Skip to content
Part 15 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Duk da hakan kokari take yi ta kamo shi, amma ta kasa. Da kyar ya iya mayar da ita gadon, ya tashi da kyar yana numfarfashi.
Rarrafawa ya yi ya dauki wayarsa da ta jefar Allah yasa wayar bata fashe ba. Lambar Nuhu ya kira yana magana da kyar. Sai dai har ya sauke maganarsa Nuhu bai fahimci komai ba, kawai dai yasan babu lafiya. Da sauri suka fito shi da matarsa suka shigo dakin. Halin da suka gansu ne yasa ya kira aka tattage su sai asibiti.

Sai dai fa duk yadda aka so a shawo kan matarsa abin ya ci tura. Gara shi ya dan ji sauki. A hankali ya zare karin ruwan da ake yi masa, ya sami likitocin ya yi masu bayanin aikinsa, ya kuma roke su zai dubata. Cikin gaggawa aka amince masa, saboda halin da Meenal take ciki zata iya rasa ranta a kowani irin lokaci.

Cikin ikon Allah ta farfado da sunan mijinta, hawaye suna bin idanunta. Yana nan zaune yana dubanta. “Yaya don Allah kada ka tafi ka barni.” Karasowa ya yi yana magana a hankali, “Idan na tafi na barki ince na barki da wa? Gani a kusa da ke. Ki daina tayar da hankalinki irin hakan, zazzabi ne kawai ya dan kama ni amma sai kika fini shiga rudu? Haba Meenal.” Hannunsa ta kurawa ido da taga alamun anyi masa Karin ruwa. Lumshe idanun tayi barci ya kara kwasarta.

Sai da tayi kwana biyu Doctor yana kula da ita. Har masu asibitin sai da suka dinga rokonsa suna da bukatarsa, za su dinga biyansa ko nawa yake bukata. Girgiza masu kai kawai ya yi ba tare da ya amince masu ba. Bayan sun dawo ne Nuhu yake tambayar me ya same su? Doctor ya mayar masa. Jinjina kansa ya yi ya ce, “Tirkashi! Gaskiya ba karamin so Meenal take yi maka ba. Wannan duk ranar da aka ce babu kai babu ko shakka binka zata yi. Ashe akwai mata masu son mazajen su haka?”

Doctor ya yi murmushi kawai ba tare da ya iya tankawa ba.
Meenal ta fito rike da tea, ta gaida Nuhu ta karasa kusa da mijinta. “Ga tea dinnan kasha da zafinsa.” Karba ya yi yana mata godiya. Kafe shi tayi da ido har sai da ya shanye, sannan ta miko masa magunguna.

Meenal ta daina yin wani barcin kirki tana kula da duk wani motsinsa. Cikin dare ya dubeta da kulawa ya ce, “Meenal idonki biyu bude idanunki.” Budewa tayi tana dariya, shima murmushin ya yi ya ce, “Meenal Allah yana son mutane masu yarda da kaddara. Tayar da ciwonki da kike yi sakamakon wani dalilinki babu kyau.

Mahaifiyarki ma ta rasu ta barki a lokacin da baki wuce shan nono ba, kuma Allah ya rayaki bare kuma rashi na? Meenal idan bani da lafiya ina jin tsoron ki sani saboda kada ciwon ki ya tashi. Baki san idan yana yawan tashi daga nan zaki iya rasa ranki ba? Ni kuma idan kika mutu inyi yaya? Haba Meenal ba zaki tausaya min ba?”

“Yaya bana sanin lokacin da ciwon yake tashi. Bansan yadda zan yi indakatar da faruwar hakan ba.”

Hannayenta ya kama dukka biyun, “Ki daina tsaro na, idan Allah ya gadama kina zaune kina gadina zai zare rayuwata ba tare da saninki ba. Baki isa kiyi wa Allah wayo ba Meenal. Idan kika fara jin kin shiga rudani, ki yi ta karanta Innalillahi wa inna ilaihirraji un, Hasbunallahu wani imal wakil. Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni min khaira minha. Zaki sha mamaki. Wallahi ciwon nan ba zai tashi ba, zaki dinga samun natsuwar da kika rasa. Ina son sai mun fita ne inhada aikin da zanyi da naki, saboda anan bamu da kayan aikin. Da zarar nayi maki aiki insha Allahu zaki nemi ciwonki ki rasa gaba daya. Kinyi min alkawarin daina irin wannan rikicewar?”

Manne masa tayi sosai, “Zan kiyaye insha Allahu. Amma don Allah kada kayi ciwo.” Shafa kanta kawai yake yi, ba tare da ya iya furta komai ba.

*****

A guje ta fito da wayarsa a hannu tana kwasar dariya, shi kuma duk ya rikice saboda wata lamba da ta aiko masa da sako baya son ta gani. Tana gudu ta bude wayar. Cak! Taja ta tsaya ta ware idanunta. Jikinta a sanyaye ta dawo ta mika masa wayar kawai ta koma ciki.

Tagumi tayi tasan waye mijinta baya neman mata, idan ma ya fara zata yi masa uzuri kasancewar bata taba kama shi da makamancin laifin nan ba.

Karasowa ya yi ya zuba hannayensa bisa guiwowinta, “Meenal dina ta yarda da mijinta?” Tabe baki tayi ta ce, “Gaskiya a’a.” Kasa daurewa tayi kawai ta kama dariya. “Meyasa ka tsareni da idanu?” Murmushi ya sakar mata. “Saboda wani abu da nake so a jikinki ki bani shi kyauta mana.”

Zaro idanu tayi, “Menene abun? Don Allah dauki na baka ko menene.” Mi’kewa yayi yana tafiya, ta biyo shi da gudu ta haye bayansa ta zuro fuskarta ta wuyansa ta fasa ihun da yasa ya toshe kunnensa da sauri. Ta sauka ta runtuma da gudu.

Meenal kenan ita dai babban damuwarta ayi ta guje-guje to angama mata komai. Ya rasa dalilin da yasa yake yi mata kallon tausayi.
Yana son ganinta a cikin farin ciki. Hakan yana danne duk wata damuwa da yake ciki.

Yau ma jin ciwon yana son tashin masa ya mike ya koma kasa, bata iya kwanciya sai a jikinsa, shi kuma ko yaya ta taba shi sai ya ji komai yana sauya wurin zama a jikinsa. Cikin dare ta laluba bata ganshi ba, ta mike a tsakiyar gado tana shirin kwantsama ihu, tare da zaro idanu tana son fara kuka, ta ji ya toshe mata baki,

“Gani nan fa Meenal.”
Rungume shi tayi tsam a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya. Zama ya yi kawai ya yi tagumi. Duk shi ya koya mata wa’innan abubuwan. Gadon ya mayar da ita, ya. Ya kwanta kawai kusa da ita yana lumshe idanu.

Ga mamakinsa ta makalkale shi tana sauke ajiyar zuciya. Tausayinta ya kama shi, dole zai yi mata yadda zata gamsu, ba zai sake cutar da ita ba. A ranar wani irin wasa suka yi, hakan ta cire kunya ta mayar masa da martani da ya sami saukin ciwon cikinsa sosai. Har kullum Meenal tana mamakin abinda ya hana mijinta karbar hakkinsa, bayan tana kula da yadda idanunsa ke sauyawa. Kamo fuskarsa tayi ta manna masa sumba, “Kana da damuwa kana boye min why?”

Rufe idanunsa ya yi, “Babu komai barci kawai nake ji.” Jawo bargo tayi ta rufe su, “Oya muyi barci kada wani abu ya cijeka.” Rungume juna suka yi barcin yana sake kwasarta. Kamar a mafarki take jin zafin jikinta, cikin sauri ta yaye bargon ta tashi da sauri tana bubbuga shi cikin rudewa. Yana jinta amma sai ya yi kamar yana barci,

“Yaya ka tashi baka da lafiya.” Wannan karon dauriyarsa ta kare, hannayenta ya kamo, “Meenal jikina kamar wuta, bana son ki rude. Idan kika fita hayyacinki babu wanda zai iya taimakon mu a tsohon daren nan. Ki natsu ki ji abinda zan gaya maki.”

Duk yadda taso ta daure abin yaci tura. Addu’a ta dinga karantowa har ta dan sami natsuwar dora hannu akai cikin shesshekar kuka ta ce, “Wayyo ni Meenal!” Gaba daya ta bashi tausayi. Hannunsa ya kai bisa kanta ya sauke mata su.

“Ki je falo ki dauko min magunguna na. Sai ki dibo ruwan sanyi ki goge min jikina ko zafin zai ragu.” Kafafunta suna wani irin rawa ta fice. Har ta kusan falon ta sake dawowa jikinta yana wani irin bari, tasa kanta a kirjinsa. Yana iya jiyo yadda kirjinta ke kara. Ta kwatanta fita ya kai sau uku tana sakewa dawowa. Hawayen nan kamar ruwan fomfo.

A karo na karshe ta karasa ficewa zuwa falon. Saboda tsananin rudewa ta kasa gano inda magungunan suke, kawai ta yanke shawarar tabar neman maganin ta koma kila mutuwa zai yi, yake son sai ta bar wurin.

Har ta kusan kofa ta hango maganin ta koma kafafunta suna wani irin rawa, ta kwaso magungunan, ta dibo ruwa.
Tana shiga dakin taga baya motsi. Sakin ruwan tayi da magungunan, tana girgiza kai. “Shikenan! Shikenan haka rayuwata zata yi ta tafiya babu sauran jin dadi. Shikenan Ahmed kaima ka tafi. Ah…” Ta kasa karasa kiran sunanta sakamakon wani hajijiya da ya debeta, ta fadi kasa da karfi. Duk da haka babban burinta ta isa gare shi. Bakinta ya datse, tasan wani sabon jarabawa ce ta sameta, sai kuma wani ikon Allah zata iya hayewa.

Kafin wani lokaci ta koma mahaukaciya, bakinta yana rawa take nuno shi. a take abinda ya gaya mata ya dinga dawo mata, “Zan iya mutuwa. Bai kamata ki dinga kuka dan ina ciwo ba.”

Kuka ta rushe da shi mai karfi, “Don Allah Ahmed Don Allah Ahmed. Ni marainiya ce, Babana zai sami daman kashe ni, tunda babu idanunka, ka taimakeni ka dawo.”

Kuka take yi, kukan tausayin kanta, kuka take yi kukan rayuwar baya zata sake dawo mata, kuka take yi kukan ina zata dosa? Kuka take yi kukan wa zai sake tausaya mata? Kuka take yi kukan wa ta sani a garin Abuja? Kuka take yi, kukan waye zai rarrasheta idan anbata mata, kuka take yi kukan menene makomarta? Kuka take yi, kukan wani namijin ne zai zama me sadaukarwa kamar Ahmed?”

Tana jin fitsari ta kasa tashi, sai yinsa da tayi a kasa. Tana son ta motsa sai dai jikinta kamar andaure. Tunawa tayi da abinda mahaifinta ya gaya masa, “Kana nufin har duniyar ka shirya barinta?”

“Idan nace maka komai ina nufin har duniyar na shirya barinta.”

“Ahmed ka tafi ka barni? Nima zan bi duniya, nima zan nausa wata duniyar da babu wanda zai sake jina. Zan je inyi rayuwa ni kadai har Allah yasa inbiyoka. Ahmad ba zan jima a duniyar ba.” Kuka ya sake sarke mata. Lokaci guda bakinta ya datse, hakoranta suka dinga hadewa da juna, lokaci guda harshenta ya lankwashe. Kafin wani lokaci kuma jikinta ya saki gaba daya. Wayyo rayuwa! Duniyar ba bakin komai take ba, yanzu-yanzu suka gama wasa da dariya, cikin kankanin lokaci Allah ya yi yadda yake so da bayinsa. Tabbas Meenal ce abar tausayi. Makomarta ita ce babbar matsalar.

<< Meenal 14Meenal 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×