Skip to content
Part 33 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Hamsin Da Tara

Kamar yadda suka saba a kowace rana tun bayan kwanciya jiyyar da Sarkin ya yi, mafiya yawan wadanda suke lazumtar fadar sukan zo su shiga cikin gidan, su dube shi, sannan su dawo fadar su zauna. A yau ma kamar kullum suna zaune jigum-jigum a fadar tamkar masu zaman makoki, sai kawai Kunkuru ya tashi ya dare kujerar sarautar nan!

Nan take kuwa hankalin dabbobin da ke zaune a wurin ya kai matukar tashi, wasu suka harzuka suka fara gurnani! Da ya lura da wannan alama sai ya yi farat ya mike tsaye, yana cewa, “Ku saurara, sakon Sarki zan karanta muku kawai in matsa. Dama na zauna a wurin ne don hanklinku ya dawo kaina gabadaya.”

Da ya ga sun fara komawa hayyacinsu sai ya ce,

“Na yi yawo a duniya daga cikin teku zuwa doron kasa sama da shekaru dubu. Na ga dauloli da shugabanni da al’umatai iri-iri. Amma ban taba ganin adalin Sarki irin wannan Sarkin naku ba. Haka kuma ban taba ganin wata al’uma mai biyayya ga Sarkinta kamar ku ba.”

Da suka ji haka, sai dukkan wadanda suke mike tsaye suka zauna. Hakan kuma ya kara masa kuzarin ci gaba cikin saukin rai, “Na dade ina mamakin irin girman son da kuke yi wa Sarkin nan, amma da kadaita da shi sai na fahimci ashe ma shi ya fi son ku. Ina nufin yana tsananin son ku fiye ma da yadda kuke son sa. Kodayake, ba zan fada muku irin tanade-tanaden da ya shaida min yana yi muku ba, domin sirri ne.”

Sai wani kaso na dabbobin suka hau magiya cewa, “A taimaka a fada mana, don girman Ubangiji Al Karim.”

Ya yi shiru, sai da aka dauki dan lokaci suna waccan magiyar sannan ya ce, “To abin da dai zan iya fada muku yanzu shi ne, a lokutan da muke hira bayan kammala cin abincin dare, ya sanar da ni wadansu masu tsananin nuna masa so da masu yi masa biyayya daga cikinku. Sannan ya sanar da ni cewa yana so daga cikin wadannan masoya nasa ya yi wa wasu kyauta ta yankan shakku! Kuma daga cikin yana so ya yi wa wasu sarauta, ya tura su gundumomi su ci gaba da mulki, a matsayin wakilansa a wannan yankuna. Sannan ni ma ya yi min wasici da cewa in rike wadannan masoya nasa da kyau, duk abin da suka nema a wurina in yi musu. Domin yana da yakinin za su so ni, saboda sun san yadda shi ma yaka so na. Tun da mai son ka yana son abin da kake so.”

Da suka ji wannan bayani nan take sai fuskokinsu suka washe. Kowannensu ya shiga burin jin an furta wadannan masoya, da burin jin sunansa a ciki, don ya ji a ina sunansa ya fada kuma me zai samu. Don haka sai suka ci gaba da yi masa magiyar cewa ya daure ko kadan ne daga ciki ya fada. Shi kuwa da ya ga sun hau turbar da yake so sai ya ce.

“Hakika ba don yadda Sarki ya fada min muhimmancinku a wurinsa ba, kuma ba don kar in bata muku rai ba, da ba zan fada muku ba. To amma tun da haka ne, gobe zan fara sanar da ku wani bangare na batutuwan da ya yi. Domin akwai abubuwan da ko ambtaru ban yi ba ma, bayan wadannan.”

Suna cikin wannan hali, ita kuwa can matar Sarki da ba ta san wainar da ake toyawa ba, ta aika aka kirawo mata Malam Kahuhu. Da Jakadan ya iske shi a gida, shi kuwa sai ya ce a koma a ce mata tun da dai ya zo dubiyar Sarkin jiya ba kuma zai dawo yau ba, sai gobe. Domin bai kamata a ga yana ta sintiri gidan Sarki ba, a matsayinsa na malami ba basarake ba.

Da jakadan ya dawo ya sanar da ita, sai ta kara komar da shi ta ce. “Ka ce masa na hada shi da Ubangiji Al Karim ya sanar da ni abin da ya tofa a ruwa jiya ya ce a ba wa Sarki. Domin na lura bayan na ba shi ruwan ne ya samu damar tashi ya kashingida tsawon lokaci da ya kwanta jinyar nan.”  Da Jakadan ya zo ya sanar da shi sakon ta, sai ya dan yi shiru na wani lokaci cikin alamun nazari, sannan daga baya ya ce da shi:  “Ka ce mata aya ce daga ayoyin littattafan Ubangiji Al Karim. Wato aya ta tamanin da daya  a cikin sura ta goma daga littafin Al Kur’ani mai tsarki. Idan ta iya karanta littafin sai ta rika karanta wannan ayar sau bakwai ta tofa a ruwa ta ba shi ya rika sha, ko kuma ta sa wani ya yi masa.”

Har Jakadan ya ba da baya kuma sai ya kira shi, ya ce masa, “Ka ce mata idan sa wani za ta sa ya yi, to ta sa dabbar da aka haifa, ba wadda aka kyankyasa daga kwai ba. Idan kuwa ba makawa dan kwai ne zai yi, to ta sa wanda aka yi kwancinsa, ba wanda aka binne kasa da lokaci suka kyankyaso ba. Saboda ‘ya’yan da mahaifiyarsu  ta kyankyashe ta kwanta a kansu suka ji duminta, ta kuma ciyar da su, zukatansu suna da taushi. Saboda sun san muhimmancin  soyayya. Amma wadanda suka gan su kawai tsulum a duniya ba tare da samun soyayyar iyaye da dangi ba, sun fi kekashewar zuciya. Saboda ba su da wani abu mai kama da soyayya a zukatansu. Don haka kuma ba lallai su ji tausayi da burin ganin abu ya tafi daidai tsakanin al’uma ba.”

Jakadan ya gyada kai cikin alamta gamsuwa, sannan ya ce. “An gama Malam.” Ya tashi fur, y alula.

<< Yini Sittin Da Daya 32Yini Sittin Da Daya 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×