Skip to content
Part 10 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

A hankali ciwo yake shigar Alheri haka kuma ta yanke shawarar tayiwa Malam Adamu magana ya musuluntar da ita tunda ita ba cocin take zuwa ba, kuma musulunci yana burgeta. Cikin ikon Allah ta musulunta. Haka idan malam Adamu yana karantar da yara takan tura Meenal, sai dai sau tari idan ta turo Meenal sai ya koreta sai ankawo kudin Makaranta.

Alheri ta zauna ta rubuta min dogon wasika tana bani labarin duk wahalar da ta shiga, daga karshe ta rokeni indauki Meenal ta zama ‘yata a duk ranar da sakon nan ya riskeni, haka bata son Meenal tasan ta hanyar da aka sameta.

Haka suke rayuwa da ita da ‘yarta cikin kazanta. A lokacin bakin Meenal ya bude sosai ta kware a surutu.

Cikin daren ranar laraba take duban ‘yarta duba me dauke da abubuwa kala-kala. Ta dubi ‘yar da kulawa ta ce mata “Meenal kawo min ruwa insha.” Meenal din ta fita tana neman ruwa babu ta nufi wani gida ta mika masu kwano cikin maganarta ta yarinta ta ce a sammata ruwa. Aka zuba mata ta dawo ta ba Alheri da ta ci sunan Maryam, tasha ruwan. Tana shafa kan yarinyar albarka kawai take sa mata. Tausayin yarinyar yayi mata yawa, dan haka ta rungumeta tsam a kirjinta. A wannan lokaci Allah ya zare ran Alheri, a wannan daren Meenal ta tabbata mareniya. Allah babu ruwansa, da ba haka ba tabbas da Allah ya bar Alheri ko dan Meenal.

Meenal tana tashi ta dinga kuka tana tayar da Mamanta ta kawo mata abinci yunwa take ji, amma shuru babu motsi. Meenal tana nan zaune a kofar akurkin sai ajiyar zuciya take yi, bakin nan ya bushe. Ta sake komawa kan gawar tana bubbugata tana fad’in Mama ki tashi yunwa nake ji. Daga karshe ta mayar da kanta kan gawan ta kwanta tana ajiyar zuciya. Sai yamma sosai Meenal ta fito tana gayawa Malam Adamu Mama taki tashi. A lokacin ne aka leko aka ga gawanta har ya sandare. Alheri dai ta bar gidan duniya.”

Kuka sosai Umma ke yi kamar yanzu akayi mutuwar. Dr. Bakori ya sunkuyar da kansa yana jin Karin imani yana ratsa shi. Muryar Umma ya ji ta ci gaba da bayani,

“Malam Adamu ya jagoranci yi wa gawanta Sallah aka rufeta. A ranar Meenal kwanan kuka tayi tana neman mahaifiyarta. Haka babu tausayi Meenal ta ci gaba da kwana a cikin dakin awakin da mahaifiyarta ta gina. Idan gari ya waye ta dauki kwano taje roko. Sannu a hankali ta saba da bara, haka idan ta dawo zata shiga cikin dakin awaki ta kwanta. Idan kewar uwar ya motsa mata tasha kukanta.

Malam Adamu ya tausaya mata ya kwashi abubuwan da mahaifiyar ta bari ya dawo da Meenal cikin gidansa. Yana mamakin karamar yarinya ta saba da matsalolin rayuwa.

Duk da hakan bata da kwanon abinci a gidan Malam Adamu sai taje tayi bara sannan take samu ta ci. Haka idan bata samu ba dama tara hannu zata yi Saude ta zuba mata abincin a hannunta shikenan ta gama cin abinci. Lalle da ace Meenal ba kafin Allah ba ce da tuni ta dade da bin mahaifiyarta.

Haka zata kwana a waje tana murkususun ciwon ciki babu me kallonta bare a ce mata sannu. Wataran Saude ta kama ta tayi ta dukanta tana rantsuwa ta sace mata naira biyar. Har ya zamana jikin Meenal duk tabon duka ne na Saude. Da asuba ana doka sanyi Meenal tana waje tana wanke wanke. Tun tana yi baya fita har ta saba.

Idan sun koreta sai ta koma makwancinta da uwar ta kwanta kawai tana kuka. Zai yi wahala ka dubi yarinyar nan baka zubar mata da hawaye ba.

Kayan jikin Meenal kadai idan ka kalla ba zaka so sake marmarin dubanta ba. Gaba daya sun yayyage almajiri ya fi Meenal kyan gani. Daga karshe aka hau dora mata talla, idan bata siyar ba a ranar da wayan wuta za a zaneta. Yunwa ya riga ya gama cinye Meenal. Kallo daya zaka yi mata ka fahimci ba lafiyayya ba ce.

Akan bola anan Meenal take zama tana neman abinda zata iya ci, duk zafin rana ko tsananin sanyi.

Ana ruwan sama Saude zata wurgo ta waje haka zata rabe cikin ruwan nan ya kare akanta.

A lokacin ne ni kuma mijina ya rasu. Ya rasu ya barni da ‘yata Nafisa. Don haka ina fita takaba hankalina ya dawo kan Alheri da take yawan zuwar min a cikin mafarki. Dole na kama hanya nazo gidan da nake da tabbacin anan take. Ina zuwa naga gidan ya rushe hankalina ya tashi na shiga gidan Malam Adamu. Ina zaune na kafe Meenal da ido da aka gama zaneta saboda bata yi wanke-wanke ba. Tana kuka tana aikin. Tausayinta ya kama ni na koro masu bayani akan ni ‘yar uwar Alheri ce. Anan take aka nuna min Meenal a matsayin gudar jininta aka kuma kawo min tarkacenta. Ina karanta wasikan nan ina kuka. Na dube su cikin kuka nake ce masu, “Alheri mutumiyar kirki ce dan uwanku Musulmi ya sanyata a cikin wannan halin.”

Jikinsu duk ya yi sanyi na jawo Meenal na rungumeta ina kuka. Wata makwafciyarsu ta dinga bani labarin irin wahalar da Alheri tasha da ‘yarta.

Na kawo Meenal gidan Yayana domin nima iyayena sun rasu, na gaya masa komai ya tausaya kwarai kuma ya yi alkawarin taimaka min akan tarbiyyan Meenal. Haka ya hada min da ‘yarsa Rufaida ya ce duk inrike su.

Kaji mafarin dawowar Meenal gidana. Bayan Meenal ta fita daga wannan kangin na mayar da ita mutum. Na sata a Makaranta me kyau ta goge. Allah ya jarabceni da son Meenal fiye da yadda nake jin son Rufaida, da ‘yata Nafisa.

Kasancewar Nafisa ce ‘yar karama sai suka dauki soyayyar duniyar nan suka dora ta akan Nafisa. Ko Makaranta suka je suka dawo da tsarabar Nafisa a jaka.

Ni kuma na mayar da hankalina wajen tunanin hanyar da zan bi wajen sanar da mahaifin Meenal halin da ake ciki da ‘yarsa. A wannan lokacin ne yaron makocin mu Lukman yake shiga gidana, ta hakane shakuwa me karfi ya shiga tsakaninsa da Meenal. Gaba ɗaya ya shagwabata. Ban damu ba ban kawo komai a raina ba, sai ma murna da nake yi. A lokacin ne na sake yin aure.

Wanda na aura dukan mata yake yi, hakan yasa a lokacin farko Meenal ta fara kyamatar halayyar maza. Haka kawai sai ya shigo ya kama fad’a da zarar na tanka duka ne zai biyo baya. Dalilin hakan yasa Meenal ta tsane shi, daga karshe ya rabu dani adalilin ya ce min sai dai in rabu da Meenal na nuna masa mutuwa kaɗai ce ta isa ta rabani da ita.

Haka na ci gaba da zama babu miji, da zarar anzo za a aureni sai ace ai shegiya nake riko. Lukman ya kasance namijin da ke faranta ran Meenal bata jurewa rashin ganinsa ko da na rana guda ne.

Meenal tana da shekaru goma sha shida a duniya, a lokacin duk wani kyanta ya gama bayyana, haka bata mance wahalar da tasha ba, sai dai ta mance mahaifiyarta ta rasu, ta fi ganina a matsayin uwar da ta haifeta. Nafisa ta kasance ‘yar kanwarsu da suke matukar so kamar suyi hauka. Haka Lukman ya kasance namijin da take so fiye da kanta. Sai babbar kawarta da shakuwarsu yake ba mutane mamaki.

Rukayya babbar aminiyar Meenal ce tana iya sadaukar da komai akan Rukayya. Sau tari idan Lukman yana nuna mata baya son alakarta da Rukayya takan yi dariya ta ce Yayana matsayin kowacce daban. Meenal tana karyata duk mutanen da suke cewa ƙawa ba ta da amana. Ta yarda Rukayya zata iya boye aibunta don kawai ta siya mata mutunci. Abinda Meenal ba tasani ba Rukayya da sauran kawayenta sun tsani su ga wani abu na cigaba ya sameta. Hatta Lukman din sun sha samunsa suna gaya masa Meenal tana kula samari haka har dakin samari tana zuwa. Daga karshe sun tabbatar masa da Meenal yaudararsa zata yi dan uwanta zata aura. Hakan yasa Lukman ya fara tsanar Meenal.

Lokacin da ya fara juya mata baya, Meenal ta fice hayyacinta domin tun tana ‘yar karamarta tayi mugun shakuwa da Lukman. Ganin zan iya rasa Meenal yasa na kira Lukman nayi masa fada dan haka suka dawo kamar da.

Ranar na tafi gidan Yayana na bar direba ya dauko su idan lokacin tashi daga makaranta tayi. Meenal da Nafisa suka fara dawowa. Rufaida kuma suna can suna zana jarabawa.

Ganin bata ga Lukman duk sai ta damu tayi tagumi. Nafisa ta dubeta ta hau jikinta ta cire mata tagumi, “Anti me yake damunki?”

Ta kamo yarinyar ta rungume a kirjinta, “Nafisa ban ga Yaya Lukman ba ina jin gabana yana fadiwa. Yaya Lukman ya gaya min ba zai iya rayuwa da kowacce mace ba sai ni Meenal. Ina son Yaya Lukman kema ki taya ni sonsa kin ji?”

Nafisa ta gyaɗa kanta tana dariya, “Anti nima kina sona? Wai anti bamu da Baba ne?” Meenal ta yi murmushi ta ce, “Na fi son ki fiye da komai Nafisa. Ki bar maganar iyayen mu ba sa son mu, Umma da Baba Sani sun ishe mu rayuwa. Gaya min abinda zaki ci inje indafa maki yanzu.”

Nafisa ta yamutsa fuska, “Indomie zan ci anti.” Da sassarfa ta shiga kichin ta samarwa Nafisa da Indomie.

Tana nan zaune Nafisa ta kara zuwa kusa da ita tana duban Meenal, ” Anti kada ki damu da abin da zai sameki. Nidai kiyi min addu’a kawai. Nasan ba zan kai ki girma ba.” Meenal ta zaro ido sai ta hau kuka da rawar baki, Ta ce

“Nafisa meyasa kike irin maganar nan? Nafisa kada ki sake fada kinji?” Rungume Nafisan tayi gabanta yana wani irin fadiwa. Tana jin da ta rasa Nafisa gara ita ta rasa rayuwarta. Miƙewa ta yi ta nufi gidan su Lukman tana son ta gaya masa kalaman Nafisa. Har ta kai kofa Nafisan ta ce, “Anti ki jirani mu tafi tare.” Dawowa tayi ta sake rungumeta tsam a jiki, ” Nafisa na haramta maki fita ko nan da can. Don Allah Nafisa ki taimakeni kada ki fita ke ce dukkan rayuwata.” Nafisa ta goge nata hawayen tana duban Meenal har ta fice.

Kai tsaye ta nufi ɗakin Meenal ta ciro doguwar rigarta tasa tare da hayewa kan gadonta ta yi ruf da ciki.

Meenal tana shiga sashen Lukman taga ansakaya ƙofarsa don haka ta shiga kawai ba tare da tunanin komai ba. Abinda Meenal ta gani yasa kwakwalwarta neman fashewa. Rukayya ce da Lukman suna aikata masha’a.

Mutanen da Meenal ta mikawa amana yau sune suke cin amanarta. Wannan abu da Meenal ta gani bana jin har ta koma ga mahaliccinta zata iya mance shi. A hankali take ja baya gaba ɗaya sun firgita. Da gudu ta fice daga gidan tana kuka tana rike kirjinta da ke yi mata nauyi. Da ƙyar take jan numfashinta. Kai tsaye dakina ta shige tana rizgar kuka. Da gaske take karyata abinda idanunta ne suka gani ba labari aka bata ba.

Tashi ta yi da ninyar cewa Nafisa tazo su bar gidan za su bini zuwa gidan Yayana. Kara da ta ji yasa ta nufi hanyar ɗakinta da gudu jikinta yana kyarma. Ashe bayan fitarta Lukman ya cewa Rukayya kawai zai je ya kashe Meenal kada ta sanarwa iyayensa abinda ke faruwa. Kai tsaye ta bashi goyon bayan ya kashe ta din kawai. Don haka ya dauko wuka ya nufi ɗakinta, ganin Nafisa a kwance yayi zaton Meenal ce idonsa ya rufe ya dago yarinyar nan ya caka mata wuka har sau biyu. Ya juya zai fita kenan ya ci karo da Meenal, ruɗewar da ya yi yasa ya tureta ya fice da gudu. Meenal ta zama zararriya gata ‘yar yarinya karama ta kama Nafisa da jini ya ba ta mata kaya. Jinin ya fallatso mata a fuska ta dinga juya hannunta jikinta yana karkarwa.

A lokacin ne na dawo ni da Rufaida kai tsaye dakin Meenal muka nufa. Innalillahi wa inna ilaihirraji’un Doctor sun kashe min Nafisa sun kashe min ita na rasa Nafisa har abada narasa ‘yata.Meenal bata gane komai Meenal zaune ita ba me rai ba ita ba matacciya ba. Haka hannunta bai daina nuna Nafisa ba. Rufaida tana ganin wannan aiki ta sume agurin ni kuma sai inkama Nafisa sai inkama Meenal da a wurinta ne kadai zan iya samun karin bayani to Meenal babu baki jikinta kawai ke rawa kamar anjona mata shokin. Allah sarki Nafisa ta dameni da zancen mutuwa ashe tafiya zata yi. Bana jin har mu mutu zamu mance wannan bakar ranar. Bana jin Meenal zata warke daga wannan masifar.

Bansan wa ya kira ‘yan sanda ba sai ga su sun zo babu tausayi suka kama hannun Meenal da ke rawa suka sanya mata ankwa. Sai a lokacin ta saki wani ajiyar zuciya tare da hawaye masu zafi haka sai a lokacin ta fasa wani irin kuka me karfi kafin kuma numfashinta ya dauke gaba daya.”

Hajiya Salma tana kawowa nan kuka ya ci karfinta. Ji take yi kamar yanzu ne abin ya faru. Tana jin dacin rashin ‘yarta kwaya ɗaya tal. Kallo ɗaya zaka yi wa Doctor Bakori ka fahimci yana cikin halin baƙin ciki da tausayi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Meenal 9Meenal 12 >>

1 thought on “Meenal 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×