Skip to content
Part 13 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

“Babu tausayi bare imani aka wuce da Meenal a sumen. Yaya Sani da ya sami kiran gaggawa yazo ya sami Nafisa a shimfide bata motsi. Duk yadda zan kwatanta maka irin tashin hankalin da muka shiga ba zaka fahimta ba, idan ba kana wurin ba. Meenal tana farfadowa aka rufeta da duka, bata iya cewa eh bare a’a sai dai aga tana duban hannayenta tana kukan fitar hankali.

Gidan da Meenal tayi rayuwa ita da mahaifiyarta, dama ina yawan kaita gidan, ina gaya mata ni da ita muka yi rayuwa a gidan, a lokacin da duniya ta juya mana baya. Ita kanta unguwar har yanzu bata sami cigaba ba, haka kuma mala Adamu da Saude tuni sun bar unguwar. Gidan dama ya riga ya rushe sai ‘yan lunguna da ba za a rasa ba. Haka aka suturta Nafisa aka kaita makwancinta. Tashin farko da shiga kotu Meenal ta ki yin Magana, sai idanu kawai da take kallon kowa. Ganin Rukayya a kotun babu kunya, yasa ta dinga nuna hannu aka rasa me take nunawa hannu, kafin a ankare ta zube a wurin.

Kaji mafarin samun ciwon zuciyar Meenal. Kai tsaye aka daga karan kuma aka wuce da ita gidan yari.

Hankalina ya gaza kwanciya har sai da na biya kudade aka mannawa Meenal ciwon hauka. Shiga kotu na biyu aka ce mahaukaciya ce, sannan alkali ya kashe karan. Meenal tana jin ankashe karan tasa kuka ta durkusa bisa guiwowinta ta daga hannayenta, sai a lokacin aka ji muryarta,

“Ku taimakeni ku kasheni ni na kashe kanwata Nafisa da kaina. Idan baku bi mata hakkinta ba, ko kun barni zan kashe kaina. Nafisa meyasa kika yi min haka? Meyasa kika tafi kika barni? Lukman ka cuce ni, ka cuceni ka tafin min da farin cikina. Zan dauki fansa da hannayen nan nawa. Rukayya me nayi maki? Meyasa? Meyasa?? Innalillahi wa inna ilaihirraji’un. Umma ki taimakeni ki bari nima su kashe ni. Mutanan da na yarda da su sun datse min rayuwa. Ko na zauna Umma ba zaki ji dadin zama da ni ba, zaki gwammace in mutu. Ummaahhh.” Kuka ya hana sauran maganar fitowa. Tana son sake magana amma kuka ya hana. Hakan yasa kowa ya amince da kwakwalwarta babu lafiya. Tana tirjewa aka sata a mota sai gida. A bakin Gate Baba Sani ne tsaye yana huci.

“Wallahi Meenal ta gama rayuwa a cikin gidan nan. Ki tafi duk inda zaki je amma ba cikin zuri’armu ba. Butulu kawai.”

Meenal ta sakko kafafunta babu takalmi kanta babu dankwali kamar mahaukaciya, ta karaso gaban Baba Sani tana dubansa cikin kuka, “Baba nima ba zan iya zama a cikin gidan nan ba. Haka ko hanya bana fatan insake hadawa da unguwar nan. Zan tafi Baba, zan tafi… Idan ka cigaba da kirana butulu sai inga kamar ba Umma ce mahaifiyata ba.

Ko tsunto ni kuka yi ne? Na tafi ba zaku sake ganin fuskata ba.” Tana kuka ta juya tayi titi ba tare da ta sake ko da waigawa ba. Shi kansa Baba Sanin jikinsa ya yi sanyi. Ina kallo Meenal ta bacewa ganina.
Meenal tana ficewa ta tari abin hawa kai tsaye gidan da tayi rayuwa da mahaifiyarta ta nufa. Har ta sauka bata cewa me adaidaita sahu komai ba, hakan yasa shma ya kama gabansa yana tunanin mahaukaciya ya dauko.

Kwanciya tavyi akan inda kasa ya taru ta kwantar da kai tana aikin kuka. “Lukman me nayi maka? Meyasa ka kashe min kanwata? Ka raba ni da farin cikina. Zan dauki mataki da hannuna zan kasheka. Na tsani maza bana son namiji ba zan taba yafewa namiji ba.” Kuka take yi tana birgima a cikin kasan nan. Tana jin tausayin mahaifiyarta fiye da komai.

Cikin dare tsoro ya shigeta ta koma can lungu ta makale tana rawan sanyi.

Ni kuma a ranar nace na bar unguwar nima, dole yayana ya bani wani gidansa, na koma. A ranar saboda kuka har muryata ta dashe, ban yi shuru ba sai da yayana ya ce min yasa a nemo Meenal ta dawo.

Da sassafe na tashi na dauki mota ni da Rufaida muka je neman Meenal. Haka kawai nayi tunanin inbiya ta gidan mahaifiyarta kila can zata je. Ina zuwa na sameta a yashe a wurin ba ta ko motsi. Hankalina ya tashi ina kuka Rufaida tana kuka, muka kira aka taimaka mana aka sa ta a mota sai asibiti.
Binciken farko aka tabbatar da zuciyarta tana gab da bugawa. Da kyar aka samo kan Meenal ta sami lafiya.

A babban falo Baba Sani ya ajiyeta yana tambayarta yadda abin ya faru cikin lallashi. Cikin dakewa take bamu labarin abubuwan da suka faru. Sai da ta kai karshe sannan kuka me karfi ya taho mata. Baba Sani ya mike yana huci, “Kiyi hakuri Meenal ki dauki hakan a matsayin jarabawa. Ni zan nemo Lukman sai na tabbatar da anhukunta shi.” Abinda bamu sani ba tuni Lukman ya bar garin, babu wanda yasan duniyar da yake.

Tun daga nan Meenal ta tsani maza, ba ta son maza su matso kusa da ita. Gara kawaye tayi su kala-kala suna cin amanarta. Watarana munje Super Market sai na ji wata mata tana cewa mijinta, “Yallabai zo ka ga wata yarinya me kama da Husna. Kai yarinyar nan kamanninta da ‘ya’yana ya baci.” Hon Munnir ya dawo da baya ya dubi Meenal duba sosai. Hankalinsa ya tashi matuka. Bai ce komai ba ya jawo hannun matarsa suka fice. Sai da suka shiga mota ya ce ya yi mantuwa ya dawo. A lokacinne na ganshi. Ido cikin ido muke duban juna. Daga bisani ya ce yana son magana da ni.

Na saki hannun Meenal da ta kafe shi da idanu babu ko kiftawa, muka koma gefe. Dubana ya yi duban mamaki ya kira sunana, nima na kira nasa. “Ina Alheri?” Tambayar da ya fara jifana da ita kenan. Kai tsaye na gaya masa ta rasu, na bashi labarin wahalar da tasha daga karshe na nuna masa Meenal, na kuma tabbatar masa da lokaci nake jira zan dauki Meenal in kaita har Gombe.

Wani duba ya yi min fuskar nan babu rahama, “Da kuwa na zama ajalinki. Ni zaki kawowa shegiya gidanmu? Ina shirin karbar sarauta zaki kawo min matsala? Kin yi kadan. Ina kuma baki shawara ki ja rayuwarki da ‘yarki idan bah aka ba zaku fada matsala daga ke har ita.”

Wa’innan kalaman su Meenal ta tsinta a sama, a lokacin da take karasowa wurin. Hakan yasa Meenal ta kare masa kallo, “Lokacin da babu kai bamu damu ba, don haka a yanzu ma ba zamu damu don ka bayyana ba.” Kallonta ya yi yana dariyar mugunta. Kawai ya wuce.
A wannan rana Meenal tasha kuka, akan tozarcin mahaifinta. Haka a wannan rana ne Hon Munnir ya aika aka gano masa inda muke zaune da tarihin abubuwa akanmu. Rana ta farko yasa aka sace Meenal yasa aka kaita wani daji. A jikin wata bishiyar goruba aka daureta, duk motsin da zata yi sai bishiyar ta soketa. Haka yasa aka dinga azabtar da ita, duk a dalilin Meenal tazo a shegiya.

Yarinyar da ba ta san lokacin da akayi cikinta ba. Haka aka yi ta neman Meenal ba a ganta ba.
Cikin ikon Allah wani maharbi ya taimaketa ya kwanceta, ya tafi da ita gidansa, har sai da ta sami lafiya sannan ta kwatanta gidana. A ranar da aka dawo min da ita, raina ya baci ina tunanin daukar mataki, kawai naga Meenal tazo gabana tasa hannu ta shake wuyana, tana kuka tana zaro idanu kamar Aljana, “Salma! Kin cuceni, mahaifina ya sanar da ni ke ce kika bi shi saboda kyansa kika nemi ya aikata zina da ke, da yaki amincewa kika sa masa magani a lemu. Meyasa zaki yi min haka? Meyasa zaki lalata min rayuwa? Burinki ya cika, nima yanzu burina zai cika. Kashe ki zan yi sannan inkashe kaina. Ina abin burgewa a rayuwar yaudara irin ta maza da har zaki mallaka masa kanki?”

A lokacin hankalin Meenal ya riga ya gushe, ni kuma ina kuka ne, a dalilin da mahaifiyar Meenal tana raye sakayyar da Meenal zata yi mata kenan? Kwace kaina nayi da kyar ina dubanta duba na tausayi, nace mata, Amashe har namiji zai iya gaya mata magana ta yarda? A nan ne na fara bata labarin abinda mahaifinta ya yi wa Alheri, sai na mayar da labarin kaina saboda bana son tasan ba ni ce na haifeta ba, tashin hankalinta yafi hakan. Meenal ta durkusa bisa guiwowinta tana kuka, tana neman afuwana. A lokacin na kasa magana tunanin mafita kawai nake yi.

Kwankwasa kofa naji, dan haka Meenal ta mike zata je ta bude, har ta kai kofa, na dakatar da ita, nace ta koma ta zauna. Shuru tayi tana kallona daga bisani ta koma ni kuma na bude. Kawai ji nayi anwatsa min wani abu a fuska, ya sauka har wuyana. Gigitacciyar kara nasa, hakan sa Meenal karasowa da gudu tana tambayar ko lafiya. Dama Rufaida bata gidan tana gidan Baba Sani. Haka maigadi ya karaso da gudu. Ba komai bane face Acid da aka watsa min.

Meenal tana ganin fuskana ta kwala kara mai karfin gaske, ta yi hanyar fita da gudu, bata sani baa she bango ta nufa, sai ji tayi ta buga kanta da karfin tsiya. Anan ta fadi jini ya wanke mata fuska. Ni kaina bansan yadda akayi ba sai a Asibiti na tsinci kaina, fuskata kuwa tuni ta lalace. Cikin gaggawa Baba Sani ya shirya yasa aka fita da ni kasar. Acan aka gyara min fuska. Doctor munsha wahala matuka a hannun Hon Munnir. Da haka har Rufaida tayi aure aka barni daga ni sai Meenal. Ka ji tarihin Meenal, ka ji rayuwar Meenal. Hon Munnir bashi da burin da ya wuce yaga ya kasha Meenal. Saboda tsoron kada a hana shi zama sarki akan abin da ya aikata. Tasha gwada samari da kawaye, amma sai ta same su da halayya iri daya.”

Doctor Bakori ya mike tsaye kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce, “Meenal tana yawan zuwa wani wuri da wuka a jikinta, amma na rasa waye take son kashewa a cikin mutane uku, Lukman, Rukayya, da kuma mahaifinta Hon Munnir.” Umma ta mike jikinta na rawa ta zaro idanu, “Wuka kuma? Indai da gaske Meenal tana fita da wuka tabbas a cikin mutane ukun nan duk wanda ta samu zata iya kashewa.”

Doctor Bakori ya dago cikin tashin hankali, “Duk abubuwan da suke faruwa da sa hannun kawayenta biyu aka shirya su.

Halima, da kuma Farida. Na hadu da su yau a mashaya, kuma na gansu tare da wata babu abinda ya bambanta fuskarta da ta Meenal. Da ace bansan Meenal sani sosai ba, da babu abinda zai sa bance Meenal ba ce. Bana jin ko ke kika ganta zaki ce ba ita ba ce. Lamarin Meenal akwai sarkakiya, wanda a yanzu amsoshin su yana gun mutane hudu. Meenal, Hon Munnir, da kuma kawayenta biyu Halima da Farida. Sannan kuma waye Alhaji Khalid?”

Baki bude Umma take kallonsa, da ace bata san Doctor ba da tabbas sai ta kira shi da makaryaci.

“Halima kuma? Tirkashi! Halima da ta nuna mana duk duniya babu wacce take so sama da Meenal? Halima da take kwana akan Meenal idan bata da lafiya? Tayaya muke zaton zamu gama lafiya, bayan mun kasance masu cin amanar ‘yan uwan mu musulmai?

Alhaji Khalid ya tako har gidan nan ya zo da ya ji labarin abubuwan da suke faruwa, ya ce min shi zai dauki nauyin Meenal, haka kuma ta dauke shi a matsayin uba.

To ina jin yaji labarin zuwan Alhaji Khalid ne, dan naji labarin yana neman rayuwarsa. Amma ta yaya zai yuwu aga wata Meenal din?”

Kallon agogo ya yi dare ya fara yi, ya dan yi taku daya zuwa biyu, “Wannan ne rudanin da na shiga. Gobe zan koma gurin Meenal. Da farko tausayin Meenal yasa na aureta. Amma yanzu da nasan wacece ita yasa na amince da ita a matsayin wacce nake so.

Zanje gobe injaddada mata matsayinta a zuciyata. Mahaifinta yana jin kunyar duniya, bayan ya kasa jin kunyar Allah a lokacin da yake aikata barna? Ni zan dauki Meenal zan kaita gaban kakanninta a cikin masarauta, ba zata fito ba sai da albarkar kakanninta, ko da kuwa mahaifinta bai sa mata ba. Na yi alkawarin ba zan tare da maatata ba, har sai na dawo mata da farin cikinta. Har sai na nuna mata maza suna suka tara.

Insha Allahu da albarkar iyayenta zata tare a gidan mijinta.

Zaki taimaka ki nemo min adireshin pastor kakanta shima zan kai masa shegiyar da yake gudu, tunda addininsu babu kaddara.

Zamu zuba ko ni ko Hon Munnir! Sai da safe Umma. Allah ya biyaki.”
Har ya kai bakin kofa zai fita ya ji muryar Umma tana magana, “Kada ka fita a cikin daren nan Doctor.”

Juyowa ya yi ya jefeta da murmushin da ta kasa gane manufarsa, kawai yasa kai ya fice.

Tun a hanya ya fahimci ana binsa, hakan yasa ya yi ta sakin murmushi muryar Umma yana masa karaji a kunne akan rayuwar Meenal. Ji yake da yana da iko da ya cirewa Meenal dukkan rayuwarta ya dawo da shi cikin jikinsa. Dole zai kyale su su kama shi, ta hakanne zai samu ya cimma burinsa. Ta yaya zai yi kwanciyar dadi bayan Meenal tana can cikin zarnin fitsari?

Tsayawa ya yi a gefen titi ya fito kawai ya rufe kofar motar ya zauna a bisa mota yana karkada key din motar. Suma kashe motar suka yi amma sun kasa fitowa. Da murmushinsa ya karaso motar ya bude kawai ya shiga, “Anturo ku ku dauko ni. Zaku sha matukar wahala ku iya kama ni idan ba ni naso hakan ba.

Zaku tara mutane fiye da ashirin wajen kai ni gidan uban gidanku baku ci nasara ba. Ni ba sakaran namiji bane, duk abinda nake yi ina yinsa a cikin lissafi. Misali na kai dare a waje, nasan ina tare da marasa tsoron Allah da suke nemana. A irin wannan lokacin kamata ya yi ace ma bana garin nan. Any Way, muje nima ina da bukatar ganinsa domin amsa min wasu tambayoyi. Muna iya tafiya.”

Gaba dayan su anrasa wanda zai iya magana saboda mamaki. Daya daga cikin su ya ce, “Yallabai ina jin tsoron inga mutum ya shiga matsalar Hon Munnir, sam bashi da hali me kyau. Mu kanmu mun kusa barinsa wallahi. Hatta matarsa da ya taba aure sai da ya sace ta da kansa ya dinga gana mata azaba.”

Doctor Bakori ya boye mamakinsa ya ce, “Nan gaba mahaifiyarsa zai sato ya hukunta ta. Ya kamata kuyi wa kanku fada domin kuwa idan ya tashi barewa harda ku zai bare.” Dukkansu suka jinjina kai. Dayan ya ce, “Lokacin da ya yi Sanata ai yasha jinin mutane ba na wasa ba. Wallahi tsoronsa nake ji.”

Suna isa wurin Doctor ya ce, “Ku tsaya. Rikeni zaku yi sosai ku nuna masa kun kamo ni ne. Idan ba haka ba zaku iya shiga matsala. Kun zama abokaina da zarar na bar nan zan samar maku da abin yi ku bar bin hanyar bata.” Dr. Bakori ya yi amfani da hakanne saboda idan ya sami hadin kansu zai fi samun abinda yake so. Dukkansu sun ji dadin furucin Doctor.

A gaban Hon Munnir suka zube shi ya dago yana dubansa, “Kasa ankama ‘yarka ta cikinka. Kana tsoron Allah kuwa? Meyasa baka ji kunya a yayin aikata zina ba? Sai yarinyar da ba ta ji ba ba ta gani ba.”
Fuskar Hon Munnir ya sake sauyawa saboda ɓacin rai,

“Doctor kana da tsaurin idanu. Ban shirya karbar ‘yar shegiya kuma arniya ba. Mahaifina ma shirin kawar da shi nake yi daga duniya, bare wata ‘ya da aka Haifa a waje. Ina da ‘ya’ya uku da nake matukar so kamar raina, sun isheni rayuwar duniya, ba sai ankawo min baragurbi ba. Doctor mu bar maganar nan pls, meyasa ka yaudare ni?

Aurenka da Meenal bai dameni ba, tunda dai a yanzu tana matsayin gawa ce.

Ya maganar Alhaji Khalid? Ina son a kashe shi saboda yasan sirrina.
Idan kuma ka ki zan hukuntaka fiye da tunaninka.” Murmushi ya sakar masa, “Har kullum ina yawan gaya maka da ka daina yi min gadara. A yanzu idan na gadama zansa asirinka ya tonu ina nan wurin. Kafin yaranka su kama ni nasan za su zo saboda sanin halinka na rashin dabara.

Akwai abokaina a Gombe da suke da hanya kai tsaye na ganin Sarki, na basu Hotuna da duk abubuwan da suka danganci Meenal. Nace masu idan suka ga kwana biyu basu ganni ba, kawai su nufi fadan mai martaba su sanar da shi komai, haka su nufi Police Station su gayawa duniya kai ka kashe ni.
A kalla nabi hanyoyi kala hudu akanka, ban yarda na fada hannun mutananka ba, nima sai da na shiryawa hakan.

Da ina da ninyar tona maka asiri da tun ranar da naga kana baiwa ‘yarka ruwan wanke-wanke zan yi hakan, haka tun a ranar zan sanar da babban amininka kana neman rayuwarsa. Idan ka shirya muyi magana ta hankali ina ganin zaka ji daɗin yin aiki da ni, kuma har ka mutu asirinka ba zai taba tonuwa ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Meenal 13Meenal 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.