Skip to content
Part 1 of 2 in the Series Marigayiya by Habibu Hudu

Ga al’ada ko kuma in ce ga yadda na sani kuma na saba gani tun ina karamina shine duk gidan da aka yi mutuwa to ana jingine duk wani abu na annushuwa da nishadi da duk dangoginsa har zuwa kwana uku ne ko bakwai ko kwanaki arbai’n ko kuma abinda gidan mamacin suka tsara, amma dai mafi rinjaye an fi jinginewa ne har zuwa kwanaki bakwai, kai ba iya gidan da akayi mutuwar kawai ba hatta wasu masu makwabtaka da gidan mutuwar kanyi irin wannan karar don taya gidan mutuwar jimamin abinda ya samesu. Amma ni a mutuwar matata abin ba haka bane. Ban sani ba ko za ka yi mamaki in kaji a matsayina na dan musulmi na shaida maka cewa ranar da mai dakina ta rasu aka gayyato masu kalangu da kidan kwarya suka cashe a gidanmu wai duk don murnar mutuwar matar tawa. Muna makabarta wajen binne gawar matar tawa labari ya ishe min cewa ga masu kalangu can suna cashewa a gidan mu sai naji abin banbarakwai kamar a mafarki, har na kagauta a kammala in je in ganewa idanu na.

Na halarci jana’ida da dama kala kala wanda bazan iya cewa ga yawansu ba amma in ka dauke jan’idar Marigayi Sarkin Kano Alh Ado Bayero da Marigayi Tsohon Gwamnan Kano Alh Abubakar Rimi da matarsa Sa’adatu Abubakar da kuma Umar Abdulaziz Baba Fadar Bege da kuma shiek Mahmoud Jafar to banga wata jana’ida da ta hada mutane kamar ta matata ba wajen yawan dandazon jama’a. bayan an sanya ta a rami an jera tukwane an soma zuba kasa sai wani sabon hawayen ya soma zubowa daga idanuna.

Rarrashin da ake yi min ne da kuma ban hankuri yasa na kasa yanke kukan da nake yi. Bayan an kammala duk abinda ake wa mamaci a makabarta na game da addini da al’ada sai aka soma ficewa daga makabartar ban san ba lokacin da na yanke jiki na fadi.

Na dai farka ne kawai na ganni a kwance kan shimfida a cikin dakina, ga kuma kannena mata guda biyu a kaina suna min fiffita, ganin na farka ne yasa kararmarsu ta fice daga dakin da hanzari ta nufi tsakar gida tana mai fadin “Kuzo ku gani ya farfado” Har mahaifiyata ta shigo dakin tayi min sannu ban iya tunano gaba daya abubuwan da suka faru gareni ba, abu guda daya da na fi tunanowa shine ina tsaye a kan kabarin matar tawa ina zubbar da hawaye wanda hakan ma ina rokon Allah yasa ya zama a mafarki. Na tashi zaune sai faman rarraba idanu nake yi lokaci guda kuma ina jiyo sautin kalangu da shantu gami da kidan kwarya a tsakar gidan mu sai na soma kokonton cewa lallai ba mafarki nake ba domin na tuna da labarin da aka bani tun ina makabarta. amma duk da haka sai na daure na tambayi mahaifiyar tawa cewa “Hajiya me ke faruwa ne a gidan? Cikin rashin fahimta ta tambayeni cewa me ke faruwa kamar yaya? Kaina a kasa na ce da ita “Naji kamar ana kalangu da kidan kwarya

“Ba kama bace” Ta dan bata rai “Abinda kunnuwanka suka jiyo maka gaskiya ne” “Hajiya ji nake mutuwa akayi amma ake cashewa haka? Bata bani amsa ba sai ta tashi ta fice daga dakin ta barmu mu biyu da kanwata mai bina a haife ‘yar shekara goma sha shida. Bayan ficewar Hajiyar ne sai Kanwata Zulai take labarta min cewa “Mu kan mu babu yadda bamu yi ba da Hajiya akan wannan kidan tunda mutuwa akayi amma ta dage wai wannan abin farin ciki ne dole a yi murna” Mamaki ya fito karara a fuskata “Menene kuma abin farin ciki” “Wai mutuwar anti Rumee” Mutuwar matar tawa shine abin farin ciki “Haka dai hajiya ta fada” inji zulai har makwafta sun yi mata magana amma taki ta hankura wai ita babu wanda ya isa ya hana mata nuna farin cikinta akan wannan sha’anin. Na dan jima ban yi magana ba itama kanwar tawa bata yi magana ba . na soma kokarin mikewa tsaye amma jiri ya hana min mikewar daga na yi yunkurin mikewar sai in dawo kamar zan fadi gudun kada in yima kaina rauni sai na dawo na zauna ina mai duban Zulai gami da tambayarta “To yanzu kuma a ina ake yin zaman makoki? Zulai ta bude baki wato alamun mamaki “Wanne irin zaman makoki kuma” Ta dan yi shiru bayan ta numfasa sai ta dora da cewa “kaima kasan hakan ba zai yiwu ba, Hajiyar da ta ce duk wanda yayi mata ta’aziyya bata yafe ba to ta yaya kake tunanin zata bari a yi wani zaman makoki a wannan gidan.

Ban sani ba ko za ka yi mamakin jin cewa Mahaifiyata data haifeni itace umul’abaisin rugujewar rayuwata , da kuma shigata duk matsalolin na rashin dadin rayuwa da na samu kaina, Wanda ita tunaninta kaunace ta nuna min akwai abubuwa guda ukku wanda ba zan taba mantawa dasu ba sai dai ko in bayan raina wanda akansu zan gina wannan labarin da zan baka yanzu.

Na farko itace sanadiyar zuwana gidan mahaukata na biyu kuma shine itace sanadiyar gurguncewata wato rasa kafafuwana guda biyu, cikon na ukun kuma shine wanda babu dadin ji wanda in ka ji shi sai kaji kamar ka tsine mata wato da ta zamanto sanadiyar ajalin mata. ZAN BAKA LABARIN AMMA INA SON KA YI MIN ALAKALANCI WAI SHIN KAUNA CE TA NUNA MIN KO KUMA TSANA CE?

Abinda ya faru a shi ne, kwana daya ne ya rage a daura auren mu da Rumy Muktar ya sameni a kasuwa wajen harkokina ya ke shaida min cewa “Hajiya tace a sanar dakai cewa tana son yau din nan kaje ka samu yarinyar da zaka aura ka kaita a yi mata gwaji.”

“Wanne irin gwaji kuma” cikin rashin fahimta na tambayeshi.

Kansa a kasa yace “Wai gwajin cuta mai karya garkuwan jiki, an zo har gida an shaida mata cewa wai Rumasa’u tana da kanjamau.”

Na dade kaina a sunkuye ban yi magana ba daga karshe nace “To amma Mukhtar kai kanka kasan Rumy bata da kanjamau ko.”

Bai yi magana ba sai nine naci gaba da cewa “To yanzu menene abin yi?

“Babu wani abin yi da ya wuce abi umarnin hajiya.”

Nima na mike tsaye, bayan dan gajeren tunanin da nayi sai nace da Mukhtar “To amma yanzu ta yaya kake ganin zan tunkari Rumy da wannan maganar?”

“Ni kuwa ina ganin kamar ba matsala bace” Inji muktar “Ai kawai zuwa zaka yi ka sanar da ita halin da ake ciki.”

Da yaji ban yi magana ba sai ya dora da cewa “In ta yarda sai kuje.”

“In kuma bata yarda ba fa” Na fada ba tare da na kawar da idona daga kallonsa ba.
“Bana jin zata ki amincewa.” Inji Mukhtar

Ni kuma nace “saboda me?”

Farat daya ya bani amsa da cewa “Saboda so da kaunar da take yi maka.”

Duk da cewa ina a cikin bacin rai to sai da wannan maganar tasa ta bani dariya “Wannan ba hujja bace, ban yi tsammanin zata yarda ba, Mukhtar ina son ka fahinci cewa ba kowacce yarinya bace zata lamunci wannan kazafin….

“Tsaya don Allah” Inji Mukhtar. ” Ni nasan irin kaunar da Rumy take yi maka tabbas zata amince da duk abinda zaka je mata da shi, wannan kenan. Sannan kuma kana zuwa wajen Hajiya da wannan zancen wato sabanin abinda ta umarceka to ina mai tabbatar maka da cewa sunan aurenku fasasshe don haka shawara ta rage naka.

Da haka muka yi sallama ya tafi ya barni. Yana tafiya nima na kama hanya ban zame koina ba sai gidan Mahaifiyata. naje na sameta na sanar da ita cewa na ji sakonta a wajen Mukhtar amma daman nazo ne in shaida mata cewa Rumy bata dauke da wannan cutar da ake magana a kanta. Na shafe kusan awa guda ina lallamin Hajiya akan ta yarda dani amma taki yarda sai dai in nayi magana tace ni karamin yaro ne ban san inda kaina yake min ciwo ba, wai ban san ciwon kaina ba. Daga karshe tace taji ta yarda amma tana son ta gani a rubuce. A daidai lokacin ne kuma Rumy ta kirani a waya tana yi min neman gaggawa ban san ko neman menene ba amma haka muka yi sallama da Hajiya na kama hanya zuwa unguwar su Rumi.

Duk da cewa da akwai ‘yar tazara daga wajenmu zuwa unguwarsu to sai da na shafe a kalla minti talatin kafin in karasa unguwar tasu, kuma kafin in karasa din ta kira ni a waya yafi sau goma tana tambayata cewa ina daidai ina, wanda hakan ya tabbatar min da cewa lallai ba lafiya ba.

Na isa unguwar tasu ne ana dab da shiga sallar la’asar kasancewar da alwalata yasa ban karasa kofar gidan nasu ba sai da na bi jam’in sallah a cikin wani masallaci da ke lokonsu, Muka idar bayan an fito sannan na karasa gidan nasu.

A kofar gida na sameta a tsaye tana jirana tabbas nasan ni take jira, kallo daya nayi ma fuskarta na tabbatarwa da kaina cewa ba lafiya ba. ba kamar yadda muka saba gaisawa ba wannan karon sama sama ta gaida ni tun kafin in gama amsa gaisuwar tace min “Zan tambayeka amma kar ka boye min”
Bance komai ba na yi kasake ina sauraronta a yayin da taci gaba da cewa “Wanne sako ka turo Mukhtar wajena?

“Yaushe kenan? na fada cikin rashin fahimta.

Taci gaba da cewa “Bai dade da tafiya ba.”

“Ni ban turo shi wajenki ba.”

“In kai baka turo shi ba to an turo shi daga gidanku.”

“To a gaskiya ban san zancen ba, amma me yace miki?”

Ta soma zubar da hawaye “Mukhtar Yace Hajiya tace sai ka kaini a yi min gwajin cuta mai karya garkuwan jiki.”

“Hakane” Nace “Tabbas Hajiya ta aiko shi wajena da wannan zancen.”

“To wacce shawara ka yanke?”

“Kawai na yanke shawarar ba zan je ba.”

“Kayi kuskure, ba’a ketare umarnin iyaye musamman Mahaifiya domin ba mamaki ko ita ta hango maka wani abu da kai baka hango ba. Don haka in har ka shirya to bari in shiga gida in fito sai muje ayi mana gwajin.”

Da farko na yi tsammanin ko gatse take yi min amma bayan fitowarta sai na tabbatar da gaske take.

******

Mun je wajen gwajin sai dai wai tunda magana ce ta aure to ba ita kadai ya kamata ayi ma gwajin ba dole aka yi mana mu biyu. bayan dan gajeren jira da muka yi sai aka bamu sakamakon mu a cikin rufaffiyar takarda muka kama gabanmu. akan hanyarmu ta komawa ne Rumy tace in bude sakamakon in duba ni kuma nace bazan bude ba domin in har na bude to tamkar na yarda ne cewa tana dauke da kwayar cutar. don haka zan je in baiwa mukhtar sakamakon ne ya kaiwa Hajiya tunda daman shi ta aiko.
Bayan na kai ta gida sai nima na wuce gida kai tsaye akan hanya na buga ma mukhtar waya cewa yazo ya karbi sakamakon gwajin mun dawo. Ina shiga daki na warware takardar. Takardar rumy na soma dubawa wanda sakamakon yayi min matukar kyau nayi matukar jin dadin abinda na gani. sakamakon ya nuna cewa Rumy bata dauke da cutar Kanjamau. Ban damu da duba tawa takardar ba don ina da garanti a a kaina. Mukhtar ya iso ko fitowa daga motar bai yi ba yayi min hon na fita na kai masa takardar ya karba ya tafi.

Tunda ya karba ya tafi Shiru shiru bai dawo ba har kusan sallar isha’i na buga masa waya amma a kashe, ba wani abu bane yasa nake nemansa sai don yazo mu kammala shirye shiryenmu kasancewar washe gari daurin aure.

Karfe takwas da kwata na dare naji tsayawarsa a kofar gida na fita a daidai lokacin da shima ya fito daga cikin mota. Muka jingina a jikin motar yana mai mai fadin “Kaga shiru ko?”

Ban yi magana ba ya kwashe gaba daya abinda ya faru a tsakaninsa da mahaifiyata ya sanar dani cewa lokacin da ya kaiwa Hajiya sakamakon gwajin nan bata yarda da sakamakon ba sai da ta sa aka je har gida aka dauki Rumasa’u a mota aka je tare da ita Hajiyar wajen gwajin duk da haka ma bata yarda ba sai tasa aka je waje daban daban har waje hudu kuma duk ana samun sakamako guda cewa Rumasa’u bata dauke da cuta mai karya garkuwan jiki. daga nan ne Hajiya ta yarda ta saduda.

Bayan ya gama bani labarin sai muka tattauna yadda harkokin bikin zasu kasance. ba wani dogon surutu muka yi ba, muka yi sallama ya kama gabansa nima na shiga gida.

Kasan duk wanda yake doki na aure musamman ma irin nawa wanda akayi gwagwarmaya ayi kamar ba’a yi ba to zai yi wahala mutum ya samu damar barci a daren da za’a daura auren. to haka na samu kaina a jajiberin daurin auren nawa ko kadan ban runtsa ba. sai kusan sallar asuba ne na dauko takardata ta wajen gwaji zan hada ta da ta wajen Rumy wadda Mukhtar ya dawo min da ita.

Na warware tawan anan ne sakamakon nawa gwajin ya nuna cewa ina dauke da kwayoyin cuta mai karya garkuwan jiki.

******

Ban samu zuwa daurin aure ba, hakazalika ban samu damar halattar walima ba. na kashe wayata, na tsani kaina na kyamaci kaina. ban san inda zan sa kaina ba, a ranar da za’a yi daurin aurena ina can ina ta zirga zirga wajen gwaji sai da naje gwaji kusan waje takwas amma duk abu daya ake magana akai wato ana tabbatar min da cewa ina dauke da kwayoyin cuta mai karya garkuwan jiki. wannan sintirin ne ya hana min halattar daurin Auren nawa.

Nasan a irin labarin da na ke baka tabbas zaka iya yi min wani kallo na daban tunda kaji nace ina dauke da kwayoyin cuta mai karya garkuwan jiki. Ko da yake bansan sauran kabilu ba amma abinda na sani shine a al’ada ta kasar Hausa in dai aka ji ance mutum yana dauke da irin wannan lalurar to ana yi masa kallon dan iska ne mazinaci, to kar kayi min wannan kallon ina mai tabbatar maka da cewa ni ba dan iska bane, tunda na ke a rayuwata ban taba yin zina ba. ko ka yarda ko kar ka yarda iya abinda zan fada maka kenan, don haka nan gaba zaka ji yadda na gamu da wannan cutar.

Gaba daya na rasa abinda zanyi, wannan shine ga koshi ga kwanan yunwa. Daga karshe na yanke shawarar barin garin amma sai bayan nayi sallama da amaryata.

******

Har aka gama surutai da barkwanci irin na abokan ango a wajen sayen baki ban ce kala ba su kuma sauran abokan ango musamman ma Mukhtar basu san dalilin yin wannan jungum din ba. Haka suka karashi barkwancinsu suka yi sallama da amarya nayi musu rakiya zuwa kofar gida bayan sun tafi na mayar da kofar na kulle sannan na dawo cikin gida inda na tarar Amaryar tawa a tsaye a tsakar gida, ina shigowa ta rike hannuna muka shiga falo mukayi abu na farko da addini ya tanada ga mata da miji a daren farko wato nafilfili da godiya ga Allah da ya cika mana burinmu.

Bayan kammala komai ta tashi ta shiga uwar daka ni kuma na haye doguwar kujerar falo na mimmike akan kujerar na shiga karanta wasikar jaki. Ni kaina ban san tunanin da nake yi ba a haka na kasance har kusan karfe biyu na dare, na dawo hayyacina ne a daidai lokacin da naji ana taba jikina, duk da cewa ba barci nake yi ba to sai da nayi firgigit na tashi zaune, a tsaye a kaina sanye da kayan barci babu abinda ba’a gani na daga surorin jikinta in ba mutum ya kura mata idanu ba to ba za’a taba cewa da akwai wani abu a jikinta ba tsikar jikina ta tashi naji wani yarrr a sakamakon rike hannuna da tayi ta kamani na mike, hannunta rike da nawa ta ja ni tana gaba ina baya har muka shiga uwar daki. Ta zaunar dani a gefen gado, ta yi iyakar kokarinta akan in sanar da ita abinda ke damuna amma ban fada mata ba kuma tayi fushi sosai akan hakan amma naki kulawa. Duk da haka ta danne fushin nata, amma babban abinda yafi bakanta mata rai shine lokacin da ta nemi muyi kwanciyar aure sai na ki yarda. anan ne naga bacin ranta sosai. saboda tsabar kuka har wani shidewa ta ke yi. nayi rarrshin duniyar nan amma taki hankura bata saurareni ba ma balle taji abinda nake fada mata.

Marigayiya 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×