
Amma idan abin shi ya motsa mishi na fushi ko halin da ya saba yana jimawa ba tare da ya neme ni ba sat da tun da na samu na fara shawo kanshi ta wannan hanyar al’amuran gidana sun dan fara yi mun sauki.

Na farko dai ya daina zaman karfe sha daya ko sha biyu a waje, idan yayi dare to
karfe goma, duk kokarin da nayi kuma na ganin na gane ko na fahimci abin da yake yi a wajen na gagara.

Tun da na lura da shi na gane ina janye hankalinshi da irin shigar da nake yi mishi, kullum da irin wacce nake canzawa. Ko da ba ya cewa komai kuma ina gani a aikace.

Sai dai abubuwa kullum da irin wacce take zuwa. Shirin da nayi musamman don naje gida yau amma sam Ishak ya ki yarda, duk kuwa da na gaya mishi cewa Umma zanje gayarwa saboda rashin lafiyar da take yi.

Har Hindu da Móminta sun je sun dubota amma sam shiya ki barina ya kuma ki żuwa shi ya dubota.

Kullum sai dai na kirata a waya. Na záuna na buga tagumi duk wani abu da nake Rokarin ya rage mun Bacin rai ya ki.

Da ya dawo kuwa ban fasa yi mishi abinda na saba ba. Amma gari na wayewa da na kara rokonshi ya ki, ban ce mishi komai ba.

Yana fita sai na shirya na dauki gyalena burina bai wuce naga halin da Umma take ciki ba, tunda ni dai zamana da ita ban taba jin tayi wata rashin lafiya ba.

Don haka hankalina a tashe yake ba kadan ba. Jikin nata babu dadi sosai, amma duk da haka ban zauna ba don kuwa kwata kwata ban fi awa daya ba na dawo.

Na dawo duk da dai ban ji dadin ganin da na yi wa Umma ba, na samu saukin damuwar rashin Zuwa dubata da.ban yi ba kwana da kwanaki.

Ban dade da shigowa ba sai ga Ishak ya shigo ina yi mishi sannu bai tsaya amsawa ba sannan yanayinshi gaba daya ya canza.
Ina ki ka je? Shi ne tambayar da ya fara yi mun. Nan da nan na kama inda-inda kan in san abinda zan ce tuni ya dauke ni da mari kauu!

Duka Ishak ya yi mun mai shiga jiki, sannan yayi ficewarshi ya komawurin aiki.

Tun daga lokacin wani irin zazzabi yaa rufe ni wanda yafi kama da na bacin rai da bakin ciki.
Bai dawo ba sai can cikin dare. Ina zaune a tsakiyar gadona har a lokacin kukana bai kare ba.

Washegari, kuwa ga zazzabi, ga karin tsamin jiki, Don haka ko, tashi nayi abin karyawa ban yi ba. Sai da naji yunwa tana neman nakasa ni ne na tashi na lallaba na hada tea na sha.
Har dare yau ma ban samu nayi abinci ba, don kuwa ko sallah da kyar nake iya mikewa nayi.
Haka nan yau ma da ya dawo sha dayan dare bai leko ni ba, dakinshi ya shige da gari ya waye ya yi sammako kamar dai dabi’arshi ta da.

Nayi kukan takaici har na gaji nayi shiru, Ishak wane irin mutum ne wanda ko kadan bai san hakkin zaman aure ba?

Amma kuma shi yana so ya sanyawa mutum dokar rashin adalci kuma yabi.

Lallabawa nayi na shiga gidan su Hindu duk da sanin da nayi me hakan yake nufi idan har ya gane.

Momi tana ganina ta fara salati. “Ba ki da lafiya ne Hauwa’u? Na ce, “Eh Momi.
Hindu nake nema.” Ta ce, “To je ki gida gata nan.” Hindu ce ta gyara mun gida ko ina, sannan na sa ta tayi mun faten tsaki don abinda zan iya ci kenan.

Na kuma yi matukar sa’a na samu na sha sosai nayi wanka na dan samu karfi a jikina.
Ita ce kuma ta taya ni nayi girki sosai, tuwon semovita miyar kubewa danya da taji tantakwashi da naman rago na’ hada komai na ajiye wa Ishak a wurin cin abincinshi na shige daki na kwanta.

Duk da dan (Paracetamol) din da na samu na sha jikina bai yi sauki ba, sai dada tsananta yake yi.

Da sassafe na lallabo na shiga dakin Ishak yana zaune yana duba wasu takardu rabon da na saka shi a idona kwana hudu kenan yau.
Yanayin da ya ganni a ciki bai hana shi yamutsa fuska ba. Wane irin abu ne haka ke wai wacce irin yarinya ce? Kin ga yadda ki ka yi wujiga-wujiga kuwa?

Don Allah can wuce ki gyara jikinki kafin ki zo mun nan muryata tana rawa ta
ce, “Ba ni da lafiya ne.” “To idan ba ki da lafiya sai ki zo mun haka? Mits! Fita don Allah kije kiyi wanka wawiyar yarinya kawai.”

Dawowa daki nayi na zauna sai da na sha kukana ya ishe ni sannan na mike na lallaba nayi wanka na saka doguwar riga mai gyale na zauna na hada tea din da zan sha.

Ruwan lipton ko birebi ban iya ci ba, na koma na sake kwanciya don ko Paracetamol din da zan sha ba ni da shi ya kare.

Ishak bai fito ba sai wajen sha daya kasancewarta Asabar. Sanye yake da Jeans blue a shirt long sleeve wuce muje.


Hijabi na dauko muka fita zuwa asibiti. Muna zaune a gaban Likita bayan ya tabbatar mana ciki ne da ni karami, ya kuma rubuta mana prescription na magunguna wadanda muka karba a chemist din asibiti muka kamo hanyar komawa gida.
Tsananin zazzabin da ke damuna vasa ban ma lura na gane hanyar da Ishak yabi ba sai da ya ce mun fita ki shiga ina jiranki.
Na duba naga a kofar gidanmu muke, cikin sauri na bude kofar motar na shiga.
A kicin na samu Umma taji sauki sosai, na durkusa a gefen kicin din tana kallona.
“Hala kema ba ki da lafiyar ne ko naga kin zama haka?” ban bata amsa ba sai kuka da na fara yi mata.
“To menene kuma na kuka ai hakuri za ki yi ba a yiwa ciwo kuka Hauwa’u, ki zama jaruma. Ban daina kukan da nake yi ba har ta gaji ta ce “Ko dai kina da wata matsala ne?”

Ban san me zan cewa Umma ba, ta gaji da tambayata ta ce “Uhm, hakuri fa ake yi da komai ma da ki ka gani na duniyar nan, ballantana zaman aure. Kada ki sa wa kanki wata damuwa game da lamarin mijinki tunda dai bai gaza miki da komai ba. Bai zama lallai sai ka samu yadda ka ke so a kowanne lokaci ba, kin gane?”

Na tashi na yi wa Umma sallama na fito muka dawo gida da Ishak. Wanda tsawon watanni goma sha daya da nayi da shi a matsayin matarshi ta aure bai sa shi ya yi tunani rana daya yaje ya gaisa da iyayena da suka ba shi aurena ba. Har kuma da rashin lafiyar da Ummana tayi.

Ciwo sosai nayi na wajen wata kusan guda ina kwance ko aikin gida bana iyawa, sai Hindu ta shigo tayi mun.

Ban samu saukin laulayin da naketyi ba sai ana gab da sallah, ba ta fi sati biyu ba.
A cikin akwatina na dauki atamfa daya da shadda mai laushi na bayar aka kaiwa
Umma don ta dinka atamfar ta bayar da dhaddar don a dinka wa su Tasi’u, tunda bani da kudin da zan saya musu. Ni kam Ishak yayi mun har kala biyu masu kyau sosai, ban ma san da su ba sai da ya karbo su daga wurin Tela.

Daga ni har shi din shirin sallar muke yi ba kadan ba. Ta bangare na dai wannan ita ce sallar da zan yi ta farko a dakin aurena.
Shi kuma yayi sayayya na abinci ba kadan ba. Nayi cincin, cake, sannan nayi
miya mai dadin gaske da taji naman saniya. Sannan na soya naman kajina gaba daya. Ga kunun zakin da nayi wanda ya ji kayan yaji sosai da busasshen dankali.

Hindu ce ta shigo da sassafe tun kafin a tafi sallar Idi ta rinka mika mun abincin gidajen makwabta saboda sammakon da nayi na gamawa.

Tayi sallama a bakin kofä saboda sahin da tayi Ishak na nan, na amsa mata na fito ina tambayarta akwai,sauran gidan da ba a baiwa ba ne?

Ta ce, “A’a.” Na ce, “To don Allah idan kin yi wanka sai ki kai mun na gidanmu ta ce, “To.”
Na shiga daki da shiri na shiga wanka. Ke zo nan. Ishak ne ya kira ni. Kwanakin baya ba na hana yarinyar nan shigowa gidan nan ba? Ba na ce bana so ba? Gidannan wai shin ba gidana ba ne?

Idan na ce bana son abu menene dalilin da yasa ba za a bari ba, ki kiyaye ni fa! Me take zuwa ku ke yi? Gulma ko ba ki munanan shawarwari da koya miki dabi’un banza? To ya ishe ni haka.”

Karo na farko da al’amarin Ishak ya gundure ni na zuba mishi ido ina kallonshi.
Yana dandanna wasu lambobi ne a waya, alamar zai yi kira. Kamar na ba shi amsar maganganunshi sai naga ba zan iya ba.
Yayi mun kwarjini da yawa sai kai na wuce shi na shiga bandaki nayi wankana ns fito. Lokacin nan kuwahar ya gama shirinshi. Jamfa ce a jikinshi dogųwa ta yadin shadda geitzner ja. Tayi mishi wani irin kyau.
Ban taba ganin ya saka babbar riga ga wata kila don baya ra’ayinta. Yana rike da
hularshi yana kokarin karyata haka kawai na ga kalanta bai yi mun ba.

Na mika hannu na dauko watamai ruwa ja da brown da wani ratsin nace ko za ka ajiye wannan ne ka saka wannan zuba mun ido ya yi yana kallona. A hankali na ce mishi na gane kamar tafi shiga da kayan. Ya mika hannu ya
karba bayan ya ajiye ta hannun nashi. Ya karyata ya saka a kannan shi sannan ya feshe jikinshi da turare. Yayi mun kyau a idona. Ina matukar son yin mu’amalla mai kyau da Ishak irin wacce nake ji ana bada labari,
Don na san rayuwa ce da take faruwa a zahiri. Ya juyo da kallonshi gare ni, nima shi nake kallo.

“Zan tafi hawan Idi, ana saukowa zan dawo, don zan yi baki daga office dinmu.

Ayi mun shiri na abubuwan ci sosai don suna da yawa.” Na ce,To Allah ya bada sa’a.” Ya kuma amsa mana lbadunmu. ” Ya ce,
“Amin.Ya fita.

Zama nayi na yi kwalliya ta burgewa ba kadan ba, na dauko yadin material wanda Ishak ya karbo mun daga gun Tela na saka ya kuma karbi jikina ba kadan ba.

Gashi kuma na fara yin kibar ciki ga fatata da ta yi haske tayi laushi zan iya cewa ban taba yin kyau irin hakan ba.

Hindu ta shigo ita ma tayi kwaliya sosai ta shadda da ta sha ado. Ta ce, “Kai Aunty Hauwa, kin gan ki kuwa? Kin ga irin kyan da ki ka yi?
Nayi murmushi na ce, Haba Hindu, har na kai ki? Ta ce, “Haba wane ni, keta dubi kalari kin san yadda ado yake yi wa farin mutum kyau kuwa?”

Na ce,”Ke kuma ga ki doguwa kin san kyau yana ga dogon mutum.” Gaba daya muka yi dariya. Na ce mata to barka da sallah, Allah ya maimaita mana.”

Ta ce,”Amin.” Ta kwashe manyan food flask guda biyu da na cika da abincin gidanmu, daya dai miya ce da taji nama don kuwa raba miyar nayi biyu na juye rabi.

Dayan food flask din kuwa soyayyen naman kaji ne da cincin da kek. Na saka mata a nan ne don kaninta ne zai rike gudun bari.
Ban zuba shinkafa ba don nasan Umma zata dafa. Na shiga shiryawa Ishak abincin bakinshi komai na tanadan mishi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mai Daki 5Mai Daki 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×