Skip to content
Part 19 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

“Ahmad ka tashi? Don Allah ka tashi kaji?” Shuru ya sake yi wanda hakan ke nuna mata ba buɗe idanun zai yi ba. Ita kam ko a haka Allah ya bar mata shi ta gode masa.

Meenal ta zama abar tausayi, ta rame tayi baƙi. Haka har ɗanfillo ya dawo suka cigaba da jinyar Ahmad amma babu alamun zai tashi.

Haka satittika suka juye suka koma watanni. Abin ya isheta. Ganin Ahmad a cikin datti yana sanyata kuka. Bata da kuɗi a hannunta sai Gold ɗinta. Dan haka ta cire Gold ɗin ta miƙawa ɗanfillo ta ce ya taimaketa ya je ya siyar mata da zoben Gold ɗin, tana da tabbacin kuɗin zai isa har ta kai shi asibiti. Ɗanfillo ya ƙarewa zoben kallo cike da rainin wayo.

“Abunda bai wushe naira talatin ba zaki ce yana da shaɗa? To ni ban shirya aɗinga yi min dariya ba.” Shuru tayi kawai tana dubansa, “Ka taimaka ka shiga cikin gari ka tambayi inda masu saida Gold suke idan ka kai masu za su auna su baka kuɗin.”

Ɗanfillo baya son dogon musu ya karɓi zobe ba dan ya amince da abinda take gaya masa ba. Wata rigar ya cilla ya tafi garin shiriritarsa ya saki zoben a can. Ko da ya duba bai gani ba bai damu ba, a ganinsa idan ta dame shi zai je ya siyo mata wani ya bata.

Meenal tana zaune tayi tagumi kawai tana duban Ahmad da ke kwance kamar matacce ta ji shigowar Ɗanfillo. Dubanta ya yi ya ce, “Ki shirya zan nuna maki wani ganye ki shiga daji can can shiki ki samo ayi mashi magani ya warke.” Meenal ta gyaɗa kai ta ce, “Ina zoben?” Ko ajikinsa ya ce mata ya faɗi. Bata sake magana ba ta koma ta ɗago fuskar Ahmad tana shessheƙan kuka, “Ka yi min alkawarin kana tare da ni ba zaka bar wani ya cutar da ni ba. Yau gashi kana kwance kana shan wahala Yayana. Bansan ya zanyi inkaika asibiti ba. Idan ka mutu ba zan taɓa yafewa kaina ba.”

Ruwan hawayen suka ɗinga zuba suna sauka a ƙirjinsa. Cak ta daina kukan tana jin yana motsa hannunsa. A hankali ya buɗe idanunsa da sunanta a bakinsa, “Meenal, Meenal.” Sai kuma ya yi shuru. Farin ciki yasa kawai ta ɗinga dubansa idanunsu a sarƙe da juna. Ƙoƙari yake yi sai ya tashi, ta girgiza masa kai, tayi ƙoƙarin ta taimaka masa ya ɗan jingina kansa amma ta kasa. Hannunta ya riƙe, sai a lokacin ya ji zafi daga kafaɗarsa. Ya ɗan rintse ido ya koma ya mayar da kansa yana ajiyar zuciya.

“Zaka ji sauƙi mu dawo kamar da. Zaka koma gaban su Hajiya cikin farin ciki. Bari inje inyi alwala ingodewa Allah da ya yi min wannan baiwar.” Yana kallonta ta fice. Rintse idanunsa ya yi yana tambayar kansa ina ne nan? Me ya faru da Meenal ta koma kamar tsohuwa? Har tsawon wani lokaci ya ɗauka anan? Meenal tana bashi tausayi. Yarinyar ta saba da wahala.

Tana idarwa ta dawo kusa da shi jikinta har rawa yake yi. Duk da baya jin wani ciwo sai tsamin jiki hakan bai hana shi yi mata magana ba cikin muryar marasa lafiya. “Anan wurin akwai babban Chemist? Ina son inbada saƙon kayayyakin da zan kula da kaina.” Cikin rawar jiki ta nufi mota ta kwaso duk wasu abubuwa da ta yi amfani da wasu wajen cire masa bullet.

Duk yadda yaso ya tashi ya kasa hakan yasa ya haƙura kawai. Bayani ya ɗinga yi mata na yadda zata yi amfani da su. Kafin wani lokaci Meenal tayi masa dressing. Yunwa yake ji kamar me? Baya son ya gaya mata ya tashi hankalinta. Shigowar Ɗanfillo yasa duk suka kafe juna da ido. Sai yanzu ya fahimci a inda yake. Farin ciki ya kama Ɗanfillo ya fice aguje sai gashi ya dawo da biredi da ruwan shayi.

Meenal taji daɗin abinda Ɗan fillo ya yi domin ta karanci yunwa a ƙwayar idanunsa. Don ma tana dabara tana zuba masa duk wani abin ruwa me gina jiki a baki. Karɓa tayi tana ɗiban biredin kaɗan tana tsomawa a ruwan tea sannan ta miƙa masa. Haka tayi ta bashi har ya ce ya ishe shi, sannan ta goge masa bakin.

Har baya son sauya fuska saboda yadda Meenal ta kafe shi da idanunta. Ɗanfillo ya taimaka suka ɗaga shi daga kwancen da yake. Bayan ya fita ne ya ce ta taimaka tayi masa alwala.

Tuni tayi cilli da wata kunya ita ke yi masa komai. Dubanta ya yi ya ce, “Lokaci baya jiran mu zan ɗan ƙara kwana biyu inga yadda ƙafar zata yi. Ita ce kaɗai matsalata indai na iya miƙewa babu shakka ba zamu sake sati a ƙasar nan ba. Zanje inyiwa bawan Allan nan aikin ciwonsa inyi naki sannan indawo infuskanci rayuwarki gaba ɗaya. Na tabbata Allah ya barni a raye ne saboda incika dukkan burikanki.”

Sarkin kukan tuni ta fara hawaye, ta shafi fuskarsa. “Ba zan sake barinka ka shiga hurumina da mahaifina ba. Ba zan ƙara yarda kayi nesa da danginka ba. Haɗuwata da kai babu abinda ta haifar sai masifa da tashin hankali. Ka yafe min Yayana.”

Rintse ido kawai ya yi ba tare da ya iya furta mata komai ba.

Wasa-wasa sai da Ahmad ya share sati bai iya takawa ba. Duk da kullum sai angwada yin hakan. Hankalin Ahmad yana kan mutumin da zai yiwa aiki akan ciwonsa. Yasan angwada neman layukansa ba a samu ba. Yana da buƙatar buɗe Email ɗinsa ya tura saƙon gaggawa.

Yau yana zaune ya yi shuru shi kaɗai Meenal taje samo kararen da zata dafa masa magani. Bai san ta dawo har ta ajiye ba. Sai jin tafukan hannayenta ya yi a fuskarsa. “Don Allah meyasa kake tunanina bayan gani a kusa da kai?” Jikinta ya ƙurawa idanu yadda duk ta lalace, sannan ya aika mata da murmushi. “Zo ki zauna kusa da ni nayi kewarki sosai sannan ki bani labari. Amma bana son kuka.”

Kusa da shi ɗin ta zauna ta maƙale masa. Duk da irin warin ranan da take yi hakan bai sa ya ji ba, sai ma sake ɗora fuskarsa da ya yi a wuyanta yana cewa, “Nayi kewarki Meenal. Nayi kewar rigimarki.” Dukkansu sun faɗa wata duniyar da suke tuna rayuwarsu a baya.

Ɗanfillo da ya jima tsaye da sandarsa yana ta kallonsu a ƙufule, ya ce “Kana gurgu amma baka daina ishkanshi ba. Yaushe zaka warke? Daga yau Aradu na bar shake shuwa nema maka magani da ni kake yi.”

Ganin basu san ma yana magana ba yasa ya taho kansu ya kwaɗa sallama. Ahmad bai saketa ba bai kuma daina bubbuga bayanta ba. Shi dai ɗan fillo da ya yi ta kallon irin iskancin nan gara ya nema masu mafita kawai su tafi.

Yana nan zaune tun ranar da ya buɗe ido rufewa ke masa wuya. “Baby Meenal ina son ki kaini cikin gari. Amma kafin nan ki fara duba motar ki gani ko zata yi aiki. Zamu shiga cikin gari muyi abubuwa mu dawo nan. Idan na gama shirina ko zan iya takawa ko ba zan iya ba zanje inceci rayuwar mutumin nan.

Meenal ta ce, “Meyasa ka damu da dole sai kayi aikin nan ne? Ka bari ka sami lafiya tukun.” Girgiza kansa ya yi, “Na rasa dalilin da yasa nake son dole sai nayi aikin nan. Nima idan naje can akwai ƙwararrun likitoci za su duba ni.” Bata sake magana ba kawai ta cigaba da matsa masa ƙafafu a hankali.

Ɗan fillo ya nemo bakanike ya dudduba motar ya yi duk abubuwan da ya kamata. Sannan suka taimaka Ahmad ya shiga motar mai gyaran ya tuƙa saboda sai sun shiga banki sannan zai sallame shi. Meenal ta ɗinga kaiwa da komowa har suka samu suka ciro kuɗi masu yawa suka sallami mai gyara.

Kai tsaye wajen aski suka wuce aka yi masa gyaran fuska sannan ta sake tuƙa su yana nuna mata hanya suka shiga kasuwa. Dogayen riguna ta kwaso da jallabiya sai ‘yan ƙananun abubuwan buƙata.

Haka ya wuce wani kamfanin gine-gine ya gaya masu irin ginin da yake buƙata da kuma inda filin da za a gina yake. Suka tabbatar masa za su bi shi a baya suga wurin. Kai tsaye ya wuce inda ake harkokin waya ya siya waya da sabon layin Airtel saboda garin can babu mtn. Haka sai da ya buɗe Email ɗinsa saƙonni rututu suka yi ta shigowa. Tuni ya sauke lambobinsa da ke cikin Email kasancewar akan Email ɗin yake saving ɗin duk wata lamba. Bai buɗe saƙo ko ɗaya ba suka kama hanya tare da magina.

Sai da Ɗan fillo ya kai shi gurin wanda ke siyar da fili a unguwar. Wanda arhansa ma ya ɓaci. Ya siya wawakeken filin ya ce a gina Masallaci. Haka daga can baya aka hau yi masa ginin gida na zamani.

Shi dai Ɗan fillo tunda yaga abin arziƙin nan bakinsa ya mutu. Aiki akeyi babu ji babu gani. Ɗan fillo ya baiwa kuɗi ya siyo katifa suka shimfiɗa a cikin bukkan nan.

Ta Email Dr. Bakori ya ɗinga musayar saƙonni a tsakaninsa da abokinsa Doctor Peter. Ya tabbatar masa mutumin yana nan kwance a Asibitin su bai ma san wake kansa ba. Hankalinsa ya tashi matuƙa ya gaya masu duk irin abubuwan da suka faru da shi, amma kuma yana tafe a cikin sati ɗaya insha Allahu. Godiya suka yi suka fara shirya masa yadda zai taho ba tare da wata matsala ba.

Duban Meenal ya yi har yanzu bata dawo da haskenta ba, ya miƙa mata hannu. Ta ƙaraso da sauri ta kwanta a jikinsa. A hankali ya furta mata, “Idan muka fita sai kin dawo asalin Meenal ɗinki sannan zamu dawo. ” Murmushi kawai tayi ba tare da ta iya furta komai ba. Ta sani indai Ahmad yana cikin hayyacinsa ba zai taɓa barinta tasha wahala ba. Hatta wannan baƙin tuwon da take ci ta daina ci yanzu. Ɗanfillo ke shiga cikin gari ya samar masu abinci.

Shafa kanta ya ɗinga yi har barci ya yi awon gaba da ita. Kafe ta ya yi da idanu yana ƙara jin tausayin yarinyar a zuciyarsa. Zai mayar da ita abin kwatance.

Cikin kwanaki ƙalilan ya gama shirya komai da taimakon asibitin da zai je gare su. Haka ginin da yasa ayi yayi tsawo. Hankalinsa bai kwanta ba sai da ya ganshi a cikin jirgi kusa da Meenal ɗinsa. Ajiyar zuciya ya ƙwace masa ya tabbata wata rayuwar kuma zai sake fuskanta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Meenal 18Meenal 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×