Skip to content
Part 6 of 6 in the Series Malam Jatau by Haiman Raees

Fitowa ta 1

(jikin Malam Jatau fa ya yi ƙamari tunda jakinsa ya sakar masa harbi, su kuma matansa har sun fara aikin nasu. Gashi nan dai a kwance rashe-rashe tare da matan a tsakar gida)

Ta Mai-gari: Oh Allah mai iko, Malam Jatau yau kai ne kwance rashe-rashe kamar ɗan kaciya har ba ka iya gane mutane. Lallai kowa ya ɗau duniyar nan da zafi ya bani ya lalace.

Abu: Faɗi da ihu ki ƙara da kururuwa. Wannan magana taki babu ja, wai kare ya mutu a saura. Ni abin ma har ya fara bani tsoro, sai ka ce wanda aka yi wa asiri?

Delu: To kada kuma a saki layi kamar yadda aka saba, gama na ga ni ake so a jaza wa tsiya don an ga ranar girkina ne abin ya faru da shi. Ehe, li’ilafi ƙuraishin, aniyar kowa ta bishi.

Abu: Ahayye! Ayyuriri!! Dama masu iya magana sun ce ‘mai kaza a aljihu ba shi jimirin as. Yau dai gashi kin kama kanki da kanki.

Ta Mai-gari: A’a fa Abu, kada kuma ki jawo mana wata damuwar alhali ba mu fita daga wata ba. Mu bar wannan maganar don Allah.

Delu: Ai da kin barta ta yi. Dama mai hali ai ba shi dainawa sai dai sauƙi.

Abu: Oho dai, shakulatin ɓangaro, ungulu ta ga mushen mota.

(daga nan suka ci gaba da surutansu)

Fitowa ta 2

(Bayan watanni biyu. Malam Jatau ya warke sarai. Matarsa Abu ta sauka lafiya, ta samu wata macen sun zama su uku kenan. Ranar suna ta zagayo har an sa wa yarinya suna Jummai. Sai dai kuma malam Jatau ya hana kowa taɓa naman ragon sunan. Gashi nan ya haɗa murhu da kasko a ƙofar gida wai shi zai toya naman da kanshi. Ana iya jiyo muryar mutane a ciki da wajen gidan)

Malam Jatau: (yana magana shi kaɗai) gara in toya kayana da kaina in raba wa kowa yadda na ga dama. In ba haka ba na lura ni zan ji a salansa.

Marka: (ƙanwar Malam Jatau ce, ta zo kusa da shi ta tsaya) Yanzu fisabilillahi Yaya wannan wane irin abu ne? Haba Yaya, wannan ai ba daidai ba ne. Dubi mutane fa sai kallon ka suke yi.

(ana iya jiyo cece-kucen mutane suna magana akan abinda malam Jatau ke yi)

Malam Jatau: (bai ko kalleta ba, sai ma kiran ‘yarsa ya yi) Ke Lantai!

Lantai: (‘yar Malam Jatau ta biyu kenan) Iye.

Malam Jatau: Ja’ira! Ba na hana ki cewa iye ɗin nan ba. Maza ki ce wa Balele ya je wurin Delu ya amso min man gyaɗan nan. Shi kuma Ilu ya yi sauri ya ɗauko min naman ga wuta nan ta kama zan fara aiki kada rana tai min.

Lantai: To Baba. (sai ta nufi cikin gida)

Marka: Don girman Allah Yaya ka bar wannan rigimar haka nan ka zo mu shiga cikin gida in ya so sai mu ƙarasa daga ciki.

Malam Jatau: Ke! kin ganki ɗin nan mai kama da balama in ba ki wuce kin bani wuri ba sai na make ki. (ya kai mata bugu ta goce)

Marka: To amma Yaya ai gaskiya nake faɗa. Ta yaya za a ce kai ne za ka yi suya da kanka a ranar sunan matarka kuma a ƙofar gida? Haba ai wannan ba yi ba ne. Sai ka ce wani ɗan daudu?

Malam Jatau: Aha! Shikenan dama abinda kike so ki faɗa kenan. Wato ni ne ɗan daudun ko? Yau kuwa ni da ke ne. (sai ya bi ta ta arce. Mutane suka yi ta yi musu dariya)

Lantai: (ta dawo hannu fayau) wai mama ta ce wai ba za a wai bayar wai da man ba kuma wai shi ma wai Yaya balelen wai kuma shi ma kuma ba zai kuma wai zo ba.

Malam Jatau: Lallai yau za kuwa a yi ta (sai ya kutsa kai cikin gidan. Ga mata nan cike maƙil, amma haka nan ya shafa wa idanuwansa bula sai da ya ɗauko naman da man ya fito da su ya fara toyawa)

(mahaifiyar Malam Jatau da ake kira Uwani za ta zo wurin tana dafe da ‘yar sabdarta, za ta rufe shi da faɗa)

Uwani: Kai Jatau! Ina Jatau ɗin yake? Kai yaron nan akwai ɗan banza. Wallahi in ba ka tashi ka bar wurin nan ba ina iya kwaɗa maka sandar nan yanzu yanzun. Yau ga ɗan nema kai.

Malam Jatau: Na’am Mama. Ni dai da da hali da an barni na ƙarasa aikina.

Uwani: Ai ni ka ke maida wa magana? Fitsarar za ka gwada mini? Iye?!

Malam Jatau: A’a, ba haka ba ne mama.

Uwani: To in ba fitsara ba duk garin nan ka taɓa jin namijin da ya toya naman sunan abinda aka haifa masa da kanshi? Ko dai ka zama ɗan daudu ne ba mu sani ba?

Malam Jatau: Haba mama, ya za ki dinga kirana da ɗan daudu? Ni fa irin rabon nan da matan ke yi ne a cikin gida ba ni gane irinsa. A yi rabo shi mutum sai dai ka ga an bashi wani ɗan higgwannana!

Uwani: Yau ga ɗan banza, yanzu saboda wannan dalilin ne ya sa ka yanke shawarar toya naman da kanka? Yau kuwa za ka gamu da ni. (sai ta bi shi a guje tana kai mai duka da sabdarta. Da ya ga ba arziƙi sai ya arce ita kuma ta sa aka shige da sauran kayan cikin gida. Mutane kuma suka yi ta musu dariya)

Fitowa ta 3

(Malam Jatau ya hawo kekensa zai je ƙauyen su Delu domin ya gaida iyayenta, za su yi kiciɓus da wasu baƙi a hanya)

Malam Jatau: Ku kam hala dai baƙi ne?

Haidar: (Ya miƙa masa hannu tare da yi masa sallama) Eh ƙwarai mu baƙi ne. Sunana Haidar, wannan kuma matata ce, Nadiya. Daga Kaduna muke, shin ko nan ne ƙauyen Taiki?

Malam Jatau: To maraba maraba. Eh nan ne ƙauyen Taiki, amma akwai ‘yar tafiya kaɗan kafin ku isa cikin gari sosai. Ku kuwa me ya kawo ku wannan ƙauye namu?

Haidar: (Ya yi murmushi) Ban san sunanka ba, ko za ka iya faɗa min?

Malam Jatau: Ni sunana Jatau. Amma kowa na kirana da Malam Jatau na Delu da Abu.

Haidar: Da kyau malam Jatau. Ni da matata mun zo yawon buɗe ido ne da kuma shaƙatawa a wannan ƙauye naku mai albarka. Muna fata za ku karɓe mu hannu bibiyu.

Malam Jatau: (yana washe baki) A haba wa zai ƙi baƙo? Ai muna maraba da duk wanda zai shigo matuƙar da alheri ya zo mana. Ba don sauri nake ba ma da da kaina zan sauke ku a gidana.

Nadiya: Kai aiko da mun ji daɗi. Amma duk da haka mun gode da karamcinka. Bari mu hanzarta, kasan gari na ruwa.

Malam Jatau: Hakanan ne kuwa. Allah ya sauke ku lafiya.

Haidar: Amin. Mun gode sosai.

(Daga nan Malam Jatau ya ja kekensa ya wuce. Su kuma waɗannan mata da mijin sai suka bishi kawai da kallo, bayan ya wuce sai suka kalli juna kawai suka yi dariya sannan suka wuce)

‘Yan Wasa

Malam Jatau – wani mutumin ƙauye

Delu – matar malam Jatau ta fari

Ta Mai-gari – matar malam Jatau ta biyu

Abu – matar malam Jatau ta uku

Malam Audu – abokin malam Jatau

Uwani: mahaifiyar Malam Jatau

Ladiyo – yar Jatau

Marka – ƙanwar Jatau

Sambo – mai tireda

Shekarau – abokin Malam Jatau

Ɗangwandi – abokin Malam Jatau

Ɗantakarda – ɗan Malam Jatau

Talle – ɗan Malam Jatau

Sabbinani – ɗan Malam Jatau

Ganjarma – ɗan Malam Jatau

Jummai = ‘yar Malam Jatau

Lantai = ‘yar malam Jatau

Ilu = ɗan malam Jatau

Balele – ɗan malam Jatau

Sidi – maƙwafcin Malam Jatau

Ɗanliti – wani yaro

Lato – wani yaro

Haidar: Wani mutumin birni

Nadiya: Matar Haidar

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Malam Jatau 5

1 thought on “Malam Jatau 6”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×