Skip to content
Part 29 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

Tayi kuka fiye da wanda tayi na rasuwar Bilal, kukan da bata tabayin kalar shi a tsayin zaman duniyarta ba. Saboda akwai banbanci a kuka na rashi, akwai kuma banbanci a kukan sanin cewa kaine da laifi a wannan rashin, kuka ne tayi na dana sani kan abubuwa da dama. Yanda duk zata so raba nata laifin da Dije da kuma Gwaggo da suka dorata akan bin Malamai ta kasa, sosai take so ta boye bayan ko da kuruciya ce dan samun sauki. Amman da hankalin ta lokacin, ko da kuwa da shekaru za ayi amfani wajen auna hakan, balle kuma zaman gidan miji da kuma yawan yara.

Ba abokai nagari da zatayi shawara da su bane ta rasa a lokacin, da ta dora kacokan laifin akan su Hajiya Dije. Tana zagaye da yan uwanta da suke matukar kaunarta. Yan uwan da ta gujewa saboda suna gaya mata gaskiyar da bataji. Sai ta dinga ganin kamar babu kaunar nan da tayi tunanin akwaita a tsakanin su. Da sun fada mata abinda take son ji kamar yanda su Gwaggo suka dingayi. Yanzun ne da hankalinta ya dawo jikinta take tunani kala-kala. Ko da asiri Mami tayi ta aure Abbu ba zai zama dalilin da itama zata ce ta fara shiga Malamai ba, wannan ba uzuri bane ba sam.

Balle da idanuwanta bata shaida hakan ba, Gwaggo ta fara kawo mata wannan tunanin. Kuma ta hau ta zauna saboda yayi dai-dai da abinda take son ji. Akwai tarin son zuciya a abinda tayi. Yanzun tunanin cutar da Haris ko da yaya ne sai da ya sa kanta sarawa saboda tarin kaunar da takeyi mishi. A baya idanuwanta ya rufe da soyayyar da taga Abbu yana nuna mishi, tana manta lokacin tata kuruciyar da girma, da kuma yanda kaf kowa yake maganar kusancin da take da shi da nata baban. Bata kuma duba kalar kusancin da take da shi da Bilal ba, da yanda duka yaranta sukan ce tafi son Bilal akan su.

Tunani ne kala-kala yake mata yawo yanzun. Son zuciya ya kaita ya barota, abinda taso da dan wani sai Allah ya juya shi kan nata yaron, ko ma tace nata yaran. Tana ta takamar tana kula da abinda yake faruwa da su, sai ta kasa fahimtar a baudadden halayya irin na Rayyan akwai tarin abubuwan da yake fuskanta. Balle kuma ta kalli Bilal da kullum take dorawa nauyin kula da Rayyan din. Sai ta maida hankalinta wajen raba abinda kaddara ta rigada ta gama rubutawa, a karo na babu adadi tayi kokarin cutar da Layla. Da yake kaddara na biye da su sai gata da cikin Bilal ta hanyar da Ayya zatayi komai da zata iya dan kaucema faruwar hakan.

Yanzun da take wannan tunanin sai abin ya kara tsoratata, saboda tana jin yanda cikin jikin Layla ne kwai daya da Bilal yake da rabon samu a duniya. Kwan da bata damu da hanyar da ya samun ba in dai zai taka duniya ta rike shi a cikin hannuwanta. Har cikin zuciyarta take jin son abinda yake cikin Layla din. A gefe daya kuma tana tunanin da idanuwan da zata kalli Rayyan yanzun. Zata so ta fada mishi da ita ya kamata ya raba laifin da yake jin ya mishi nauyi. Amman hakan ma ba mafita bane a hargitsin da yake ciki. Idan ta gaya mishi zata kara rikita shi, amman tana bukatar yafiyar shi, duk da take mahaifiyar shi wannan hakkine mai girman gaske.

Balle kuma yanzun ta kula da Rayyan din ya samu lafiya. Saboda kalar kusancin da yake tsakanin su a yan kwanakin nan, ba zata kara jefa shi cikin hargitsi ba. Zata fara da dai-dai ta tsakanin ta da Ubangijin ta da farko, sauran zasu fi zuwar mata da sauki, zata roki Allah da ya saka sauran lamurran zuwa mata cikin sauki. Tana nan zaune a daki taji an kwankwasa, sai da ta share hawayenta sannan ta amsa, ta dauka ma Rukayya ce, sai taga Rayyan ne, yanda ya fara sauko rabin fuskar shi yana sakata runtsa idanuwan ta kafin ta sake bude su akan shi, dan yayi mata kamar Bilal, manya kayane a jikin shi farare kal sai hula ruwan omo mai cizawa.

“Ayya yanzun zan wuce, Bappa ya karaso.”

Numfashi ta sauke tana kallon shi.

“Har kana da natsuwar komawa?”

Tayi tambayar a sanyaye, kafadu Rayyan ya dan daga mata. Idan ma bashi da natsuwar komawa ba zai zauna ya jirata ba. Tunda bashi da tabbacin ranar zuwanta ko zata zo din. Komawar shi yafi mishi, ko bakomai zai samu abin yi banda zama cikin dakin su yana duba hanya kamar zai ga shigowar Bilal kowanne lokaci.

“Zai ragemun tunani, idan na koma din”

Kai ta jinjina mishi, wani irin yanayi take ji a zuciyarta da ba zai misaltu ba.

“Kayi wa Abbun ka sallama?”

A hankali ya girgiza mata kai, ya shiga dakin Abbun ya samu harya fita. Yana yawan shiga yanzun, saboda yana rage mishi zafin da yake ji a zuciyar shi, ba wai suna hira bane ba. Yanzun ya san rashin son surutu halin shine, kawai yanajin dadin yanda yake iya zama waje daya da Abbu din batare da yaji iskar dakin tayi mishi kadan ba. Idan labarai Abbu yake kallo zasu kalla tare, har sai ya gaji da zaman sannan yake tashi yayiwa Abbu sallama ya koma nasu dakin. Jiyama a dakin Abbu suka ci abincin dare tare, abinda bai tabayi ba a iya yanda zai iya tunawa.

Yaji dadin abin saboda shine abu na farko da ya saka a cikin shi duk tsayin jiya. Yana daki yana kukan da ya kasa tsayawarwa sai da ya tsaya da kan shi. Ya fadama Abbu cewa yau zai tafi, amman basuyi sallama ba yau din.

“Ya tafi sanda na shiga. Zan kira shi a waya…”

Ya furta a hankali yana juyawa.

“Allah ya tsare ya bada sa’a. Ka kula da kanka.”

Hannun kofar da yake rike da ita ya murza sosai, addu’ar Ayya na nutsar da wani abu cikin kan shi, sai da ya hadiye yawi sannan ya amsa da,

“Amin thumma amin.”

Harya bude kofar yana shirin fita ta kira sunan shi, dan juyawa ya yi.

“Idan na kiraka ka daga Rayyan.”

Kai ya jinjina mata yana ficewa, duk da wani abu a tare da shi na fada mishi ya bata hakuri, da duk lokuttan da ta kira shi yana kallo bai daga ba, ba laifin shi bane ba, a lokacin yanajin magana da ita takura ne, shisa yakan zabi yaki dagawa. Amman abinda yake saka shi kuka yanzun ya kula bashi da wahala. Shisa ya zabi yin shiru, hakurin da zai bata zaiyi shi ta hanyar kiran wayarta kafin ita ta kira shi. Da wannan tunanin ya fice daga dakin, yana nufar dakin Mami da ya dade a tsaye bakin kofa yana tunanin shiga.

Wani numfashi yaja mai nauyi yana fitarwa kafin ya shiga dakin da sallama yana cire takalman shi daga bakin kofa ganin Mami zaune a falon, amsawa tayi tana dorawa da,

“Rayyan…”

Bata hadu da shi ba tun ranar rasuwar Bilal, bata ma fita ba saboda dalilai kala-kala, daya daga cikin babban kunya da nauyin Rayyan din kan yanda ta yanke mishi hukunci batare da ta tsaya taji bakin shi ba. Ga shi duniyar duka bata mata dadi a kwanakin, bata da lafiya amman ba zatace ga guri daya da yake mata ciwo ba. A cikin zaman makokin Bilal bata da natsuwar kirki, mutuwar bata daketa ba sai bayan an watse sadakar ukku, saboda zuciyarta bata da natsuwa kar Layla ta gifta cikin danginsu wani ya kula da cikin da take dauke da shi. Nasihar duk da Abbu yayi mata ta kasa natsuwa.

Batajin akwai wanda zai taba gane halin da take ciki. Ita kadai tasan abinda take ji. Shisa Layla din ma ta kasa samu ta zauna suyi wata magana. Tana hango yanda ba rayuwar yarinyar bace kawai ta canza harda tata. Da ace tana da mahaifa ko daya da suka rage da taji sauki, zataje wajen su ko kuka tayi su fada mata magana mai sanyi, su karfafa mata gwiwar daukar kaddarar da ta sameta. Amman babu, maraicinta bai taba tsaya mata irin na yanzun ba, saboda Ahmadi na bata dukkan kulawa. Bata da bakin da zata amsa tambayoyin mutane, kunnuwanta da zuciyarta basu da karfin jure ma maganganun su.

“Mami”

Rayyan ya kira cikin sigar gaisuwa yana karasawa cikin dakin sosai. Kallon mamaki take bin shi da shi, sai take ganin kamar akwai abinda ya canza a tare da shi da bashida alaka da mutuwar Bilal. Kujera ya samu ya zauna yana sauke numfashi a hankali, jin shirun yayi yawa yasa Mami fadin.

“Abinda ya faru… Kayi hakuri, na yanke maka hukunci da sauri.”

Murmushi mai ciwo Rayyan ya yi.

“Baya nufin bani da laifi, ina da laifi mai yawa Mami… Ki yi hakuri.”

Idanuwanta taji sun cika da hawaye, shi baizo dan wani abu ba sai dan Layla. Ba Ayya bace kawai tayi tunani akan cikin da yake jikin Layla, har shi dinma, Bilal bai bar mishi wani abu da zai dinga tunawa da shi ba, ko da hotone yana bukata, suna da hotuna da yawa tare da Bilal, dan shi din baya gajiya da daga camera din wayar shi. Wani lokacin ma yana harar shi haka zai dauke su yana dariya, da zai samu duka wannan hotunan da yaji dadi, ko su zai dinga dubawa, yana bukatar wani abu banda kayan sakawa na Bilal. Cikin da yake jikin Layla ne abu mai girma na Bilal da zai dinga dubawa.

A daren jiya bayan rokarwa Bilal gafara da kuma Rahmar Allah harda cikin jikin Layla ya hada. Sosai yake jin son kan da yayi a cikin hakan, saboda yaga Layla, yaga yanda ta koma. Ba karamin kalubale yake hangoma rayuwarta a tare da cikin ba. Amman babu yanda zaiyi, bai isa ya hana zuciyar shi son ganin abinda zata haifo ba. Jinin Bilal ne, yaro ko yarinyar Bilal ce, yana son gani, shine kwai kwara daya na Bilal. Duk da zuciyar shi ta kasa hasko mishi Bilal din da Layla, cikin ya manne a wani waje cikin zuciyar shi, shisa yazo ya bama Mami hakuri, baice ita dole sai taso cikin ba, amman karta tsangwama wa Layla, tana cikin wani hali da alama.

“Dan Allah kiyi hakuri Mami, bansan ya kike ji ba. Amman naga Layla… Duka abin ya fara tabata kafin mu ya taba mu, kiyi mata fada, ki zageta idan hakan zaisa ki samu sauki, amman dan Allah kiyi hakuri, ki yafe mata. Ki yafe ma Bilal, nima ki yafe mun… Duka mu din masu laifi ne.”

Hawayen da take rikewa ne suka zubo mata, tunda take bata taba jin Rayyan yayi magana mai tsayin wadda yayi ba yanzun. Ba kalaman shi bane suka sakata kuka, yanayin yanda yayi maganar ne, sai da ta goge hawayen sannan ta iya amsa shi da.

“Allah ya yafe mana gabaki daya.”

Mikewa Rayyan yayi, ganin yanda take ta share hawaye shisa bai iya sake cewa komai ba ya fice daga dakin. Ya so ya ga Layla, amman bai da karfin zuciyar cewa Mami tayi mata magana. Zai kirata a waye idan ya tashi. Yana fita daga dakin mikewa Mami tayi tana share wasu sababbin hawayen da suke zubo mata. Sannan ta iya nufar dakin Layla da ta tura, a zaune ta sameta a kasa, ta dora kanta saman gado, karasawa Mami tayi tana zama gefen gadon, sai da ta zauna, Layla taji gadon ya motsa sannan ta san ta shigo.

Nata hawayen da suke zuba ta goge da sauri, muryarta a dishe tace,

“Mami…”

Wani irin kukane ya kwacewa Mami da yasa Layla matsawa tana dora kanta a jikin Mami din, itama kukan takeyi.

“Dan Allah Mami ki yafe mun, ba zan sake ba. Dan Allah Mami, ban san ina zan saka raina ba, ina jin tsoro Mami…sosai ina jin tsoro.”

Layla take fadi tana wani irin kuka.

“Shikenan ko Mami? Babu wanda zai sake ganina da mutunci, kowa zai ce mun yar iska… Wallahi Mami ni ba yar iska bace, ki yarda dani, ban san me ya faru ba, kuskurena daya na dauka, nice naje gidan su Hamma, da banje ba, kuskure daya nayi Mami, amman kowa ba zai jini ba, kowa ba zai mun uzuri ba ko? Kema bakya sona yanzun, na san kin daina sona, Abbu ma haka, na muku laifi, Mami za’a zageku saboda ni…”

Hannu Mami ta dora saman kan Layla tana son ta bude baki tace mata tayi shiru, amman ta kasa magana. Tunda abin ya faru ta tattara hankalinta kan yanda mutane zasuyi mata surutu, sam bata duba Layla ba, kaddara ce ta fadama yarinyar, irin kaddarar da take zama darasi akan mutane da yawa. Batayi tunanin halin da Layla take ciki ba, kalar tunanin da takeyi, abinda take ji ita. Duk batayi tunani ba, da gaskiya sosai a zantukan Layla, kuskure daya tayi, amman babu wanda zai mata uzuri, su duka babu wanda zai musu uzuri.

Tasan mutane da yawa zasuyi mata kallon uwar da tayi sakaci akan tarbiyar yarinyar ta. Batace ana iyayi a tarbiya ba, amman ana kuskure, ba kuma kullum kuskuren yakan zama sakaci ba. Tsanani na zama mafita a cikin tarbiya, wasu lokuttan kuma tsananin kan zama silar gurbacewar tarbiya, haka sanyi akan tarbiyar ma. Abu daya zata iya cewa ta fahimta a cikin tarin kalubalen da yake zagaye da kula da kuma tarbiyar yara, shine babu abinda yake isa, kullum ka kara idan zaka iya, kayi kokarin karawa koya ne, ka fahimci yaranka, saboda duka kalar tarbiyar su bata zama daya.

Akwai banbanci a cikin tarbiyar yaran da suke gabanka ko da suke nakane gabaki daya. Halayen su shine abinda zai banbanta wannan tarbiyar, lokacin da wani yake bukatar tattashi, nasiha da tsantsar kulawa, wani a cikin su, fada harma da duka yake bukata. Kuskure daya a cikin yanayoyin biyu zai iya kwance maka tufka ta bangaren igiyar ka, tsayin igiyar zai sa ka kasa ganin warwarewar tufkar da wuri sai lokaci ya kure maka. Hakan ya faru da ita akan Layla, yanda ta dora tarbiyar sauran yaran itama da shi tayi mata riko, soyayyarta ta rufe mata idanuwa, ta kasa gane cewa tana bukatar riko daban da na sauran.

A wasu lokuttan kuma sai ta sakarma Abbu yanke hukuncin, saboda tana tunanin nashi tunanin yafi nata. Amman kaddarar nan ta nuna mata akwai fanni na tarbiya da iyaye maza suke bukatar taimako a kai, ba wai jayayya akan hukuncin su ba, amman yin kokarin fahimtar dasu kuskuren da yake cikin hukuncin ko da rai zai baci abune da yake da matukar muhimmanci. Sai addu’a, ita ce abu daya da take da karfin sauya kaddara, ta fahimci abubuwa da dama, duk da ta fahimce su a kurarren lokaci, hakan baya nufin ba zasuyi mata amfani ba.

“Mami dan Allah ki taimaka mun.”

Layla ta furta cike da bukatar neman dauki, tana sake matsawa jikin Mami, kamar zata koma cikin ta, ta boyewa duk wani tashin hankali da yake cikin kaddarar ta. Sai da Mami ta tabbatar idan tayi magana muryarta ba zatayi rawa ba sannan tace

“Ban tsaneki ba Layla, babu wani abu da zakiyi dan tsane ki, duk da na kasa hana zuciyata tsanar abinda kikayi…nima inajin akwai laifina a cikin hakan. Ba zan miki karya ba, a watannin nan da zasu zo, gabaki daya rayuwar mu babu wani abu da zaizo da sauki…”

Sai da ta numfasa sannan ta cigaba.

“Ciki ko karkashin inuwar aure ne ba abu bane mai sauki balle akasin hakan. Rayuwar ki da tamu duka ce tayi sauyi na har abada, Allah Ya san dalilin hakan, shi ya dora mana, zamu karbi kaddarar da hannu biyu mu gode mishi a dukkan yanayi, sai ya taimake mu ya kawo mana saukin da bamuyi zato ba.”

Sosai Mami taci gaba da tausasa Layla din, tun tana kuka har tayi luf alamar bacci ya dauketa. Kallonta Mami tayi, akwai darasin da ta kasa koya mata, akwai tarbiyar da kaddara ta gyara mata akan Layla, ta hanyar da ta zame musu darasi gabaki daya. Hawayenta ta sake sharewa a karo na babu adadi.

“Allah Ka san yanda zakayi da mu, Allah Ka kawo mana sauki a cikin lamurran mu. Allah mun gode maka a cikin kowanne yanayi.”

Shine abinda Mami take fadi a zuciyar ta tana maimaita hadi da bin bayan addu’ar da,

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Domin samun saukin da yake cikin fadar kalmomin a yayin tashin hankali.

*****

Sai da ya bude gaban motar Bappa ya shiga bayan ya jefa jakar shi bayan motar sannan ya maida hankalin shi kan wayar shi yana kiran lambar Abbu daya dauka a bugun farko yana kiran sunan Rayyan din daya amsa ta hanyar yin sallama yana dorawa da,

“Abbu ina kwana.”

Amsawa Abbu yayi, kafin Rayyan yace,

“Na shiga dakin ka naga ka fita. Daman zan kara maka sallama ne, gamu zamu kama hanya ni da Bappa.”

Ta dayan bangaren Abbu ya amsa,

“Ma shaa Allah. Allah ya tsare muku hanya ya taimaka. Ayita hakuri kaji Rayyan, addu’ar ka wa Bilal tafi tunanin shi yawa.”

Muryar Rayyan can kasan makoshi ta fito.

“In shaa Allah. Na gode Abbu”

Ya furta kafin sukayi sallama. Bappa da yake tukin shi a hankali ya juya ya kalla.

“Kasan wani da yake aiki a First Bank?”

Rayyan ya tambaya, cike da mamaki Bappa ya dan kalli Rayyan kafin ya mayar da hankalin shi kan titi.

“Akwai kanwata Habiba, acan take aiki.”

Dan numfashi Rayyan ya sauke, tunanin yau kwana biyu yake mishi yawo akai, amman tsoron furtawa yakeyi. Sosai zuciyar shi take bugawa.

“Zata iya duba mun bank statement din account haka, sai ta tura maka ka bani?”

Sai da Bappa ya sha round sannan ya amsa Rayyan din.

“Ban san ya tsarin su yake ba, mu tsaya bank din mana ka duba… Kana da account da First Bank ne? Na dauka UBA kake amfani da shi.”

Girgizawa Bappa kai Rayyan yayi, yana rasa ta inda zai fara fada mishi, saboda a cikin kan shi ma maganar batayi kama da ta mai hankali ba. Amman dole ya tabbatar, zaifi samun nutsuwa idan ya tabbatar, ya san mene ne depression, idan bai tabbatar ba tunani zai iya zautar da shi, yana bukatar ya tabbatar kafin komai ya zauna mishi harya samu ya koma dai-dai.

“Kar kai mun wa’azi Bappa, kar kai mun wa’azi ina so in tabbatar da wani abune, ina bukatar in tabbatar da wani abu.”

Murmushi Bappa ya yi.

“Banyi alkawarin ba zan maka wa’azi ba.”

Dafe fuskar shi Rayyan yayi da hannuwan shi biyu, kafin ya furzar da numfashi yana bude su.

“Account din Bilal ne.”

Yayi maganar cikin karamar murya.

“Rayyan…”

Bappa ya fara, amman kai Rayyan ya girgiza mishi.

“Dan Allah Bappa, kar kace mun komai tukunna, idan akwai yiwuwar ta duba mun, ka taimaka mun, ina so in tabbatar, tunanin banga gawar shi ba yana mun wahala, mutuwar Bilal ta kasa zauna mun inda ya kamata ta zauna, kafin ka fara na kalli abin ta fuskar likitanci, ina so in tabbatar.”

Numfashi Bappa ya sauke yana dan rage gudun motar kafin ya kalli Rayyan yana sake mayar da hankalin shi kan titi.

“Zan kirata, yanzun zan kirata, amman zan fada maka gaskiya ko baka son ji. Ba lallai sai kaga gawar Bilal bane zai zamana ya rasu, akwai dubban mutanen da labarin mutuwar su baizo ma ahalin su ba, amman sun musu zaman makoki… Ka saka kanka a matsayin su, kuma sun hakura, hakurin nan ba zabi bane ba Rayyan, dole ne, na san me kake ji, naga gawar Mama da ta kowa, amman kullum na shiga dakinta sai naga kamar zan ganta…”

Gyaran muryar Bappa yayi kafin yaci gaba da fadin,

“Zan maka karya idan nace har yanzun babu wani bangare na zuciyata da bayason tashi da safe yaga komai ya kasance mafarki. Ka yarda dani zaka hakura a hankali, ciwon ba zai taba bari ba, amman zaiyi sauki, zaka koyi zama da shi yau da gobe… Idan duba bank statement din Bilal zai baka yardar da kake nema shikenan”

Tunda ya fara maganar shiru Rayyan yayi yana jin shi, kuma zantukan na zauna mishi, dan sun tokare mishi makoshi har wani daci-daci yake ji a cikin shi, yana ganin Bappa ya sauka daga gefen hanya a hankali yayi parking, sannan ya dauki wayar shi da take ajiye akan cinyar shi yana danne-danne. Sai da ta fara ringing sannan Rayyan yasan kira ne Bappa yayi, kuma ya saka ta a speaker. Har ta kusan yankewa sannan aka daga da sallamar da Bappa ya amsa.

“Ya Bappa, ina dan aikine haka…”

Kai Bappa ya jinjina.

“Habiba ko zaki dan taimakawa abokina ki duba mishi bank statement din shi, ya yarda wayar shine haka, to sim din da yake ganin alert yana ciki, kafin yaje yayi swapping idan babu matsala, da zamu shigo bankin tare da shi, amman bamu samu dama ba, muna hanyar Kaduna.

Ta dayan bangaren Habiba ta amsa da,

“Na dauka sai da yamma zaka wuce ai… Ya fadi account number din na shi da email sai in tura mishi”

Kai Rayyan yake girgizawa Bappa, bayason yin magana kar taci, amman so yake yace a tura ana Bappa.

“Wayar ce bai siya ba tukunna, idan babu damuwa ki tura a nawa, barin miki text din account number din da email din.”

Wani irin numfashi mai nauyi Rayyan ya sauke jin tace babu matsala. Wayar Bappa ya mika mishi bayan sun gama. Da kan shi ya rubuta account number din Bilal da kuma sunan shi cikakke. Sannan ya mikama Bappa wayar ya saka email din shi yana turama Habiba, ya sake mikawa Rayyan din wayar, ya tayar da motar suna hawa titi sosai. Bappa najin da shi kadai ne zai saka karatu ko waka yanaji, amman shi din mutum ne da yasan hakkin mutane, zai iya tambayar Rayyan din ko zai iya kunnawa, amman yaga baya cikin hankalin shi, saiya hakura.

Shisa yake mamakin mutanen da zasu kasance daki daya da wani, ko a makaranta sai su kunna kida ko karatun Qur’ani ganin duk dakin musulmine batare da tunanin ko wani a ciki baya jin yanayin sauraren wani abu ba. Shisa idan bashi kadai bane yakan zabi yayi amfani da earpiece, to yanzun wayar da zai saka a jiki tana wajen Rayyan da ya tattara hankalin shi kacokan ya mayar kan wayar, lokaci zuwa lokaci yakan dangwala yaga ko sako ya shigo shine bai gani ba. Har suka fita daga cikin garin Kano bai daina dubawa ba, ko da suka shiga inda babu network ma haka, har ya dawo sannan yaga sako ya shigo.

Jikin shi har kyarma yakeyi, da yake yasan lambobin sirrin bude wayar Bappa din, da hanzari ya danna yana budewa, kai tsaye email din ya bude yana dudduba kwanan watan da kudi suka fita, zuciyar shi na wani irin bugawa kamar zata fito ta hau titin da suke tafiya a kai ganin ko jiya an cire dubu daya a account din Bilal din, sai da ya hada kan shi da gaban motar yana wani irin maida numfashi, dariya ce ta kwace mishi a lokaci daya kuma wasu hawaye masu zafi na digowa suka sauka jikin motar, dan ya gansu, kokarin mayar da su yakeyi, jikin shi babu inda baya kyarma.

Yanda zuciyar shi take bugawa ne yasa shi kasa cigaba da duba wayar sai da yaji ta dan nutsu tukunna, a kwanakin bakwai an cire kudi sau hudu, dago kan shi yayi yana kallon Bappa.

“An cire kudi, Bilal ya cire kudi Bappa…Bilal ya cire kudi”

Rayyan yake fadi zuciyar shi na cigaba da dokawa. Bappa bai ce mishi komai ba, baiyi magana ba, haka har suka isa garin Kaduna Rayyan na duba wayar kamar yana tsammamin Bilal zai iya fitowa daga cikinta, lokaci zuwa lokaci yakan juya yace ma Bappa.

“Bilal ya cire kudi.”

Ko kuma.

“Kasan shine yake cire kudi haka kadan-kadan har fada muke saboda ina ganin wahalar da yakeyi, sai yace mun idan ya ciro da yawa zai dinga siyan abubuwan rashin dalili.”

Haka yaita surutai, Bappa bai dai tanka mishi ba har sai da suka shiga cikin gidan su suka zauna sannan yace,

“Rayyan.”

Kallon shi Rayyan yayi, yanayin da yake ji babu wani abu da zai misalta shi, a jikin shi ya dinga jin yanda Bilal bai bar shi ba, daman yasan Bilal ba zai barshi haka ba.

“Zai iya yiwuwa an tsinci ATM dinne, ka bude zuciyar ka da yiwuwar hakan.”

Kai kawai Rayyan ya jinjina ma Bappa yana mika mishi wayar shi ya mike. Ban daki ya shiga da nufin watsa ruwa. Yaga kudin da ya rage account din Bilal din dubu takwas ne, shikam akwai kudi da yawa a account din shi, ga na bautar kasa da aka basu, ga wanda Abbu bai daina tura mishi ba, sannan inda suke bautar kasar ma suna biyan su albashi me kyau. Da murmushi a fuskar shi yayi amfani da wayar shi da ya shiga bandaki da ita yana turama Bilal din kudi ta bankin shi.

“Na san ba zaka barni ba Bilal.”

Ya furta yana shafa screen din yar karamar wayar ta shi, yana jin kamar Bilal din yana tare da shi, ba zai sake zancen nan da Bappa ba, ba zaiyi zancen da kowa ba kuma. Saboda ba zasu yarda ba, zai bar abin a ran shi, shi kadai har sai Bilal din ya dawo sun gan shi. Lumshe idanuwan shi Rayyan yayi.

“Kar tafiyar taka tayi tsayi, ka waiwaye mu da ka samu nutsuwar da kake bukata.”

Ya furta a zuciyar shi, kafin ya bude idanuwan shi, da tunani kala-kala a cikin kan shi, hannun shi yakai kirjin shi yanajin kamar an fifita mishi ciwukan da suke ciki, saboda komai yayi wani irin shiru, ciwon da yake ji kamar anyi ruwan shi an dauke.

<< Martabarmu 28Martabarmu 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×