Skip to content
Part 11 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Jikin Hon Munnir ya yi matukar sanyi, lalle ya hadu da wanda yafi shi sanin duniya. Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ce, “Ina jinka, idan hanyar ta yi dai-dai da ra’ayina ai shikenan.”

Doctor Bakori ya mike ya zauna suna fuskantar juna, “Ina son ‘yarka Meenal. Idan Meenal ta rasa rayuwarta a ta dalilinka, ina tabbatar maka sai na karar da kaf din zuri’arku.

Dangina ma ba zan daga masu kafa akan Meenal ba, bare kai da kake matsayin surukina. Angaya maka halin da mahaifiyar Meenal ta shiga amma baka tausaya mata ba, sai ma kama Meenal da kayi ka daure a gindin bishiya me dauke da ƙayoyi, hakan bai yi maka ba, sai da ka sake dauko ta ka hada ta da ruwan wanke-wanke. Kai Allah shi kyauta! Wallahi ko makiyina ba zan iya yi masa wannan rashin imanin ba.

Ina son kasa a warware sharrin da akayiwa Meenal a sake ta, don ina da bukatar matata. Zan dauke Meenal mu bar kasar nan, wanda kai zaka dibi rabin dukiyarka ka mallaka mata, a matsayin kasonta tun da ba ta da gadonka.

Ba zan taɓa barin asirinka ya tonu ba, domin idan muka fice ba zaka sake jin koda labarinta ba. Idan aka saketa gobe nayi maka alkawarin jibi zan yi wa Alhaji Khalid allura ya bar maka duniyar, tunda shine kadai matsalarka. Hajiya Salma kuma bamu da matsala da ita, domin da zata tona asiri da tuni ta tona, ita kanta bata son Meenal tasan ba ita ce ta haifeta ba. Hakan ya yi maka?”

Hon Munnir ya saki murmushin jin daɗi ya ce, “Yaro me hikima. Hakan ya yi kuma nayi na’am da hakan. Zansa a sako Meenal gobe zan hankada wacce tayi kisan inmika ta.” Dr. Bakori ya dube shi,

“Wacece tayi kisan?”

“Kawarta ce Farida ta yi kisan, Halima ta hada mana tarkon yadda zamu yi, saboda angaya min tana yawan zuwa mashaya da wuka saboda anan saurayinta da ya kashe mata kanwa yake, yawan zuwa. Shiyasa muka yi ta amfani da zuwan da take yi muna kafa mata tarko ta hanyar kashe jama’a.

Daga bisani kuma nasa aka kawo min fuska irin na Meenal muka sawa wata. Angaya min kai ka fara ganewa ba Meenal ba ce, gaskiya kaifin tunaninka yana burgeni.” Ahmed ya girgiza kai, “Ba kaifin tunani bane, karfin so ne yasa haka.”.

“Yanzu dare ya yi ka bani masauki.” Hon Munnir ya sake duban Dr. Bakori zai so ‘yarsa Husna ce ta sami miji kamarsa. Cikin sauri ya kawar da zancen ta hanyar cewa, “Ba zan bari a fito da Meenal ba har sai kayi wa Alhaji Khalid allurar nan.”

Gyada kansa ya yi yana lumshe idanunsa, “Babu damuwa bana son a shiga da ita kotu ne kana iya amsota ka ajiyeta a gidanka kana jin labarin mutuwarsa ka bani matata. Amma da sharadi abinci mai kyau zata ci kamar yadda kaima zaka ci.”

Hon Munnir ya amince da maganar Dr. Bakori dan haka suka bashi masauki anan. Duk da ya rufe kofa hakan baisa ya iya rintsawa ba. Domin babu yarda a tsakaninsa da mutumin da yake harin rayuwar mahaifinsa.

Da sassafe ya fice daga gidan yana dagawa yaransa hannu. Mahaifinsa ya kira ya kora masa dukkan abinda ke faruwa. Shuru ya yi na wasu ‘yan dakiku daga bisani ya gaya masa yadda abin zai kasance.

Wannan karon ba Sokoto ya tafi ba, kai tsaye Gombe ya wuce. A katon falon Alhaji Khalid Dr. Bakori ne yake yi masa ‘yan gwaje-gwaje daga bisani ya ce kowa ya fita ya basu wuri.

Alhaji Khalid ya dube shi da mamaki, sai dai bai ce komai ba har sai da dakin ya rage saura su biyu. “Alhaji turo ni akayi in kasheka.”

A firgice Alhajin ya dago kai yana duban Dr. Bakori. “Me nayi da za a ce ka kasheni? Bana jin ina da abokin fada, haka bana jin na taba sa’insa da wani da har zai nemi rayuwata.”

Dr. Bakori ya yi murmushi yana jinjina halayyar mutane kamar ba za a mutu ba.

“Abokinka ko ince Amininka Hon Munnir shi ya turo a kasheka. Saboda kasan sirrinsa na ‘yarsa Meenal yana tunanin zaka ruguje masa tsari wajen sanarwa mai martaba. Haka zalika ni ne na auri ‘yarsa Meenal da ke can a kulle. Zabi biyu ya bani ko in kasheka ya fito min da matata ko kuma inbarka da rai matata tayi zaman gidan yari.”

Alhaji Khalid yayi shuru. Hawaye suka cika masa idanu, “Akan wannan dalilin Munnir zai nemi rayuwata? Da zan tona masa asiri ai da tuni na tona masa. Yanzu menene shawara?”

Dr. Bakori ya saki alluran guban yana murmushi, “Ko bera ba zan iya kashewa ba, bare mutum. Ban tanadi amsar da zan baiwa Allah ba, a ranar da babu Hon Munnir bare insa ran zai iya taimaka min. Kawai yanzu ka kira amintaccen wani likitanka ya kai ka asibiti ya boye ka daga nan a fito a gayawa duniya ana nemana nayi maka allurar guba. Kada ka damu da bata min suna da zaka yi, na gama shiryawa komai. Ace likitoci sun dukufa akanka don baka mutu ba, amma a kowani irin lokaci kana iya rasa ranka. Idan ya ji labarin ana nemana zai fi shiga rudani gudun kada asirinsa ya tonu zai so inyi nisa da garin. Amma kafin nan bayan na bar gidan nan kasa a kira shi a waya a matsayinsa na babban amininka a gaya masa anyi maka allura mai dauke da guba. Babban damuwata ya bani matata ba tare da wata matsala ba. Ni na barka lafiya.”

Har ya kai bakin kofa ya ji muryar Alhajin yana magana, “Me kake so inbaka Doctor.”

Girgiza kansa ya yi, “Ba yanzu ba, akwai lokacin da nima zaka rama min abinda nayi maka, amma ba da kudi ba.”

Washegari aka fitar da Meenal ta hanyar damko Farida, da Halima. Wannan abu ya ba Meenal mamaki tayi ta duban su tana sakewa. Hawayenta ta sharce
“Yanzu Halima ni zaki yaudara? Me nayi maku? Wani irin kyautatawa ce da kawa take yiwa kawa wanda ni ban yi maku ba? Halima bana jin zuciyar da kuka sanyata a cikin kunci zata iya yafe maku. Bana jin macen da kuka kunyata a ranar daurin aurenta zata iya yafe maku.”

Kukan ta cigaba da yi, Farida ta bata amsa da cewa, “Mahaifinki ma yaci amanarki bare mu da haduwar bariki ce kawai? Idan da wanda ya kamata ki tsinewa ba zai wuce jahilin mahaifinki ba, da ya zabi duniya akanki.”

Duk irin abinda Hon Munnir ya aikatawa Meenal sai da taji zafin zagin da Farida tayi masa. Uba har abada uba ne komin lalacinsa. Tasan har ta mutu ba zata iya kankare jininsa a jikinta ba, haka shima. Sunkuyar da kai tayi kawai ta wuce su, tana sake waigen Halima. Bai kamata tayi mamaki ba idan ta tuna Lukman da Rukayya.

Bata ga su Umma ba haka direba din da ya dakkota bata san shi ba. Haka gidan da aka kaita aka ajiye bata taba ganin gidan ba.

Kayan sawa ta samu hakan yasa ta nufi bandaki ta gasa jikinta da ruwan zafi sannan ta fito tayi Salloli ta zauna ta dan ci abincin kadan ta kwanta shuru.

Dr. Bakori da tun safe ya kama hanya ya dawo Kano ya shiga Hotel din da ya kama ya yi kwanciyarsa. Yana son ya dan huta yaje ya dauko motarsa. Sai da Alhaji Khalid ya tabbatar masa angama shirya komai kafin Dr. Bakori ya kira Hon Munnir ya ce masa ya gama aikinsa yasa yaransa su dauko Meenal su kawo ta Hotel din da ya sauka tun jiya zai yi waya a bata key idan ya zo zai dauketa daga wurin kwata-kwata. Daga nan ya tura masa account number ya ce ya tura mata dukiyarta.

Hon Munnir bai aikata aiki ko daya da Dr. Bakori ya ambata ba har sai da ya sami kiran gaggawa akan abinda ke faruwa da da Alhaji Khalid sannan ya mika Meenal ya kuma basu zunzurutun kudi har naira Miliyan hamsin.

Dr. Bakori ya fito da kansa bakin harabar Hotel din suka gaisa suna dariya, sannan suka umarci Meenal da ta fito. Tana fitowa suka kafe juna da idanu babu ko kiftawa.

A hankali ya taka ya isa gareta. Tana son yin kuka ya girgiza mata kai tare da dora yatsunsa a bakinta, “Shihhh… Bana son kuka Meenal. Ok?” Gyada kanta tayi, tana bukatar samun makwanci a faffadan kirjinsa. Don haka ta kwantar da kanta luf. Yana jin yadda faduwar gabanta ke tsananta. Hannu yasa ya zagayota yana lumshe idanu.

Daya daga cikin yaran ya yi gyaran murya. “Yallabai a titi ake.” Firgigit suka yi daga shi har ita. Sai da ya saita muryarsa da ke barazanar shakewa sannan ya ciro key din mota ya mika masu. “Ku je inda kuka dauko ni ku kawo min motata.”

Dr. Bakori ya tura ƙyeyan dayan, “Maza kuyi sauri sarakan sa ido.” Dariya suka yi sosai suka ciro kudaden nan suka bashi ya karba tare da kamo hannun Meenal suka shige ciki.

A dakin nasa shirya kayansa kawai yake yi ba tare da ya dubeta ba. A hankali ta karaso jikinta duk a sanyaye tana matukar jin kunyarsa. Hannu ta kai kan rigar da yake ninkewa itama ta rike da alamun tana son karasa aikin ne.

Kafe juna suka sake yi da idanu a karo na biyu. Wani irin sanyi ke huda dukkan ilahirin jikin su, tare da wata natsuwa da ke shigar kowanne daga cikin su. Lumshe idanunta tayi gabanta na fadiwa dan jin numfashinsa gaf da ita ta riga ta sadakar kissing dinta zai yi. Idan kuwa hakan ya faru zata iya sumewa, saboda wani sabon al’amari ne da ba zata iya kwatanta yadda zata ji ba.

Shuru taji dan haka ta bude idanun da suka cika da ruwan hawaye. Akan fuskarta yake magana, wanda gaba daya ya gama kashe dukkanin jikinta, “Meenal ki natsu babu abinda zan yi maki.”

Ajiyar zuciya ya kwace mata da karfi wanda hawayen fuskarta ya zuba har baki. Hannu yasa ya ɗauke hawayen. Wani ajiyar zuciya ta sake saki mai ‘yar kara. Gaba daya ta tafi wata duniya da ita kanta bata taba shigar irinta ba.

Shi kansa ya shiga wata duniya da ba zai iya jawo kansa daga cikinta ba.

Motsa bakin take yi wanda yake nuna masa zallar tana son abinda yake son yi. Yana kokarin yin wani abu aka kwankwasa kofa.

Dr. Bakori ya yi ajiyar zuciya ya zare jikinsa. Jiri ke son kwasarta dan haka ya kwantar da ita ya bata peck a goshi, “Sorry bari induba.”

A sarke ya hada kalmomin ya fitar da su. Yana budewa ya ga masu kawo abinci ne dan haka ya karba kawai ya juya ya rufe kofar. Akan gadon ya biyota da abincin ya ce ta tashi ya bata. Da hannayensa yake mika mata abincin. Ita dai bude bakin take yi tana karba.

Rike hannunsa tayi tana girgiza masa kai kamar zata yi kuka, “Idan kin koshi zan daina baki ba sai kin yi kuka ba. Bana son kuka idan kina kuka zamu bata. Bari a kawo min motata inkaiki gidan Umma ko?”

Tuntuni abinda take bukata kenan ta kasa yi masa magana. Dan haka da sauri ta gyada kanta. Yana son tayi magana yana son ya ji sassanyar muryarta. A kowani lokaci Meenal tayi magana shi kadai yasan yanayin da take jefa shi na farin ciki ko da kuwa maganar bacin rai ne.

Cikin sauri ya gama kintsawa a lokacin ne kuma yaran Hon Munnir suka dawo. Su suka kwashe masa kaya zuwa Mota shi kuma yana rungume da Meenal har cikin mota. Yaran suka raka shi har gidan su Meenal saboda samun wuri.

Anan suka yi Sallama. Ahmad ya rubuta masu cheque na miliyan biyu, ya ce su rike zai kira su insha Allahu zai taimaka masu. Aikuwa sun ji dadin kyautar nan domin a tsakaninsu da Hon Munnir kyautar dubu hamsin ce daga nan bai taba yin sama ba, suma sai ya jima bai basu ba. Don haka suke ganin kyautar nan tamkar kyautar Aljannah akayi masu amma ta duniya.

Umma da ta gama kallon labaran abubuwan da suka faru ta kosa ta ga Meenal dinta. Tana bude kofa Meenal ta rungumeta. Sai a sannan ya ji muryar Meenal cikin kuka, “Babana duk shi ne ya zama silar shigana wannan matsalar tare da taimakawan kawayena. Saurayina ya kashe min kanwata ya ja na shiga gidan yari kullum fargaba nake yi gari ya waye domin bansan wacce kaddarar ce zata sake samuna ba. Umma ina son kiyi dogon tunani Abbana shi ya haifeni kuwa? Ya kamata ace yana jin wani abu ransa a game da ni. Umma ki karyata ni ki mari fuskata indawo hayyacina. Ki gaya min ba Hon Munnir ne ya haifeni ba.”

Dr. Bakori ya kafe su da idanu. Yarinyar tana bashi tausayi. Wayarsa ya dora a kunne yana Salati, “Yaushe Hon Munnir ya rasu? Hatsari kuma?”

Cak! Meenal ta daina kukan hakan yasa ya daina amsa wayar yana kallonta. Wasu hawayen ke sake fita daga idanunta, ” Doctor mahaifina ya rasu? Innalillahi wa inna ilaihirraji’un. Wayyo rayuwa ya zaki yi min haka? Hon Munnir meyasa? Meyasa zaka tafi ka barni a duniyar? Shikenan haka rayuwata zata cigaba da tafiya?”

A natse ya karaso gabanta ya rike kafadunta. “Mahaifinki yana nan da rai cikin koshin lafiya. Nayi hakanne saboda inbaki amsar da kike tambayar Umma. Mahaifinki har abada mahaifinki ne. Haka kamar yadda kike jin kaunarsa duk irin izayar da ya yi maki haka shima yake jin irin wannan ƙaunar a zuciyarsa. Da Hon Munnir baya sonki da tuni ya kasheki, kashe ki a cikin minti biyu ba zai yi masa wahala ba.

Ki zauna kiyi nazari sosai ya taba tsayawa agabansa anyi maki izaya? Ki tuna sosai kila akwai lokacin da ya taba dakatar da mutanensa idan suna wahalar da ke a gabansa. Kiyi wa mahaifinki uzuri har gobe kin kasa tsanar mahaifinki kamar yadda ya kamata ki yi. Ki dauka wannan kaddararki ce. Nayi maki alkawarin sai zuri’arku sun yi alfahari da ke. Zaki zama abar kwatance. Kiyi hakuri zan wahalar da mahaifinki a dai-dai lokacin da yake da bukatarki. Ina son kiyi min alfarma ki mance sharri ki dawo da alkhairin da bawa ya yi maki komin kankantarsa.”

Hannu yasa ya dauke hawayen idanunta. Umma ta gama amincewa Dr. Bakori shine wanda Allah ya turo rayuwar Meenal domin ya daidaita masa ita. Gaba daya suka shiga falon suka zauna. Umma ta dubi Meenal ta ce, “Meenal kiyi hakuri ki dauki abinda zan gaya maki a matsayin abinda bamu isa mu sauya ba.”

Doctor Bakori ya girgiza mata kai, “Umma abinda zaki gaya mata ba wata matsala ba ce, ya zama dole ta sani. Ba Umma ce ta haifeki ba, mahaifiyarki ‘yar wani pastor ce. Samun uwa kamar mahaifiyarki abu ne mai matukar wahala. Yau da mahaifiyarki tana raye sai nayi mata abinda zata mance bayanta. Ta zama jarumar uwa. Hakika duk wanda ya rasa uwa ya rasa mafi yawan gatansa. Allah ka sakawa iyayenmu mata da alkhairi.”

Sannu a hankali Umma ta cigaba da warwarewa Meenal wacece ita. Kafin Umma ta karasa har Meenal ta sume agun. Dr. Bakori ya dafe goshinsa, yana jin anya da wata ‘ya mace me irin kaddarar Meenal? Shi da kansa ya yi ‘yan dabarunsu har ta farfado da wani irin kuka mai karfi, sai dai sabanin abinda suke tunani shi take furtawa,

“Mahaifiyata kin fiye min kowa da komai. Dama ace kina raye da na gwada maki soyayyar da zaki yi tunanin babu wata ‘ya ta kwarai kamar ‘yarki. Hon Munnir ka cuceni ka cuci rayuwata. Allah ka gaggauta saka wa mahaifiyata.”

Rungumeta ya yi yana bubbuga bayanta, a take ta nemi kukan da take yi da karfi ta rasa, “Kada bacin rai yasa ki fada magana mara kyau akan wanda ya haifeki. Bana so Meenal bana so. Kin sami tarbiyya, har yanzu baki rasa Uwa ba. Umma ta baki duk wani gata da kike nema. Kiyi wa mahaifiyarki addu’a. Ki natsu ki dinga addu’a a maimakon kuka da damuwa.”

Juyowa suka yi suka ga Babu Umma ta shige d’aki tana risgar kuka. Mutuwar kawarta ta dawo mata sabuwa. Rayuwar da kawarta tayi na wahala ya dawo mata cikin rayuwarta.

Ganin lokaci yana kara wuce wa yasa ya nunawa Meenal hanya alamun tabi bayan Umma. A daki ta same ta suka rungume juna suna kuka. Daga baya Umma ta ce, “Ya isa haka. Ga Dr. Bakori nan. Idan kika kasa yi masa biyayya ba zan taba yafe maki ba Meenal. Abinda zaki yi masa kenan ki biya shi. Allah ya yi maki albarka.”

Umma ta raka su har gaban mota. Meenal tana share hawaye tana kallon gidan su kallo me kama da na karshe suka bar gidan. A hanyar Abuja gudu kawai yake kwararawa baya hangen komai sai Abujan nan. Anan ne zai fara aikinsa na gaba akan Meenal da Hon Munnir.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Meenal 10Meenal 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×