Skip to content
Part 14 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

Kwance yake yana juyi. Maganganun Bilal ne suke mishi yawo, duk idan ya zauna haka kawai sai su dinga dawo mishi. Baisan me yasa Bilal din zai fada mishi su ba.

“Tuntuni ya kamata in maka magana Hamma, tun ranar farko da naga hannun Layla cikin naka ya kamata in tuna maka rashin dacewar haka, in tuna maka yanda tasowa gida daya a karkashin kulawar Abbu bai saka halaccin nan a tsakaninku ba. Ka daina tabata, idan kana son ta ne kayi wani abu a kai ta zama mallakin ka, amman ka daina…”

Bai amsa Bilal din ba sanda yayi mishi maganar, a cikin makaranta ne, shi yayi jarabawar safe, Bilal din kuma yana da ta azahar, haka ma Layla, baisan dalilin su na shigowa makarantar tun wajen sha biyu saura ba. Layla na karasowa wajen yaji ta riko mishi hannu ta baya, kusan rabin jikinta akan nashi, zai iya cewa ta rungume shine ta gefe.

“Hamma…”

Ta fadi cike da wani nishadi da baisan dalilin ta nayin shi ba. Kuma a gaban Bilal din ya bambareta daga jikin shi. Ba zai manta da hawaye tabar wajen ba. Bai tuna rana daya da ya cewa Bilal shi yana son Layla ba, maganar ma wata irin dirar mikiya tayi mishi, tana hautsina wani abu a tare da shi da baisan yana a nutse ba. Yana zaman shi lafiya, yana lallaba rashin natsuwar da yake fama da ita a duk rana, Bilal yazo ya kara mishi wani tunani na daban. Ya saka shi yana neman ma’anar alakar da take tsakanin shi da Layla. Bai saba yawan magana ba, rabin da kwata na maganar da yakeyi a rayuwar shi tsakanin shi da kan shine, a iya tunanin shi maganganun suke makalewa.

Kuma bai saba yiwa kan shi karya ba, yasan yanda yake jin Layla da ban da yanda yake jin su Rukayya, da sai yace ita din matsayin kanwa take a wajen shi. Duk da a ranar ne maganganun Bilal suka saka shi tantance hakan. Shi baice yana son ta ba, bai taba tunanin wata soyayya ba, bayajin yana da natsuwar janyo wata duniyar shi da take a hargitse. Me yasa ma Bilal din zai hargitsa mishi lissafi har haka, yanzun yana saka duk lokacin da jikin Layla zai hadu da nashi sai yaji wani irin tashin hankali na daban. Ya kuma rasa ta inda zai fara hanata rike shi ko da shi bai kokarin riketa ba.

Musamman idan Bilal din yana wajen, sai ya kasa hada idanuwa da shi, akwai tarin abubuwa da Bilal yake nuna mishi bai kamata ba, amman yawancin su tun kafin ya fadi ya rigada ya sani, baisan yanda zai ya bari bane ba. Yawan hada jiki da Layla na daya daga cikin abin da ya kasa gano rashin dacewar shi sai da Bilal din ya tunasar da shi, sai dai kamar ko daa yaushe, ya kara kasancewa cikin jerin abinda baisan ta inda zai bari ba. Bilal ya sake mishi magana jiya, shine magana ta biyu akan abu daya

“Nace maka idan son ta kakeyi kayi wani abu a kai ba zaka saurareni ba wannan karin ma ko?”

Batare da ya daga kai ya kalli Bilal din ba ya amsa da,

“Ni bance maka son ta nake yi ba.”

Kai Bilal ya jinjina yana furta, “Yayi kyau.”

Rayyan zai karya idan yace abin baya damun shi, gabaki daya komai ya kara jagule mishi. Shisa jiya yana gama jarabawar shi ya fita daga cikin makarantar bai jira Bilal ko Layla ba. Amman da tunanin ta cike da kan shi ya kwana, yau ma yana gama jarabawa ya gudo gida. Ya san za taita neman shi. Yana ma iya ganinta tazo gidan. Ko motsi yaji cikin gidan sai ya lumshe idanuwan shi yana jiran yaji shigowar ta, har bayan azahar, ko abinci ma ya kasa ci. Har zane ya fara, amman ya kasa samun natsuwa, mikewa yayi ya dauki riga ya saka a jikin shi, dan ya cire yabar singlet ne sanda ya dawo sallar azahar.

Alwala yayi tun daga gida, saboda kar lokacin sallah ya kama shi a inda ba zai samu ruwan leda da zai alwala ba, ba shi bane zai saka ruwa a butar da baisan rabonta da wanki ba ya kuskura bakin shi, ya kuma wanke fuskar shi ya dauki wasu cutukan. Mikar hanyar da zata hada shi da makarantar su yayi, sanda ya shiga kuwa ana kiran sallar la’asar. Dan haka ya wuce masallaci ya gabatar da sallah yana fitowa, hanyar department din su Layla ya tsinci kan shi da nufa. Yasan ta fito daga jarabawa, tun daga nesa kuwa ya hangota da wasu riga da wando da sukayi mishi kama dana kasar indiyawa, sai dai tsakar rigar har kugunta, ya nade kanta da mayafin da ya rufe iya wuyanta.

Dariya takeyi da alama, su hudune a tsaye. Ita da kawarta da har yanzun bai san sunanta ba, Anisa kawai ya sani a duk tarkacen kawayen Layla da bata rabuwa da yawo da su a cikin makaranta. Itama dan dakin su daya da Laylar, sam baka raba bakinta da kiran Anisa. Wani irin zafi yaji kirjin shi ya dauka ganin daya daga cikin samarin ya rankwafa kusan saitin kunnen Layla yayi mata maganar da tasa ta kwashewa da wata irin dariya. Daga yanayin yaron duk da bai karasa ba, yasan da wahalar gaske ya wuce sa’an Layla din. Shisa zafin kirjin shi ya karu, bai ga dalilin da zaisa ta dinga dariya da yan yara kananu haka ba.

Har tuntube yake duk da babu wasu duwatsu a hanyar

“Layla!”

Ya kira daga nesa kafin ya karasa, muryar shi dauke da kashedi da wani irin yanayi da ba zai fassaru ba duk a tattare, ita ma Layla juyawa tayi tana hango Rayyan din, akwai wani abu tattare da fuskar shi da yake sanar mata da wahala bai dauketa da mari ba inya karaso, duk da hannun shi kan sauka jikinta da tayi laifi da batayi ba, wannan karin dai tana ganin tayi laifin ne amman bata san kona meye ba, ga kafafuwan ta kamar an dasa su a wajen. Da niyyar zuwa gidansu da sun gama labarin da sukeyi take tsaye a wajen.

Saboda bata gan shi ba, jiya da ta kira wayar shi bai dauka ba, ta kira Bilal dan ya ba shi, yana karba yace,

“Ba kin kira ban dauka ba? Meye?”

Can kasan makoshi ta amsa shi da,

“Ba komai.”

Kashe wayar yayi a kunnenta, abin ya mata zafi, ta kirane taji lafiyar shi tunda taje neman shi har ajin su bata gan shi ba. Ya hanata magana da kowa a cikin ajin, shisa bata tambaya ba, wanda suka gwada mata magana ma bata amsa su ba ta wuce abinta. Sai dai ya bata mata rai kamar ko da yaushe da yanayin yanda ya balbaleta da fada dan ta kira shi, babu kalar abinda bata fada ba kafin bacci ya dauketa, na yanda zai sani, yanda ba zata kara neman shi ba, itama tayi fushi, amman tana tashi da safe bayan tayi sallar asuba wayar shi ta fara nema taji a kashe.

“Ka huta ai, kawa kanka Hamma.”

Ta furta tana jin babu dadi a ranta, har suka shiga jarabawa tana gwada kiran shi amman wayar a rufe take jinta. Ta kira Bilal yace mata yana makaranta, idan ya gama jarabawa shima zai zo ya dubata. Rayyan na karasowa abokanta da suke tsaye ya fara tsarewa da idanuwa yana musu wani irin kallo kamar zai rufe su da duka, yaran ko sallama basu tsaya yiwa Layla ba suka kama hanya suna wuce wa.

“Ina wuni…”

Yarinyar da take kokarin labewa kusa da Layla ta furta cikin siririyar murya, itama idanuwan Rayyan ya kafeta dasu, tana sadda kanta kasa ta juya tabi bayan sauran.

“Hamma…”

Layla ta kira tana son tambayar shi dalilin da duk zai kokarar mata abokai haka, amman yanayin fuskar shi ta hanata furta komai.

“Layla”

Wani saurayi daya zo wucewa ya kira da murmushi a fuskar shi yana dorawa da

“Ya jarabawar?”

Murmushin karfin hali tayi mishi, zatai magana Rayyan ya damqi hannunta yana kallon saurayin

“Bata son magana da kai.”

Ya fadi yanajin wutar da take kirjin shi tana karuwa. Murmushin shi saurayin ya fadada yana wucewa batare da yace komai ba

“Uban kowa kulawa kikeyi? Bakya jin magana ko Layla?”

Kai ta girgiza mishi tana kokarin kwace hannunta da take ji ya rike shi kamar zai tsage mata kashi, kamar hakan yaji ya saki hannun nata yana kamo kunnenta guda daya yana sakata fadin,

“Wayyoo Allah na Hamma…zaka tsigemun kunne… Hamma dan Allah.”

Ta karasa muryarta na karyewa, sake murda kunnen ta yayi yana mangare mata kai, dai-dai lokacin da idanuwanta suka sauka cikin nashi tun karasowar shi wajen, saboda ya dade da koyon kallon fuskar ta batare da idanuwanta sun hadu ba, kwalli ta saka da eyeliner da yasa idanuwan nata kara gudun bugun da zuciyar shi takeyi.

“Bar nan, mayya kawai.”

Ya fadi yana sauke idanuwan shi daga cikin nata, idanuwan Layla cike taf da hawaye ta raba shi, tana kasa yiwa Bilal da yake tsaye bayan Rayyan din magana saboda kukan da yake shirin kwace mata. Shima baice mata komai ba, kusan ya riga Rayyan karasowa department din su Layla din, ya tsaya gaisawa da wani abokin shine daya kwana biyu basu hadu ba, akan idanuwan shi komai kuma ya faru. Sai da tabar wajen sannan yace,

“Ka kori wanda suke tare, ka kuma kore ta itama”

Juyawa Rayyan din yayi yana kallon Bilal.

“Bana son ganin ta da wasu.”

Yana dorawa da.

“Kuma ba kullum nake son ta a kusa da ni ba.”

Rayyan ya karasa maganar kirjin shi na zafi har lokacin, juyawa yayi yana bin bayan Layla da sauri. Bilal ya bishi da kallo yana ganin Ikon Allah, da dan gudu ya hada har ya taddo Layla da ya kama hannunta tana fisgewa, sake kamata yayi yana yin gaba ya soma janta. Zuwa wannan lokacin Bilal kuma baisan kalar tunanin daya kamata yayi ba. Abu daya yake ganewa a halin yanzun, yanda zuciyar shi take zafi kamar zata fito daga kirjin shi. Kiri-kiri yake ganin shakuwar da soyayya mai zafi ce zata haifar a tsakanin Rayyan din da Layla amman Rayyan ya karyata.

Bilal ya rasa wa Rayyan yake kokarin karyatawa, kan shi, shi din, ko kuma soyayyar da take tsakanin su da alamu suka nuna basu da iko da ita. Lumshe idanuwan shi Bilal yayi yana sauke wata irin ajiyar zuciya. Yana bukatar Aisha a irin lokacin nan, idan tayi mishi hirarta zuciyar shi zatayi sanyi ya sani. Yau kanta ciwo yake yi, dan sai da ya fara rakata kofar hostel tukunna, tace mishi zata kwanta. Idan ya kirata ba zataki dagawa ba, idan kuma yace yana son suyi magana ma ba zata ki fitowa ba. Zai zamana mai son kan shi da yawa, hakan ya saka shi tafiya kawai.

Motar da Abbu ya basu ta zamana kamar horo yanzun. Kiri-kiri abokai suka durfafeta, sai a tafi yawo a kone man ba za’a zuba wani ba, ga yanda Bilal yaga suna wujijjigata tunda basu san ciwonta ba, shisa ya kira Abbu yaji ko akwai inda zai iya zuwa ya ajiye motar, duk idan bukatar amfani da ita ya tashi sai yaje ya dauko. Akwai abokin Abbu din anan Zaria, kuma da yake Samaru ne, sai babu nisa. Can din ya kaita ya ajiye. Rayyan bai ko tambaye shi ina motar take ba, tunda ko kafin ya kai haka yakan shirya ya taka zuwa makaranta. Sam abin hawa bawai ya dame shi bane ba.

Yanke hukunci tare machine yayi zuwa gida, ya hango kamar Rayyan tsaye ta wajen gate, karasawa Bilal yayi.

“Hamma…”

Ya kira, a gajiye Rayyan ya kalle shi.

“Ina ta jiran ka tun dazun.”

Ya kamata ace ya daina mamakin halayen Rayya.

“Ni kake jira?”

Kai Rayyan ya daga mishi da ya saka shi jan numfashi.

“Da ban biyo ta nan ba fa? Na samu machine daga cikin makaranta? Sai kayi ta jira anan din? Me yasa baka kira wayata ba?”

Kafadh Rayyan ya daga mishi kawai, bayason wata doguwar magana. Wayar shi baisan caji ya kare ba sai dazun, kuma ya ajiye a gidane. Ba wasu masu kiran shi yake da ba, amfanin wayar kalilan ne a wajen shi. Juyawa yayi ya fara tafiya, Bilal na bin shi suka jera suna fita daga cikin makarantar. Hannu ya saka a aljihu ya dauko kwalin sigarin shi.

“Dan girman Allah Hamma kar ka sha, idan baka kokarin ragewa ba zaka iya daina wa ba sam.”

Bilal ya fadi, yana kallon yanda lokaci yasa labban Rayyan har sun fara duhu saboda hayakin da yake bukama cikin shi, yau ma tunda sassafe da sigarin ya karya. Allah ne shaidar Bilal har a sallah yanzun addu’ar barin shan yake wa Rayyan. Kara daya ya zaro yana sakawa a bakin shi kafin ya mayar da kwalin aljihun shi, ya dauko lighter ya kunna. Sai da ya zuqa ya fitar da hayakin sannan yace

“Ka barni Bilal, bana jin dadi.”

Numfashi Bilal ya fitar.

“Sai aka ce sigari ce jin dadin?”

Kara sauri Rayyan yayi yana cigaba da zukar sigarin cike da kwarewa.

“Allah ya kyauta.”

Cewar Bilal da zuciyar shi take kara yin zafi. Kafin su kai gida sai da Rayyan din ya sha kara hudu na sigarin. Shayi suka sha da cin cin din da Layla ta kawo musu. Bilal na daukar takardun shi ya fice daga dakin dan karatu zai koma cikin makaranta yayi, tsallaken kwana daya yake da shi kafin jarabawar shi da ita kadai ta rage a zangon. Rayyan kwanciya yayi yana runtsa idanuwan shi da suka fara nauyi da alamun bacci, duk da yamma tayi. Idan baccin ya kwace mishi yasan sai dai wani ikon Allah zai samu ya runtsa da dare. Kuma kwakwalwar shi na bukatar hutun. Akwai tarin abubuwan da yake bukatar saka mata na jarabawar shi ta gaba.

A hankali bacci ya dauke shi da mafarkin Layla kwance a gefen shi da baisan dalilin da yasa ta kutso mishi cikin mafarki ba. Duk da yana wata duniya daban bai hana shi furta.

“Mayya…”

Cikin kan shi a duniyar ba.

*****

Rayyan suka tsaya jira su dukkan su, shine karshen gama jarabawa, duk sun riga shi. Aisha ma da aka kirata a gidan su dan azo daukarta ca tayi musu zasu taho tare da su Bilal, da yake babu wanda bai san shi ba a gidan, babu kuma wanda bai aminta da shi ba sai suka amince. Ran safiyar asabar duka suka shirya. Bilal yaje ya dauko motar daga gidan abokin Abbu, dan ran juma’a yaje yakai an duba lafiyarta ya kuma zuba mai. Daga gida da suka dauki kayan su makaranta Bilal ya nufa. Yana kallon Rayyan daya bude gidan baya ya zauna, baice mishi komai ba.

Dan tun jiya rabon da suyi magana, daya gaishe shi da safen nan kai kawai ya daga mishi, yan shiru-shirun sunzo fiye da kowanne lokaci, yakan dade Bilal bai gan shi a yanayin nan ba. Yasan ko me zai fada asarar bakin shi zaiyi, ba amsa zai samu ba. Abinda bai sani ba shine rabon Rayyan da ko gyangyadi kwana biyu cur, baccin ranar daya kan samu ya neme shi ya rasa. Duniyar a cunkushe yake jinta. Ga shi jiya ma bai samu ya ga Layla ba sam-sam. Ta zo ma gidan nasu da bata gan shi ba jiya batayi ba, ya sa ran zai ganta.

Watakila fushi take yi mishi tun shekaranjiya, ba zai iya tuna kan me yai balbaleta da fada ba, fadan kawai yake iya tunawa. Har waya da safen nan ya dauka da niyyar kiranta yaji ko ta gama shiryawa sai kuma ya fasa. Zai ganta babu jimawa, a bakin kofar hostel kuwa suka same su ita da Aisha suna ta hira. Bilal ya fita ya saka jakunkunan su a bayan mota. Aisha tsaye tayi cikin rashin sanin inda ya kamata ta shiga ta zauna ganin Rayyan din a baya, ta dauka ita da Layla ne zasu zauna a gaba. Layla ta samar mata mafita da ta bude bayan motar tana shiga. Hakan ya sata bude gidan gaba ta zauna, Bilal ma ya shigo yaja motar.

Sun gaisa dashi da safe, kara gaishe da shi Aisha tayi tana juyawa tace

“Hamma ina kwana.”

Kai kawai Rayyan ya daga mata, da yake ta fahimci halin miskilancin shi da mutane da yawa zasu iya dauka wulakanci sai ta juya kawai. Layla kallon shi tayi, yayi kyau sosai sosai cikin farin yadi da ya saka. Yau harda hula, bawai baya saka manyan kaya bane kwata-kwata, yakan dai kwana biyu bai saka ba. Ga dinkin rigar dogon hannune mai links, ta kasa daina kallon shi, kyau yayi mata yau fiye da kowanne lokaci, zuciyarta har wani kumbura take da tarin soyayyar shi da batasan yawan ta ba. Amman inda take Rayyan bai kalla ba, asalima kan shi ya jingina da kujerar motar yana lumshe idanuwan shi.

“Hamma…”

Ta kira, muryarta iya kunnuwan shi, jiya fushin da ta kwana tana yi mishi bai yini ba, son ganin shi ya danne mata komai. Yanayin da har ya saka tunanin ko da gaske ne? Maitar da Mami take karyata cewa ta gada ta bangaren mahaifiyar ta, duk da zuwa yanzun shi kadai dinne yake kiranta da,

“Mayya…”

Saboda idan har da gaske bata kasance mayya ba ya kamata ace zuciyarta ta hakure da shi, ya kamata ta sama musu sauki su duka biyun, sai dai kamar yanda batasan lokacin da ta fara son shi ba, haka bata san ta inda zata fara dai nawa ba. Idan ma yaji bai nuna mata alamar hakan ba, son jin muryar shi takeyi da dukkan zuciyarta.

“Hamma.”

Ta sake furtawa, tana dan kallon su Bilal, hira suke sosai, da alama hankulan su baya kanta. Sake kallon Rayyan da bai motsa ba har lokacin tayi, tun kiran farko da tayi mishi yaji ta, asalima tun daga nesa ya hango ta, ta saka material ruwan toka, sai farin mayafi, yau idanuwanta ya fara hangowa zuciyar shi na tsinkewa, sai dai yana dauke idanuwan shi daga kallon nata ya mayar dasu kan yanda tayi kyau sosai, sai yaji yanayin daya kwana biyu baiji ba, riketa yake so yayi, wani kusanci yake son samu da ita komin kankantar shi. A kwanakin nan biyu da yayi su a hargitse ganinta ya saka shi jin kamar daya riketa koyayane wani abu zai natsa mishi.

Da kyar ya raba idanuwan shi daga kanta yana kallon Bilal da suka hada ido ta mudubin gaban motar, kai Bilal din ya girgiza mishi a hankali, kamar yana san abinda yake tunani, kamar yana son fada mishi karya fara aiwatarwa. Wani irin yanayi zuciyar shi ta shiga lokaci daya, idanuwan shi a bude suke, kuma safiya ce, baisan me yasa yake ganin duhu ba. Tana zagayo ta shigo ya zabi ya rufe idanuwan shi, har wani dumi jikin shi yake dauka da son rike ko da hannunta ne. Ya rasa kalar sabon da yayi haka da haduwar da jikin su yake yawan yi.

Jin Layla tayi shiru yasa shi kara runtsa idanuwan shi yana kokarin fitar da numfashi a tsanake, ba lokaci yake gani ba, banda sautin karar mota da yake nuna alamar sun dauki hanya babu abinda yake ji, sai numfashin Layla da baisan ya akayi kunnuwan shi suka tsinto mishi shi ba. Kusan yanajin bugun zuciyar ta ta hakan. Kafin yaji dumin hannunta cikin nashi da yake akan kafar shi. Kamar hannun na da ikon kan shi na budewa ta saka yatsunta a ciki tana dumtsawa, yanayin da yaji har kasan zuciyar shi

“Nagode…”

Ya furta a hankali yana kara dumtsa hannunta, saurin kallon fuskar shi tayi, sai taji kamar godiya yayi mata, amman bata ga alamar ya motsa komai a fuskar shi ba. Da badan wasa da yake da hannunta da ta saka a cikin na shi ba sai ta iya rantsewa da cewar bacci yakeyi. Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, tana jin kamar yau akwai abinda yake damun shi fiye da kullum, watakila kuma tunaninta ne kawai. Aisha bacci tayi dan ita sai dai in iskar mota bata fara kadata ba. Ta mudubi Bilal yake kallon su, da alama Rayyan ma bacci yakeyi, Layla kuma ta kwanta a kujerar ne tana fuskantar shi, idanuwanta akan shi kamar a duka duniya babu wani abu da ya taba daukar hankalinta irin Rayyan din yana bacci.

Yanayine da ya sa na wasu dakika Bilal ya manta da tuqi yakeyi saboda zafin da kirjin shi ya dauka. Yana kallo Layla ta daga hannunta da nufin taba fuskar Rayyan din, duk daukarta bacci yake, kamar zare ta gani a gefen fuskar tashi kan kasumbar da ta sha gyara, lokacin da yai saurin damkar hannunta da dayan hannun shi, lokacin kuma da Bilal ya taka motar yana kaucewa karawa wata mota da ta ke tahowa, ba Rayyan ba hatta Aisha sai da ta bude idanuwanta tana fadin,

“Subhanallah…”

Shima Bilal din duk wata addu’a da tazo bakin shi yi yake. Sun kusan mintina biyu kafin ya samu natsuwa dan ya rage gudun motar sosai. Rayyan kuma hannun Layla daya damqa ya saki yana kokarin saka idanuwan shi cikin nata duk da yanda zuciyar shi tayi wata irin dokawa.

“La hawla wala quwwata ila billah.”

Ya furta a cikin kan shi ganin kamar ya hada idanuwa da mage, kwayar ce kawai da ta Layla take a zagaye, ta mage kuma a tsaye. Dan runtsa idanuwan shi yayi, yana komawa cikin kujerar ya kwanta yana bata damar sauke nata, tana kula da yanda ba kullum yake kallon cikin idanuwanta ba. Kamar yasan duk idan yayi sai taji wani abu yana fisgarta a cikin su kamar igiyar ruwa. Bata da wasu kalamai da zasu fassara asalin yanda take ji duk idan ya kalleta, ta sha kallon mutane sun nitse a cikin ruwa a fina-finai daban-daban, takan kuma ji a labaran yau da kullum. Bata taba hasaso yanda yanayin yake ba sai lokacin farko da ta fara mallakar hankalinta, lokacin da Rayyan ya saka idanuwan shi a cikin nata.

Sai taji ta tsundum cikin ruwan da batasan da bata ganin farkon shi balle karshen shi, take numfashi ya soma mata barazana, yau ma hakan take ji, dan har bakinta ta dan bude tana fitar da iska daga cikin shi. Zuu din wayarta ya dan taimaka mata sosai, da alama sun dan sake shiga wajen da network ya dawo, dan daga fuskar wayar tayi tana saurin mayar da ita ta kife, ta kalli Rayyan taga ya mayar da kan shi, idanuwan shi a rufe suke kuma, duk da haka zuciyarta kamar zata fito saboda bugun da ta kara, sakonnin duka daga group din.

“Sirrin ma’aurata zalla.”

Yake fitowa, group din da tun tana hangen su Nanaa da kawayenta sun tattaru a ajinsu ana shewa ana kus-kus a kai cikin yanayin da yai bala’in jan hankalinta har ta fara lekasu, ba sai an gaya mata ba, tasan su Nana sun girmeta, kamar basuyi nasarar da tayi ta samun makaranta da wuri ba. Da yake sun jima suna son yin magana da ita tana sha musu kamshi dan yanayin wayewar su baiyi dai-dai da ra’ayinta ba, har group din ya zama sanadin da take kula su. Ranar da aka sakata wuni tayi da waya a cikin aljihun wando, sai take ganin duk wani sako da yake shigowa ta manhajar WhatsApp dinta kamar wani na kallon ta, kamar wani na kallon kalar abinda take gani take kuma karantawa da bai kamata tayi ba.

Rannan da Ainau Mardiyya da suke kusa da dakin su sanda ta shiga ayi mata kitso suna hirar waya sai taji kamar da ita Ainau take, kasancewarta daliba itama yar aji hudu, sauran yan dakin nasu ma duk yan aji hudune, a cikin su kuma Dina ce takan mata kitso, wata yar asalin garin Kaduna yaren bajju, taji Hausa kamar bahaushiya. Hirar illar wayar da tafi amfaninta yawa a zamanin sukeyi, Ainau na fadin

“Yanzun fa zamani yazo da kana iya kokarin ka akan tarbiyar yaranka, kana tsaye ba dare ba rana, da addu’a dan neman kariyar abinda baka gani wayar hannu na warware maka tufka.”

Dayar yar dakin su Ainau din Kamila na karbe zancen da,

“Wallahi, abin da tsoro, idan baka kai zuciya nesa ba, waya tsaf zata zama halakar ka, ka hana yara waya wani katon banza ya yaudare su da kwadaita musu ita a waje…”

Tabe baki Dina da takewa Layla kitson tayi.

“Idan ka basu ma ba tsira kayi ba, kinsan wani group dana gani kwanaki kuwa? Hankalina yayi bala’in tashi, a wayar Gift kanwata nagani…nasa Maman mu ta karbe, amman naki nutsuwa.”

Sosai Layla ta takura, tanajin kamar da ita suke, kamar wata ta leka wayarta taga abinda yake faruwa, taga tarin labaran da bata taba cin karo da abinda ya girgiza duniyarta yana rike tunaninta irin kalar labaran ba, abinda take hasashe ne ake nuna mata yanda yake faruwa cikin yanayin da bata taba hangowa ba, ita kuma Allah yayita cikin jerin mutane masu bin kwakkwafi, dole tana sauka gida zata fadama Naana zata fita daga group din idan sun koma makaranta sai a mayar da ita, saboda Mami na da kula, Mami na kuma da bincike, kuma a karo na farko zuciyarta a tsorace take da Mami taga wannan group din.

Rayyan daya kara dumtsa hannunta yana murza yatsunta ya yanke mata tunaninta dan yanayine da taji har tsakiyar kwanyarta, sai yake tuna mata daya daga cikin labaran da ake tattaunawa a kai jiya a group din, wani abu daya tsaya mata a makoshi ta hadiye tana jin wani irin yanayi da bata da fassarar shi yana saukar mata. A haka suka shiga garin Kano, tana jinta sama-sama. Aisha suka fara saukewa suna wucewa gida. Sanda suka sauka, kafafuwanta babu kwari take jinsu, Rayyan kuma bai jirata ba ya shige gida, hada idanuwa tayi da Bilal da yake binta da kallo cikin wani sanyin yanayi kamar yana son karantarta har zuci.

“Ka sha maganin ciwon kai.”

Ta fadi tana wuce shi, launin idanuwan shi sun canza, shisa ta gane kan shine yake ciwo. Barin shi tayi a tsaye kamar batayi komai ba, kamar bata taba zuciyar shi ba. Tun da ya tashi yake dan jin ciwon kan, amman ita da Rayyan ne suka kara mishi wani sabon ciwon kan, ta kula kamar ko da yaushe, ta kuma gane kan shi yana ciwo. Numfashi yaja yana fitarwa kan shi kamar zai bude, cikin gida ya shige shima, sun fitar da jakunkunan daga baya.

<< Martabarmu 13Martabarmu 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×