Matashiya
A wata duniyar can ta daban, akwai ƙasashe, mutane, dabbobi, addinai, al’adu da sauran abubuwa masu kama da irin namu, kuma suna da zubi da tsari irin namu. Ko da yake al’amuran da ke faruwa a cikin wannan duniyar sun yi kamanceceniya da irin namu, wasu abubuwan sun sha banban da namu. Akwai labarai masu tarin yawa da suka faru a cikin wannan duniya masu tarin abubuwan al’ajabi da ban mamaki, wataƙila ma mai karatu ya yi tunanin a cikin tashi duniyar suke faruwa saboda irin kamanceceniyar al’amuran da ke tsakani, amma a zahiri al’amuran na faruwa ne a wata duniya can ta daban. Kuma a cikin wannan duniyar ce muka kawo muku labarin Haidar na birnin Sahara, yanzu kuma za mu koma wani ɓangare daban domin kawo muku wani sabon labarin. Mai karatu, shigo cikin wannan duniya mai kama da tamu ka sha labari.
*****
Shimfiɗa
A wani gari wai shi Taiki, an yi wani mutum mai suna Malam Jatau. Malam Jatau wani mutumin ƙauye ne baduniyi, amma wani lokacin in ya yi wata shiriritar ko ƙaramin yaro ba shi yin irinta. Duk da wannan, wani lokaci kuma in ya yi wata ta’asar sai ka rantse bai taɓa ko jin sunan Allah ba, amma duk da hakanan in yai wani abu wani lokaci ka rantse shehun malami ne. Abun dai kamar wanda aljanu suka shafa. Yana da mata uku, Delu, Ta Mai-gari da Abu. Matan nan nasa basu jituwa da juna, daga sun farka daga bacci har zuwa lokacin kwanciya cikin rigima da juna suke. Kullum tun daga safiya har dare cikin masifa da faɗa da juna suke. Wani lokaci shi kanshi mai gidan basu ragar mishi. Ita Delu wadda ita ce uwargida yaranta biyar da shi duka maza, ita kuma Ta Mai-gari bata samu haihuwa da shi ba tukun. Abu kuwa, shekarar su huɗu kenan da yin aure amma har ta zuba mishi yara uku, mata biyu namiji ɗaya ga kuma na huɗu nan a ciki haihuwa ko yau ko gobe.
Kashi Na Farko
Fitowa ta 1.
(Yara huɗu na wasan langa a ƙofar gidan Malam Jatau, ana iya jin muryoyinsu daga cikin gida)
Fitowa ta 2.
(A gidan malam Jatau, yamma ce sakaliya. Delu na girki akan murhu sabo da yau ranar girkin ta ne. Sai ta fara waƙar Barmani Coge.)
Delu: Kai ku kama sana’a mata, ai duk wacce bata sana’a aura ce…!
(Ta ci gaba da waƙar ta)
Fitowa ta 3.
(Malam Jatau ya dawo daga kasuwa, hannunsa riƙe da baƙar leda, gashi nan a ƙofar gida, yara za su bar wasa su zo su gaishe shi.)
Yara: Sannu da zuwa, barka da dawowa Baba.
Malam Jatau: Unguwayya, hoi! Lato kai ne ka yi cima haka? Ji cikinka kamar tulun mayya. Hm! Nan gaba riƙon ka ai sai sarki ya sa hannu. Kai Ɗantakarda!
Ɗantakarda: (Ya ƙaraso ya duƙa ƙasa gaban Malam Jatau.) Na’am Baba.
Malam Jatau: Cikin yayyenka waye ke gida?
Ɗantakarda: Babu wanda ya dawo cikinsu Baba; duk suna gona tukun basu dawo ba.
Malam Jatau: To kai zo, yi maza ka kai ma gyatumarka wannan ka ce ta aje min ina shigowa, bari in kwanto jakin can tun kafin dare ya yi.
(Ya miƙa masa baƙar ledar da ya zo da ita.)
Ɗantakarda: To Baba. (Ya karɓa ya shiga gida. Ga shi nan ya zo gaban Delu ya duƙa har ƙasa ya miƙa mata)
Ɗantakarda: Inna ga shi in ji Baba wai ki aje mai za ya kwanto jakinsa yana shigowa yanzu.
Delu: To ɗan nan me muka samu kuma yau? Buɗe mu gani.
Ɗantakarda: A’a bani iya buɗewa, saboda Baba cewa ya yi in baki ki aje mai ha ya dawo, bai ce in buɗe ba.
Delu: A’aha! Yau ga yaron banza! Ni za ka yi wa wa’azi? In duƙa in haifi ɗa ya ce zai min wa’azi? Duniya ina za ki da mu ne? To ni miƙo min in duba, ja’iri!
(Ya miƙa mata ya fita wajen yara su ka ci gaba da wasa. Ita kuma ta karɓi ledar ta fara dubawa.)
Delu: Ah lallai yau abin da gama, mai gida har da su gwaiba da lemo muka samu, ayyuririri!!!
(Abu mai tsohon ciki ta fito daga ɗaki ta zauna bisa wundi ta ciro fatala tana fifita da shi.)
Malam Jatau: (Ya shigo gida yana biye da jaki a baya, sai ya hango Abu a zaune, dama ɗakinta ne a farko.) Salamu Alekum. Gafaran ku dai masu gida.
Abu: Alaikassalamu, Maigida sannu da isowa, (ta kashe murya) yi haƙuri kasan jikina yayi nauyi bani iya tashi balle na tarboka.
Malam Jatau: (Yana washe baki.) Zainabu Abu kenan me tagwayen suna. Amarya ba kya laifi ko kin kashe ɗan masu gida!
Abu: (cikin alamun kunya da kissa) Kai Maigida baka rabo da zolaya, kada dai ka bari uwargida ta ji, ka santa da masifa fa.
Malam Jatau: (cikin raɗa) Ai gaskiya ne, bata ma ji ba ai . Kin ga na kawo miki gwaibar da kika tambaye ni jiya kuwa. Bari in karɓo miki.
Delu: (cikin fushi da ɗaga murya) Ɗan wa za a kashe? Ai wallahi sai dai ɗan wata na dai nawa ba. Ina jinka kai kuma baƙin munafuki! Wato a ranar girkin nawa ma ba za a kula ni ba amma an iya kula wannan tsohuwar makirar ko. (sai ta fashe da kuka) Wayyo ni Delu ina zan sa kaina!
Malam Jatau: Subahana, yanzu Delu ni kike kallo kike kira na da munafuki? Yanzu ashe don na kula da ita bisa juna biyun da take ɗauke da shi shikenan kuma ya zama abin munafunci? Haba mana Delu na, dama kin huce bisa ga wannan kin dawo siffar ki ta gaske, don na san bai wuce kishi ne ka damun ki ko? Haba mana Delulun Jatau! ni da ke fa mutu ka raba takalmin kaza!
Delu: (Tana sheshshekan kuka) Ba wani nan, ai kullum haka kake mini romon baka kana zalunta ta. Yanzu ‘yan kayan marmarin nan da ka kawo ba don na buɗe ledar na gani ba da shikenan ayi banda ni. Kuma duk da haka ma ai na ji kana cewa wai na wancan makirar ce mai ƙaton kai, kuma har raina ya biya wallahi.
Abu: Ke ce dai makira algunguma mai ƙashin tsiya wadda bata son ci gaban kowa sai kanta. A haka za a ƙare kutiri kamar muciya.
Malam Jatau: Kun ga ya isa haka nan, menene na wani cece-kuce sai ka ce wasu kaji, ba dai kayan marmari ba ne? Ai sai a raba kowa ya samu ko? Su kenan kuɗin jikina na siyo su dama saboda mai juna biyun nan ta nuna tana so tun shekaranjiya.
Delu: Maigida kana jin irin zagin da take min amma ko ka tsawatar mata ko? Ni dama na sani duk wani raini da wulaƙanci da nake fuskanta a gidan nan kai ke jawo min shi tunda baka shigar min in ana yi min wani abu. Yanzu gidan nan babu sauran mai ganina da mutunci sai ‘ya’yana. Su ma na lura sun ɗan fara canza min, Allah ya sa dai ba wani mugun abun aka yo mana ba.
Malam Jatau: Kayyasa! Ni kam ki yi shiru mana Delu.
Abu: Ai Maigida ka barta ta ci gaba da zubar da mutuncin nata ko ma samu abin tattakawa. (Ta dafe ƙugu tana nishi) wai Allah na, cikin nan dai da alama ‘yan biyu ne. Maigida miƙo min gwaibar nan don Allah, zuciyata tashi take.
Malam Jatau: (a rikice) Zainabu! Zainabu! Subahanallahi! Sannu sannu to bari in kawo miki.
(Yai maza ya nufi inda ledar take da nufin ya ɗauka)
Delu: (tai maza ta wafce ledar) Billahillazi bata isa ba, jar uba! Ranar girkin nawa? Taɓɗijam! Wallahi babu wanda ya isa yai min wannan cin kashin a cikin gidan nan.
Malam Jatau: Haba mana Delu, baki ganin halin da take ciki ne ke kam?
(Suna cikin haka za su fara jiyo kuka daga ɗakin Ta Mai-gari. Duk za su yi shiru suna saurare)
Malam Jatau: A’aha, kamar kuka nake ji a ɗakin Ta Mai-gari, ita kuma ko lafiya take kuka?
Delu: (Ta yi tsaki) wa ya sani mata, jikanyar ɓaure abu ba abu ba sai su fashe da kuka.
Abu: Maigida ni dai miƙo min ko ɗan lemon ne in samu in sha, haraswa nake jin yi wallahi.
Malam Jatau: (Ya yunƙura kenan zai karɓe ledar daga hannun Delu sai ya ji Ta Mai-gari ta sake fashewa da kuka daga cikin ɗakinta.) Kai wannan kuka na lafiya ne kuwa? Bari dai in duba. (ya nufi ƙofar ɗakin ya fara magana) Ta Mai-gari, Ta Mai-gari lafiya dai ko? Ko rasuwa aka yi ne?
Ta Mai-gari: (ta fito tana share hawaye) ba rasuwa aka yi ba Maigida ina yini.
Malam Jatau: Lafiya. Amma in ba mutuwa akai ba wannan irin kuka Ta Mai-gari mi ya kawo shi?
Delu: Me fa ya kawo shi in ba gulma da kinibibi ba, wannan in da mayya ce in ta kama ka ko ƙashi bata bari.
Abu: Uhmm! Maigida ni dai miƙon gwaibar.
Ta Mai-gari: Allah sarki ne! Masu ‘ya’ya dai sun huce takaicinsu. Dubi yadda ake nan da nan da su, mu kuwa shiru kake ji kamar maye ya ci shirwa. (Ta ci gaba da kuka.)
Malam Jatau: Haba Ta Mai-gari daina kukan hakanan ya isa, haihuwa ai Allah ke bada ta ko?
Ta Mai-gari: I, Haka nan ne malam. Amma irin wariyar da ake nuna min a gidan nan abin yayi yawa.
Delu: Kya dai gaji da kisisinar ki ta gado ki bari, mu dai mun riga mun haifa kuma ko yau muka mutu muna da masu yi mana du’a’i, ehe!
Malam Jatau: Ashsha! Wannan magana bata kamace ki ba Delu.
Ta Mai-gari: Da ka barta ta faɗi abinda ke ranta Malam, ai kasan kowa tarbiyyar gidansu yake nunawa.
Malam Jatau: A’aha! Wai yanzu duk cikin ku babu me iya haƙura ta yi shiru ne kam?
Abu: (Ta rushe da kukan ƙarya.) Wayyo ni za su ja min hasara abin da ke cikina ya mutu, Maigida don Allah bar tasu ka miƙo min kayan marmarin nan, maƙoshina har zogi shi ka min wallahi.
Malam Jatau: Subahna! Ke Delu ki dubi girman Allah ki bani ledar nan in ba ɗiyar mutane, kin san in bata ci ba fa ana iya rasa abin da ke cikinta ko su duka biyun.
Delu: (cikin ɗaga murya) Ta mutu mana, can ga su Gada, wai zomo da ya ji kiɗan farauta. Yo ni da ashe baka san da zan iya mutuwa ba sa’ilin da nake da cikin Ganjarma sau nawa zan ce ka siyo min tsire ka ƙiya? Na ce sau nawa? Ai dole ka sadda kai ƙasa kamar me jiran haddi tunda ba ka da gaskiya.
(Malam Jatau ya sadda kai ƙasa kawai ya rasa abin yi.)
Abu: Ka yi wa Allah Maigida ka miƙo min gwaibar nan, ɗan nan sai ƙorafi yake min a ciki. (Ta rushe da kuka.)
Delu: Haka tara! In ji kishiyar ƙonanna!
Ta Mai-gari: Allah mai iko, ni ko ta ni ma ba a yi.
Malam Jatau: Ayya ratata! Shi kenan to ku kashe ni ku huta. Na ce ku kashe ni ku huta tunda haka kuke so. (Sai ya faɗi ƙasa yana shure-shure kamar zai mutu.)
Ta Mai-gari: Subahanallahi! Malam! Malam! Me ya same ka ne, ku miƙo ruwa don Allah, Malam.
Delu: (Ta yi maza ta ɗebo ruwa ta zo tana shafa mishi tana kuka.) Maigida ka tashi don Allah. Daga wasa kuma shikenan sai suma?
Abu: Ni dai ku miƙo min gwaibar nan in ɗan ci don Allah.
Delu: Ku ji min kafira fa! mijinki na kwance rai ga hannun Allah amma ke ta gwaiba kike?
Abu: Ke ce dai kafira ba ni ba!
Ta Mai-gari: Ku yi wa Allah ku yi shiru ku taya ni mu kama shi mu kaishi ɗaki.
(Yaran Malam Jatau Talle, Sabbinani da Ganjarma za su shigo, Sabbinani ne zai yi sallama.)
Sabbinani: Salamu Alekum. A’aha me ya samu Baba haka na ganshi kwance kamar ba ya numfashi?
Ta Mai-gari: Yauwa, gara da Allah ya kawo ku. Ku taimaka ku kai shi ɗaki don Allah.
Delu: (Ta durƙusa gaban Malam Jatau tare da rushewa da kukan ƙarya.) Wayyo ni mai gidana, muna cikin magana da shi kawai sai gani muka yi ya faɗi. Allah ya sa dai ba Lantana ce ta lashe shi ba. ‘Ya’yan nan ku ɗauko shi ku kai shi ɗakina, yau can yake da kwana.
(Su Ta Mai-gari da abu za su riƙe baki kawai suna kallonta cike da mamaki.)
Sabbinani: Subhanallahi! Ashsha. Sannu Baba, kai Talle kama ƙafafun, Ganjarma kama min nan mu ɗaga shi.
Ganjarma da Talle: To Yaya.
(Za su kama shi tiƙi-tiƙi su kai shi ɗakin Delu, ita ma sai ta tashi ta bisu hannunta riƙe da ledar da ya shigo da ita.)
Abu: (cikin tausasa murya) Haba Yaya Delu, ke kuwa yanzu wucewa za ki yi ba za ki bani ‘yar gwaibar ba?
Delu: Ke dai wallahi in da mayya ce kika kama mutum sai kin karshi tukun. Ungo dai ba don halin ki ba (Ta jefa mata guda biyu sannan ta wuce. Ita kuwa Ta Mai-gari baki kawai ta riƙe tana tafa hannu saboda mamakin irin halin Delu, daga baya ta shige ɗaki.)
Ta Mai-gari: Allah ka shirye mu, muma ka ba mu masu jin ƙanmu. (ta shige ɗaki)
Abu: Amin dai kam. (Ta jawo gwaibar ta goge a jikin zaninta tana tunawa.)
Masha Allah wani sabo kenan Allah y basira
Eh sabo ne wannan, na gode sosai.
Masha Allah gsky labarin yana daɗi Allah ya ƙara ɗaukaka
Amin. Jazakallah Khair
Mashaa Allah! Labarin Malam Jatau yayi armshi matuka. Muna nan biye da kai. Allah Ya kara basira.
Amin Yallaɓai. Jazakallah Khair.
Ma sha Allah, labari ya tsaru Allah ya kara basira
Amin. Jazakallah Khair
Hhhhh akwai rikici kenan a gidan malam Jatau. Allah ya ƙara basira
Amin. Na gode sosai.
Allah ya kara basira
Amin. Jazakallah Khair.
Very nice
Amin. Jazakallah Khair.
Labarin Malam Jatau ya yi bazata, ganin yadda kowa ta kansa yake yi sai sa’adda ta babban bango ya warwas, duk da haka son zuciyar masu ita bai karkato ba. Wannan labari ya yi.
Ina godiya sosai.
Tofa! Malam Jatau akwai wayo.
Lallai kam wannan haka yake. Ina godiya sosai.