Skip to content
Part 34 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Sittin

Da safe, sai Dila ya yi wa gidan Malam Kahuhu tsinke. Ya kuwa ci sa’a, yana kofar gida yana  darasu. Bayan sun gaisa, sai ya samu wuri ya zauna har sai da ya sallami daliban, sannan ya matso suka gaisa. Ya ce.

“Alaramma kwanan nan biyu ba ma haduwa,  shi ya sa ce yau dai kafin in wuce fada ya kamata in biyo mu dan zanta.”

Kahuhu ya yi murmushi sannan ya ce, “Ka kuwa yi dabara. Ya jikin Sarki?”

Dila ya ce, “Da sauki, wannan safiyar jakada ya ishe ni cewa ka bayar da addu’a jiya kuma in dai aka tofa masa ya sha yana jin dadi.”

Kahuhu ya ce, “Alhamdulillahi!”

Sannan ya ce masa, “Ko za mu je ka duba shi?”

Kahuhu ya ce, “Ina da niyyar hakan.”

Dila ya ce, “To a daure dai Malam, ai aikin lada ne.”

Sai ya yunkura, “To bari in shiga in dauko carbi in fito.”

Bayan dan lokaci kadan ya fito suka kama hanya. A hanyar ne kuma ya tambaye shi. “Ni kuwa zan so in ji karin bayani game da wancan batu da ka fara a fada kwanaki game da bil’adama.”

Kahuhu murmushi, sannan ya ce, “Wato kana ban mamaki kuma kana burge ni. Babu dama ka ji wata ‘yar kofa ta ilimi sai ka leka ka ga me ta kunsa.”

Da ya ji haka sai ya tintsire da dariya, “To ai Akaramakallahu mu da haka muke karatun namu, sai dai a yi ta hakuri da mu.”

Kahuhu ya ce, “Ai dabara ce mai kyau, shi ilimi dama ba ya nufin abin da ka je makaranta a ka koya maka kadai. Abin da duk ka ji, ya amfane ka ko ka amfanar da wani da shi, ko kuma ya yaye maka duhun jahiltar sa da ka yi a baya, to shi ne ilimi.”

Ya kalle shi ya ce, “Tsakanina da Ubangiji Al Karin ina son ka, kuma ina jin dadin kasancewa tare da kai. Domin bayan Kakana Dilyawa ban taba samun wani wanda kalamansa suke amfana ta kamar ka ba.”

Kahuhu ya ce, “Yanzu na kara tabbatar da maganar mahaifiyata. Ina rokon Ubangiji Al Karim ya so mu baki daya.”

Dila ya ce, “Amin, kuma ba don kar mu shagala da waccan maganar ba, ai da na ce…”

Ya yi dariya, “Kar ka damu, bari in cire labarin in fada maka maganar. Ba na mantawa watarana bayan abin da zai faru ya faru sai ta ce min. ‘Dama ai wanda duk ka ji kana son sa, kuma kuka dade tare, kanwarku na jiko a masaki guda, to babu bukatar sai ya furta maka yana son ka ma.”

Da alama Dilan ya ji wannan sai ya dau haske, kuma murmushinsa ya fadada. Sannan ya ce. “To mu koma wancan batun kuma.”

Cikin fara’a Kahuhun ya ce, “Malaminku bana ko raba daya biyu ya ci karo da matsala a rayuwa, bayan rashin soyayya irin ta mahaifa da dangi da ya taso da ita. Shi ya sa ba ya iya fadar alkhairin komai, sai sharrinsa.”

Dila ya ce, “Malaminsa dai Akaramakallahu.”

Har yanzu fuskarsa tana sake, ya ci gaba, “Amma a ka’ida su bil’adama rukunai hudu ne, haka mabambantan masana daga cikinsu sukan yi ittafaki.

Dilan ya ce, “Na’am.”

Ya ce, “Kodayake da fari dai, kakana ya ce min. ‘Ainishin Kakan mutane an halicce shi ne da kasa. Kuma wannan kasar kala-kala ta wurare daban-daban aka hada aka gauraya. Don haka ne su ma ‘ya’yansa suka saba a launi da dabi’unsu. Kowa yana halayyarsa ne bisa tasirin nau’in kasar da ya fi rinjaya a jikinsa.”

Dila ya ce, “Toh!”

Ya ce, “Amma kakana na biyu Kahudada, wanda shi ne kakan mahaifina shi ne ya yi mana bayani dalla-dalla. Domin shi ya zagaya sosai cikin bil’adama ya yi rayuwa da su. Tun da ya ji tarihin birnin Basrah da manyan malaman da suka rayu a ciki, sai kawai ya niki gari ya tafi can ya tare. Ya yi mu’amula da manyan malamai a can kwarai. Amma babban abokinsa shi ne Imam Al Jahiz. Wanda masanin duniyar dabbobin nan da har yanzu bil’adaman ke tinkaho da shi. Wanda ya rubuta littafin Kitabul Hayawan.”

Dila ya ce, “Na taba jin an ambace shi, lokacin da ake binciken masu koya wa bil’adaman dabi’un dabbobi.”

Ya ce, “Yauwa, to tare suka zauna suna ban gishiri in ba ka manta da wancan kaka namu.”

Dila ya ce. “Na’am.”

Ya ci gaba, “Ya ce mana, a majalisin malamin ya kara haduwa da wani Alhudahuda, wanda da shi ne suka hadu suka yi mafi yawan bincikensu. Farkon lokacin da suke tashi bincike haikan game da dabi’un bil’adaman. Wani babban masanin Girkawa suka fara tambaya, sai ya ce musu. ‘Mutane, bisa dabi’arsu kaso hude suke rabuwa; akwai ‘Songuine’ da ‘Choleric’ da ‘Melancholic’ da kuma ‘Phlagmetic’ kuma kowannensu dabi’unsa sun sha bamban da na dan’uwansa.’”

Dila ya ce, “Yarensu ne wannan kalmomin kenan.”

Kahuhu ya yi dariya, “Kai ma zai zama yarenka ai, ba dai kana son karatu ba?”

Ya ce, cikin dariya. “Ubangiji Shi gafarta Malam.”

Shi kuwa ya ci gaba, “Sannan suka je gun wani Malamin makaranta mutumin Yalamlam. Shi ma ya ce da su, “Mutane iri hudu ne a duniya; dole kowannensu ya kasance ‘Wuddi’ ko ‘Ta’abiri’ ko ‘Tahalili’ ko kuwa ‘Mutafarrij.’”

Dila ya ce, “Ikon Ubangiji! Wannan dai kamar harshen Larabawa ko?”

“Kuma harhenka, kai mai son karatu ba,” In ji Kahuhu.

Dila ya kara dariya, ya ce, “To na yarda.”

Ya ci gaba, “Ya ce wataran kuma da suka je wurin Masanin Dibbu, sai ya ce musu ‘Ai muna la’akari da dabi’ar mutum wurin ba shi maganin da ya fi dacewa da cutarsa. Domin daga cikin mutane akwai ‘Dam’ akwai ‘Sauda’ akwai ‘Safra’ akwai kuma ‘Balgam’.”

Sai ya ce, “To fa, abin dai tafiya yake yi Malam.”

Ya ce, “Amma bayan sun gama yawonsu sun dawo majalisinsu, sai suka taras  dalibai suna ta zane a kan kasa, suna tattauna hisabi a junansu, su kuma sun tafi a kan cewa ai mutane hudun nan ‘Nari’ ne da ‘Hawa’i’ da ‘Turabi’ da kuma ‘Ma’i’.”

Sai Dila ya ce, “Yauwa, to wannan shi na taba ji ni ma. Amma kuma yanzu fa ni duk ka rikita min nawa karatun Malam. Dama tun a can baya ina ta tunanin ya ya za a yi a danganta mutum da wuta da iska. Na dai yarda, dama kuma na sha ji cewa an halicci mutum daga kasa, haka kuma an ambaci ruwa ko a littafi Mai tsarki.”

Kahuhu ya yi dariya. “Kasar da ruwan duk kana ganinsu a jikin su ne?”

Cikin dariya shi ma ya amsa. “Ina fa, kawai dai an fada kuma na yarda.”

Sai ya ce masa.

“To a fahimtar wadancan masana dibbu; duk tsarin samuwa ya ta’allaka ne akan rukunai hudu, wadannan rukunai su ne, ruwa da wuta da iska da kuma kasa. Kowanne a cikin wannan rukuni yana da abin da ya kunsa sawa’un sanyi ne ko dumi”

Dila ya ce, “Na’am.”

Ya ce. “Amma bari in ba ka misali.” In ji Malamin: “Wuta tana dauke da dumi mai bushewa.  Da za ka jefa yanki jikakke a cikin wuta, za kaga sai ruwan jikinsa ya bushe ya kame sannan zai kone. Wannan yana nuna cewa ita aba ce mai kuna da bushewa. Wato wuta bata da damshi ko kadan.”

Ya ce, “Gaskiya ne.”

Ya ci gaba. “Iska kuwa, tana dauke da damshi da dumi. Da ace za ka shiga sahara lokacin zafi, idan ka auna ruwan da ka sha a sa’a biyu, ka kuma shiga lokacin sanyi da iska ka auna ruwan da ka sha na sa’a hudu, za ka taras  bai kai rabin na sa’a biyun lokacin iskar zafi ba. Sakamakon cewa ita iska  a karan- kanta aba ce mai dumi amma da damshi, sabanin wuta da take dumi da bushewa.”

Dila ya ce, “Toh!”

Ya dora: “Shi kuwa ruwa,  ya kebanta da dabi’a mai dauke da sanyi da damshi. Ko ka lura da cewa gabar kogi ta fi ko ina sanyi a dajin nan?”

Ya ce, “Wallahi haka ne Malam.”

Ya ci gaba, “Wanann yana nuna ainihin dabi’ar ruwa ne duk inda ya zauna ko an dade ba a zubar da shi a gun ba yana nasar wurin da halinsa na sanyi da damshi.”

Dila ya ce, “Tabbas Malam.”

“Ita kuwa kasa.” Ya ci gaba,  “ta kebanta da damshi da bushewa.  Za ka gan ta a bushe amma in aka tona ta zuwa wani dan zango za ka gan ashe ruwa ne kundum a cikinta. Don haka ita ba ta bushewa a kan kanta sai dai zafin rana ya busar da ita. Rana tana matsawa za ka ga ta dawo kan dabi’arta ta asali, koda kuwa a lokacin zafi ne.”

“Sannu Malam.” In ji Dila.

Sannan ya ce masa, “To wadannan abubuwan duka akwai abubuwa masu irin dabi’unsu sak a jikin dan’adam din kuma. Bari in kamo wasu zararrukan, sai in hada da wadannan in kulle maka. Tun da na san kai kana da kaifin kwakwalwa.”

Dila ya yi dariya. “Kana zuga ni sosai Akarami.”

Ya ce masa. “Sanin  da na yi maka ne ai.”  Ya ci gaba: “Ka san a can sama mun ambaci Dam da Sauda da Safra da Balgam.”

Ya ce, “Haka aka yi Malam.”

Ya ce, “To shi Dam,  ai jini kenan. wanda dabi’arsa dumi da damshi ya yi daidai da dab’iar Iska kenan.”

Dila ya ce. “Iko sai Ubangiji.”

Ya ce, “Safra kuwa wata ‘yar jaka ce a jikin hanta wadda tana dauke da wani ruwa launin rawaya mai diga lokaci-lokaci a hanji, ruwan yana da dandano mai matukar tsami, wanda ke taimakawa wurin  narka abinci. Dabi’arta dumi da bushewa, wanda shi ne daidai da dabi’ar Wuta.”

Dila ya ce, “Sannu Malam.”

Ya ce, “Sauda ma ‘yar jaka ce a tsakanin halittar hanta guda biyu. Tana dauke da wani ruwa kore-kore baki-baki. Ruwa ne mai matukar daci da aikinsa wanke hanta. Dabi’arsa sanyi da bushewa, shi kuma shi ne daidai da dabi’ar Kasa.”

Dila bai iya cewa komai ba sai gyada kai a sannu cikin mamaki.

“Sai kuma Balgam, wanda wani ruwa ne a jikin bil’adaman,  kamar tsinkakkiyar majina.  Yana da yauki a jikin tsokarsu da kwakwalwa da inda mahadar kashi take ake samun sa. Shi kuwa dabi’arsa sanyi da damshi.”

Dila ya ce. “Dabi’ar ruwa kenan.”

Malam Kahuhu ya ce, “Dila Sarkin Azanci.”

Dilan ya ce, “Lallai yanzu da ka fara hade su, sai na ji na fi fahimta”

Ya ce. “To ai dukkansu in muka tafi haka za su hade. Kuma za ka taras dukkan dabi’un bil’adaman suna rabuwa ne daidai da wadannan dabi’un rukunnai hudun.”

A daidai wannan lokaci suka isa kofar gidan Basaraken, bayan sun nemi iso an kuma yi musu izini, sai Dilan ya ce da shi, “Malam ka koro batu fa.”

Kahuhu ya yi dariya ya ce, “Duk ranar da ka tashi son jin tarjamar karatun ka riske ni ko dai ranar alhamis ko juma’a a gida. Sai mu tattauna ba tare da kowa ya katse mu ba. Amma dai abin da zan ce maka a yanzu shi ne, kamar a cikinmu tsintsaye ne, idan ka kalli Cakwaikwaiwa za ka taras ta cika surutu da son ta burge  da burin komai ake na yayi sai ta san shi. Ita kuwa Shaya, ba ta da yawan zance kamar ta. Amma za ka taras duk inda ta samu tsintsaye ita dai burinta ta ja gaba, kowa ya bi ta. Kuma kullum burinta a tafi a yi wani abu. Ita kuwa Kurciya in ka dube ta, sai ka taras rayuwarta daban ce. Ita kullum cikin taka-tsantsan take, zai yi wuya ka ji muryarta ma in ba a cikin iyalinta ba. Ga ta da tsarguwa, komai sai ta yi masa kallon kurulla. To kuma ita ma duk da haka in ka dawo kanmu, sai ka ce gara ma ita ta fi mu magana. Irinmu kamar raba-danni ne a cikin tsumtsaye. Ko bishiya muka je muka taras sa tsintsaye, sai dai mu koma can gefe mu yi kamar ruwa ya ci mu.”

Dila ya ce, “Sai an taba ku a sha karatu ba.”

Dukkansu suka yi dariya, sannan ya ce, “To kana ganin ya dace a yi wa tsintsaye kudin goro a cikin halayyarsu?”

Dila ya ce. “Ina fa?”

Ya ce, “To kamar haka ne babu adalci cikin yi wa bil’adama kudin goro.”

Cikin mamaki Dila ya ce, “To wai Aramma me ya sa ba ka shararu wannan bayanan ba a fada kwanaki?”

Ya yi dariya, “Mu shiga Yallabai, mu muna karatu ne don amfanin kanmu da makusanta, ba don neman suna ba ai.” 

Da suka shiga sai suka taras da Zaki a kwance dakaka, kamar yadda suka gan shi wadancan lokuta da suka zo. Sai bayan sun fara yunkurin tambayar ina saukin da aka ce ya fara samuwa, sannan cikin mamaki suka ga ya daddafa ya kashingida! Cike da farin ciki suka hada baki: “Ubangiji Ya kara maka yawan rai.” Matarsa da ke gefensa ta amsa. “Amin.” Sannan shi ma ya dage cikin cije baki ya ce wa Kahuhu. “Na hada ka da Ubangiji Al Karim ka fada min wane irin ciwo ne wannan yake damuna?”

Kahuhu ya ce, “Ubangiji shi ne mafi sani, amma ni ina kyautata zaton sihiri ne.”

Zaki ya waiwaya ya dubi Matarsa, suka hada idanu, sannan kowannensu ya gyada kai cikin wani salo mai bukatar sharhi. Sannan ya dube su ya ce. “Bayan Jakadana Carki babu wanda ya san ina iya magana yanzu, sai ku da kuke wurin nan. Don haka ina so ku ja bakinku ku yi shiru zuwa wani dan lokaci ku ma.”

Bayan wannan batu sai suka shiga tattauna wasu batutuwan da suka gabata, har zuwa lokacin da wasu suka kara neman iso. Su kuwa suka yi sallama suka tafi.

<< Yini Sittin Da Daya 33Yini Sittin Da Daya 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×