Ruwa ya dinga kwarawa kansa a cikin ɓoyayyen hotel ɗin da ya yi wa kansa masauƙi. Hakan ya gaza samar masa da natsuwa. Kalaman Meenal ya fi fasa aurensa zafi da raɗaɗi a zuciyarsa. Dole zai kasance Meenal tana tare da wata matsala akan namiji. Amma meyasa yarinyar bata aikata bincike kafin yanke hukunci? Ta yaya zai zaɓi fasa auren Salma a cikin minti talatin kafin ɗaurin auren su?
Dr. Bakori yana jin inama ya riski ranar mutuwarsa da irin wannan rana. Yana jin nauyin iyayensa, shi kansa ya so ya daure a ɗaura auren nan. . .