Skip to content
Part 5 of 5 in the Series Matakan Nasarar Iyali by Hamza Dawaki

ABINDA YA SHAFI KUDI

Tsakure

Kuɗi sun kasance sinadaran gudanar da rayuwarmu ta yau da kullum. Shi ya sa mutane kowa ya raja’a domin ya mallake su. Wanda ya yi nasara shi ne wanda yake iya sarrafa su gwargwadon samunsa. Ashe kenan neman sanin yadda za a sarrafa kuɗi abu ne mai matuƙar muhimmanci. Wannan takarda ta yi tsokaci dangane da muhimmincin tsara al’amarin da ya shafi hidimar kuɗi tsakanin iyali. Abu ne sananne cewar kowacce alaƙar rayuwa na samun nasara ne gwargwadon amincin da ke tsakanin masu tafiyar da alaƙar. A ƙarshe, an ba da shawarwarin yadda za a inganta zamantakewar aure kan abin da ya shafi hidimar kuɗi.

Gabatarwa

Kuɗi shi ne gishirin rayuwa, wanda inda aka rasa shi, za a sha wahala amma idan an samu wajibi ne a yi takatsantsan wajen sarrrafa su. Ana gina rayuwar ne bisa zummar tabbata da juna har abada, watau mutu-ka-raba. Kenan sanin wani abu da yake alaƙa da yadda za a sarrafa kuɗi a cikin iyali yana da matukar muhimmanci. Ingancin aure yana faruwa ne daga irin amincin da ma’aurata suka yi wa junansu. Soyayya ita ce mafari, to amma idan tafiya ta yi nisa, akwai wasu manyan ginshiƙai da suke maye gurbinta, waɗannan ginshiƙai kuwa sun haɗa da sauke nauyin haƙƙin aure, mutunta juna, amana, ban gaskiya da kuma tasrifin abin hannu, ma’ana kuɗi da dukiya.

Tsakanin kuɗi da zamantakewar iyali

Iyali na da alhakin samar da kuɗaɗen da za su warware buƙatun rayuwa na yau da kullum. Irin waɗannan buƙatu sun haɗa da abinci da za a ci, sutura, magani, ilimin yara da sauran ɗawainiya. Shi ya sa Farfesa James Whinney ke cewa, “kuɗi su ne sirrin kyakkyawar alaƙar rayuwar aure.”

Anan ba ana magana ne akan yawan kuɗin da iyali suka tara ba ne, amma ana magana ne akan hanyoyin da suka bi suka sarrafa kuɗin wajen biyan buƙatunsu na yau da kullum.

Idan ya zamana a rayuwar aure babu dabarar da za a iya sarrafa kuɗi idan buƙatar hakan ta taso, zai kasance kenan an shiga hauma-hauma da tangarɗa. A wasu ƙasashen, kamar Ingila da Amerika da sauransu, da zarar an ɗaura aure tsakanin miji da mata, to duk dukiyar da suka mallaka ta zama tasu gaba ɗaya. Hakan ke sa wa koda rabuwa ce ta zo, to sai an raba dukiyar dai-dai wa dai-da kowa ya ɗauki kasonsa. Wannan ta sa iyali suke ɗaukar hayar ƙwararrun masu iya lissafin kuɗi da ƙididdiga su taya su lissafi idan rabuwar ta zo. Irin waɗannan ƙwararru ana kiransu  da suna ‘Forensic Accountants’. Wannan ta sa a can ƙasashen, duk wanda zai yi aure sai ya shiga wani aji na musamman kan yadda ake tattali da sarrafa kuɗaɗe.

Me ya kamata iyali su aiwatar wajen kyautata dangantakar aurensu ga lamarin da ya shafi tasrifin kuɗi. Bari mu yi duba daga janibin Maigida da Uwargida ko Amarya.

Maigida kan gida

Miji shi ne jagoran iyali, shi ne mai samar musu da muhalli da abinci da sutura. Shi ne mai ɗaukar ɗawainiyarsu idan basu da lafiya. Shi ne majiɓincinsu wajen ilmi da tarbiyya da walwalarsu. Don haka shi ne mai fita hidimomi da hada-hada ya samo kuɗin da za a tafiyar da waɗannan abubuwa. Wajibin sa ne ta kowanne janibi ya zamana an samar musu nutsuwa da walwala da jin dadi gwargwadon irin halin da Allah ya hore masa.

Maigida ya kamata ya zamana yana jan iyalinsa a jiki ta fuskar abin da ya shafi hawa da saukar kuɗin da yake samu. Sai dai a bisa binciken da malamai a harkar kuɗaɗen iyali kamar yadda Dakta Francis Nmeribe ya nunar, mazaje ba sa son sakarwa matansu wani abu da ya danganci irin hanyoyin da suke samun kuɗi. Kuma ba sa shigar da su cikin shawarwarin yadda za a kasafta su. Da yawan mazaje, suna ganin mata a matsayin cima-zaune (liability) da ba su iya komai ba sai karɓar kuɗi da kashewa.

Wannan kuwa kuskure ne, ya kamata kowanne magidanci ya riƙa shawara da iyalinsa tare da bayyana musu wani sirri (in ma ba duka ba) na daga abin da ya shafi dukiya da kadarorinsa. Dakta Dave Ramsey ya bayyana wasu hujjoji da ya gane ganin ya kamata maigida ya riƙa nunawa matarsa wani abu daga ababen da ya mallaka na kuɗi ko kadara.

  1. Lalurar rashin lafiya ko hatsari na iya samun maigida, ta yadda za a buƙaci kuɗi da gaggawa. Idan uwargida ta san inda lalitarsa ke boye, komai na iya zuwa da sauƙi.
  2. Mace a gida tamkar manaja ce a ofis, akwai wasu bukatun gaggawa da ke iya tasowa a cikin gida. Yana da kyau a riƙa ba ta ‘imperest’ domin gudun ta kwana. Wannan zai sa gida ya samu maslaha, kuma ba za a damu maigida da tarin ƙananan basussuka ba.

Idan mun lura da kyau, mafi yawancin matsalolin zamantakewar aure suna farawa ne daga irin yadda magidanci ke sarrafa tattalin arzikin gidansa. An bayyana cewar da zarar maigida yayi wa tattalin arzikin gidansa rikon sakainar kashi, to ya samu tasgaro a rayuwar iyalinsa da kimanin kaso 30%.

Don haka yin amfani da kyakkyawan tsari wajen sarrafa kuɗi a gida tare da shawarar iyali na da kyau ƙwarai wajen inganta alaƙar rayuwar aure.

Uwargidan ran gida

Mace a gida tana da muƙamin sakatariya, manaja, sufabeza da heliman. Domin duk abin da za a aiwatar a cikin gidan nan sai an tuntuɓe ta walau kai tsaye ko ta bayan fage. Mace ita ce ran gida, domin duk gidan da babu matar aure a cikinsa, yana cikin garari. Ita ke kula da tsabtar gida, ta ajiye komai a muhallinsa, ta kula da yara sannan ta girka abincin da za a ci kowa yayi walwala da farin ciki.

A taƙaice mace na taka muhimman muƙamai a cikin gida. Kasancewar ta matar aure, tana da alhakin hidima ga mijinta wajen tattalinsa da yi masa girki da aiwatar da umarninsa da kuma faranta masa wajen kwanciya. Tana taka rawa a matsayinta na uwa, ta fuskar kula da yara da taimakawa maigida wajen tarbiyyar su. Har ila yau tana taka muhimmiyar rawa a matsayin ƙwararriyar ma’aikaciya mai gudanar da abubuwan da suka shafi zamantakewar gida na yau da kullum.

Dukkan waɗannan ɗawainiya suna tafiya ne gwargwadon ƙarfin tattalin arzikin da maigida ya sakar mata. Domin babban aikin mace a gida shi ne naƙaltar yadda ake tasrifi da kuɗaɗen da kasafin gidan ke samu. Ɗaya daga cikin halayyar mace tagari shi ne,  naƙaltar yadda za a sarrafa kuɗin da gida ke da shi watau wanda maigida ya bayar ta hanyar da ya dace. Komai ƙanƙantar kuɗi, in dai mace ta san yadda za ta alkinta su, ba karamar daraja hakan zai ƙara mata a zaman aurenta ba.

Rayuwar mace a matsayin uwa ya fi kowanne muhimmanci ta fuskar da ya shafi harkokin kuɗi. Yawancin manyan attajirai na duniya da aka yi da waɗanda ke cin duniyarsu a halin yanzu, da za a duba tarihin rayuwarsu za a ga cewar uwa tayi tasiri ƙwarai wajen koyar da su yadda ake sarrafa kuɗi a zamantakewar aure. Wanda wannan horon ne yayi tasiri a gare su har suka nakalci yadda ake faɗi – tashi a samu nasara.

Akwai muhimman abubuwa guda biyar da ya kamata mu yi koyi da su daga iyayenmu mata wanda za mu aiwatar da su a rayuwar aure ta fuskar tattalin kuɗi. Tasirinsu na da muhimmanci ga yadda za mu riƙa aiwatar da rayuwarmu ta yau da kullum. Waɗannan abubuwa su ne kamar haka;

a. Ajiya (Saving)

Mace ta san yadda ake ajiye kuɗi ta yadda idan buƙata ta taso sai ta yi amfani da su. Mace na da basirar ajiya komai ƙanƙantarta tare da kau da kai ga ajiyar har sai amfaninsu ya zo.  Duk matar da aka ga tana facaka da kuɗi ana ƙaddara cewar bata samu cikakken horo daga mahaifiyarta ba.

b. Tasrifi (Budget)

Abin da ake nufi da tasrifi watau ‘budget’, shi ne sanin hanyoyin da za a alkinta kuɗin da ake samu ta hanyar da za a samu gamsuwa da biyan buƙata.

Mace uwa ta san irin abubuwan da gida ke buƙata da yadda za a samu cikin sauƙi da rahusa. Ta san irin kasafin da za ta yi wa bukatun gida batare da an shiga rububi ba.

c. Iya ciniki (Negotiation)

Mace ta yi ƙaurin suna wajen iya tayi da lallaɓa ciniki har a zo kan yadda za ta iya biya. A shekarar 2007, wani bincike a Indiya ya nuna cewar mata su ne kan gaba wajen iya taya kayayyakin masarufi ta yadda suke samun rara su adana saboda bukatun gaba. Haka nan, Kristy Rampton, wata malama akan halayyar zamantakewar aure tana da ra’ayin cewar, mace na iya sarrafa gidanta idan ta yi amfani da basirar nan da Allah ya ba ta na iya ƙulla ciniki.

d. Haƙuri (Patience)

Haƙuri ba ya ɓaci“, in ji marigayi Ɗan Maraya Jos. Haƙuri na ɗaya daga manyan sinadaran nasara a rayuwa. Haka ma a cikin al’amarin da ya shafi kuɗi da ciniki, haƙuri na taka muhimmiyar rawa. Ballantana kuma a rayuwar aure. Irin haƙurin da mace ke nunawa wajen sarrafa kuɗin gidanta yana sa wa ta zama jaruma mai hasashen alheri tare da cimma dukkan burin da ta sa a gaba.

Masanin ɗabi’un ɗan Adam, Mista Crystal Paine, ya bayyana cewar ɗabi’ar maza ne ba sa iya ɗaukar kuɗi haka siddan su ba wa matansu sai idan akwai dalili. Ya ƙara da cewar haƙuri da kawaici irin na mata ne ke sa wa ba sa iya buɗe baki su roƙi mazajensu duk da irin ƙuncin da suke iya tsintar kansu. Sun gwammace su riƙa ririta abin da suke iya samu daga taskar Allah suna lallaɓawa a haka. Mace tagari tana da tsantsar haƙuri da jure talauci, wanda hakan nasara ce a rayuwar iyali.

e. Maida Hankali (Determination)

Mace idan ta ƙuduri aiwatar da abu tana da ƙoƙari da dagewa kan ganin burin nan nata ya cika. Wanann kuwa ya faru ne sakamakon haƙuri da juriya da Allah ya bata. Wani masanin falsafa na cewa, “duk mijin da yake son cimma wani buri na kuɗi a rayuwarsa. To ya haɗa kai da matarsa. Da sannu za ta kai shi gaci.”

Hannu daya ba ya daukar jinka

Duk ƙoƙarin miji wajen inganta rayuwar iyalinsa ta fuskar sha’anin kuɗi, wata ran sai an samu tasgaro. Haka nan duk ƙoƙarin mace wajen tattalin gida da alkinta arzikinsa, ana iya gamuwa da matsala. Bai kamata kuɗi da dangoginsa su hana iyali sakewa da walwala ba.  A wannan gaɓar, ga wasu shawarwari da ya kamata iyalai su duba domin warware matsalolin da ka iya tasowa kan sha’anin kuɗi.

  1. Ya kamata maigida ka ware wani kaso na kuɗi ka ba wa matarka saboda gudun ɓacin rana.
  2. Maigida ya ƙarfafawa matarsa gwiwar gudanar da sana’a ta hanyar bata jari da shawarwari da sauransu.
  3. Idan maigida ka ci bashin matarka, ka biya ta akan kari ba sai an kai ruwa rana ba. Malam Paul Grey na kamfanin Kent Finance, yana da raayin cewar bashi tsakanin miji da mata kamar haƙorin giyar mota ne, ɗaya na juya ɗaya. Bashi ba zai taɓa ƙarewa tsakanin miji da mata ba. Inda mishkilar take kurum shi ne miji ya yi mirsisi ya ƙi biyan matar. Da kuwa zai yi ta maza ya biya ta, nan take zai iya ɗaukar wani bashin daga gare ta ba tare da ta ji komai ba.
  1. Maigida ya kauda kai ga abin hannun matarsa. Ya zamana baya tsoma mata hannu a cikin dukiyarta har sai idan ta nemi hakan daga gare shi.
  2. Kada maigida ya zamana mai bin ƙwaƙƙwafi da luguiguita bin bahasin yadda aka kashe kuɗaɗen da ya bayar na gudanar da gida. Sai dai ba laifi ba ne ya tambayi bayani idan buƙatar hakan ta taso. Ana kiran wannan da KISS (Keep It Simple Smart) a turance.
  3. Maigida ya samu lokacin da zai rika tattaunawa da iyalinsa dangane da tsare-tsaren da yake son aiwatarwa a gidansa.
  4. Kada uwargida ta zama mai almubazzaranci da dukiyar mijinta. Duk abin da za ta aiwatar ta yi shi bisa nazari da lura da irin samun maigidan.
  5. Mace ta zama mai taimakawa mijinta idan tana da hali. Iyayenmu da kakanni a lokuta da dama sun sha jinginar da kadarorinsu domin agazawa mazajensu.
  6. Kar ki hana mijinki aikata alheri daga dukiyar sa. Ka da ki shiga tsakanin mijin ki da ‘yanuwansa
  7. Idan maigida ya nemi shawararki, ki yi tunani ta fuskoki da dama, misali ki yi tunani ta fuskar uwa, ƙanwa, abokiya, yaya sannan ki ba shi shawarar da ta dace.
  8. Kada ki ɗorawa maigida buƙatar kuɗi da ba zai iya ba. Matuƙar yana kula da wajibabbun haƙƙoƙi, sauran duka nafila ne.
  9. Kada ki damu mijiki da yawan bani – bani. Namiji ba ya son roƙo musamman abin da ya shafi kuɗi. Idan gidanki na cikin buƙatar kuɗi, yi ƙoƙari ki nuna masa hakan a aikace.
  10. Iyaye su riƙa koyawa ‘ya’yansu hanyoyi da dabarun tattalin dukiya, su koya musu dabarar nema da tanadi da wadatar zuci da kuma kyautatawa. Wannan janibi ne mai faɗi wanda ake kira ‘financial discipline’.

Kammalawa

Rayuwar zaman aure da iyali na cike da ɗawainiya iri – iri. Abu ne mai kyau miji da mata su fahimci kansu ta fuskar abin da ya shafi harkar kuɗi tare da yin maslaha da junansu kan abin da suka amince da shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Matakan Nasarar Iyali 4

3 thoughts on “Matakan Nasarar Iyali 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×