Skip to content
Part 16 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Sanyin Asuba ya farfaɗo da shi, yana ɗan waiwayowa idanunsa suka sauka akan Meenal. Shuru ya yi ya zura mata idanu kawai yana nazarinta.

Bai san lokacin da wani ƙarfi ya zo masa ba. Ya tashi ya ɗauko ta cak ya dawo da ita kan gadon. Kayayyakin aikinsa da ya siya musamman saboda lalurarta ya kwaso ya fara bata taimakon gaggawa. Sai da ya tabbatar numfashinta ya daidaita ta koma barci sannan ya lallaɓa ya kwaso magungunansa. Dole yana buƙatar cin wani abu tukuna, don haka ya haɗa tea yasha sannan ya haɗiyi magungunan. Daga nan ya gabatar da Sallah.
Zama ya yi kusa da ita yana tunani.

“A haka rayuwar zata tafi? Ko zazzaɓi nayi sai ciwon Meenal ya tashi? Idan kuma na mutu ya zata yi? Ba zata yi tawakkali ba?”

Yana nan shuru akanta sai wajen sha ɗaya ta farka. A hankali ya kama hannayenta yana ƙirƙiro murmushi. Kafin tayi magana ya zare mata ƙarin ruwan ya miƙe ya kaita banɗaki. Bata da ƙarfin hana shi tana kwance a jikinsa taji ya tsoma ta a cikin ruwan ɗumi.

Yana mata wankan ya tsaya shuru yana kallon yadda hawaye ke zuba a idanunta.

“Meenal! Meyasa?” Abinda ya iya furta mata kenan don shi kansa fitar da kalamai suna masa wahala.

“Yaya baka mutu ba? Don Allah kada ka sake tafiya ka barni kaji? Idan ka tafi nima zan mutu.”

Manna mata sumba ya yi a bisa kumatunta. Sannan ya fara yi mata magana akan fuskarta. “Kada ki damu Meenal muna tare insha Allahu. Dole zamu yi gaggawan tafiyar nan saboda inyi maki aikin zuciyarki kina shan wahala.”
Kasa amsa masa tayi saboda abubuwan da yake yi mata.

Da kansa ya yi mata alwala sannan ya fito da ita.
Ji yake kamar har Sallar ma zai yi mata. A hankali yake bata kalace tana kauda kanta yana lallaɓata har ya samu ta ci. Shuru dukkan su sukayi basu da wata walwala.

Tana nan kwance ya fice, a lokacin ne taji kamar muryar Nuhu. Lallaɓawa tayi da nufin fitowa sai ta ji muryarsa, “Nuhu bana son wata magana pls ka ƙyale ni ni nasan dalilina nayin hakan. “

Nuhu ya maido masa martani, “Dalilinka ba dalili bane. So kake ka illata kanka? Kana son ka sami matsala ka kashe kanka ka bar yarinya a cikin masifa? Wannan abinda zaka yi fa ba wai wani abu ne daban da ba mallakinka ba a’a halak ɗinka ne. Idan Meenal ta sani da gudu zata amince ko don samun sauƙinka.”

Jikinsa ya bashi da mutum a falon don haka ya juyo kawai yana kallon yadda hawaye ke zuban mata har baki. Koƙari ya yi ya isa gareta amma tuni ta juya da gudu tana kuka. Nuhu ya taɓe baki, “Allah ma yasa ta ji duk abinda muke tattaunawa. Na barka lafiya.

Gun matarsa ya nufa ya kwantar da kansa a cinyoyinta yana juya kansa. “Meenal!” Da sauri ta ɗago kansa tana dubansa, “Yaya ina da alaƙa da ciwonka? Zan iya taimakonka? Ka gaya min ko menene nayi maka alƙawarin zan aikata don Allah Yaya. Ni nasan kana da damuwa amma ka gagara gaya min meyasa? Gaya min matsalar mijina.”

Baya jin zai iya gaya mata matsalarsa. Tunda ya iya haƙuri shekaru talatin da biyu babu ‘ya mace kuma bai mutu ba, baya jin zai gagara riƙe kansa har zuwa lokacin da matarsa zata sami farin ciki. Har yanzu Meenal tana cikin damuwa, har yanzu jinta take yi kamar tafi kowacce ‘ya mace zama ƙazama tunda aka haifeta ta hanyar ƙazanta. Yasha tashi cikin dare ya ji tana kuka tana roƙon Allah, akan ya dawo mata da danginta. Haƙiƙa kowani ɗan adam yana son zama cikin danginsa. Yana ji a jikinsa ko wannan ne aiki na ƙarshe da zai yi sai ya dawowa Meenal da farin cikinta.

“Meenal babu abinda nake buƙata a wurinki kamar inganki cikin farin ciki da walwala. Idan kika yi min haka kin gama min komai.”

Riƙo hannayensa tayi ta ce, “Amma…” Kafeta da idanu da ya yi yasa ta sunkuyar da kanta. “Tashi mu je yau mu shiga kichin inga ko kin iya girki.” Da zumuɗi ta miƙe ta ce kwanta ne ka jirani zan baka mamaki.

Tana fita ya mayar da kansa ya kwanta shuru. Ya rasa meke damunsa. Yana jin damuwa kamar wani abu yana shirin faruwa da shi. Yana fatan koma menene Allah yasa yazo masa da sauƙi.

Wayarsa ya ɗaga da ke neman agaji. Ganin Alhaji Khalid ne yasa ya ɗaga. Bayan sun gaisa ne yake koro masa bayani, “Idan kana da wata lamba ka kirani da ita.” Kafin yayi magana ya kashe wayar.

Dr. Bakori ya dubi wayar yana mamaki. Kawai ya tashi ya fice ba tare da Meenal ta sani ba. Tana can tana ciro abubuwa a cikin freezer da suka yi ƙanƙara.

Bai wani jima ba ya siya layin ya dawo ya sa a ɗayar wayarsa kai tsaye ya siya kati ta bankinsa sannan ya danna lambobin Alhaji Khalid ya kira shi.

“Doctor. Akwai matsala. Ina tunanin a cikin satin nan Mai martaba zai shigo Abuja. Na gama shirya maka komai, sai kuma ga wani amintaccen yaronsa ya gaya min ka taɓa basu kuɗi, ya ji cewar har yanzu Hon Munnir yana neman rayuwata. Ba wannan ne abin tashin hankalin ba, yadda Hon Munnir yaje mtn Office aka haɗa masa wayarka da tasa, ta yadda duk irin wayar da kake yi yana sane kuma yana iya ji. Dan haka duk wani shiri da kake haɗawa da irin wayar da muka yi yana nan a cikin wayar Hon Munnir. Yanzu haka ya tura wasu yaransa har Abuja ayi farautar rayuwarka. Doctor ina cikin ruɗu ko zan haɗa shi da ‘yan sanda ne?”

Dr. Bakori ya saki ajiyar zuciya mai ƙarfi, ” Kada ka damu yallaɓai wannan ba wata matsala ba ce. Duk dabara da wayon Hon Munnir sai na cimma burina. Zan ɗauki mataki kafin zuwan wannan ranar.”

Kashe wayarsa ya yi ya cigaba da dube-dube. Kuɗaɗen Meenal suna cikin banki yau zai gaya mata Pin ɗin Atm ɗin da duk abinda ya shafi bankinsa, saboda halin rayuwa. Yasan Hon Munnir wannan karon da ƙarfinsa zai fito. Don haka ko Hon Munnir ko kuma Dr. Bakori a cikin su dole mutum ɗaya ya yi nasara.

Duk wasu abubuwansa masu mahimmanci ya ɓoye su wuri me wahalar gani. Ihun Meenal yasa ya fito zuwa kitchen ɗin a firgice.

A zaune ya sameta akan kanta ɗin kitchen ɗin da akayi kamar baranda. Ido kawai ya zuba mata, ta ɗan kashe masa ido ɗaya. Yarinyar tana bashi ciwon kai. Hannu ta ɗaga masa, “Sauke ni Yaya na kasa sauka.”

Sharewa ya yi ya ce “Ta yadda kika yi kika hau ta nan zaki bi ki sauka.” Taɓe bakinta tayi ta cigaba da zuba idanu akan abincinta da ke tashin ƙamshi. Shi kuma ya juya ya koma falo.

Ihunta ya ji, amma ko alama bai leƙo ba yana nan kwance a doguwar kujera. Ganinta ya yi ta fito hannunta duk jini. A gigice ya kama hannun yana dubanta hankali a tashe,

“Menene haka Meenal? Kin ga abinda yasa bana son kina wasa da ihu ko? Yanzu kin ji ciwo na kasa zuwa induba ki duk a tunanina wasa kike yi. Sorry bari inɗauko abubuwan gyara ingyara maki.” Turo bakin tayi tana kuka ita a dole tana fushi da shi.

Yana gyara hannun yana ɗan satan kallonta, “Ai na baki haƙuri ko?” Shuru tayi tana kallon yadda ya cire sartsan da ya shige mata hannu da wani ɗan ƙaramin almakashi. Rintse idanunta tayi a lokacin da zafi ya shigeta. Rungumeta yayi yana bubbuga bayanta, har sai da ya tabbatar zafin ya ragu sannan ya cigaba, yana yi yana kallonta, tana sauya fuska zai dakata.

Bayan ya gama ne ta haye kujera tayi tagumi kawai. Da kansa ya zubo abincin yana jin daɗi a ransa yau zai ci abincin Meenal. Tana zaune ta kafe shi da idanu. Yana kai abincin baki ya shiga yamutsa fuska. Itama ta ɓata rai tana jin haushin zai ce abincinta babu daɗi. Ya ɗago ya zuba mata idanu yana girgiza kai alamun bata iya abinci ba.

Tagumi tayi itama tana girgiza kai alamun zata yi kuka. Da hannu ya kirawota ta tashi ta zo kusa da shi. A kunne ya raɗa mata, “Girkinki akwai dadi kamar yadda mai girkin take da daɗi.” Batasan lokacin da ta rungume shi ba tana ɓoye kanta.

Kullum yarintar Meenal ƙara bayyana yake yi, haka miskilanci da sarauta irin na ubanta sukan bayyana a jikinta a lokuta da dama, wanda ita kanta bata san tana yi ba.

Miƙewa yayi ya ce zai ɗan fita. Miƙewa tayi tace masa tana zuwa. Yana tsaye yana kallonta aguje ta shiga ta sauya kaya ta ɗauko takalma da hijabinta a hannu. Bata ja birki ba sai a gabansa. Shidai tsayawa ya yi yana kallon ikon Allah. “Sorry Yayana bari insa takalmin.” Da yake takalman mai igiya ne sai ta kasa sanyawa saboda sauri ga hannunta akwai ciwo. Ta ɗago tana dubansa, “Can you help?” Yau dai yana ganin ikon Allah. Sunkuyawa ya yi ya sanya mata sannan ya miƙe yana faɗin “Sai na dawo.” A baya take binsa kawai tana bashi labaran da ita kanta bata san makamar labarin ba.

A wajen motarsa ya tsaya, “Na gode da rakiya. Sai na dawo.” Hannunta ta riƙe, “Wash! Walh ko Yayana idan baka fita da ni ba ciwon zai ɗinga yi min zafi zanyi ta kuka ni kaɗai a gida.”

Idanu ya zaro, “Haba Meenal wannan ɗan ciwon ne kike yiwa raki? Shiga motar muje.” Yana juyawa tayi masa gwalo caraf a idanunsa. Hannu yasa da nufin kamo ta ta zille tana yi masa dariya.

A hanya suka tsaya suka yi siyayya. Tana kwance a jikinsa yana tuƙi. Apple take gutsura ta sa masa a baki sannan itama ta ci. Wayarsa ya miƙa mata ta kira Umma suna ta shan hirar su. Yana jin su shi tunaninsa ina zai je da Meenal? Bayan yau ya gama haɗa duk wani dalili da zai sa ya haɗu da mutanen Hon Munnir.

A gidan abincin ya ajiyeta yana kula da wasu mutane da suke binsa. Murmushi ya yi ya haɗata da Ice cream ya ce yana zuwa. Tana nan zaune ta hango wani kamar Lukman. Ajiye Ice cream ɗin tayi ta shiga binsu. Babu ko tantama Lukman ne da Ruƙayya. Tunani take yi inda zata sami wuƙa, dan alƙawari ne tayi sai ta kashe su.

Yaron Hon Munnir ya kira Ahmed har tashi uku bai ɗauka ba, cikin sa’a a kira na huɗun ya ɗauka. “Hello yallablɓai duk yadda ake ciki kada ka rabu da Meenal. Hon Munnir ya turo wasu mutane biyu mace da namiji da Meenal take neman su ido rufe. Idan ta haɗu da su zata ce zata bi bayansu daga nan za a sace ta.”

Sai yanzu Dr. Bakori ya fahimci tsantsar wautar da ya yi na barin Meenal. Tabbas yasan halinta zata ce zata biyo su. A gurguje ya daina bin mutanen da yake bi ya dawo da baya. Sai dai babu Meenal babu dalilinta.

Hankalin Dr. Bakori ya yi matuƙar tashi. Cikin ƙanƙanin lokaci ya gama birkicewa. Leƙe ya ɗinga yi lungu da saƙo, sai hangota ya yi tana shirin shigewa wani ɗan ƙaramin hanya. Da sauri ya bi bayanta, tana sanya ƙafafunta ɗaya yana fizgota. Gaba ɗaya ta zube a ƙirjinsa. Doctor Bakori ya tura kansa cikin wurin. Idanu ya zubawa Lukman yana jin wani irin takaici yana shigarsa, ” Ka koma ka gayawa wanda ya turoka Meenal tafi ƙarfin ku. Tunda bai iya kasheta a watannin baya ba, bana jin a yanzu ɗan ƙaramin tarkon ku zai iya kama ta. Wannan ya zama karo na ƙarshe da zaku sake shiga rayuwar Meenal. Idan ba haka ba zan ɗauki mataki mai tsauri.”

Dukkansu sun kasa magana, ita kuwa Meenal ta shammaci Dr. Bakori ta ciro ƙaramar wukar da ta ɗauko a kitchen ɗin restaurant ɗin ta cakawa Lukman gefen ƙirji, ta zaro ta sake ƙoƙarin caka masa Dr. Bakori ya riƙe hannunta yana mamakin a ina ta sami wuƙa? Kokawa suka shiga yi da Doctor akan ƙoƙarinta na sake cakawa Lukman wuƙa. Ganin zata iya jawo masa matsala yasa ya ɗauke ta da wani mahaukacin mari, wanda yasa ta dawo hayyacinta. Shikuwa Lukman neman hanyar guduwa kawai yake yi . Azaba ya ishe shi. Ita kanta Ruƙayya ta gigice tana ta ɓoyewa a bayan Lukman.

Dubansa tayi cikin bushewar zuciya, “Ni ce zan zama ajalinka. Tunda ka kashe min ƙanwa ka jefa rayuwata cikin masifa ni sai na zama silar ƙarar da dukkan zuri’arku.”

Ahmed ya fizgo hannunta suka ɓace daga gurin. Tun a hanya yake mata masifa har suka dawo gida bai daina ba. Ko tari mai ƙarfi ta kasa yi.

Tun kafin motar ta gama tsayawa ta buɗe saura ƙiris ta faɗi ya rintse idanunsa da ƙarfi ya kwala mata kira, “Meenal!” Cak ta tsaya jikinta yana kyarma. Tsoronsa ya shigeta, marin da yayi mata ya yi matuƙar razanata. Hannun Ahmed bai da kyau ko kaɗan. Da sauri ya fito ya riƙe kafaɗunta ya girgiza da ƙarfi. Yau ransa ya kai matuƙa a ɓaci, “Meenal! Ki dawo hayyacinki pls! A yanzu ke matar aure ce ba budurwa ba. Meyasa zaki kai hannunki jikin namiji har ki caka masa wuƙa? Meyasa? Meyasa??”

Idanunta a rintse take magana hawaye basu daina zuba daga rintsattsun idanunta ba, “Doctor! Lokaci ya zo da idan ba zaka iya jurewa ba ka sake ni kamar yadda muka yi alƙawari. Wallahi sai na ɗaukarwa ƙanwata fansa. Da hannayensa ya kashe min Nafisa😭 kuma sai ka dangantani da matar aure wajen karɓar ‘yancina? Yadda Nafisa ta bar gidan duniya Lukman shima sai ya bari.”

Buɗe idanunta tayi da suka koma jazir. Gaban Ahmed ɗin ta dawo ta bugi ƙirjinsa da ƙarfi, ga dukkan alamu ta fita a cikin hayyacinta. “Doctor kana ganin maƙiyina ka janyeni daga gareshi? Kana kallonsa ya sake ɓace min? Menene amfanina a duniyar nan idan ban kashe Lukman da Hon Munnir ba? Idan na bar su babu shakka ni za su kashe.”

Tana maganar cikin kuka tana sarƙewa. Tsoro ya ji kada ciwonta ya tashi dan haka ya rungumeta sosai a ƙirjinsa yana shafa bayanta, “Ya isa haka Sweetheart. Allah yana tare da mu, ba zai bar wani bawa ya cutar da mu ba. Calm down pls.”

A haka ya ɗinga gaya mata kalamai yana shafa bayanta, har ta koma ajiyar zuciya. Ɗaukarta ya yi cak ya shigar da ita ɗaki. Akan gado ya shimfiɗar da ita. Shi yasan inda yake taɓa mata yanzu ta hau dariya, hakan ya yi mata cikin abinda bai wuce minti goma ba fararen haƙoranta suka fara bayyana tana zillewa tana riƙe hannunsa. A haka suka afka wata duniya me wahalar fita.

A kunnenta ya raɗa mata, “Zan yi kewarki Bebina.” Cak ta dakata da dariyar tana dubansa, “Zaka je wani wuri ne? Kullum ina kusa da kai ba zamu taɓa yi wa juna nisa ba.” Bai bata amsa ba, amma ya tura mata ɗan saƙon da tayi matuƙar karbarsa.

A farfajiyar gidansu, Ahmed ne ke rufewa Meenal idanu ta hana shi sakat wai sai sunyi wasan ɓuya. Yana gama rufe mata idanun ya koma can wajen bishiya yana kallonta. Sanye take da riga da wando masu kyau kanta yana ɗaure da gyalen doguwar rigarta. Tayi masa kyau kamar ‘ya’yan turawa. Harɗe hannayensa kawai ya yi yana ta aikin murmushi. Komai tayi burge shi take yi.

Duwatsu ya samu yana jefa mata sai ta ji kamar tafiyarsa ta waiga. Ya shagala sosai a cikin tunani bai san lokacin da ta cire abun ba. Sai ganinta ya yi a gabansa tana turo baki, daf da bakinsa take magana bayan ta manna jikinta a ƙirjinsa, ” Shi ne ka barni ina ta haukana ni kaɗai.” Bai ce mata komai ba har sai da ta lalubi bakinsa ta tura masa sweet ɗin da take ta faman tsotsa. Zata zare jikinta ya girgiza mata kai.

Sun jima a cikin yanayin sai da ƙafafunsu suka gaza ɗaukarsu sannan ya saki ajiyar zuciya ya zame kansa yana shinshinar wuyanta.

<< Meenal 15Meenal 17 >>

1 thought on “Meenal 16”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×