UBA MAFI UWA - 2
Wannan shi ne kashi na biyu a maudu'in 'Uba Mafi Uwa.' A kashi na farko mun dauko bayanai tun daga tushe; wato dun daga inda yaro yakan gadar kwayoyin halittar da suke samar da kamanni da halayyarsa. Da tasirin da mahaifi yake da shi a wurin wannan jariri tun yana ciki, har zuwa irin gudunmawar da zai iya bayarwa yayin nakudar haihuwarsa. A wannan gabar kuwa, za mu dubi tasirin da zai iya yi gare shi ne bayan zuwansa duniya, a halin yarintarsa.