Yafi mintuna sha biyar tsaye yana juya hular da ya kamata ace tana sanye a kan shi. Yau na daya daga cikin ranakun da suke da muhimmanci a rayuwar shi, ranar daya kamata yayi ta da mutanen da suke da muhimmanci a wajen shi, bai ma su Abbu gardama ba da sukace ya bari Layla tayi arba’in, yarinyarta ta danyi kwari sannan. Duk da ba wannan dalilin bane ya saka shi jiran, har a kasan zuciyar shi Bilal yake jira, a cikin kwanakin babu ranar da zata wuce idan ya kira gida baiyi tsammanin zasuce mishi Bilal din ya dawo ba.
Watakila harda kewar Bilal da yake ji a duk wata gaba ta jikin shi, kamar zuciyar shi na son gaya mishi baiji mutuwar Bilal yanda ya kamata ba saboda yana tunanin kamar bai rasa shi ba. Tun lokacin daya fara tunanin aure yasan baya bukatar wata hayaniya, a daura mishi aure kowa yayi fatan alkhairi ya tafi. Idan akwai abinda ya hango bai wuce shi da Bilal zaune a daki suna cin abinci suna hira bayan an daura aure, amman bayajin zai samu hakan yau. Baiyi kokarin danne Layla ba, ya tambaye ta.
“Wanne irin biki kike so Layla? Dan Allah ki fada mun, bikin ki ba zai dawo sau biyu ba…”
Ita ma din tana daya daga cikin mutanen da basa son wata hayaniya ta biki, tuni suna fada ita da Jabir, bikin su daga su sai mutanen da suke da kusanci da zuciyoyin su suke bukata a lokacin bikin su.
“Bikin da zan zama matar ka Hamma, daurin aure, shi kawai nake bukata.”
Duk yanda idanuwanta ke kara gudun zuciyar shi sai da ya jima yana kallon cikin su yana neman gaskiyar maganarta. Baya son taji cewa kamar ita din bata cancanci kalar bikin da take mafarki ba.
“Wai me kakeyi ne har yanzun?”
Bappa da a gidan ya kwana duk kuwa yanda Rayyan din yace mishi ba wani abu za’ayi ba, ya koma gida da safe ya dawo.
“Ina ruwan ka dani ne Rayyan? Gidan nan naga na Abbu ne, kuma baice in tafi ba…”
Har a zuciyar shi yaji dadin zaman Bappa din, tunda kusan kwana yayi yana kallon ceiling cike da tunani kala-kala har wayewar garin.
“Ku fa ake jira.”
Haris ya fadi yana leko kan shi, turarukan daya hango na saka shi shiga cikin dakin sosai. Dauka yayi ya sake feshe jikin shi, Rayyan na bin hular da take kan shi da kallo, zuciyar shi na matsewa a cikin kirjin shi.
“Hular Bilal ce ko?”
Ya bukata muryar shi can kasan makoshi. Kai kawai Haris ya daga mishi yana ficewa daga dakin. Kamar yanda ya fadawa Rayyan cewa zaije Zaria ya kwashe kayan su haka akayi. Rana daya ya ware, da wani irin karfin zuciya ya shiga garin Zaria har zuwa unguwar su Bilal. Harya shiga cikin gidan ma haka, ya san duk yawancin yan gidan, da Abdul ya fara cin karo daya karaso da sauri suna gaisawa yana dorawa da.
“Ina Bilal? Lambobin shi gabaki daya a rufe, mun kasa samun lambar Rayyan, kaima taka tayi wahala saboda babu yan set dinku da sukayi saura, wallahi tunda aka dawo muke tunanin ko lafiya..sai yanzun muke tunanin kalar zaman da mukeyi da yanda ya kamata ace kowa yana da adireshin gidan kowa ko da halin ziyara bai samu ba.”
Wani murmushi mai ciwo Haris yayi, zuciyar shi daya dauka ta dake yaji tana rawa, muryar shi ma a raunane yaji ta lokacin daya kalli Abdul da fadin,
“Ya rasu, hatsari yayi. Ya rasu…”
Ya karasa maganar wani abu na tokare mishi makoshi.
“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”
Din da Abdul ya furta cike da tashin hankali na saka shi raba Abdul ya wuce cikin gidan. Da yake ya karbi mukulli a wajen Ayya, shiya dauko ya saka yana bude dakin, bai shiga tashin hankali ba sai daya kunna kwan dakin yana ganin yanda yayi wata irin kura kamar mutane basuyi rayuwa a ciki ba. Dakin yake karewa kallo, yana hango wajeje da lokuttan da suke zaune a ciki shi da Bilal, sai yaji har kirjin shi ma zafi yake. Ba zaice ga mintinan daya dauka a cikin dakin ba kafin yaji.
Shigowar yan gidan su Bilal din da babu wanda yace mishi komai, dakin suka fara taya shi sharewa.
Kusan babu wani abu da yayi, su suka dinga hada komai, duk yanda ya so ya kwashe komai saiya kasa, daga takardun da yake tunanin suna da muhimmanci sai suttura ya dauka, sauran hatta da katifa nan yabar ma su Abdul da yake ganin yanda mutuwar Bilal din ta dake su sosai. Lambar shi suka karba da fadin zasu shiga Kano suyi wa Ayya gaisuwa. Kai kawai ya jinjina musu yana ficewa ya shiga motar shi da aka loda kayayyakin a ciki. Sai daya zauna sannan yaji jikin shi na rawa ba kadan ba.
Rayuwa aikin banza, babu wani abu da yake da tabbaci a cikinta, ba mutuwar Bilal kadai yake ji ba, harda tashi mutuwar yake hangowa, duk tarin burukan da suka ci shi da Sa’adatun shi mutuwa zata iya yanke musu shi, ga Bilal nan da Aisha, ya tabbata yarinyar bata taba hango auren wani ba Bilal ba, soyayya tun firamari ake yinta, ta ina zata fara yanzun? Wa zata budewa zuciyar ta, wanne waje ma zai samu bayan ko ina cike yake da kaunar Bilal? Hawayen da yaji ya share a kasan zuciyar shi yana fadin.
“Allah ya jikan ka Bilal, kai din mutumin kirki ne. Allah ya sa mutuwa hutun ka ce.”
Sai dai daya ajiye kayan Bilal a dakin su akwai wanda ya dauka, duk yanda yaso ya barwa Rayyan komai saiya kasa, ciki harda wannan hular da ya saka a kan shi, tare sukaje suka siya da Bilal ba zai manta ba, shi da kan shi ya dauketa ya dora ma Bilal din a kai.
“Hamma ni fa bana son wannan zanen, ina da shigen shi.”
Maganar Bilal din ta dawo mishi a lokacin.
“Ni ina son shi, tunda ni zan biya.”
Dariya Bilal yayi.
“Jiba ikon Allah, dan zaka sai mun shine ba zan zabi abinda nake so ba? Yaushe aka taba yin haka?”
Shima dariyar ya yi.
“Yau za’a fara idan ba’a taba ba.”
Sai kuma ya dinga yawan ganin Bilal din da hular, duk kuwa yanda manyan kaya ba damun shi sukayi ba.
“Na dauka baka son zanen?”
Ya tambaya yana saka Bilal din yin dariya.
“Dana dan shiga haske da ita rannan sai naga ya danyi kyau.”
Hannu Haris ya kai da nufin cire hular daga kan Bilal daya kauce yana dariya.
“Ba’a kyauta a kwace Hamma.”
Shi din da Bilal zai iya cewa kamar abokai ne ba Yaya da Kani ba, ba zaiyi son kai ba, tunda ya kula kusan kowa zaice da kadan shakuwar da take tsakanin Rayyan da Bilal tafi wadda take tsakanin su. Amman yau Rayyan ya saka shi jin wani iri, yanda ya tambayi hular Bilal ce a kan shi kamar babu wanda yake da damar saka wani abu na Bilal banda shi, kuma har ga Allah bai san ya akayi ya sakata ba, har sababbin huluna yana da su daya keta siya na tanadin bikin shi da aka hada lokacin shi dana Rukayya. Kawai ya dauki wadda hannun shi ya fara kaiwa ne, sai kuma akayi dai-daito ya dauki wannan din.
Shisa ya daga mishi kai kawai yana ficewa, ba zasu fara gwada waya fi kusanci da Bilal ba. Musamman yau din, wani irin numfashi Rayyan yaja yana fitarwa cikin yanayin da ya saka Bappa kallon shi.
“Idan ya mutun kuma fa? Bappa idan ya mutun da gaske ya zanyi?”
Rayyan ya karasa muryar shi a tsorace, saboda da gaske baisan yanda zaiyi din ba idan ya rasa Bilal na har abada.
“Hakuri… Shi zakayi Bilal, hakurin da kowa yakeyi a yayin rashin, hakurin da su Ayya sukayi…”
Kai Rayyan yake girgizawa Bappa, saboda yanajin kamar bai shirya ba, kamar ba zai iya ba. Ba duka labarin Bappa ya sani ba, kadan daga ciki da Rayyan ya fada mishi sai kuma sauran guntayen da yake tattarawa a kullum, sai ka dauka labarin ka cike yake da hargitsi, sai kaji na wani saiya saka ka gode Allah da kalar taka kaddarar.
“Hakuri zakayi Rayyan, ayyukanka zaka cigaba da gyarawa idan kana son sake rayuwa da shi.”
Cike da rashin fahimta Rayyan ya kalli Bappa, kalaman Baba ne shima zai ara yau, duk da sun jima basuyi mishi aiki ba, amman sun gyara abubuwa da yawa a tare da shi, sun samar mishi natsuwar da yake fatan su samarwa Rayyan a yanzun.
“Rayuwa ba ita bace karshen mu, duk da itace farkon mu, amman karshenta mu musulmai shine farkon wata rayuwar, kasan Bilal da ya tafi ba sauri yayi ba, mu da muke nan lokaci muke jira. Ka gyara ayyukan ka, duk da basu bane zasu tsirar damu, amman ka gyara a duk rana dan ka samu damar tambayar Bilal idan ka natsu waje daya a aljanna, idan ya rigaka wuce karya jira na tsayin lokaci. Ba nan bane karshen zaman da zakuyi Rayyan, ka sani, ina tuna maka ne kawai.”
Numfashi Bappa ya sauke.
“Soyayyar da zaka yiwa Bilal a yanzun tana cikin yawan addu’ar ka ba kuncin ka ba… Ka karasa ka fito mu tafi.”
Cewar Bappa yana ficewa daga dakin, numfashi Rayyan yake ja yana fitarwa. Wani irin ciwo zuciyar shi takeyi da yanda yake son tursasa mata amincewa da sun rasa Bilal amman wani bangare nata yana mishi taurin kai. Ruwa ya karasa ya dauka ya sha, abinda yakeji yana nan tokare da kirjin shi, hular shi ya dora saman kan shi yana zira takalma a kafar shi ya fita shima. A bakin kofa ya tsaya yaja numfashi yana danne abinda yake ji kafin ya samu ya dora murmushi saman fuskar shi.
*****
Zaune take a gefen Rayyan a cikin dakin Abbu, ta hade yatsunta da take wasa dasu waje daya. Gani takeyi komai da yake faruwa kamar mafarki tun da safe da ta tashi, da taimakon su Rukayya ta shirya, da yake Sa’adatu yar gidan Yaya Ayuba tana kunshi ita tazo har gida tayi wa Layla din. Kafin wani lokaci ta fito tsaf a amaryarta, tayi wani irin kyau cikin leshin da ta saka kafin a dawo daurin aure. Akwai banbanci kadan a yanda ta hango aurenta da kuma yanda ya kasance a yau din, ba mutanen bane sukayi kadan, wasu a cikin sune babu, musamman Bilal da kewar shi take tabata a cikin kwanakin.
Amman akwai kowa da take fatan ace ya kasance a cikin duk wani hoto da aka dauka na bikin, ba wani taro akayi ba tunda duk yan uwane kawai. Sau daya taga Nur tunda ba rigima yarinyar gareta ba, itama ba zatace ga wanda ya kawo mata ita ta bata tasha ba aka sake daukarta, daman ba yini takeyi a wajenta ba, idan Rukayya bata shigo ta dauki yarinyar ba ko Huda zata shigo ko wani a gidan, idan an dawo mata da ita kuka tayi, sai kuma dare yayi, wani lokacin har goma na dare, zatace haihuwar Nur tayi, amman a kwanakin da tayi a duniya bata san wani abu rainon yarinyar ba.
Sai take ganin kamar labarin ta yasha bamban dana sauran mutanen da suka samu yarinya ta hanyar da ta samu tata, saboda akwai yarda da kaddara a cikin nata lamarin, bata fuskanci kyamata daga yan gidan su ba, amman hakan baya nufin laifinta ya wanke, baya nufin zai mantu, da duk ranar da Nur zata gifta ita kadai ta isa ta tunasar da kowa. Shine abinda yake cin ran Layla, abinda yake damunta yana kuma saka mata tunanin Bilal fiye da yanda ya kamata. Laifukan sune take gani zai taba Nur babu kuma yanda zata iyayi.
Yanda kowa yake son saukaka mata ranar yau har mamaki ta dingayi. Ta kuma yi kokarin ganin bata sa kokarin su ya tashi a banza ba, murmushin duk da ta dora akan fuskarta a hotunan daga zuciyarta ya fito, tana da tarin dalilai na yin farin ciki koya yake, tana zagaye da mutanen da suka tabbatar mata babu wani yanayi na rayuwa da zata shiga da zasu kasa karbarta, da zai canza kaunar da suke mata. Kowa ya fadi abinda zai fada in dai suna tare da ita zai zo mata da sauki. Murmushin da Rayyan yayi mata bayan sun hada ido da safen ya samu wajen zama a zuciyar ta.
Bata san ko wani ya lura ba, ko ita kadai ta fassara murmushin shi da.
“Tawa, tawa har abada.”
Yana kara sata jin kamar a mafarki, yanzun ma har Abbu ya fara da fadin,
“Yau kam kalamai sun mun karanci, nasiha ya kamata inyi muku, sai dai na rasa abinda zan fada muku a cikin yan mintina da ban fada muku shi a duk tsayin shekarun da na samu a tare da ku ba…”
Saboda sosai yake mamakin me yasa sai an aurar da yarinya ko yaro sai a dauko shi a kai wajen iyaye wai suyi mishi nasiha. Musamman yara mata, ko da bikin baida haka aka kawo mishi ita, yarinyar ma tana ta kuka bayajin zata fahimci duk wani abu da zai fada mata, shisa ya kalli kanwar shi da take rike da ita yace,
“Nasan yarinyata, na san tarbiyar da na bata, ba ita zanwa nasiha ba, ku turo mun yaron.”
Hakan kuwa akayi, shi yayiwa fada, shi ya baiwa amanar yar shi, kamar yanzun yanda ya kalli Rayyan da fadin,
“Ga amanar ‘yata nan Rayyan, kayi hakuri da ita a lokacin da zata kuskure maka, ka kauda kai a lokacin da nata idanuwan suka rufe ko da kuwa kaine da gaskiya. Zamana da Ayyar ka bai kawo mu yau ba sai da hakan, hakurin da ake jaddadawa mata mu ya kamata a jaddadawa shi, kayi hakuri, kayi hakuri da duka halayenta, karka cutar da ita, kanwar ka ce ita kafin yanzun ta zama matar ka, ka kula da ita kamar yanda kake so a kula da su Rukayya, ka kare martabar ta kamar yanda zaka so a kare ta yaranka wata rana, karka daga mata murya kamar yanda ba zaka so in dagawa Ayyar ka ba.”
Idanuwan shi Rayyan ya saka cikin na Abbu kafin ya dan daga kan shi, yana jin nauyin maganganun Abbu din da girman amanar daya dora mishi.
“Zanyi magana da yarinyata Rayyan”
Abbu ya fadi yana saka Rayyan din mikewa ya fice daga dakin, zuwa lokacin idanuwan Layla cike suke taf da hawayen da suka fara zubo mata.
“Abbu…”
Ta kira muryarta na karyewa, wannan karin ba da kukan da takeyi ba, da tarin kaunar da takeyi mishi, da godiyar da bata da kalaman da zata fara yi mishi ita, batama san ta inda zata fara ba, saboda akwai tarin abubuwa da suka fi karfin godiyar. Kallon ta Abbu yayi yana jin yanda zuciyar shi ta karye, su duka yaran yake kula da yanda girman daya fi shekarun su ya saukar musu, yanda tarbiyar da rayuwa take bawa dan adam ta saka sukayi wani irin laushi da kalaman shi zasu dauki wani lokaci basuyi musu wannan tasirin ba.
“Kar zamana da Mamin ki ya zama tsanin da zaki gina taki rayuwar auren, ba lallai tazo iri daya da tamu ba, sai kinyi hakuri Layla, kinji? Zaki iya kiran mu ko da yaushe, kin san haka ko?”
Kai ta daga ma Abbu wasu sababbin hawayen na kara zubar mata. Da kan shi ya mike yana kamata ta mike, kuka takeyi sosai dan zaka iya fahimta da yanda jikinta yake bari. Abbu ya rakata har wajen mota inda ta toge tana girgiza mishi kai, dan wajen shi aka fara kawota.
“Mami… Abbu…Mami na.”
Layla take fadi tana jin wani irin tsoro na ratsata. Zama matar Rayyan ne mafarkin ta, amman bata dauka haka zai kasance ba sai yanzun da zata bar gida, yanzun da bata san me rayuwa ta tanadar mata a cikin gidan shi ba, musamman yanda zataje mishi din, tana da yakinin shima ba haka ya hasaso auren shi ba, bai hango bayan mata harda yarinya za’a tafar mishi da ita ba, shine abinda ya kara gigita lissafinta. Kafin Abbu yayi wani motsi Layla ta kubce daga rikon shi tana bude lullubin da yake kanta saboda bata ganin hanya sam, da sauri gudu-gudu take nufar bangaren Mami, tun daga bakin kofa take kwala mata kira harta shiga can cikin dakin inda Mami take zaune a gefen gado tana sharar kwalla.
Tana daga cikin mutanen da suke ganin ranar da ka aurar da ‘ya ya kamata ya zamana rana mai girman gaske a wajenka, bata ga dalilin da zai saka ta fara kuka da za a kai mata yarinya gidan aure ba, tunda abin farin cikine, sai da ta wayi gari safiyar yau ko giccin Layla ta gani sai taji idanuwanta sun cika da hawaye. Saima da Jafar ya shigo bayan an dawo daurin aure yana kamata ya jata dole akayi hotuna da ita. Ta ga da gaske dai auren Layla aka daura, da gasken tafiya zatayi, balle kuma da aka shigo aka fita da ita, tana zaune ne tana jiran su tasan za’a kawo Layla ace tayi mata nasiha.
Bata tsammaci ganin Laylar ta shigo a firgice haka ba.
“Mami…”
Layla ta sake kira a karo na babu adadi ta karasa cikin dakin tana fadawa jikin Mami tare da sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya.
“Ni bana son sakarci, ke baki san yanzun girma ya kamaki ba? Ki dagani karki karyamun kafada.”
Mami take fadi cikin karfin hali, amman ta kasa raba Layla da jikinta, idan ma akwai abinda take sonyi bai wuce sake riko Layla din ba. Addu’a ce yi mata takeyi ba tun yau ba.
“Allah ya saka miki albarka a gidan auren ki Layla. Allah kar ya saka hawayen ki su zuba a sanadin kaddara ta gidan aure.”
Shi Mami take furtawa a ranta, har sai da matar Yaya Ayuba ta shigo dakin tana kama Layla dakyar ta fita da ita. Da kanta ta saka Layla a mota suna jiran Rayyan ya fito tunda su kadai zasu tafi abinsu, ba wani rakata za’ayi ba. Sai Bappa da zai kaisu, yana zaune a gaba cikin mota suna jiran Rayyan din. Shi kuma bangaren Ayya ya tafi yace mata sun wuce ya kuma karbo Nur da yasan tana can.
“Ayya zamu wuce ne… Ina Nur?”
Rayyan ya fadi bayan ya shiga dakin Ayya din, kallon shi takeyi cikin fararen kayan shi, ya sake wasu duk da na safen ma farare ne, amman da babbar riga. Wannan kuma babu babbar riga, yayi kyau. Sai taga yau fuskar shi tayi mata fayau, ana cewa yana kama da ita, amman akwai wani abu a fuskar shi da yake mata kamar Abbu yau din nan.
“Rayyan”
Ta kira da wani irin yanayi, nauyin hakkin shi take ji a duk rana, ta kasa samun karfin zuciyar fada mishi balle ta roke shi ya yafe mata, ta samu damarmaki da yawa tana kasawa, batasan me yasa yau din bakinta ya subuce da fadin.
“Laifina ne, komai daya faru laifina ne, ni nayi kuskuren da ku da Bilal kuka biya, Bilal ya biya fiye da kowa, alhakin Haris da naso cutarwa ne ya kamani Rayyan, alhakin shi ya sa ka dauki shayin daya kamata ya sha ka sha… Shine mafarin komai.”
Kallon ta Rayyan yakeyi tunda ta fara magana saboda yanda kalamanta suke dukan kunnen shi da wata irin iska.
“Me yasa?”
Ya bukata muryar shi na fitowa can kasa kafin ya dora da,
“Ayya me yasa sai yau?”
Duk ranakun da zata iya fada mishi maganar da zata fada sai ta zabi yau da yake neman duk wata natsuwa da zai iya. Hannu Ayya ta kai tana share hawayen da suka zubar mata, itama ba zatace ga dalili ba, amman abin ne yake cinta, musamman shekaranjiya zuwa yau. A shekaranjiya da ta zabi ta biya gidan Hajiya Dije da kanta bayan ta dawo daga kasuwa ta gayyace ta bikin Rayyan din duk da tun cikin rasuwar Bilal rabon da suyi magana, ta gwada kiran wayarta taji ta a rufe shisa ta biya. Sai ta sha mamakin jin Hajiya Dije tana gidan iyayenta.
Gidan kuwa ta biya, ta sha mamakin ganin yanda rayuwa tayi da Hajiya Dije, wani irin hawan jini ne ya kamata, ta fadi, tashin da tayi a asibiti babu idanuwa, shine bayanin da Mamuda, dan uwan Hajiya Dijen da yake zaune a gidan su da shiya gada aka kuma bata daki daya ya fadama Ayya, amman data shiga wajen Hajiya Dije sai labarin ya banbanta dan kuka Hajiya Dije takeyi kamar zata tsiyayar da abinda ya rage cikin idanuwanta.
“Kinga inda rayuwa ta kawoni ko Maimuna? Hawan jini sukace a asibiti, ni nasan ba hawan jini bane ba, hakkin Balaraba ne, sharadin magani na karya ya dawo kaina, dan Allah Maimuna ki taimaka mun, bansan wa zan fadawa ba ya fahimta sai ke, ki taimaka mun Alhaji saki dayan daya rage tsakanin mu yai mun, yanda nake tsugunnen nan suma wallahi sai sun tsugunna.”
Ko sallama Ayya batayi mata ba ta tashi ta fice daga dakin, saboda tsoro Hajiya Dije ta bata, zame mata tayi kamar wata dodanniya. Makantar da take tare da ita bata zame mata ishara ba ita, neman hanyar da zata cutar da wasu take karayi maimakon neman yafiyar su, da gaske akwai mutanen da basu da rabo, tun daga ayyukan su a doron duniya zaka gane hakan, ba zatayi shisshigi ba shisa ba zata yankewa Hajiya Dije hukunci ba. Baccin kirki ma a ranar bata samu ba, ta gaji, sosai ta gaji da barin abin a cikinta shisa ta fadawa Rayyan din. Kallon shi tayi da nufin magana sai ga Huda ta shigo rike da Nur da take kuka, hannu Rayyan ya mika ya karbi yarinyar.
“Na bata ruwa taki ta sha, banga Adda Layla ba…”
Kai Rayyan ya jinjina ma Huda yana cewa,
“Ina jakar goyon ta? Ki dauko mun da feeding bottle din, kiyi sauri.”
Ficewa kuwa tayi da sauri, baisan inda zai saka kalaman Ayya ba ko abinda yake ji, shisa ya kwantar da Nur a jikin shi yana kokarin ganin tayi shiru, dan jijjigata yakeyi a hankali.
“Rayyan…”
Ayya ta kira, amman bai kalleta ba, kirjin shi zafi yakeyi na gaske. Huda da ta dawo ta taimaka mishi yayi strapping Nur daya goya a ta gaba yana karba feeder din ya fice daga dakin batare daya cewa Ayya komai ba. Inda motar Bappa da aka saka Layla a ciki take ya karasa ya bude ta dayan bangaren ya shiga, yana jin addu’ar da mutane suke binsu da ita. Amman sam hankalin shi ba’a kan su yake ba lokacin daya ja murfin motar yana fadin,
“Muje Bappa”
Ya sake tallabe Nur da ya dan kalla yaga tayi shiru, sumbatar gefen fuskar yarinyar yayi yana gyara zaman shi hadi da sauke numfashi. Addu’ar duk da tazo mishi ita yake karantawa ko zai samu natsuwa har suka karasa Hotoro inda gidan daya kama yake.
*****
Da yake ba mai gadi gare su ba, sai da ya tsaya Bappa ya fita da motar, da suka hada ido da shi yace mishi.
“Koma mene ne karka sauke a kanta.”
Saboda ya kula da yanayin Rayyan din, bai amsa shi ba, da addu’a ya kulle gate din yana saka sarka da kwadon da yake jiki ya datse, sai bayan ya rufene ya laluba aljihun shi ya tabbatar da mukullin yana nan, kafin su fara neman taimako a hauro a yanke kwado. Sai da ya dauki ledojin shi da ya ajiye a kasa sannan ya kama hannun Layla da take kuka har lokacin ya jata suna nufar bakin kofa, ganin yayi tsaye ya sata dan kallon shi, addu’a ta ga yanayi cikin yanayin da ya tunasar da ita itama tayi. Suka shiga da sallama bayan kiran sunan Allah, bai saki hannunta ba sai da suka shiga dakin baccin su sannan. Ya ajiye ledojin ya zagaya gefen gadon.
Nur ya kwance a hankali yana zarota, duk motsin da tayi sai gabanshi ya fadi karta tashi, ya samu ya kwantar da ita. Bai cewa Layla komai ba har lokacin. Kofar falon yaje ya rufe ya dawo. Zuciyar shi wani iri yake jinta harya shiga bandaki, alwala ya daura ya fito yana kallon Layla da ta goge fuskarta itama tana mikewa tunda ta samu tsarki tun satin daya fita. Alwala ta dauro sukayi sallah ita da shi, tana zaune ya sake tashi ya shiga bandaki, ruwa ya watsa ko zai dan samu sararin abinda yake ji ya mishi tsaye a kirji.
Daya fito kaya ya sake, shaddar ta ishe shi, nan kasa inda Layla take zaune ta sadda kanta ya zauna a gefenta, sai lokacin ta kalle shi, farar riga ce ya saka T-shirt, da alama bai goge jikin shi ba dan fuskar shi da alamun ruwa a jiki har lokacin, kamar damuwa take karanta a shimfide a fuskar shi, yanda yaji idanuwanta na mishi yawo ne yasa ka shi kallon cikin nata idanuwa yana girgiza mata kai.
“Wani abune daban Layla, ba ke bace ba.”
Saboda zai rantse yana jin sautin tunanin ta cikin kunnuwan shi, idanuwanta da yake ganin hawaye a ciki na saka shi gyara zaman shi ya saka hannuwa yana riko fuskarta.
“Na san banda wani abu da zan baka Hamma, ba haka na hango yau ta kasance mana ba…”
Layla ta ke fadi wasu hawaye masu zafi na zubo mata. Kai Rayyan yake girgiza mata, sam bayason inda tunaninta yake so ya dauketa.
“Bana so, bana son wannan shirmen tunanin naki. Kin zo mun dake, kin zo mun da Nur, kin bani duk abinda nake so harda abinda banyi zato ba, dan Allah ki bari, karki kara mun damuwa da tunanin nan naki… Raina a bace yake, amman bake bace.”
Ya karasa maganar yana matsawa sosai ya sumbaci goshin ta, yana sake sumbatar kuncinta kafin ya riko ta jikin shi yana sauke wani irin numfashi, ya manta yanda kusanci da ita haka yake samar mishi natsuwa, ya manta yanda jinta a jikin shi kawai yake kwantar da duk wata murya da take neman daga mishi hankali, sosai ya kara riketa a jikin shi yana sumbatar duk wani waje da labban shi zasu iya sauka kafin ya sake riketa kamar zai koma jikinta.
“Na gode Hamma…”
Layla tace tana dorawa da,
“Na gode da ka zamar dani matar ka.”
Dariya yayi mai sauti yana sake riketa.
“Na gode da kika zama matata, na gode Layla. Ba zan miki alkawarin baki farin ciki ko da yaushe ba, amman In shaa Allah zanyi kokarin ganin kinyi farin ciki koyaya ne a duk ranar da zan samu aronta tare dake, Na gode… Na gode.”
Yana jin amsarta ta yanda ta kara shigewa a jikin shi, Ayya tace itace mafarin komai, tace laifin duka nata ne, baisan ko Layla da take jikin shi bane ta sauya tunanin shi, bai san ko dan Ayya din daga jikinta ya fita ba, amman ya kasa dora duka laifin a kanta, ya ga fuskarta, ya ga idanuwanta, ba tun yanzun yasan duka rayuwarta ta ta’allaka ne wajen ganin ta kare su daga duk wani abu da zata iya ba. Idan da ta hango abinda tayi zai iya tabasu ba zatayi ba, yana ganinta ita da Haris, tana kaunar shi kamar daga jikinta ya fito. Kuskure ne tayi, kowa baifi karfin yayi kuskuren ba, ko da akwai son kai a cikin shi, baice ran shi bai sosu ba, baice ba za’a dauki lokaci ba kafin ya daina jin ciwon abin. Amman zasu kai wajen, kamar yanda shi da Layla suka kawo yau.