"Ahmad ka tashi? Don Allah ka tashi kaji?" Shuru ya sake yi wanda hakan ke nuna mata ba buɗe idanun zai yi ba. Ita kam ko a haka Allah ya bar mata shi ta gode masa.
Meenal ta zama abar tausayi, ta rame tayi baƙi. Haka har ɗanfillo ya dawo suka cigaba da jinyar Ahmad amma babu alamun zai tashi.
Haka satittika suka juye suka koma watanni. Abin ya isheta. Ganin Ahmad a cikin datti yana sanyata kuka. Bata da kuɗi a hannunta sai Gold ɗinta. Dan haka ta cire Gold ɗin ta miƙawa ɗanfillo ta. . .