Skip to content
Part 4 of 5 in the Series Matakan Nasarar Iyali by Hamza Dawaki

UBA MAFI UWA – 2

Wannan shi ne kashi na biyu a maudu’in ‘Uba Mafi Uwa.’ A kashi na farko mun dauko bayanai tun daga tushe; wato dun daga inda yaro yakan gadar kwayoyin halittar da suke samar da kamanni da halayyarsa. Da tasirin da mahaifi yake da shi a wurin wannan  jariri tun yana ciki, har zuwa irin gudunmawar da zai iya bayarwa yayin nakudar haihuwarsa. A wannan gabar kuwa, za mu dubi tasirin da zai iya yi gare shi ne bayan zuwansa duniya, a halin yarintarsa.

Da uba ake rainon da

Binciken da Dr. Arthur Brennan ya jagoranta a Jami’ar Kingston ya tabbatar da cewa. Da zarar an haifar wa mutum da ko ‘ya, nan take jikinsa yake samar da sinadarin prolactin, wanda zai ba shi damar samun juriyar raino! Sinadarin prolactin sinadare ne da yake a jikin mata. Wanda ake yi wa lakabi da “mothering hormone”. Shi ne yake taimakawa wurin gina dukkan wata dabi’a da suffa da suke nuna cewa yanzu mace tana daidai da ta zama uwa. Kamar budewar kugu da girman mama da dangoginsu. Kodayake ba wai sam babu shi ba ne kaf a jikin namiji, amma dan kadan ne.

Abin sha’awar shi ne, a wannan bincike, an gwada yawan sinadarin a jikin wani magidanci mintuna sha biyar kafin haihuwar matarsa. Aka kara gwadawa bayan ta riga ta haihu, har ya ga jaririn. Sai ga shi sinadarin ya karu matuka bayan haihuwar! Ko me ya sa ya karin, kuma ko menene alfanon karuwar?

Kamar yadda na ambata a baya, wannan sanadari akan yi masa lakabi ma da sinadarin uwantaka (mothering hormone). Wato dai shi ne bayan samar da duk wata suffa da ya kamata ta kasance a jikin uwa, kuma yake samar da duk wata dabi’a da za ta taimaka mata wurin juriyar raino da kulawa da jaririnta. Kamar haka ne kuma shi ma uba kan sami karuwar wannan sinadari a jikinsa. Wanda hakan yake ba shi damar tsayawa ya taya matarsa wannan rainon a lokuta da dama.

Sau da dama za ka sami namijin da ba ruwansa da wani daukan yara kanana, ko yi musu wasa. Wani ma ko haihuwa aka yi in aka miko marsa jariri sai ya ce shi ai bai iya daukan jarirai ba. Amma da zarar an haihu a gidansa sai kuma ka taras da shi har ya iya yi wa jariri rawa cikin kankanen lokaci.

Watakila jin wannan canjin zai sa ka tuno cewa, ai yawanci ma mutum mai zafin kai ko mai yawan dukan yara a gida. Irin wanda duk yaran gida shi suke tsoro din nan, da zarar ya haifi da daya sai kuma ka ga ya yi likis. Yanzu ko tsawar kirki ya dena yi wa yara ma. A lokaci guda kuma watakila za ka so jin me ya janyo hakan?

Samun haihuwa yana rage wa uba zafin-kai

Sanannen abu ne cewa, yayin da mutum yake a mataki na samartaka, akan samun sa da zafin-kai. Wato bai cika barin ko ta kwana ba. Haka nan, yakan kasance mai zafin hannu, ta yadda za ka taras da zarar yaro ya yi rashin-ji a gabansa ba ya shayin dukan sa. Shi ya sa ma za ka taras a mafiya yawan gidajenmu yara sun fi jin tsoron yayyunsu, maimakon iyaye. Saboda su ne take-yanke za su ladabtar da yaro. Abin mamakin shi ne, me ya sa kuma idan wadannan samari su ka yi aure su ka haihu sai su yi likis, kamar ba su ne wadancan masu zafin hannu ba?

Sinadarin testosterone da yake jikin dan’adam, shi ne sinadarin mazantaka, da yake taimakawa wurin angiza namiji ya iya shiga cikin kowane aiki ko wasanni na kasada da jarumta. Shi ne kuma yake sa wa mutum jin isa ya zama bai cika juriyar daukar kowane irin raini ba. Ba wai ga bil’adama kadai ba. Ko a cikin dabbobi sinadarin ne kan yi tasiri wurin angiza su su yi ta fada da juna, musamman a kan mace. Masana suna ganin da dai za a zuke sinadarin testosterone kaf daga jikin namiji, to babu shakka da kuwa ya zama wani solobiyo.  Domin akan kara  ko karfafar sanadarin  yayin da aka so kara kwazo da juriyar yan wasanni.

Amma yayin da mutum ya haifi da, nan take sai sinadarin testosterone din nasa ya ragu da kaso mai tsoka. A lokaci guda kuma prolactine yana karuwa. Sai hakan ya kasance wani rufdugun damatsa guda biyu masu janye shi ta karfi daga waccan nahiya ta zafin-kai. Testosterone, wanda shi ke jagorantar fannin kuzari da kafiya da duk wani abu da ya shafi rashin jin shayin komai, ya ragu.  Sannan kuma prolactine da zai tankwara shi, ya ba shi damar yin kamanceceniya da uwa ya karu. Wannan shi zai sa ka taras nan take mutum ya sauya daga yadda ka san shi a baya.

Me wasannin da uba yake yi wa ‘Ya’yansa?

Kodayake, ba lallai ne a ce muna fahimtar komai haka siddan ba tare da bincike ko zurfafa tunani ba. Amma hakikanin gaskiya shi ne, komai da muke yi ko mu ka ga yana faruwa a kusa da mu, akwai dalilin yi ko faruwar san. Idan mu ka yi tsai, mu ka duba yadda iyaye suke yi wa yaransu kanana wasa, za mu iya fahimtar lallai yanayin wasan ya sha bambam matuka, daga na uwa zuwa na uba. Watakila idan za ka waiwaya kadan ka hango yadda uwa take yi wa yaronta wasa, sai ta taras abin bai cika wuce yi masa rawa da ‘yan wake-wake ba. Wata irin rawar nan da za ta zauna, ta rika dan daga shi sama kadan tana yo kasa da shi. Tana yi masa wakar “Kandiyeye in ma ka rawa.” Ko “Taho-taho dan yaro kyakkyawa in ma ka tawai.” Da dangoginsu.

Ko a yayin da mata suke yi wa yaro irin wannan rawar kuma idan mun lura, za mu iya ganin kafafuwansu su na shinfide a kasa. Wato da ma dai yaron zai subuce daga hannu, kan cinyar uwar zai fado. Ba dandagaryar kasa ba. Amma uba sabanin wannan ne nasa.

Yayin da uba ya tashi yi wa dansa wasa, za ka taras shi ne yake iya jefa shi sama ya cafe. Shi ne yake kama hannun yaro ya yi ta jujjuya shi a sama, yana hajijiya da shi. Har wani lokacin sai yaro ya kai matakin da in aka ajiye shi ma ba zai iya tsayawa a kan kafafunsa ba.

Abin da ba mu sani ba shi ne, wannan wasa akwai sakonnin da yake isarwa. Kadan daga sakonnin da wasan mahaifi yake isarwa ga da, su ne: Yaron zai fahimci duniya wani gida ne na gwagwarwaya. Wato dai kai tsaye, ka iya cewa yana koyar da jarumta. Harwayau, yana nuna wa yaro cewa, yana da iyaka. Akwai wurin da bai isa ya je ba. Misali, yayin da aka jefa shi sama. Yana lura da cewa ba wai sararin ne ya kare shi ya sa ya dawo ya yo kasa ba. A’a, iyakar inda dai zai iya zuwa kenan. Da sauran fa’idodi makamantan wadannanne, wadanda kuma suna tasiri a rayuwar wannan yaron.

Uba mai nishadantarwa ne

Laverne Antrobus ta tattauna da wasu kananan yara masu shekaru biyar zuwa bakwai, game da yadda mu’amularsu da iyaye a gida take. Sai ga shi yaran sun tafi a kan cewa iyayensu maza su ne abokan wasa mafi nishadantar da su. Wannan kuma ba zai yi mana wata wahalar fahimta ba. Saboda idan mun kalli gidajenmu ma, za mu iya saurin fahimtar cewa, yayin da yaro ya wuce shekaru biyun farko, uwa ba ta cika damuwa da yi masa irin wasan da yake bukatar motsa jiki ba. Dama dai ita wasanta da yake bukatar motsawa shi ne waccan rawar, kuma da zarar yaro ya zama barden-goyo to ya wuce ta kenan.

A daidai lokacin da yaro ya fara kwari, ya ga yana iya tafiya har da gudu a kan kafafuwansa, lokacin ne yakan fi bukatuwa ga wadancan wasannin na kiriniya. Amma ita a lokacin ta ajiye nata wasan, ta gama. Uba shi yake kula yaro a daidai wannan lokaci a yi ta guje-guje da tsalle-tsalle. Wani lokacin ma har sai uwa ta rika ganin bai dace a biye wa yaran ba. Har ma ka ji tana cewa, “Wai kai ma da girmanka ka rika biye wa yara kuna irin wannan wasan. Sai mutum ya gama gyara wuri ko zo ku bata masa.” 

Irin wadannan wasannin su suke sa ya sau da dama za mu ga idan uba zai fita daga gida, sai yaro ya nace sai ya bi shi. Sai dai a shawo kansa da kyar, ko kuma a rabu yana ta kuka. Domin shi yana ganin abokin wasansa mai nishadantar da shi zai tafi ya bar shi.

Kai, ba ma wasa kadai ba, a cikin yadda muke magana da yara kawai, akwai muhimmin tasiri da alfano da maganar uba take da shi, wanda kuma ba a samu daga uwa. Ya kake tunanin mace goyon-gwauro za ta kasance?

<< Matakan Nasarar Iyali 3Matakan Nasarar Iyali 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×