Skip to content
Part 2 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Ruwa ya dinga kwarawa kansa a cikin ɓoyayyen hotel ɗin da ya yi wa kansa masauƙi. Hakan ya gaza samar masa da natsuwa. Kalaman Meenal ya fi fasa aurensa zafi da raɗaɗi a zuciyarsa. Dole zai kasance Meenal tana tare da wata matsala akan namiji. Amma meyasa yarinyar bata aikata bincike kafin yanke hukunci? Ta yaya zai zaɓi fasa auren Salma a cikin minti talatin kafin ɗaurin auren su?

Dr. Bakori yana jin inama ya riski ranar mutuwarsa da irin wannan rana. Yana jin nauyin iyayensa, shi kansa ya so ya daure a ɗaura auren nan kamar yadda Salma ta buƙata. Sai dai kuma shi ba wawa bane, haka ba mahaukaci bane da yana ganin ƙaton rami zai zurma da ƙafafunsa.

A gefensa wayoyinsa ne zube dukkansu suna neman agajin gaggawa. Tun lokacin da labarin fasa aurensa ya iske dubban jama’a wayoyinsa suka kasa samun hutu.

Ya tabbata da ace bai san halin mahaifinsa ba, na mara masa baya akan dukkan abinda ya kawo, da tabbas sai ya ɗaura masa aure da Salma a yau ɗinnan.

A hankali ya zaro wayar da likitoci kaɗai ya ware masu ita, saboda gudun kiran gaggawa kada yazo bai ɗauka ba. Saƙo ne ya shigo a gajarce, ya buɗe, yana karantawa ba tare da ya gundura da sake bin rubutun ba.
“Dr. Bakori muna neman agajinka akan wannan mara lafiyar tamu ɗin nan da rayuwarta ke barazanar komawa ga Mahallicinta. Taimakonka a wannan lokacin yana da matuƙar mahimmanci.”

Girgiza kai ya ɗinga yi, ya furta a bayyane “Meenal sai dai ki mutu amma ba zan taɓa taimakonki ba. Namiji kika tsana don haka kin haɗa har da mahaifina kenan. Namiji ya gama taimakonki a gidan duniya.”

Rintse idonsa ya yi yana kallon hoton dukkan abubuwan da suka faru a cikin mintuna talatin da suka rage aurensa ya ƙullu a tsakaninsa da Salma.

Kiran mahaifinsa shi ne kira na ƙarshe da ya yi tozali da shi, haka shi ne lokacin da ya kashe dukkan wayoyinsa.

Meenal ce kwance tamkar matacciya, domin ciwon ya daɗe bai yi irin tashin da ya yi a yau ba. Umma tayi kuka har ta ji babu daɗi. Haka yayar Meenal Rufaida tana zaune idanun nan sun kumbura. A dalilin hakanne Umma bata so Rufaida ta sani ba, sai dai gaba ɗayan su a lokacin suna cikin gidan bikin.

Halima da shigowarta kenan ta dubi Umma cikin tausayawa ta ce, “Me namiji ya yi wa Meenal? Meyasa ta tsani maza haka? Ta tsani namiji amma kuma ga shi tana wasa da rayuwarta, wanda kai tsaye za ace namiji ya kawo ta irin wurin nan.”

Rufaida ta girgiza kai ta sharce hawayenta, “Meenal bata taɓa soyayya ba, Meenal bata san baƙin cikin namiji ba. Akwai ɓoyayyen al’amarin da ke ɗauke a cikin zuciyarta wanda ta jima da shi, haka zai yi wahala ta saba da matsalar da ke danƙare a cikin rayuwarta. Meenal tana rayuwa ne kawai, amma a zahiri ta fi zama Gawa fiye da rayayya. Ki daina bincike akan matsalar Meenal, domin ko kin yi babu abinda zaki iya samu face duhun da ko tafin hannunki ba zaki iya gani ba.”

Gaba ɗaya aka sake yin cirko-cirko aka kuma rasa wanda zai sake cewa wani abu.

Wasa-wasa sai da Meenal ta kwashe sati biyu cur a Asibiti sannan likitocin suka samo kanta. Har suka sallameta tare da dokoki masu yawa.

Ƙarfe goman dare agogon ɗakinta ya buga. A lokacin ƙarfe goman dare. Tsaf ta gama shirinta cikin riga da wando. Lumshe idanunta tayi bayan ta dubi kyanta a cikin madubi. Bata son fitar, sai dai kuma bata taɓa jin bata son ta fita, ta fasa hakan ba. Ta ƙofar baya ta bi tasa kai ta fice.

Mai Napep ɗin da ya kasance shi ta ɗauka aiki, shi ta samu yana jiranta. Tana zaune cikin napep ɗin tana ƙarewa titi kallo, kamar yadda ta saba.

‘Yan mata ne da samari suke ta cashewa a tsakiyar mashayar. Wuri ne ƙazantaccen wuri wanda duk wani ɗan musulmi ba zai yi fatan ya kasance a irin wurin nan ba. Da ƙawarta Farida suke zaune wanda ita ta nuna mata irin wurin nan. Kamar kullum Farida ce ke bada umarni, haka akwai manyan maza a tsaye akan su, saboda Meenal bata son wani ya yi mata magana. Kwalaban giya ne kala-kala zube a gaban su, hakan yasa Meenal ɗaukar kofi ɗaya wanda Farida ta zuba mata, tayi kamar ta kai baki ta faki idanunta ta watsar.

Farida ta rantse sai ta ɓata Meenal saboda ta tsaneta. Ƙawayen yanzu kenan, a fuska zaka rantse babu mai ƙaunarta a kaf ƙawaye kamar Farida. Sai dai abinda bata sani ba, Meenal ta haɗu da ƙawaye wa’inda suka fita iya haɗa munafurci. Sun fi ta ƙwarewa a iya iskanci. Hasalima da ƙawa da namiji suka samar mata da wannan matsalar. Uwa uba jigonta. Sai dai daga ita har ‘yan uwanta suna ɓoye wannan matsalar agun kowa, hakan ke sawa jama’a shiga ruɗu akan rayuwar Meenal.

Lokaci zuwa lokaci suna ɗan taba hira. Farida ta miƙe domin zagayawa don haka wurin ya rage daga ita sai masu gadinta. Daga bayanta ta ji mutanen da ke zaune suna magana, “Kai ga wani Guy can naga ya fito da kudi sosai, kawai muyi masa dabara mu bubbuge shi mu kwace komai nasa. Yauwa ga shi can ya tashi yabi lungun can. Bari Sadi ya ƙaraso muje mu far masa.”

Meenal ta ruɗe fiye da tunanin mutum. Ita kanta mamaki take yi. Kai tsaye ta bi inda ake nuna mutumin da kallo, bayansa kawai ta hango. A karo na farko da taji zata iya taimakon namiji. A zuciyarta taji bata son su taɓa lafiyar mutumin da bata san ko waye ba. Zuciyarta tayi saurin ankarar da ita, “Ba lalle bane idan shi yaga wasu za su hukunta ta irin hakan ya tausaya mata. Namiji ne fa.” Da sauri tasa hannu ta toshe kunnenta, hawaye suka shiga gangarowa har cikin bakinta, “Allah ka yafe min ba zan taɓa son namiji ba. Zan taimakeka a matsayinka na musulmi ɗan uwana.”

Miƙewa tayi ta kama hanyar da mutumin ya bi. Sai dube-dube take yi cikin lungu bata ga kowa ba. Hango shi tayi ya kife kansa a jikin bango. A lokacin ne kuma ta ji maganar mutanen ƙasa-ƙasa. Cikin hanzari ta iso gun mutumin kawai ta kamo rigarsa. Cike da mamaki yake tunanin waye ya ga maɓoyarsa har ya riƙo rigarsa. Kafin ya juyo har ta fizgo shi suka faɗa wani lungu da babu girma, hakan yasa numfashin su ke dukan juna, saboda ƙanƙantar wurin.

“Za su kashe ka, kada kayi motsi su ji inda kake. Naji suna faɗar za su kasheka ka bari su bar wurin sai ka kama gaban…” Bakinta ya kasa ƙarasa maganar da ke ɗauke da fatan bakinta. Shi kansa tunda ta fara maganar yake dubanta. Idanu suka kafe juna da shi kowanne da abinda yake saƙawa a zuciyarsa. Shi mamakin yarinya mai tarbiyya da kamun kai yake yi dalilin da zai kawo ta irin wurin nan. Wato su kansu mata halayyarsu iri ɗaya ce. Ta yaya zai iya amincewa wata ‘ya mace? A irin wannan lokacin ina mace mai ibada kamar mahaifiyarta take? Ta yaya yarinya ƙarama kamar Meenal tasan hanyar mashaya?

Tsoro ya shige shi yana tunanin ta yaya zai ba ‘ya’yansa tarbiyya don kaucewa cin amanar Allah?

Tana jin motsin su tayi saurin sake yi masa rumfa. Mamaki ya sake lulluɓe shi. Ya tabbata Meenal tafi kowa tsanarsa, ya yarda ta taimake shi ne a lokacin da bata san wa ta taimaka ba. Amma meyasa a karo na biyu bayan ta tabbatar da maƙiyinta ne ta sake taimakonsa? Abubuwan yarinyar akwai ɗaure kai.

Tana kallo suka fice suna surutai ta saki ajiyar zuciya me ƙarfi. Hannu tasa ta hankaɗa shi da ƙarfin tsiya, sai dai ko motsi bai yi ba, hakan yasa ta shiga yarfe hannunta tana jin danasanin taimakonsa.

Ta kasa magana saboda tsananin takaici da baƙin ciki. Kawai sai ta girgiza kai. Zata fice ya sa mata ƙafa. Ta dubi ƙafafunsa ta ce, “Na taimakeka kana son sa min ƙafa infaɗi ko? Namiji kenan. Indai namiji ne idan ya sami dama akan mace a take zai kasheta. Allah ba zai ƙara baka dama ba. Daga ƙarshe ku ji tsoron Allah.”

Duba ɗaya zaka yi masa ka fahimci ko a jikinsa. Barin wurin ya yi ya koma ta inda ba lalle a ƙara gane shi ba. Farida ta dube ta, “Ina kika je haka?” Bata iya bata amsa ba sai goge hawayenta da tayi cikin dabara.

Farida ta tura mata manyan kwalaban giya ta ce “Kisha wannan zaki sami sauƙin damuwar da kike ciki kullum.” Meenal tayi murmushi ta ce, “Shiga ciki ki samo min farfesu.” Babu musu ta miƙe ta wuce. Meenal ta kwashi giyan ta zube a ƙasan teburin ta miƙe ta ɗauko kwalaban da aka riga aka sha aka bar kaɗan, ta buɗe ta shafa a jikinta da kusa da bakinta, sannan ta kama lumshe idanu.

Farida tana dawowa ta ga yadda Meenal take tangal-tangal tayi saurin taro ta tana murmushi. Farfesun da ba a sha ba kenan ta nufi mota da ita ta ce wa masu tsaronta su tafi. Har kullum masu tsaron suna mamakin Meenal. Sai dai abinda babu ruwan su.

Yana tsaye yana kallon yadda Farida take kamo Meenal tana zillewa. Suna kama hanya ya mara masu baya, ba tare da sun ankara ba. A ɗan nesa da ƙaton Gate ɗin su Farida ta ajiyeta, bata jira shigarta gidan ba tayi tafiyarta. A lokacin sha biyun dare ya gota. A gurin da ta barta anan ta zauna ta haɗa kai da guiwa tana kuka kamar ranta zai fita. Muryarsa ta ji a tsakiyar kanta yana gasa mata magana a maimakon lallashi.

“Kina ‘ ya mace yarinya ƙarama kike wannan halayyar? Kin rasa tarbiyya. Kin tsani namiji, amma da namiji yana cikin rayuwarki da bai barki a sake ba. Har kullum uba ne yake damuwa da tarbiyyar ‘ya’yansa. Kowani gida kika shiga sai ansami ‘ya’ya sun fi tsoron mahaifin su fiye iyayensu mata. Namijin nan da kika tsana shi ne mutumin da tun kina ciki zai kula da asibitin mahaifiyarki, har a haifeki ya yanka maki ragon suna. Daga nan duk wani motsinki idonsa yana kai. Babu mahaifin da zai iya rintsawa ba tare da yasan lafiyar iyalansa ba.”

Meenal ji take yi kamar tunda aka haifeta ba a taba gwaɓa mata magana kamar na yau ba, ji take Dr. Bakori shine namiji na uku da ta fi tsana fiye da sauran. Bata son ya gane tana hayyacinta, tana son shi kansa ya tsaneta fiye da kowa.

Miƙewa tayi takalma a hannu ta miƙe. Jiri ne na gaske ya kwashe ta da karfi, sai dai bata kai ga zubewa a ƙasa ba Dr. Bakori ya taro ta. Tsamin giyan da ta shafa a jikinta ya buge shi. Sai dai kuma a yadda yaga yanayin buguwarta bai kamata ace tsamin ya kasance kaɗan ba. Ƙare mata kallo yake cikin ƙananan kayanta. Yarinyar ta haɗa komai da komai, sai dai ta rasa babban makamin rayuwa wato ‘tarbiyya.’ Ya taimaketa ne saboda ita ma ta taimake shi. A ƙa’idarsa idan har kayi masa alkhairi sai ya rama ko ta wacce hanya ce.

Jikinta rawa yake yi sosai saboda haɗuwar jikinsu. Yadda firgici ya bayyana a dakalin fuskarta abun ya bashi mamaki. Domin unguwar a wadace yake da hasken wuta. Tana son ta fizge sai dai yin hakan zai iya tona asirinta. Tunawa da Salma da tayi yasa ruwan hawaye soma tsiyaya. Tana ji tana gani ya sadata da bakin Gate ɗin su. A dai dai saitin kunnenta ya ce, “Ban yi zaton Ummanki zata kasa sanya idanu akan amanar da Allah ya bata ba. Kema ki ji tsoron Allah.”

Wayyo waye wannan Dr. Bakorin? Ƙaddarar ciwonta ya haɗa ta da shi, yau gashi ya sami dama yana ta gaya mata magana. Yau gashi yana son cin mutuncin uwar da tafi kowa agunta. Inama kwarjininsa zai daina dukanta, da ta nuna masa kuskurensa. Tana kallonsa ya saketa ya yi gaba. Ta sani ba zai tafi ba sai ya ga shigarta. Don haka ta kwankwasa Gate ɗin mai gadi ya buɗe. Kuɗi ta ciro ta miƙawa mai gadin ta durƙusa tana roƙonsa da kada ya bari Umma tasan ta fita,kamar dai yadda ta saba yi masa, a duk ranar da tayi irin fitar nan.. Cike da tausayawa ya ce mata babu komai. Tana shiga ya mayar da ƙofar ya rufe.

Dr. Bakori ya yi ajiyar zuciya, yana jin kamar yafi kowa damuwa. Ya zama dole ya daina wasan ɓuya da iyayensa ya koma gida. Sai dai abinda yake tsoro a tambaye shi dalilin fasa auren ‘yar uwarsa Salma. Shi kuma har abada ba zai taɓa faɗa ba.

Har ta shiga gida Hajiya bata sani ba. Gadonta ta faɗa tana shessheƙa. Ta tabbata rayuwarta tana cikin matsala ! Ta tsani maza amma kuma maza kullum sai sun bibiyi rayuwarta. Meyasa ba zata yi haƙuri da ƙaddararta ba ta zauna a gida? Yau gashi dalilin sanin wani abu duniya ta fara yi mata kallon ‘yar iska, a dalilin halinta na bincike tana son faɗawa cikin matsala. Yau gashi a dalilinta an zagi tarbiyyar ‘ya mace. Gaba ɗaya maganganun da ya faɗa akan maza ƙarya yake yi, kawai ya faɗi son zuciyarsa ce. Ya zama dole ta daina jawowa mahaifiyarta zagi idan har tana son ta ga dai-dai a rayuwarta. Miƙewa tayi da sauri ta nufi banɗaki tayi wanka tare da ɗauro alwala. Ta jima tana neman gafarar Ubangiji, haka tayi addu’a mai tarin yawa akan ya goge mata duk wani abu da ya shafi babin rayuwarta. Tana son ta mance komai tana son ta gina sabuwar rayuwa, amma ta yaya? Sai yaushe mafarkinta zai tabbata?

Ƙarfe tara agogon ɗakin ya buga ta tashi da kanta tana Salati. Ko Sallar asuba bata yi ba. Ta tabbata mahaifiyarta tayi tunanin tayi Sallah ne shiyasa bata tashe ta ba. Yau ne karo na farko da tayi wasa har shaiɗan ya rinjayeta ta jinkirta gaida Ubangijinta.

Kuka take yi a cikin Sujjadarta tana neman afuwan Allah. Ta jima a Sujjadar ƙarshe kafin ta ɗago. Kintsawa tsaf tayi ta fito sanye da doguwar rigar atamfa.

Yayan mahaifiyarta ne da wasu tsofaffi suka zo gidan. Mamaki sosai take yi da ganin su a irin lokacin nan. Da fara’a ta fara gaida Baba Sani, sannan ta dubi tsofaffin da dukkansu suna matsayin kakanninta ne ta gun uwa. Tsokanar su ta ɗinga yi suna kwasar dariya. Baba Sani ya yi gyaran murya hakan yasa ta dawo hayyacinta. Sai yanzu ta kula da Ummanta bata cikin natsuwarta. Kafe ta da idanu tayi gabanta yana faɗuwa amma sai tayi fuska.

A ƙasa ta nemi wuri ta zauna tare da sunkuyar da kai. “Meenal saboda ke muka zo gidan nan.” Bata ɗago ba, haka kuma bata ce komai ba. Hakan ya bashi daman cigaba da magana, “Yayanki Soja shi ya sameni ya ce yana sonki. Kinsan dai yadda ake matsa masa ya yi aure ja’iri ashe ke ya hango. Amma yanzu kam Alhamdulillah tunda bai fita waje ya nema ba.”

Tirƙashi! Yayan mahaifinta yafi kowa. Haka yana daga cikin namijin da take ɗaga masa ƙafafu. Yau gashi ya kawo ƙoƙon baransa akan gudan jininsa Yaya Sulaiman.

Tasan kaf dangin mahaifiyarta babu wanda ake ji da shi kamar Yaya Sulaiman. Nan take zuciyarta ta fara gaya mata Baba Sani mutum ne mai son zuciyarsa. Haka duk namiji halinsa guda da Ɗan uwansa namiji. Idan ba namiji ba waye zai iya tunkararta da maganar aure a yanzu? Ba zata iya cewa A’a ba, haka ba zata iya cewa eh ba. Har yanzu tana ganin ƙimarsa. Ɗagowa tayi tana murmushi daga bisani tayi ɗaki da gudu. Wannan alamu ne na amincewarta. Gaba ɗaya aka hau dariya, amma banda Umma da ta nausa a cikin tunani.

Bayan tafiyarsu Umma ta ƙarasa ɗakin Meenal cike da tunani. Abin mamaki fuska a sake Umma ta same ta. Zama tayi a gefenta tana dubanta, “Meenal idan baki amince da auren Yayanki ba ki fito ki gaya min insan abin yi. Meenal bana son inrasaki.” Meenal ta ɗan yi ajiyar zuciya ta tashi zaune tana duban mahaifiyarta, “Umma bazan taɓa yiwa Baba Sani jayayya ba. Amma zan tabbatar maki da dukka maza irin su ɗaya, halin su ɗaya. Ba zan taɓa yarda wai Yaya Sulaiman yana sona ba. Umma bana son ko gaisuwa ce ta haɗa ni da namiji. Haka abinda yasa ban damu ba, nasan babu inda maganar nan zata je, ni da kaina nayi maki alƙawarin sai na nuna maki dalilin da yasa Yaya Sulaiman zai auri ‘yarki. Sai kuma na tabbatar maki namiji sunansa namiji, ba za su canza ba.” Gyaɗa kanta kawai tayi tana jin tsoron farucin ‘yarta. Amma duk da hakan ta ji daɗi da bata jawo mata baƙin jini ba.

Tana ficewa Meenal ta bi ta da idanu tana cewa, “Zan tabbatar maki hatta yayanki sunansa namiji. Akwai ranar da yayanki zai mance alaƙarki da shi, akwai ranar da sai yayanki ya goranta maki.”

Dr. Bakori yana yawan faɗo mata a rai. Ta kasa cire daren jiya a idanunta. Shi ne namiji na farko da tarihin rayuwarta ta taɓa ganin za a cuce shi ta hana, shine mutum na farko da ya taɓa riƙo ta da sunan taimako bata wanke kykkyawar fuskarsa da mari ba. Shi ne mutumin da ya ci mutuncinta ta kasa ɗaukar mataki. A hankali ta rufe idanunta hawaye suna gudu a fuskarta, “Allah ka nesanta ni da duk wani da namiji.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Meenal 1Meenal 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×