Skip to content
Part 2 of 2 in the Series Marigayiya by Habibu Hudu

A haka muka wayi gari babu wata mu’amala ta kirki. Sai da muka yi kwana uku a irin wannan halin, ni dai ban sanar da ita matsalata ba. Nayi matukar tausaya mata. a cikon kwana na hudu ne bayan na fita ta buga ma Mukhtar waya ya je gidan, ta sanar dashi halin da muke ciki. Mukhtar daga wajenta bai zame ko’ina ba sai wajena ya yi kokarin in sanar dashi abinda ke faruwa amma ban sanar dashi ba, kai kanka kasan halin Mukhtar ba kasafai yake son matsawa Mutum ya fadi abu ba da son ransa ba, don haka da ya fahimci bani da niyyar sanar dashi sai ya kyale zancen amma dai yayi min nasiha sosai da fada akan abinda na yi ba kyau kuma ya kamata in gyara halina. Ni kuma nace zan gyara, da haka muka yi sallama ya kama gabansa. Na dade ina tunanin abinda yakamata in yi.

Wannan karon ma lokacin tafiyata bai yi ba amma haka na tattara nawa ya nawa na nufi gida.

Kamar kullum wannan karon ma a zaune na same ta a falo ta caba ado tayi min tarba ta mutunci da karamci, kamar yadda ta saba ta kawo min komai da komai na abinci sai da na kammala ci na samu nutsuwa sannan ta tashi ta koma cikin daki. nasan ba zata fito ba don wannan shine sabuwar dabi’ar da ta daukarwa kanta saboda haka sai naje na sameta a zaune a gefen gado tayi tagumi. ba karamin mamaki tayi ba ganin na shigo na zauna a kusa da ita, abu na farko da ya soma fitowa a bakinta shine “Mukhtar ya sameka ko?

Nayi mamakin abinda ya fito daga bakinta don haka nace “Me yasa kikace haka?”

Ta saki jikinta cikin tattausan kalami tace “Nasan na kai kararka wajensa kuma naga har ka soma canjawa.”

Na so yin magana amma ganin bata yi shiru ba sai naci gaba da sauraronta “A’a gani nayi tunda aka kawo ni gidanka kake kyamata baka taba kusantata ba balle ka zauna a kusa dani sai yau.

Nayi murmushi kana nace “Lallai rashin sani yafi dare duhu” Ta dan kwanto a jikina a yayin da ta ci gaba da saurarona “Nasan za’a yi haka.”

“Me kake nufi da kasan za’a yi haka?”

“Nasan za kiyi min wannan zargin, kodayake kar mu tsaya wani dogon turanci gara in tafi kai tsaye in sanar da ke abinda nake tsammanin zai zamanto sanadiyyar rabuwarmu.”

Jin abinda na fada yasa ta zabura ta mike tsaye ta dafe kirjinta da hannu bibbiyu tana mai fadin “Haba don Allah laifin me nayi maka da har kake tunanin rabuwa dani haka da wuri?”

Na rike hannunta na zaunar da ita ina mai fadin “Kwantar da hankalinki, babu wani laifi da kika yi min….”

Ta dada marairecewa “To amma ban yi maka laifin komai ba kake tunanin rabuwa dani?”

Tausayinta ya dada kamani “In kin saurareni bayanin da nake shirin yi miki kenan.

“RUMASA’U” Na kira sunanta cikin wata murya mai ban tausayi wanda kowa yaji sai ya tausaya min, ita kuma jin yanayin yadda na ambaci sunan nata yasa ta dada marairewa wajen saurarena naci gaba da cewa “RUMY… ranar wanka ba’a boye cibi, yau zan cire miki kokonton kaunar da kike tunanin da wasa nake yi miki. a gurguje a takaice ba wani abu bane yasa kika ga bana son kusantar ki musamman a bangaren kwanciyar aure sai don bana son in cutar dake.”

“Kamar yaya cutar dani?”

“Abinda nake nufi anan shine ina tattare da lalurar da take abin kyama ga kowa da kowa ina tattare da lalurar da bai dace in yi kwanciyar aure da ke ba.”

Wani irin kallo tayi min wanda a zuciyata sai da na yi nadamar sanar da ita abinda na fada mata, cikin rashin fahimta tace dani “Ban gane abinda kake nufi ba.”

Ban yi magana ba sai na mike tsaye dam, naje na dauko takardar gwajin nan na cuta mai karya garkuwa ta wajena na mika mata nace “Duba wannan ki gani.”

Ina tsaye ta karba ta dan jujjuya takardar ta tambayeni “Wannan fa ta mecece?”

Bayani da fatar baki ba zai gamsar da ke ba don haka in kin duba takardar za ki fi gamsuwa fiye da yadda za ki ji daga bakina.”

Ba ta yi min gardama ba ta soma kokarin bude takardar ni kuma na juya na koma falo na zauna ina sauraron abinda zai biyo baya. Kusan minti shida ina zaune kaina a kasa ina kallon darduman falon, naji motsin shigowarta falon amma ban dago na dubeta ba. har tazo dab da ni ta russuna gami da dora gwiwar hannunta akan cinyoyina abinda banyi zato ba ko kadan babu alamun damuwa a tattare da ita, nayi matukar mamaki don ban taba tunanin zan ganta a haka ba sai nake hasashen ko bata fahimci abinda takardar ta kunsa bane don haka sai na tambayeta “Kin duba takardar nan kuwa”
“Kwarai na duba” Tace “Me ka gani?”

Maimakon in bata amsa sai na sake jefa mata wata tambayar “To in har kin duba me kika fahimta?”

Ta dada fadada murmushinta “Na duba kuma na fahimci cewa kana dauke da kwayoyin cuta mai karya garkuwar jiki.”

“Tabbas haka ne” Na dada tabbatar mata.

Kusan minti guda ba wanda yayi magana a tsakaninmu ina shirin mikewa tsaye ta dada zaunar dani tace “Ina zaka je?”

Nayi shiru ban bata amsa ba, ko da ta fahimci bani da niyyar magana sai taci gaba da cewa “To yanzu wanne mataki ka dauka ko kuma in ce wanne mataki zaka dauka?”

Na dada gyara zamana “Kin ga kuwa ni ba wannan tambayar na so kiyi min ba.”

“Wacce irin tambaya kayi tunanin zan yi maka?”

“Ni a tunanina zaki tambayeni ne yadda akayi na hadu da wannan lalurar.”

Ta soma rage fara’arta “Yi maka wannan tambayar yadda akayi ka hadu da cutar bashi da amfani a wajena domin ba shine maganin lalurar ba abinda ya faru ya riga ya faru sai dai a guji gaba” Ta danyi shiru “Yanzu so na ke yi ka sanar dani irin matakin da ka dauka.”

“Ban fahimceki ba.”

“Ina nufin wanne mataki ka dauka game da zama dani.”

“Eh to ni dai abinda na yanke shawara shine rabuwar mu.”

“Kamar yaya rabuwa.”

“Ina nufin in sauwake miki.”

“Kai da wa ka yanke wannan shawarar?”

“Ba da kowa na yanke wannan shawarar ba. hasalima dai ina tsammanin a duk fadin duniyar nan ke ce ta farko da ta soma sanin cewa ina dauke da wannan lalurar sai dai ko wanda suka yi min aiki.”

“To me yasa ka yanke wannan shawarar, koda yake bana bukatar wannan bayanin Abu guda daya kawai da zan iya sanar da kai yanzu shine zan iya zaunawa da kai a haka duk da wannan lalurar taka.”

Ta tashi daga tsugunnon da tayi ta dawo kusa dani ta zauna tana cewa “Abu guda daya da zai baka mamaki shine in ce maka na dade da sanin cewa kana dauke da wannan cutar.”

Mamaki ya fito karara a fuskata, taci gaba da cewa “Kar kayi mamakin yadda akayi nasan hakan, Ta yaya kake ganin zai yiwu su boye min cewa kana dauke da wannan lalurar bayan sun san tare muka je kuma mun je ne akan magana ta aure, ai da sun boye min to da basu san aikinsu ba kenan.”

Ni dai shiru nayi ina ta sauraronta kamar mai sauraron karatu “Kamar yadda baka ci amanata ba ka fito kiri kiri ka sanar dani duk da cewa na sani wanda kai baka san hakan ba, to saboda wannan halarcin da kayi min ni kuma na kudiri aniyyar da alkawarin zama da kai a bisa matsayin matarka har rai da ajali. Don haka ina fatan bazaka gujeni ba.”

******
Da kamar ace masu fama da lalura irin tawa suna samun kulawa kamar yadda na samu kulawa daga wajen Rumasau na tabbata da ba zasu shiga wani mummunan hali ba. Misalin da zan baka anan shine Rumasau ta kula dani tamkar yadda uwa take kulawa da jaririnta, hasalima dai da taimakon shawarwarinta ne na dage da karbar magani, wanda ba zaka taba ganina ba ka ce ina dauke da wata lalura.

A bangaren rayuwar aure kuwa abu guda daya ne ba ma yi wanda kaima kasan abinda nake nufi. Duk wani wasan mata da miji babu wanda ba mayi amma ban da abu guda daya wanda a hakan muke gamsar da junanmu. Mun kasance a haka har kusan shekara guda da rabi dai dai da dakika guda Rumy bata taba nuna min kosawarta ko gajiyawa ba a game da zamanmu kullum cikin rarrashina take gami da kokarin kwantar min da hankali.

Muna da shekara biyu da aure sakon Hajiya ya same ni ta bakin Mukhtar wai har yanzu babu labarin haihuwa a wajena abu kamar wasa abin har ya kai ga idan nayi ma Hajiya magana sai dai ta masa sama sama daga karshe ta bani zabin cewa ko dai in rabu da Rumasa’u tunda juya ce ba mace mai haihuwa bace ko kuma in karo wani auren. Babu daya daga cikin wannan zabin da zai samu shiga a wajena indai ina baukatar rufin asiri na. To ta yaya ma kake ganin za’a haihu tunda ba akai ga batun shigar ciki ba, Amma duk da haka don in batar da tunanin Hajiya daga kan wannan batun na haihuwa Cikin taimakon ubangiji sai na samu wata dabara naje asibiti na hada baki da wani likita ya rubuta min takarda cewa matsalar daga bangarena ne cewa nine bana haihuwa, Na je na samu Hajiya na kai mata daga nan hankalinta ya kwanta kuma ta yarda ta gamsu da bayanin likita tunda ta gani a rubuce. daga wannan lokacin bata sake tayar da duk wani zance makamancin wannan ba. Wanda ni ban sani ba ashe wannan din shine farkon shafin dagulewar rayuwata da ta Rumy.

Kada ka gajiya duk wannan ina yi maka shimfida ne na dalilin da yasa na ce ni ba zan iya rabuwa da Rumy ba.

Cikin hukuncin Ubangiji Tun daga wannan lokaci sai ya kasance cewa Hajiya tana kaunar Rumasa’u fiye da ni danta da ta haifa, ko kadan bata kaunar abinda zai sosa mata zuciya. Masu iya magana sunce wai tsakanin harshe da hakori ma ana sabawa balle dan adam, to a gaskiya mu namu ba haka bane domin ko kaffara bazan yi ba idan nace maka in ka cire satin farko na ‘yar matsalar da muka samu ni da ita to tun daga wannan lokacin har zuwa warhaka kusan shekaru biyu da wani abu to bamu taba batawa junanmu rai ba koda kuwa da kuskure ne ko rashin sani, ina matukar alfahari da hakan.

Bana mantawa wani lokaci munje asbiti ni da Rumasa’u ta yi min rakiya wajen karbar magani sai tace min itama tana son za’a sake aunata. na yi kokarin hanata amma tace min lallai sai an auna ta, ganin ta dage sai na ja ta gefe ina yi mata nasiha gami da cewa ni banga amfanin gwajin da za’a yi mata ba “Rumy in ban da abinki ai bamu yi abinda wannan lalurar zata shafe ki ba, don haka kawai ki hankura.”

Cikin kalami mai dadi da tausasa harshe tace “In banda abin maigidana wa ya fada maka cewa ta wannan hanyar kadai ake haduwa da wannan lalurar?”

“Ban gane manufarki ba.”

“Tabbas ba zaka gane ba yanzu amma ka bari in mun koma gida zan yi maka bayani.”

Akan dole na hankura na rakata aka yi mata gwaji sai ga sakamako ya nuna cewa tana dauke da cuta mai karya garkuwan jiki, Bamu bar asibitin ba sai da ita ma ta karbi magani gami da shawarwari kuma aka dorata akan layin magani.

Nayi iyakar kokarina don ganin kada ta fahimci halin damuwar da na samu kaina a sakamakon wannan bakon alamarin amma sai da ta fahimta.

A cikon kwana uku ne muna zaune bayan mun kammala cin abincin dare zan mike tsaye sai ta dakatar sani tana cewa “In baza ka damu ba ina da wata ‘yar magana da zan yi da kai.”

Na dawo na zauna ba tare da.nace komai ba ita kuma taci gaba da cewa “Na ga kamar ka shiga damuwa tun daga ranar da muka je asibiti ban san dalilin yin hakan ba.”

“Kema kin san dole ne in samu kain….”

“Nasan abu guda biyu kake tunani.” Ta datse ni. “Watakila ba zai wuce ace ta yaya na hadu da wannan lalurar ba, to na hadu da wannan matsalar ne ta hanyar hada abin yankan farce da muke yi, da kuma yin amfani da abu guda wajen goge baki wato Brush, sanin kanka ne nice nake yi maka yankan farce da reza kuma sau da dama zaka ga lokaci lokaci ina yanke ka jini yana zuba a duk lokacin da nake maka aikin to da gangan nake yin hakan kawai don nima in samu nawa rabon to yanzu na gode Allah bukata ta biya.
Na dade banyi magana ba kaina a sunkuye daga karahe ta tallabo kaina sai taga ina zubar da hawaye, da kyar nayi karfin hali na furta mata cewa “Amma gaskiya ban ji ba dadin wannan abin naki ba.

******
Ba ni da abin ya shafa ba da nake baka labari, hatta kai kanka da kake saurarona zaka yi tunanin cewa Hajiyata zata yi farin ciki da labarin da naje mata da shi na cewa Rumasa’u tana dauke da juna biyu dan watanni uku tabbas nasan wannan tunanin zaka yi amma ga mamakina sai naga Hajiya ta canja fuska. Sai da na gama kora mata bayani gaba daya cewa yanzu ma daga Asibiti muke sai ta ka da baki tace “Amma ka bani mamaki.”

Na sunkuyar da kaina wanda ni a tunanina cewa zata yi nayi rashin kunya da zan zo mata da wannan labarin da kaina, ashe ba haka bane ita abinda ke zuciyarta daban ne, ganin nayi shiru bance komai ba yasa ta samu damar ci gaba da maganganunta “Sai yau na tabbatar da akwai abinda yake damun kwakwalwarka” bance komai ba taci gaba da cewa “Koda yake ban san matakin da ka dauka ba.”

Kaina a kasa ba tare da na dago ba nace “Hajiya kiyi hankuri don har yanzu ban fahimci maganar da kike yi ba.”

“Zai yi wahala kuwa ka fahimta amma nan gaba zaka fahimta sai dai yanzu ina son in san ko wanne irin mataki ka dauka?”

Duk da cewa ban fahimci ainihin abinda take magana akai ba to haka na daure na bata amsa “Hajiya likita dai ya bamu shawarwari masu kyau.”

Yanayin fuskarta ya canja “To yanzu tana ina?”

“Tana gida.”

“Wanne gidan?”

“Gidana.”

“To yanzu wanne mataki ka dauka.” Ta sake maimaita tambayar farko

“Mataki kuma Hajiya.”

A halin sannan Hajiya ta soma fusata “Eh mataki, ina nufin matakin zama da ita matar taka, koda yake nasan har yanzu baka fahimci inda zance na ya dosa ba amma duk da haka abu guda daya da zan sanar da kai yanzu shine ba zanyi jika da dan shege ba.

Sai naji wani banbarakwai, Gabana yayi wani mummunan faduwa “Wanne irin dan shege kuma Hajiya?
“Ina nufin dan da ba’a san ubansa ba, don haka baka bukatar jin wani dogon bayani daga bakina” Tayi shiru a daidai lokacin da ta mike tsaye ta shiga daki ta barni a zaune har ta shige cikin dakin ban fahimci abinda take nufi ba, banyi tunanin fitowarta ba da wuri haka, amma ga mamakina sai naga ba da dadewa ba ta fito, sai naga ta nufo ni hannunta da wata takarda, bayan isowarta gareni sai ta cillo min takardar tana mai cewa “In kai ka mata ni ban manta ba, ko ka manta ne cewa kai ka kawo min wannan takardar cewa likita ne yace baza ka taba haihuwa ba?

<< Marigayiya 1

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×