Fitowa Ta Daya
(A ɗakin Delu. Yaran Malam Jatau na kewaye da shi suna tambayar shi yadda ya ƙara ji da jikin)
Sabbinani: Sannu Baba. Allah ya ƙara sauƙi. Ga ruwa ka sha.
Malam Jatau: Amin, na gode sosai ɗan nan.
Talle: Amma Baba, me ya same ka ne haka?
Malam Jatau: Hmm kai dai bari, masifar iyayenku mata ce ta sa na faɗi kamar bani da lafiya. Ba don na yi haka ba da yanzu suna nan suna ta cacar bakin da suka saba. Duk su bi su tayar min da hankali.
Talle: To Baba ai mu kam ba mu da ta cewa game da wannan.
Malam Jatau: Hakanan ne ɗan nan.
Ganjarma: Af! Ai kuwa kun ga mun yi mantuwa. Malam Audu fa na waje ya ce mu yi masa sallama da Baba.
Sabbinani: I’ hakanan ne kuwa! Ya kuwa ce ka hanzarta. Ga alama ma dai samu ne domin na ga yana yi yana sa hannu ga aljihu. Kuma na ga alama aljihun na da ɗan nauyi.
(ko da jin batun kuɗi sai Malam Jatau yai wuf ya tashi ya fita a guje ya nufi ƙofar gida)
Fitowa ta biyu.
(Abu na zaune tana cin gwaiba sai ta ganshi ya fito a guje.)
Abu: A’aha! Maigida! Lafiya kuma ka fito a guje haka kamar an koro ka?
Malam Jatau: (Yana ci gaba da gudu) Ke dai bari in dawo. Ci gwaibar ki kawai. (Ya ci gaba da gudun.)
Abu: (cike da mamaki) Allah mai iko! Amma ba yanzu aka kama ka ranga-ranga aka kaika ɗaki ba? Hm
Malam Jatau: Kai! Mata dai kun cika shiga cikin abinda ba a gama da ku ba. (Ya ci gaba da gudu har ya fita)
Fitowa ta uku.
(a ƙofar gidan Malam Jatau. Malam Audu na tsaye yana jiran fitowar Malam Jatau sai gashi yq fito yana haki)
Malam Jatau: Malam Audu, Salamu Alaikum kai ne tafe da yamma haka?
Malam Audu: Alaikassalam. I’ ni ne tafe. Na kuwa ɗan jima. Da har na fara tunanin ma ko in tafi ne in dawo daga baya. Amma lafiya kake haki haka kamar wanda aka biyo shi da gudu?
Malam Jatau: (yana sauke numfashi) Yi haƙuri don Allah. Wallahi sha’anin mata ne, abin ba a cewa komai.
Malam Audu: (yayi ajiyar zuciya) Hmm. Abokina, ai ina ganin ƙoƙarinka bisa yadda kake kula da matan nan naka. Dubi yadda ni mace ɗaya ce jal gare ni, amma irin yadda take wahalshe ni, abin sai kurum kawai.
Malam Jatau: Wannan batu naka dahir ne! Amma su mata ba ka gane suna sonka har sai ka nemo musu abokiyar zama. Gama na lura kishi na sa su yi maka abinda in su ɗai ne sai ka roƙa. Kuma ta hakane kurum za ka more musu.
Malam Audu: (cike da mamaki) Af to! Ashe haka abin yake?
Malam Jatau: Yadda ka ji ɗin nan kowa ka tambaya duk faɗin garin Taiki in dai yana da mace da ta haura ma ɗaya za shi faɗa ma gaskiya ne batuna.
Malam Audu: Ai babu ja a tsakaninmu. Na yarda da wannan batu naka ɗari bisa ɗari. Kuma lallai nima zan jaraba wannan dubara domin nima a kwashi garar da ni.
(suka yi dariya suka tafa har da kekkewa)
Malam Jatau: To Malam Audu, kasan an ce ‘in ka ji kira samu ne amma banda kiran ɗan doka’, ina fata dai samu ne kaima ya kawo ka gare ni.
Malam Audu: I’ lallai wannan magana hakanan ne. Dama yanzu haka daga kasuwa nake na je na siyar da taƙarƙarin nan da nake kiwo. To shi ne na ce bari in kawo maka kuɗin nan da ka ranta min watan jiya. Gama na ga hidima ta durfafo ka, shi yasa na ce bari in kawo maka tun yanzu ko da shi ke lokacin da muka shirya bai kai ga cika ba tukun. Don in ban manta ba ai watan nan ne watan haihuwar matarka ko?
Malam Jatau: I’ Wannan watan ne kuwa. Kai amma Malam Audu kai mutumin ƙwarai ne. Ka ganni nan dama bani da ko anini. Allah mai girma kenan. Watau da ace haka sauran masu amsar bashi suke da halin kirki irin naka, ai da mutane sun zauna lafiya.
Malam Audu: Ai wannan ba kome ne ba, in mutum ya biya bashin da ake binsa ai kanshi ya sauke wa nauyi. Kuma jin daɗin wannan mu’amala shi zai sa gobe in ya zo a ƙara masa. (Ya ƙirgo fam biyu ya miƙa wa Malam Jatau) Yauwa to gasu ka ƙirga.
Malam Jatau: (cike da murna) To Masha Allah! (ya ƙidaya ya ga sun cika) ai kuwa sun cika cif! Allah ya biyaka abokina. Na gode ƙwarai.
Malam Audu: Ai ni ke da godiya abokina. Wanda ya nema aka bashi ai shi ke da godiya. (ya ƙirgo sule goma kuma ya miƙa wa Malam Jatau) ga wannan kuma gudunmawata ce ka ɗan ƙara wajen hidima.
Malam Jatau: (ya rasa me zai ce don murna) Malam Audu irin wannan hidima haka! Na ma rasa me zance. Allah dai ya biya ka da Aljanna.
Malam Audu: Amin abokina. Allah ya sa mu cikin ceton Annabi dukkan mu. Bari in ƙarasa gida in sallami iyali kuma.
Malam Jatau: Amin. Amin dai. To abokina sai mun haɗu kenan. Ina godiya ƙwarai, ka gaishe su.
Malam Audu: Za su ji in Allah ya so. Sai anjima.
Malam Jatau: To sai anjima. A huta lafiya.
(suka yi musabaha Malam Audu ya wuce shi kuma malam Jatau ya koma cikin gida.
Dakyau. Allah ya ƙara basira.