Skip to content
Part 8 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

“Na dauka kina da tarbiyya hakan ne yasa ban taba yin zaton za ki yi abin da ki ke yi a yau ba. Sake gaya mun abubuwan da ki ka ce ba kya so wadanda nake yi miki sai na kula nan gaba na daina.

Amma abinda ba zan lamunta ba shi ne, ki kara zuwa mun cikin fusata irin na yau ki ce za ki gaggaya mun bakaken maganganu kin gane ko? Ba ke ce za ki koya mun yadda zan rinka mu’amallata da wasu ba.

Ina so ki san ke din ba za ki taba zama mai sa ni ko mai hana ni ba, koyi samuna cikin nutsuwa kina yi mun magana ta yadda zan gane har kullum cewa ni ne mijinki ba ke ce mijina ba kin gane ko?

Dokata ba za ta sauka ba na cewar ban son shigowar waccan yarinyar cikin gidana ba don a zahiri ga abinda ki ka yi mun a yau wanda a da ba ki taba yi mun ba, gabanin fara mu’amallarki da ita. Na dago ido ina kallonshi “Zan kuma dauki mataki da kaina ba sai kin shiga matsala tunanin fuskantarta ba. Ba zan lamunci masu son shiga lamarin aurena ba.

Na kuma yafe miki fita da ki ka yi ki ka je gida a yau ba tare da kin nemi izinina ba sai dai ina so ki san kin fitan ne a madadin wunin da za.ki je na gaisuwar sallah.”

Na mike da nufin fita a dakin. Ya ce “Dawo ki zauna. Na dawo na hau gadon na kwanta sai dai kuka na kama yi saboda tukukin da zuciyata take yi mun.

Washegari da safe kamnar ba zan yi kwalliyar ba, sai kuma naga kaina kawai nake yi wa, don haka sai na yi kwalliyata na sanya atamfa super exclusive holland wacce ya yi mun a sallar.

Kadan ya rage na ce tafi yi min kyau a jikina a kan material din da na saka jiya, ita ma kalarta mai kyau ne kwarai, ruwan kwai da jajja da kore kadan.

Adon atamfa tana matukar sanya mutum kwarjini ba kadan ba. Na kammala shirina na fita kicin ko bi ta kan Ishak ban yi ba.

Sai da na gama ayyukana na kicin sannan na shiga dakinshi don na kwaso abubuwan da ya yi amfanida su da kuma gyaran bandakin shi.
ldon shi biyu na same shi, sabanin dazu da yake barci. Na shiga bayan gidan na gama gyarawa sannan na zo don komawa duba girkina.

“Zo mana.” Na juyo na ce “Ga ni. ” Magana yake son yi sai dai ya rasa ta inda zai yi ta, abinda na fahimta kenan.

Ya dai zuba mun ido sai da na gaji na ce “Ka kira ni. Ya ce, “Eh na gane baki nuna mun kwalliyar taki ba ballantana na ce tayi kyau, ko ba haka ki ka ce na ringa yi miki ba?”

Na juya nayi tafiyata ba tare da na ce komai ba, ina gab da gama abinci ne naji ana ta6a kofa. Na leka ta wurin da ake
ganin mutum.

Gabana ne yayi mummunan faduwa a madadin farin ciki, Sadiya Tanimu ce. Na dawo kamar na kyaleta ta gaji ta tafi, sai kuma naga bai dace ba.

Dakin Ishak na shiga har yanzu yana kwance na rasa yadda zan yi nayi mishi bayanin don nasan yadda yake daukan
baki.

Sai shi ne ya yi mun tambayar tashi ta fama Ya ya dai?” Na ce, Nayi bakuwa ne kawata ta Makaranta ce tazo.”

Bai sake kallona ba ya ce, “To menene ki bude mata mana.” Na juya na koma muka rungume juna cikin tsananin farin ciki.

Ta rike baki daidai ta shigo falo ta ce
“Kai Hauwa’u, kin gan ki kuwa? Kin yi wani irin kyau abin ma ba a ko magana.”

Na dan yi murmushi na ce “Sadiya kenan. Ta ce, “Uhm, Allah dai ya samu a danshinku. Na ce, To Amin. Kin san kuwa ban taba tunanin zuwanki ba.

Ta ce, Yaushe kuwa za ki yi tunanin zuwana? Ai ke kam Hauwa’u ba ki da kirki, daga kin yi aure sai ki ki mutane?

Na ce, Ayya, ba na samun fita ne. Ta ce, Eh ai ban ga laifinki ba ko kadan ko ni nayi aure na samu wadata haka ina za ni?

Ai sai kawai nayi zamana na yi ta shan gara. Na mike don kawowa Sadiya abinci da kayan shaye-shaye da ciye-ciye saboda hirar tata ba wani dadi take yi mun ba.

Don nasan Ishak yana jinta. Tana nufin kenan don ka samu gidan miji mai wadata shi kenan babu ruwanka da sauran mutane? Yan uwanka, iyayenka da abokan arziki. Idan kuma ya zamana shi ba shi da lokacinka kamar Ishak fa? Sai ka yi ta rayuwa kai kadai takamar ya wadataka. Lalura kuma idan ta same ka fa? Na debo abinda zan kawo mata na ajiye a gabanta tana tambayana maigidan yana nan ne?

Na ce, Eh yana barci. Na mike na shiga
dakin Ishak na zauna kusa da inda ya ajiye kanshi don nayi maganar da zan yi a hankali.
Na ce, Za kủ gaisa ne? bai ce mun komai ba har na gaji da zamana na fito na dawo falo muka ci gaba da hirar mu.

Na ce, Sadiya ya Makaranta? Ta ce, Ga mu nan mun usa gamawa muna ta shirin zana jarrabawa, Malam Ali kuwa kullum sai ya tambaye ki.

Na ce, To da yake tambayata ai sai ki ce mishi iyayena sun dauki shawarar da kullum yake ba su sun kuma aurar da ni.

Tayi dariya, Ke Malam Ali fa shakiyanci kawai yake yi miki. Amma ke kin zauna kenan ba za ki koma Makaranta
ba?

Ke kina ganin hakan ya yi miki daidai? Yanzu fa watan gobe ne za mu rubuta jarrabawa kowa kuma sai ya kama gabanshi a yi ta tafiya babu ke.

Karatu ai shi ne adon mace a duk lokacin kuma da ta rasa shi to tayi babbar asara, don kuwa ko aure ki ke yi ai ba kin rinka zama ke kadai ba kenan wata rana za a yi miki kishiya ki ka san wacce za a auro miki?

Na yi nufin katse Sadiya na ce, Ke Sadiya bar wannan maganar haka muyi wata kuma. Na dauko wata hirar ina
tambayarta, Ni kuwa ina Zubaida? Ta tabe baki ta ce, Uhum, tayi aure ita ma har ma ta haihu ai tsiranku babu yawa. Kema dai da alama cikin ne da ke tunda gashi nan har ya fito.

Aini kam yanzu idan nayi aure family planning zan yi kafin na gama karatuna sannan na fara haihuwa. Na ce To idan mijin naki bai yarda da hakan ba fa?

Ta ce, To yaushe dama zan sanar da shi, ai tuni zan je nayi abina bai ma san lokacin ba.

Ke! Cikin saurina waiwaya Ishak ne a tsaye cikin wani irin bacin rai. “Tashi ki fita a gidan nan.” Sadiya ta fara kokarin gaishe shi,
“Common get out, idiot! ‘yan banzan yara kawai marasa kunya.”

Sadiya ta mike sum-sum-sum ta fita, ni kuwa jikina sai bari yake yi ga kunya ga takaici, “Ke kuma.” Yana nuna ni da dan yatsarshi “Ki kiyaye ni na gaya miki.

Ki san irin mutanen da za ki rinka kawo mun gidana. Wanene Malam Ali?” Cikin
kuka na fara kokarin yi mishi bayani. “Shut up dalla kiyi mun bayani. Na ce,
Malamin mune na Makaranta. “Menene gaminki da shi da take yi miki maganar shi, iye?”

Taratsatsin bala’in da na gani a wajen Ishak ranar ba kadan ba ne. Na lallaba na hau gadona na kwanta, don kuwa na ga da irin wadannan abubuwan. Har hutunshi na sallah ya kare ya koma bai yarda ya kai ni gida ba, wai a madadin zuwan da nayi babu izininshi.
Yanzu kuwa kullum idan zai fita a gida kullewa yake yi, ya yi tafiyarshi da nayi mishi magana akan illar yin haka sai ya ce,
Idan ina da matsala nayi mishi waya ba zai ji kiwuiyar zuwa ba, na ce To.
Don haka yanzu ni kadai ce nake wuni a cikin gidan ko dan littattafan da nake samu na daina.

A yanzu da nake cikin watanni na takwas cikina ya bayyana sosai, kowa. yana gani nima kuma ina matukar jin shi a jikina, don kuwa abubuwa suna dan yi mun wahala, kuma ba ni da mataimaki.

Shi kanshi Ishak ya lura da hakan, amma ba zai iya hakura da halinshi ba. Tashin da muka yi yau ba mai dadi ba ne a wurina, don kuwa jikina yayi nauyi ba kadan ba, da kyar nake motsawa.

Ishak da kanshi ya ce muje asibiti. Muna zaune gaban likita ya ce, Yaron a karkace yake sakamakon da scanning dina ya bayar kenan.

Don haka za a yi kokarin gyara mishi
kwanciya, don haka Ishak yaje gidanmu ya sanar da Ummana, sannan ya dawo.

Ina zaune a bakin gadon dakin da aka bani shi kuma yana zaune a kan kujera, yanzu ya ya ki ke ganin zamu yi kenan tunda dole naje wurin aiki, kina ganin ba ki da wata matsala a kan hakan?

Na ce, Eh Umma zata zo ai. Ya ce, To tunda haka ne bari na jira zuwanta kada a bar ki ke kadai.”

Sai washegari da safe ne aka yi mun
gyaran tare da kyakkyawan kashedin kada na rinka aiki komai kankantarshi. Kwana daya na kara a ka sallamo ni na dawo gida.

Da safe Ishak ne ya tashi ya hada mana abin karyawa, ya share dakin gaba daya ya shirya cikin sauri ya fita.

Na sha shayina na koma na kwanta, wajen karfe daya sai ga dan aiken da ya saba aikowa ya kawo mun abinci. Na bude, take a way ne na abinci mai kyan gaske.”

Shinkafa fried rice da sálad da kuma
kwatan kaza. Da yamma kirana ya yi yana tambayata abinda zai taho mun da shi, na ce ni a koshe nake zan sha tea.

Duk da hakan bai fasa kawo mun wani irin gashi ba na bankararren kifi da aka gasa da lemon tsami yayi mun dadi ba kadan ba.

Don haka na ci sosai. A daren yayi “yan aikace-aikacen da zai yi bai kwanta ba sai wajen karfe goma da rabi saboda wankin da yayi na under wcars din shi.

Sanin halayyar Ishak yasa nake ta jin shakkun yi mishi magana akan shawarar da nayi aina, sai dai duk da hakan ban fasa ba.

Ina kwance a gefehshi na ce, Ko zan yi wa Umha magand ne ta samo mana wacce zamu rinka. żarňa tare runda ka ga ni ko wannan aikin ma da ka ke yi ba kai ne ya kamáta kayi ba.

Ya ce, Kin ji nayi miki wani korafi a kan hakan? Na ce, To naji ba ka yi ba amma idan nazo haihuwa fa?

Ya ce, Sai ki bari idan haihuwar tazo kiyi magana, ba zan tsaya na yi ta jayayya dashi ba don haka naja bakina nayi shiru.

llai ko ba a fi sati guda ba bayannan sa na tashi da wani irin ciwon mara ma musaltuwa, nayi ta wani irin murkususu ni kadai a daki, don kuwa Ishak baya nan bai dawo daga wurin aiki ba…

To bari mu jira dawowar Ishak din muma, sai in ce mu hadu a littafi na biyu.

Ta ku Haj. Hafsat C. Sodangi

<< Mai Daki 7Mai Daki 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.