Yau ma shiri sosai nayi mishi ban damu da korata da yayi ba jiya, don kuwa gyara nake so. Kuma na kuduri aniyar yi ta kowacce hanya in dai ba fin karfina abin ya yi ba.
Ganin da nayi ya dan ci abincin yasa ni yin niyyar yi mishi wani abincin da nufin neman burge shi.
Sai dai kash! Ban ma san abincin da yake so ba. To amma na cire wannan tunanin a raina kawai nayi abincina mai kyau kuma na burgewa na dan hada mishi da kunun zaki.
Yau ma irin kwalliyar jiya nayi. Ban kuma yi barci. . .