Skip to content
Part 14 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Dr. AA ya yi murmushi ya jawo Meenal jikinsa da ta tsura masa idanu tana jin kalaman mahaifinta. “Kada ka damu Hon Munnir, babu bukatar ka gaya min abinda duniya ke ciki, dan tuni ansanar da ni irin matakan tsaron da ke farautata. Na shiryawa karbar ko wani irin kalubale saboda Meenal. Maganar kudi kuma ka bar abinka, Miliyan hamsin ai babu laifi za su iya isarta yin wasu abubuwa, ragowar kuma da basu isa ba, mijinta zai bata.”
Hon Munnir ya jinjina tsauri irin na Ahmed, ya sake cillo masa wata tambayar,

“Kana nufin ka shirya fuskantar komai harda mutuwa? Ka shirya barin iyayenka ‘yan uwanka saboda Meenal?”

A natse ya mayar masa da amsa, “Idan ban shiryawa hakan ba, bana jin zan gwada barin su tun yanzu. Ai na gaya maka na shirya barin komai, idan nace maka komai ina nufin harda duniyar ma gaba dayanta. Ka huta lafiya.”

Wayar ya katse yana aikawa Meenal da murmushin kwantar da hankali,. Amma a badini, hankalinsa ya tashi, ya tabbata Hon Munnir yana saka masa magana ne. Kai tsaye ya kira layin Alhaji Khalid.

Bugu biyu a na uku ya daga zan kiraka kawai ya ce ya kashe wayar. Hakan ya tabbatar masa yana tare da mutane ne. Ba ayi minti biyu ba ya kira bayan sun gaisa ne Dr. Bakori ya mayar masa da yadda suka yi da Hon Munnir. Alhaji Khalid ya rike kansa, “Wato Doctor idan kaga yadda Munnir ya yi a lokacin da yaji labarin nan sai ka bude baki.

Mutane basu da amana, a gabanka kamar su goyaka. Shi da kansa yace yasa kudi ga duk wanda ya ji labarin inda kake. Kada ka damu duk abinda zai yi Allah ya fi shi. Yanzu kana ina ne da Meenal?”

“Ina Abuja, kai kadai nake jira inbar kasar gaba daya. Ina son kafin intafi ka hada min haduwa da Sarkin Gombe, kakan Meenal. Shikadai nake son gani sannan inbar kasar zuwa wani aikin zuciya na wani mutum me mulki da yake fama da irin cutar. To Asibitin sun gayyace ni ina son ganin ko zan iya cin nasara, duk da bansan wani mutum bane. Sun sa mana Date din da mutumin zai karaso asibitin sannan mu fara bashi taimakon gaggawa.”

“Ok kada ka damu. Sarki zai zo Abuja, daga Abuja shima zai bar Kasar. So zan kira na kusa da shi mutumina ne sosai haka baya kaunar Hon Munnir ni nake tausasa shi. Zan hada ku a duk ranar da ya diro garin, yana sauka a Hilton sai ku hadu da shi ku tattauna. Daga nan baka bukatar ko kudi?”
Dr. Bakori ya saki murmushin samun nasara ya ce, “Ina da kudi yallabai. Wannan taimakon kadai nake bukata da zarar na samu to ka biyani.” Suka yi Sallama tare da ajiye wayar. Damuwa ce karara a fuskarsa ya kuma rasa damuwar mecece.

Ganin ta kafe shi da idanu ne yasa ya kwantar da kanta yana wasa da gashin kanta, “Matata tana da kyau, tana da damuwa da damuwar mijinta. Tana da kulawa. Irin ki ne matar da kowani namiji yake bukatar samu a matsayin mata.

Maza tashi ki hada min ruwan wanka inga ko kin iya hadawa.”

Da sauri ta tashi ta shige bayi, amma tunani bai barta ba. Ta dan jima a bayin ya biyota, hakan yasa ta zaro idanu, bata taba ganin namiji babu riga ba.

Murmushi ya yi ya ce “Tsaya ki cuɗa min baya.” Girgiza kai tayi a rude, “Ba zan iya ba.” Jawota ya yi, “A’a zaki iya nasan ba zaki taba min musu ba.” Rintse ido tayi ganin ya cire farar gajeren wandonsa ya shiga kwamin wankan. Sabulu ya goga a fuskarsa, ya ce

“Sabulu ya shigar min ido taimaka min Meenal.” A rude ta karaso ta kamfaci ruwa a hannunta ta dinga wanke masa fuskar. Sai da ta wanke tas, sannan ta yi magana a hankali, “Na shiga uku ka bude idon mu gani.”

A hankali ya bude ya sake rufewa. “Hure min idanun ne.” Kama idanun tayi tun kafin ta bude ya bude su yana kallonta, bata fahimta ba, ta dinga hurewa yana jin iskan yana ratsa dukkan gabban jikinsa. Gaba daya ya lalace a kallonta.

Sai a lokacin ta ankare dan haka ta turo bakinta kamar zata yi kuka, yasa hannu ya jawota cikin kwamin wankan, gaba daya ta jike ita da kayanta.

Bude shawan ya yi ruwan mai dumi ya dinga sauka daga sama yana jika su. Da kansa ya salube mata kayan, duk yadda take kaucewa sai da ya rabata da komai nata. Tsarki ya tabbata ga wanda ya kagi halittar nan. Haka ya dinga nanatawa. Gaba daya jikinta fari tas! Tallafo kanta ya yi da ruwa ya gama jika suman.

“Meenal. Bude idanunki kiji wata magana.”

Kasa budewa tayi, yanayin zuban ruwan ya yi mata kama da suna cikin ruwan sama.

Hannayensa yasa a labbanta da ruwan ya jika mata su, sai suka kara kyau, yana zagaye su.
“Meenal ina…” A razane ta bude idanunta, tana son jin abinda zai furta. Hakan yasa ya yi shuru ya gaza karasawa. Idanunta masu kyau take yi masa wani irin kallo suna sake lumshewa. Bata san lokacin da ta dago habansa ba, tana dubansa kamar zata yi kuka. Ya fahimci abinda take son ji,

“Meenal ina sonki.” Kuka ta fasa, ta jima tana son ya furta mata wannan Kalmar ko da da wasa ne, hakan bai faru ba. Rungumeshi tayi tsam a jikinsa, tana kawararan hawaye, da ruwan shawan yake wanke su. Zai iya rantsewa tunda yake bai taba jin abinda ya ji a yanzu ba.

“Ina sonki Meenal tun ranar da na dora idanuna akanki. Da farko ina zaton tausayinki nake ji, sai da na ganki a mashaya, na tabbatar da sonki nake yi. Duk yarinyar da na kama da laifi indai na tabbatar na rabu da ita kenan. Ban taba soyayya ba sai akanki.” Shi kansa bai san ya afka cikin yanayin nan ba, bai san yana zaro irin kalaman nan a gaban yarinyar da kullum zuciyarsa ke nuna masa kankantarta ba.

“Yadda ta rungume shi take ta shinshinarsa yasa ya fada cikin wani yanayi, har ya sauya salon wasan. Ga mamakinsa bata hana shi ba illa hadin kai da take sake bashi. Sun mance a inda suke sai da ya mirginota ya ji su kwance cikin ruwa. Hakan yasa ya sarara mata ya kwantar da kansa a jikin kwamin wankan yana mayar da ajiyar zuciya.

A kalla sun fi minti arba’in a cikin wannan halin. Fitowa ya yi ya mika mata hannu alamun ta fito. Kudundunewa tayi tana jin ba zata taba iya rashin kunyar nan ba. Ta ya ma za ayi ta iya fitowa a haka? Fahimtar hakan da ya yi yasa ya ciro katon tawul ya mika mata. Shima kasa tashi tayi ta daura har sai da ya fice yana murmushi. Jinsa yake kamar babu wanda ya kai shi nishadi. Jin zuciyarsa yake fes! Yana jin ya shirya mutuwa tunda har ya fitar da abinda ke ransa ga macen da ta dace.

Dakinsa ya nufa ya shafa mai ya dora jallabiya me yankakken hannu. Ya jima zaune a falon sannan ta fito tana boye kanta. Tayi masa kyau cikin shigarta ta doguwar riga itama yankakken hannun gare shi. Hakan yasa duk suka dubi jikinsu. A gefensa ta zauna ya mayar da kansa bisa cinyoyinta yana cigaba da kallon film.

Hannu tasa a gashinsa tana kitse gashin. Bai ce mata komai ba. Yana jin ciwon mara baya son ya dauko lemun tsamin ta dame shi da tambaya. Dan haka ya dinga cijewa.

Dago fuskarsa tayi tana son kallon yanayin da yake suka ji karar kwankwasa kofa. Zai tashi ta girgiza masa kai, ta ajiye kansa ta mike. Maman Anwar ta gani da mijinta. Don haka ta basu hanya. Daga matar har mijin kan Dr. AA suke kallo cike da mamaki.

“Doctor kitso ka fara yi akan?” Abokinsa Nuhu ya tambaye shi yana gyara zama. Meenal ta koma ta zauna kusa da mijinta ta sunkuyar da kai. Babu zato taji yana cewa, “Wannan rigimammiyan take yi min…” Bata san lokacin da ta kankame shi tasa hannu ta rufe masa baki ba.

Daga Nuhu har matarsa suka yi yaƙe.

Meenal ta dan rusuna ta gaishe shi, ya amsa yana dariya. Doctor ya cire mata hannu yana murmushi. Ya kwantar da ita a cinyarsa cikin dabara ya sake rufe mata kanta. Haka kawai yaji yana kishin fitowar gashinta. ‘Yar hira suka yi sannan suka ce za su wuce. Meenal ta kamo hannun Doctor kamar zatayi kuka, “Yaya insanyo hijabi mu raka su?” Kafada ya ware “Dauko mu je.”

Nuhu da matarsa suka fara fita. Maman Anwar ta fara magana, “Ni nawa mijin ma ko dan gashin babu akansa, bare har inkitsa. Kai gaskiya dolensa ma ya fara barin gashi kuma ya fara nuna min soyayya irin ta Doctor. Kana zaune da mutum kullum fuskar nan kamar ta shanu?”
Nuhu ya fusata iya fusata don haka ya bata amsa, “Ko dai zaki koma gidansa ne ki aure shi? Ai sai inbaki takardarki, ni dama kin isheni.” Da Gadara ta ce, “Eh bani takardar ka gani ko ba zan aure shin ba.” Bai iya bata amsa ba, sakamakon karasowar Doctor rike da hannun matarsa.

Har gida suka raka su, ga mamakin Meenal taga gidan kaca-kaca babu ko kamshi. Dan hakane ta mike tana hamma, hakan yasa Doctor mikewa suka yi masu sallama.
A cikin satin da Meenal tayi da Doctor ta gama fahimtar waye shi, haka wani irin shakuwa ne ya shiga tsakanin su mai matukar ban mamaki. Musamman ma da bai cika fita ba. Ya yi mamakin ganin har yanzu Alhaji Khalid bai kira shi ba, gashi lokacin tafiyarsa tana matsawo, har yaje ya yi wa Meenal Passport.

Yau yana zaune a dogon kujera tunani ya yi masa yawa, domin har ankai matsayin da lemun tsami baya yi masa aikin komai. Ta baya ta rufe masa ido, ya yi murmushi ya zagayo da ita ta zauna a jikinsa. Dago fuskarsa tayi ta bashi sumba a goshi, “Yayana ina sonka.” Kwantar da kanta tayi a kirjinsa.

Ya rasa dalilin da kwana biyu yake cikin damuwa, “Meenal zan iya mutuwa inbarki, wannan duk ikon Allah ne. Idan na tafi na barki zaki iya zama abar tausayi, ba kowa zai iya kula min da ke ba. Abu daya nake so da ke ki daina daukar maza a masu hali iri daya. Ina sonki Meenal.”

Kuka sosai take yi, irin kukan da bai taba zato ba, mamaki yasa ya dagota yana dubanta, “Meyasa kuka kuma yanzu-yanzu?” Girgiza kanta tayi, “Ummana ta rasu a dai-dai lokacin da nake da bukatarta, yanzu kuma kana kirawa kanka mutuwa a lokacin da nafi bukatarka fiye da kowa. Idan hakan ya faru ni Meenal zan zama abar tausayi.”

Rungumeta ya yi yana murmushi, “Haba Meenal meyasa zaki dinga kuka kina bata min hawayen da ya kamata cikin dare zaki dinga zubar da shi, kamar yadda kike yi.” Duka takai masa a kirji tana tura kanta cikin kirjinsa alamun kunya. “Ki kwantar da hankalinki tare zamu tsufa insha Allahu.”
Shuru ya biyo bayan maganarsa.

Tunani ya yi ya kamata yau ya gwada kiran mahaifiyarsa. Lambarta ya danna ya kirata, sai da lambar ta kusa tsinkewa sannan ta daga, “Mahaifiyata haka zan mutu kina fushi da danki? Ina jin ciwo ina kwana cikin dogon tunani idan naga na kiraki baki daga ba. Kullum bana iya cikakken barci. Ko cokali idan ya fadi a hannuna sai inga alhakin mahaifiyata ne. Kiyi hakuri ki yafe min kisa min albarka, ko zan sami barci da natsuwa ko da na kwana daya ne.”

Yana maganar yana ji kamar ya zubar da hawaye. Haka jikinsa yana kara rikicewa da zafi. Jikin Ummansa ya yi matukar sanyi dama ita kanta daurewa take yi.

Cikin hawaye ta ce, “Na yafe maka Ahmed ban taba kwana da fushinka ba. Haka kullum ina yi maka addu’a insha Allahu addu’ata tana tare da kai. Yaushe zaka dawo inganka? Na damu da rashinka, ina jin damuwar rashin ganinka.”

Ajiyar zuciya suka sauke a tare, har sai da ya waigo ya kalleta yadda take kuka, “Hajiya aiki kawai zan fita inyi a Egypt da zarar komai ya kammala zan dawo insha Allahu ki sani a cikin addu’arki.” Haka suka yi Sallama cikin kaunar juna, ya juyo tare da jan hancin Meenal,

“Baki da wuyan kuka, haka idan na mutu zaki dinga yi min kuka? Muje mu shirya mu ci abincin a waje.” Tashi tayi tasa doguwar riga me ratsin bulu, shima kuma kananan kaya yasa me irin ratsin. Cike da nishadi suka fice abin su. Duban duniya ya yi mata bai ganta ba, hakan yasa hankalinsa ya tashi fiye da tunaninsa. Sosai ya gigice yana dubata. Daga bayansa ya ji dariyarta har da durkusawa tana rike ciki, “Idan ka sake yi min irin zancen dazu Wallahi zan tafi, zan tafi inda ba zaka sake ganina ba har abada.”

Bakin ciki yasa ya biyota a guje, hakan yasa ta zubar da takalmanta ta falla da gudun gaske. Duk yadda suke da tazara hakan bai hana shi kamato ba, gaba daya suka zube a kasa. Kunnenta ya murde da karfi wanda yasa ta dan yi kara. Allah ya bata sa’a ta cije shi a hannu ya saketa yana yarfe hannun, ta sake tashi ta runtuma da gudu. A wajen motarsu ta tsaya tana haki.

Yana karasowa ya yi mata rumfa da jikinsa. Kunnenta ta rike alamun ba zata kara ba. Magana yake mata idanun nan jajir, “ Meenal! Kada ki sake kwatanta hora ni da guduwarki. Ni kadai nasan irin halin da na shiga a lokacin da ban ganki ba. Idan kika sake yi min irin wasan nan zuciyata zata iya bugawa.” Shuru tayi tana dubansa, ta tabbata da gaske yake, don haka tasa hannu ta share masa gumin da ke tsattsafo masa, “Sorry Dear, ba zan sake ba.” Kankame shi tayi tana jin irin abinda yake ji. Hannunta ya kamo ya shigar da ita mota suka koma gida.

*****

Tun daga ranar ya haramta masu fita.Tana zaune a saman kujera yana zaune a kasa yana kankare mata kumba, dama shi ke kankare mata ya yanke mata saboda bata iya yankawa ba duk idan zata yanka sai ta yanke da reza.

Hankalinsu kwance suke hirar su. Meenal ta dube shi ta ce, “Yaya akwai abinda kake boye min menene Shi? Meyasa kake yawan shan lemun tsami? Ko dai baka da lafiya ne? Idan baka da lafiya mu je asibiti a duba min kai don Allah.” Baya son suna hada idanu don haka yaƙi kallonta, “Lafiya na kalau. Lemun tsamin yana maganin basir ne shiyasa.” Da mamaki take dubansa, “Kuma baya tashi basir din sai ka taba ni? Nifa ina jin tsoro kada wata matsala ta sameka.” Murmushi kawai ya yi ya ce “Lalle ma yarinyar nan kin zama mara kunya. Wato baya tashi sai na taba ki. Ina tausaya maki ashe kin girma?” Rufe fuskarta tayi tana dariya, kunya duk ta kama ta.

Kafin ta lalubo abin cewa, sai ga Maman Anwar ta shigo. Ya dubeta da ‘yar fara’a “A’a Maman Anwar ina kika baro min yarona?” Yakye tayi ta nemi wuri ta zauna, “Yana Makaranta nace bari in leko ku tunda ku baku zuwa.” Sai da ya matse mata babban dan yatsa da yasanyata ihu, “Wayyo Wallahi sai na rama ba mugunta ba?” Maman Anwar ta ware idanu tana mamakin dama wai akwai maza masu ɓata lokacin su agun matan su? Ba zata mance ba tun kazar da ta ci ranar daren farkonta, ta ciyowa kanta kazar masifa, domin kuwa basu taba yin wata basu yi fada da Nuhu ba.

Yana bata hakuri amma ina sai da ta kamo babban yatsan kafarsa ta lankwasa. Bai ji zafi ba, amma sai ya nuna mata ya ji zafi sosai, hakan yasa ta rude, “Husby don Allah kayi hakuri kada ka ji zafi kaji? Bana son abinda zai sa kaji zafi ina jin zafin nima.”

Murmushi kawai ya yi ya mike. Ganin tana shirin bin bayansa ne ya juyo tare da zare idanu, “Ina zaki je? Baki ga kinyi bakuwa ba ce?” Ita gaba daya ta mance da wata bakuwa. A kunyace ta dawo ta zauna, ita kuwa Maman Anwar sai faman yakye take yi.

Yana fita ta dubi Meenal ta ce, “Ke kuwa gaya min waye malaminki da ya kama maki mijinki haka? Wallahi Nuhu nake son kaiwa, kullum sai mun yi fada.” Meenal ta dubeta, kamar mai wayo ashe babu. Irin su ne basu yarda da soyayyar Allah da Annabi ba sai sun dangantaka da shirka. A natse ta dago ta ce,

“Allah shi ya bani ikon rike shi.” Ganin yadda Meenal tayi, babu shiri tayi mata sallama tana zaginta a zuciyarta, “Shegiya ko mutuwa zan yi nasan ba zata taba gaya min ba. Daman su da wahala kaji cikin su.”

Meenal ta shigo ciki yana kwance a gado, shi kadai yasan irin ciwon da yake ji a jikinsa. Yana jin an hau bayansa ya sauya fuska.

Ya juyo yana aika mata murmushi, “Matas! Har bakuwar ta tafi?” Tabe baki tayi, ta kwashe komai ta gaya masa. Murmushi ya yi mata ya ce, “To menene abin damuwa? Matan yanzu sun lalace agun bin boka, bayan sune bokan kansu. Meenal tunda na aureki ko da wasa baki taba bata min rai ba.

Da maza za su sami mace irinki na tabbata da anrage samun matsalolin aure.”
Shafa kirjinsa tayi ta ce, “Nafi kowa dacen miji. Haka da maza za su gane su biyo halayyarka da anhuta samun matsalar aure.” Rike hannunta ya yi don tana son rikita shi.

“Yanzu idan na taba kirjinki zaki ji dadi?” Da gudun gaske ta tashi ta bar dakin tana kyalkyaltar dariya. Ajiyar zuciya ya kwace masa, yana son dariyar Meenal. Idan tana dariya ji yake bashi da sauran matsala. A hankali ya rike cikinsa, yana tunanin ciwon cikin nan ne ajalinsa.

Ba zai iya karya alkawarin da ya yi ba, haka baya son Meenal tasan da wata matsala, idan ta sani ya sani zata mallaka masa kanta ba tare da dogon tunani ba.

Ya sani babu abinda zai nema agun Meenal bata yi masa ba. Yana juye-juye ta dawo dakin tana cewa, “Yaya. ka kira min Umman…” Wayar da ke hannunta ta saki a kasa da karfi, tayi kansa

“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un.. Na shiga uku! Yaya!! Don Allah Yaya Don Allah na rokeka kada kayi min haka.” Kuka me karfi ya ci karfinta, ta kifa kanta a kirjinsa, numfashinta yana daukewa yana dawowa. Kafin wani lokaci jini ya fara bin bakinta.

<< Meenal 11Meenal 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×