A hankali ciwo yake shigar Alheri haka kuma ta yanke shawarar tayiwa Malam Adamu magana ya musuluntar da ita tunda ita ba cocin take zuwa ba, kuma musulunci yana burgeta. Cikin ikon Allah ta musulunta. Haka idan malam Adamu yana karantar da yara takan tura Meenal, sai dai sau tari idan ta turo Meenal sai ya koreta sai ankawo kudin Makaranta.
Alheri ta zauna ta rubuta min dogon wasika tana bani labarin duk wahalar da ta shiga, daga karshe ta rokeni indauki Meenal ta zama 'yata a duk ranar da sakon nan ya riskeni, haka bata son Meenal tasan ta. . .
Wonderful