Skip to content
Part 5 of 6 in the Series Malam Jatau by Haiman Raees

Fitowa Ta 1

(Cutar mantuwa na ci gaba da damun Malam Jatau, abin ma dai kullum sai ƙara gaba yake yi. Yarinyarsa babbar wadda ake kira da Ladiyo ‘yar shekara huɗu ta yi rashin lafiya har an kwantar da su a wani ɗan asibiti da ke kusa da garin, jikin yarinya ya samu, gasu nan a hanya ya goyo ta a keke suna dawowa, sai dai ɗan rafin da ke tsakaninsu ya kawo ruwa, bari mu ji yadda za su yi)

Malam Jatau: Ashsha! Ashe kwana biyun nan haka ruwa ya taru ban sani ba? Ai kuwa ruwan nan ba zai wutu min da yarinyar nan ba a bayan keke. Ladiyo!

Ladiyo: Na’am Baba.

Malam Jatau: Ruwan nan ina ganin ba zai wutu mana gaba ɗaya ba. Amma yanzu zan sauke ki a nan in haura da keken da ɗan ƙunshin kayanmu. In ya so sai in dawo in haura da ke mu tafi ko?

Ladiyo: To Baba.

Malam Jatau: Yauwa, Allah ya shi miki albarka.

Ladiyo: Amin Baba.

(Malam Jatau ya sauke yarinya ya naɗe ƙafar wando da kyau sannan ya gyara zaman ƙunshin kayan da ke keken ya haura kogin. Ko da haurawarsa sai kawai ya hau keken ya yi gaba. Ya ma manta cewa ya bar yarinyarsa a bakin gaɓa)

Fitowa ta 2

(Tun daga nesa yara suka hango malam Jatau tafe akan keke, don haka sai suka ruga suka sanar da iyayensu a gida. Abu, wacce ita ce uwar yarinyar sai ta yi maza ta fito tana leƙe ta katanga, sauran matan su ma suka biyo ta yin leƙen tare)

Abu: Nifa sai nake ganin kamar Malam ne shi kaɗai akan keken can. Ku taya ni duba wai makaho ya so gulma.

Ta Mai-gari: Ke Abu, raba kanki da makanta wallahi. Amma nima sai nake ganin kamar shi kaɗai ne akan abin hawan nan.

Delu: Lallai kam shi kaɗai ne. To amma me ya sa zai dawo shi kaɗai? Ko dai wani abu ya same ta ne?

Abu: Bakinki ya sari ɗanyen kashi! Da izinin Allah babu abinda ya faru da ‘yata.

Ta Mai-gari: Ai ba fata ba ne, tambaya ce. Kuma ke a tunanin ki me zai sa malam ya baro yarinyar nan alhalin an ce yau za a sallamo su?

Abu: (ta dafe ƙirji) Wayyo ni! Don Allah ku daina bani tsoro. Wallahi gabana faɗi yake yi.

Delu: Gashi nan ya ƙaraso wallahi bari in san na yi kafin ya ganni. (duk za su watse kowacce ta shiga ɗaki banda Abu)

Malam Jatau: (Ya shigo gida da sallama yana ) Salamu Aleikum.

Abu: Alaikassalamu. Malam in yarinyar take?

Malam Jatau: Ke ko barin mutum ya huta ma baki yi. Wace yarinyar ma wai kike magana a kai?

Abu: Haba malam! Ya za a yi uwa ta gaza tambayar inda ɗiyarta take? Yarinyar da ka je ɗaukowa asibiti nake magana malam. Ina take? Me yasa ba ku taho tare ba? Ko jikin nata ya sake tashi ne?

Malam Jatau: A’aha ba ga yarinyar ba. (ya juya da nufin ya nuna ta akan keken sai ya ga ba ta) A’a, ina kuma ta shiga, ko fita waje ne?

Abu: Innalillahi Wa inna ilaihir raji’un! Malam ina yarinta take? Kar dai ace ka yar min da ‘ya a hanya ba ka sani. Wayyo ni Abu na shiga uku na lalace. Mutanen gida ina kuke? Ku fito ku ji Malam ya yar min da ‘ya a hanya. Wayyo ni yau na bani na lalace. Shi kenan’ yan nan ta tafi ta tafi (sai ta fashe da kuka)

Malam Jatau: A’a wallahi ni dai na san na goyo ta a bayan keke mun taho. Af! Subunalillahi! Sai yanzu na tuna. Na baro ta a bakin kogi.

Abu: (ta dafe ƙirji) Bakin kogi malam? Innalillahi Wa Inna Ilaihir raji’un. (sai ta yi waje da gudu ta nufi bakin kogin kanta babu ko mayafi)

Malam Jatau: Ke abu ina za ki je? Ke baki ji ina magana ne? Kai mata dai halinsu sai su. (ya suri keke ya bita)

Fitowa ta 3

(sun taras da Ladiyo zaune a bakin kogi ta ci kuka har ta gaji, daga nan suka ɗauke ta suka dawo gida)

Fitowa ta 4

(Malam Jatau ya siyo wani jaki mafaɗacin gaske. Gashi nan ya je bashi harawa a bayan gida sai artabu suke yi)

Malam Jatau: A’aha, ni wannan jaki kai ko wane irin jaki ne kai. Abincin ma ka ƙi yarda in baka. (in ya yi nan, shima jaki sai ya bishi)

Malam Jatau: Wannan abu dai na ga ba na ƙare bane. Don haka bari ku gani, zagayawa zan yi ta baya in kama bindin jakin nan in ta ja har sai ya nutsu. Ai dama Hausawa sun ce in ka san wata ba ka san wata ba. (sai ya yi wuf ya koma ta bayan jakin nan ya cafko bindin jakin ya fara ja iya ƙarfinsa. Da jaki ya ji zafi sai kuwa ya kai mishi harbi. Na faro a ƙafar hagu ya same shi, na biyu kuma a ƙafar dama. Azaba ta sa Jatau sakin bindin jakin nan ya durƙushe ƙasa, bai kai ga hutawa ba kuma ya ƙara mishi da duka ƙafafuwansa biyun a fuska. Nan take Jatau ya faɗi sumamme jini na fita ta hanci da ta bakin shi. A haka matansa da yaran da ke cikin gidan suka tarar da shi aka ɗauke shi ranga-ranga kamar ya mutu aka shiga da shi cikin gida)

MALAM JATAU

KASHI NA BIYAR

Fitowa ta 1

(cutar mantuwa na ci gaba da damun Malam Jatau, abin ma dai kullum sai ƙara gaba yake yi. Yarinyarsa babbar wadda ake kira da Ladiyo ‘yar shekara huɗu ta yi rashin lafiya har an kwantar da su a wani ɗan asibiti da ke kusa da garin, jikin yarinya ya samu, gasu nan a hanya ya goyo ta a keke suna dawowa, sai dai ɗan rafin da ke tsakaninsu ya kawo ruwa, bari mu ji yadda za su yi)

Malam Jatau: Ashsha! Ashe kwana biyun nan haka ruwa ya taru ban sani ba? Ai kuwa ruwan nan ba zai wutu min da yarinyar nan ba a bayan keke. Ladiyo!

Ladiyo: Na’am Baba.

Malam Jatau: Ruwan nan ina ganin ba zai wutu mana gaba ɗaya ba. Amma yanzu zan sauke ki a nan in haura da keken da ɗan ƙunshin kayanmu. In ya so sai in dawo in haura da ke mu tafi ko?

Ladiyo: To Baba.

Malam Jatau: Yauwa, Allah ya shi miki albarka.

Ladiyo: Amin Baba.

(Malam Jatau ya sauke yarinya ya naɗe ƙafar wando da kyau sannan ya gyara zaman ƙunshin kayan da ke keken ya haura kogin. Ko da haurawarsa sai kawai ya hau keken ya yi gaba. Ya ma manta cewa ya bar yarinyarsa a bakin gaɓa)

Fitowa ta 2

(Tun daga nesa yara suka hango malam Jatau tafe akan keke, don haka sai suka ruga suka sanar da iyayensu a gida. Abu, wacce ita ce uwar yarinyar sai ta yi maza ta fito tana leƙe ta katanga, sauran matan su ma suka biyo ta yin leƙen tare)

Abu: Nifa sai nake ganin kamar Malam ne shi kaɗai akan keken can. Ku taya ni duba wai makaho ya so gulma.

Ta Mai-gari: Ke Abu, raba kanki da makanta wallahi. Amma nima sai nake ganin kamar shi kaɗai ne akan abin hawan nan.

Delu: Lallai kam shi kaɗai ne. To amma me ya sa zai dawo shi kaɗai? Ko dai wani abu ya same ta ne?

Abu: Bakinki ya sari ɗanyen kashi! Da izinin Allah babu abinda ya faru da ‘yata.

Ta Mai-gari: Ai ba fata ba ne, tambaya ce. Kuma ke a tunanin ki me zai sa malam ya baro yarinyar nan alhalin an ce yau za a sallamo su?

Abu: (ta dafe ƙirji) Wayyo ni! Don Allah ku daina bani tsoro. Wallahi gabana faɗi yake yi.

Delu: Gashi nan ya ƙaraso wallahi bari in san na yi kafin ya ganni. (duk za su watse kowacce ta shiga ɗaki banda Abu)

Malam Jatau: (Ya shigo gida da sallama yana ) Salamu Aleikum.

Abu: Alaikassalamu. Malam in yarinyar take?

Malam Jatau: Ke ko barin mutum ya huta ma baki yi. Wace yarinyar ma wai kike magana a kai?

Abu: Haba malam! Ya za a yi uwa ta gaza tambayar inda ɗiyarta take? Yarinyar da ka je ɗaukowa asibiti nake magana malam. Ina take? Me yasa ba ku taho tare ba? Ko jikin nata ya sake tashi ne?

Malam Jatau: A’aha ba ga yarinyar ba. (ya juya da nufin ya nuna ta akan keken sai ya ga ba ta) A’a, ina kuma ta shiga, ko fita waje ne?

Abu: Innalillahi Wa inna ilaihir raji’un! Malam ina yarinta take? Kar dai ace ka yar min da ‘ya a hanya ba ka sani. Wayyo ni Abu na shiga uku na lalace. Mutanen gida ina kuke? Ku fito ku ji Malam ya yar min da ‘ya a hanya. Wayyo ni yau na bani na lalace. Shi kenan’ yan nan ta tafi ta tafi (sai ta fashe da kuka)

Malam Jatau: A’a wallahi ni dai na san na goyo ta a bayan keke mun taho. Af! Subunalillahi! Sai yanzu na tuna. Na baro ta a bakin kogi.

Abu: (ta dafe ƙirji) Bakin kogi malam? Innalillahi Wa Inna Ilaihir raji’un. (sai ta yi waje da gudu ta nufi bakin kogin kanta babu ko mayafi)

Malam Jatau: Ke abu ina za ki je? Ke baki ji ina magana ne? Kai mata dai halinsu sai su. (ya suri keke ya bita)

Fitowa ta 3

(sun taras da Ladiyo zaune a bakin kogi ta ci kuka har ta gaji, daga nan suka ɗauke ta suka dawo gida)

Fitowa ta 4

(Malam Jatau ya siyo wani jaki mafaɗacin gaske. Gashi nan ya je bashi harawa a bayan gida sai artabu suke yi)

Malam Jatau: A’aha, ni wannan jaki kai ko wane irin jaki ne kai. Abincin ma ka ƙi yarda in baka. (in ya yi nan, shima jaki sai ya bishi)

Malam Jatau: Wannan abu dai na ga ba na ƙare bane. Don haka bari ku gani, zagayawa zan yi ta baya in kama bindin jakin nan in ta ja har sai ya nutsu. Ai dama Hausawa sun ce in ka san wata ba ka san wata ba. (sai ya yi wuf ya koma ta bayan jakin nan ya cafko bindin jakin ya fara ja iya ƙarfinsa. Da jaki ya ji zafi sai kuwa ya kai mishi harbi. Na faro a ƙafar hagu ya same shi, na biyu kuma a ƙafar dama. Azaba ta sa Jatau sakin bindin jakin nan ya durƙushe ƙasa, bai kai ga hutawa ba kuma ya ƙara mishi da duka ƙafafuwansa biyun a fuska. Nan take Jatau ya faɗi sumamme jini na fita ta hanci da ta bakin shi. A haka matansa da yaran da ke cikin gidan suka tarar da shi aka ɗauke shi ranga-ranga kamar ya mutu aka shiga da shi cikin gida)

<< Malam Jatau 4Malam Jatau 6 >>

1 thought on “Malam Jatau 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.