Jikin Hon Munnir ya yi matukar sanyi, lalle ya hadu da wanda yafi shi sanin duniya. Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ce, “Ina jinka, idan hanyar ta yi dai-dai da ra’ayina ai shikenan.”
Doctor Bakori ya mike ya zauna suna fuskantar juna, “Ina son ‘yarka Meenal. Idan Meenal ta rasa rayuwarta a ta dalilinka, ina tabbatar maka sai na karar da kaf din zuri’arku.
Dangina ma ba zan daga masu kafa akan Meenal ba, bare kai da kake matsayin surukina. Angaya maka halin da mahaifiyar Meenal ta shiga amma baka tausaya mata ba, sai ma kama. . .