Sanyin Asuba ya farfaɗo da shi, yana ɗan waiwayowa idanunsa suka sauka akan Meenal. Shuru ya yi ya zura mata idanu kawai yana nazarinta.
Bai san lokacin da wani ƙarfi ya zo masa ba. Ya tashi ya ɗauko ta cak ya dawo da ita kan gadon. Kayayyakin aikinsa da ya siya musamman saboda lalurarta ya kwaso ya fara bata taimakon gaggawa. Sai da ya tabbatar numfashinta ya daidaita ta koma barci sannan ya lallaɓa ya kwaso magungunansa. Dole yana buƙatar cin wani abu tukuna, don haka ya haɗa tea yasha sannan ya haɗiyi magungunan. Daga. . .
Assalamu alaikum