Skip to content
Part 3 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Dr. Bakori ne zaune a tsakiyar famili ɗin na S.S Bakori. Yaso ƙwarai ayi masa faɗa kamar yadda ya zata, amma sai mahaifinsa Alhaji Sudais ya dube shi da kulawa, “Ni na haifeka, nasan halinka, nasan abinda zaka aikata. Duk da abinda kayi ya razana kowa, har yaso ya jawo taɓarɓarewar zumunci a tsakanina da ƙanina Sammani. Haka a dalilin hakan Salma ta faɗa mawuyacin hali. Nasan akwai dalili mai ƙarfi da yasa ka aikata hakan, nasan da zakayi hakan da gangar da ba zaka taɓa yarda a sanya rana ba, bare har ka bari saura mintina a ɗaura. Ba zan tambayeka dalili ba, haka ba zan bari kowa ya dameka da tambaya ba, amma ina son kaje gidan Sammani ka ba su haƙuri don ka ɓata masu ƙwarai.”

Hajiya ta girgiza kai ta ce, “Alhaji ni abinda yafi damuna da lamarin nan ba zai wuce yadda akayi ta surutai ba. Sai da ta kai Salma ta kasa fita ko da kofar gida. Kasan mutanen mu basu san menene kaddara ba. Da zarar ansami matsala a aure, basa tunawa da komai ba sa tuna cewa suna da ‘ya’yan nan a gabansu sai su hau yin maganganu marasa kyau akai. Wai ka dubi Salma kawayenta ke cewa dama babu sanin mijin suka kirkiri daura aure. Idan ba rashin hankali na mutane ba, ta yaya yarinya kamar Salma zata iya kirkirar wannan bikin har ma ta bari sai angama komai? Damuwarsu daya meyasa ba za su Dan asalin dalilin da yasa aka fasa ba? Ina goyon bayanka Alhaji ban yarda Ahmad ya fadi dalilin ba, domin yana fad’awa mutum daya kamar ya gayawa duniya ce. A bar su suyi ta laluban dalilan su.” Alhaji ya girgiza kai,

“Halin mutane yana bani tsoro. Kuma abin takaicin makiyinka yana tare da kai. Haka wani biki da na gani daga andaga bikin saboda lalura itama amaryar tasha surutu har duniya suna ganin sanya ranar bogi ce. Idan ba rashin hankali ba ko a film ban taba ganin mace me mutunci ta sanyawa kanta rana ba, bare akai ga kashe kudi da shirin biki duk ace karya ce? Kai tsaye nake kallon irin mutanan nan masu neman abin magana da jahilai. Akwai jahilci a cikin shiga abinda babu ruwanka. Ko da yake Gawa yana kwance ma ana zaginsa da fadin maganganu bare mu masu rai? Insha Allahu komai zai wuce. Salma zata dawo kamar wata matsala bata taba faruwa ba. Ba akanta aka fara fasa aure ba. Anyi hakan akan mutane dubu. Allah ya yi mata zabi da abinda yafi zama alkhairi.” Gaba daya aka amsa da Amin.

Har ya shiga daki yana juya lamarin da iyayensa ke tattaunawa. Duniyar nan tana bashi tsoro. Idan aka fasa aure ko amaryar ce ta fasa, masu magana da yawun wasu za su ce ai ango ne ya fasa.

Yau yasha alwashin zai sake lekawa mashayar nan ko zai ci karo da Meenal. Yana son ya cire yarinyar daga cikin tunaninta akan namiji. Yana so ya nuna mata tunaninta karya ne akan namiji. Yana son ya yi mata shigo shigo ba zurfi ya nuna mata babu wani ko wata da suka fi karfin jarabtar Ubangiji

Fitowa ya yi da nufin fita Hajiya ta tare shi tana dubansa, “Bana son kana fita sai inyi tunanin kamar zaka sake yi min nisa ne.” Girgiza kai ya yi tare da karasawa kusa da ita, “Hajiya babu abinda zai sake nesanta ni da ke, nima na shiga wani hali a sakamakon nesanta kaina da nayi da ku. Don Allah ki yafe…” Hannu tasa ta rufe masa baki tana girgiza kai, “Har abada ni me uzuri ce akan ‘ya’yana. Allah ya rubuta sai wannan kaddarar ta same mu, bamu isa muyi jayayya da yin Allah ba. Sai dai mu kara dagewa da Addu’a. Sai ka dawo Dana.”

Huci ya fesar me karfi yana sake jin danasani yana shigarsa. Iyayensa sun kasance masu ilimi kuma suna amfani da shi. Haka ya fice jikinsa a sanyaye.

Har karfe goman dare babu Meenal babu dalilinta. Gajiya ya yi da zaman ya mike da nufin barin wurin. Farida ya hango ta doshi kujerar da ke kusa da shi ta zauna. Tana yi masa wani shu’umin kallo. Kai tsaye ta ce, “Ka hadu ko ta ko ina. Kana da kyau matuka. Duk macen da ta sameka a matsayin miji zata zama Zara a cikin wata. Kana da natsuwarka, baka yi kama da masu irin halayyar nan ta zuwa mashaya ba. Ko kaima kana cikin damuwa ce irin na Meenal inkawo maka mafita?”

Nan da nan zuciyarsa ta hau tafarfasa. Ta yaya yarinya karama kamar wannan zata ajiye shi tana gaya masa irin wannan maganganun? Har ya mi’ke da nufin dai-dai ta mata natsuwa, sai kuma ya tuna da abinda ya kawo shi, don haka ya koma ya zauna yana addu’a har zuciyarsa ta dan yi sanyi. Ita kanta Farida tsoronsa ne ya shigeta sosai. Abin mamaki sai ta tsinci muryarsa yana mata magana, cikin natsuwa. “Wani taimako nake son ki yi min shiyasa nake ta nemanki. Ko nawa ne zan iya baki.” Sai da ta tattaro natsuwarta gudun kada ta sake fusata shi don ta kula masifaffe ne. “Insha Allahu idan na sani zan gaya maka.” Mamaki ya ishe shi. Ashe dama musulma ce? Duk kallon da yake yi mata babu abinda addininmu ya hada da mace irin wannan. Hadiye abinda ya taso masa ya yi, sannan ya dubeta a tsanake, “Ya kike da Meenal? Kuma waye mahaifinta? Ina nufin yana raye? Meyasa Meenal a cikin damuwa haka da har take kokarin kashe kanta, ta hanyar cusa tsanar namiji, wanda ya haifar mata da cutar da ko yau aka ce ta mutu babu me yin mamaki.”

Farida da ta ji hassada ya kama ta, ta dan hade rai, “Sonta kake yi ne?” Shima hada ran ya yi sosai, har sai da Farida tayi danasanin furta wannan kalaman. “Ke kin ga ni nayi maki kalar wanda zai iya nemanta? Tambayarki nayi idan ba zan sami amsa ba sai in canza gurin tambayar.” Yanzu ta gama fahimtarsa mutum ne da baya son raini. “Ok. Meenal dai Babanta ya mutu. Ni kawarta ce kamar yadda kake ganin mu wani lokacin a tare. Naji daga majiya me karfi mahaifinta ma da bakin cikinta ya mutu. Ta tsani namiji ne saboda namiji ya yi mata fyad’e har ta sami ciki. Kuma daga baya ya ce ba zai auri watsattsiya ba. Ya ce bai taba ganinta ba. Bakin cikin hakan yasa ta tsani maza. Ta mayar da shaye-shaye ruwan shan ta. Haka kuma ‘yar Lesbians ce ni kaina ta nemeni, ban dai bata hadin kai bane. Gaba daya bata da tarbiyya, babu namijin da zai yi fatan ajiye mace kamar Meenal.”

Tir’kashi! Da ace Meenal bata san halin kawaye ba, idan aka zo aka bata labarin abinda Farida take fad’a babu shakka da ta sume. Haka kawaye suke, basa kaunar kawarsu ta fi su. Wannan ke nuna cewa a shirye suke da su bata komai domin ganin kun qare a lalace. Da wahala mace ta sami cigaba kawa bata nuna mata hassadarta ba. Idan ta barki kin aure shi kenan. A yanzu maza sun gane da zarar aka fara gaya masu maganganu akan wacce za su aura, basa damuwa, don sun gama fahimtar kawayen.

Dr. Bakori da ya ji ya fara gundura da bayanin da shi da kansa ya nema ya mi’ke kawai. “Idan abinda kika fad’a gaskiya ce, ina fatan Allah ya shiryeta. Idan kuma ba gaskiya ba ce, Allah ya saka mata tun a gidan duniya. Na gode.”

Jikinta ya yi matukar sanyi. Sai dai shaidaniyar zuciyarta tana gaya mata ba zata taba barin Meenal ta sami namiji kamar Dr. Bakori ba. Mutumin da ya hada komai wajen haduwa. Kudi ya ajiye mata ya bar wurin. Gaba daya zuciyarsa ta kasa gazgata zancen Farida. Meenal bata yi masa kama da wacce zata aikata hakan ba. “To amma ai ka ganta a mashaya kuma kaji tsamin giya a jikinta.” Wata zuciyarsa ke ankara da shi abinda yake son mancewa. Girgiza kansa ya yi, ” Idan na ganta a mashaya kuma naji tsamin giya ai ban ganta da idanuna tana sha ba. Dole zan yi amfani da abinda na gani ne bawai abinda wasu suka gaya min ba. Haka wannan dalilin nata na tsanar maza ya yi masa qanqanta da har zata iya kasa rike kaddararta har ta tsani namiji haka.” Sitiyarin motarsa ya buga da karfi. “Meyasa na damu da lamarinta? Menene alakana da ita? No ya kamata inkoma bakin aikina in cigaba da kulawa da marasa lafiya tun kafin miskilan yarinyar nan ta taba min aiki. Daga yau na bar sake kutsawa cikin rayuwarta. Musulma ce ‘yar uwata ina yi mata fatan samun sassaucin rayuwa.”

Dr. Bakori ya jima yana nazarin yarinyar da ya kamata ya aura. Yana son farantawa iyayensa. Zai yi aure ne kawai ba don yana son yarinya ba, sai don kawai ya tabbatar da farin ciki a zuciyoyin mahaifansa. Sai dai tun akan Salma yake cikin tsoro da firgicin mata. Ta ina ya kamata ya fara? Meenal tana tsoron maza shi kuma yana tsoron mata.

A hankali tunanin zuwansa Islamiyya ya zo masa. Anan ne ya kamata ya duba yarinya har ma ya aureta, haka kadai zai yi ya samarwa iyayensa kwanciyar hankali.

Dr. Bakori bashi da lokacin aiwatar da hakan, don haka ya kira abokinsa Salis ya gaya masa ƙudirinsa. Salis ya ji daɗin wannan bayani ya kuma yi masa alkawarin zai je har makarantar ya sami malaman ta yadda za su gaya masa yarinyar da ta fi kowacce yarinya hankali da natsuwa. Haka suka rabu Dr. Bakori yana jin tamkar zai sake aikata kuskure ne a cikin rayuwarsa.

Garin Kaduna. Yanayin garin babu cinkoson jama’a don hakane yasa ya ji dadin tafiyar da ya yi daga Kano zuwa Kaduna domin aiwatar da wani bincike a wani asibiti da ke cikin Kaduna. A gajiye ya iso masaukinsa, don haka wanka ya fara gabatarwa sannan ya fice zuwa Masallaci. Har akayi Isha’i bai dawo ba, yana zaune yana lazimi. Tunani ne dankare a zuciyarsa na aurensa da Khadija ɗiyar Malam Adamu. Yarinyar ba wata me kyau ba ce, amma hankalinsa ya kwanta da natsuwarta. Har gwadata ya yi ta hanyar kama hannayenta a ganinsa da ita na farko, sai ta hau yi masa kuka ta dinga fushi da shi. Ya sha matukar wahala wajen lallashinta. Duk da wannan abun da tayi Allah bai sa masa kaunarta ko da na minti daya ba. Amma ya yarda ya amince zai aureta, dama damuwarsa tarbiyyan ‘ya’yansa. Ƙuncin da yake ji ne yasa shi ficewa da makullin mota a hannunsa yana sosa kunne.

Wajen shaƙatawan ya nufa ba tare da yasan me zai kai shi wurin ba. Duk yadda zuciyarsa take hana shi zuwa wurin hakan ya gagare shi. Yasan illar tunani don haka yake son raba kansa da shiga cikinsa. Wuri ya samu ɗan nesa da jama’a ya zauna yana latsa waya.

Giftawanta yasa ya dan juyo yaga ko waye. “Hasbunallahu wani imal wakil.” Haka ya dinga nanatawa. Ga dukkan alamu dai Meenal Aljana ce. Idan ba haka ba me ya kawo ta garin Kaduna bayan ya baro ta a Kano? Shigar da ke jikinta yafi komai sake firgita shi. Bakaken kaya ne a jikinta, tana sanye da safar hannu kamar wacce zata je fashi. Wani wuri ta shige hakan yasa ya biyo bayanta. Bandaki ta shiga, sai kuma ta fito a rude shima ya mara mata baya. Bata kai ga fita daga wurin ba ta ji muryarsa, “Me kike aikatawa? Ke mayya ce ko aljana? Meke damunki?” Ta juyo zata yi masa tsiwa kenan ta ji ana fadin anyi kisa ankashe wani mutum yanzu yanzu a cikin bandaki. Meenal ta zaro idanu. Kafin ta san abin yi ta sake jin ance “Wata mace ce ta shigo tana sanye da bakaken kaya da alama bata gama ficewa daga wurin nan ba, don haka a yi sauri a rufe Gate. Hantar cikin Meenal ya sake kad’awa. Kafin tasan abin yi Dr Bakori ya fizgo ta cikin zafin nama ya bi ta baya ya kaita cikin motarsa. Bai san meyasa ya rude da yawa ba. Rigar ya ce ta cire. Ta fi shi shiga rudu don haka ta cire bakar rigar, sai ga farar riga a ciki wanda ya bayyana kirjinta. Kura mata idanu yayi shi kadai yasan yanayin da ya shiga.

Cikin ikon Allah ya fizgo kansa da karfin tsiya ta hanyar addu’a. Yana kallon tsabar rudewa a kwayar idanunta. “Me ya yi maki kika kashe shi? Zaluncin naki har ya kai ki fara kashe maza?”

A hankali ta sauke jajayen idanunta akansa. “Na tsani namiji amma ba hakan ke nufin zan iya kashe ko da kiyashi ba. Da zan iya kisa ina tabbatar maka da na kashe Lukman da wa’innan hannayen nawa. Da zan iya kisa ina tabbatar maka da mahaifina ya zama mutum na farko da zan datse kansa da wa’innan hannayen nawa. Amma a yanzu zanje inmika kaina in ce masu ni ce nayi kisan domin bani da burin da ya wuce indaina rayuwa a doron kasa. Ina son insanar maka kaine namiji na uku da na tsana fiye da sauran. Da zan iya kisa kaine zaka zama Gawa na uku a cikin tarihin kashe-kashe na.

Juyawa tayi hawaye na gudu a kuncinta. Kokarin bude kofar motar take yi, yasa tattausar hannunsa da yake tsananin yiwa mutanen da ba muharramansa ba rowarsa, ya rike nata hannun. “Sai yanzu na fahimci ke mahaukaciya ce, baki san ciwon kanki ba. Ada ina tunanin akwai wani gagarumin laifi ne da akayi maki da har kika tsani maza. Ashe karamin laifi ke sanya ki tsanar namiji? Idan kika mika kanki ga hukuma zaki yi danasani, musamman yadda mahaifiyarki zata gaza shiga jama’a gudun a dinga nunata ana cewa ta kasa baki tarbiyya bayan mutuwar mahaifinki.”

Cak! Ta dawo ta kurawa hannayensu ido hawayen yana sauka a bisa hannunsa. Dr. Bakori ya gaya mata maganar da ya kashe mata dukkanin ilahirin jikinta. Kwantar da kanta tayi hawaye yana cigaba da kwaranya a bisa fuskarta. A karo na farko da ya ji tausayinta ya kama shi. Zare hannunsa ya yi, yasa dan yatsa ya dauke mata hawayen, “Ki yi wa kanki fad’a ki gina rayuwarki ta hanyar da mahaifiyarki zata yi alfahari da ke. Ki daina zuwa mashaya.”

Kwankwasa glas din motar da ake yi ne yasa ta kankame jikinta tana Salati. Wani dan sanda ne ya leko yana magana, “Ya kamata ku bar wurin nan anyi kisa, amma kuma ankama wacce tasa a yi kisan Allah yasa basu fita daga wurin ba. Ku yi maza ku bar wurin.” Dr. Bakori ya saki kakkarfar ajiyar zuciya ya ja motarsa suka fice. Sai da suka nausa titi kafin ya dan waiwayo, “Ina zan kai ki?” Duban hanyar tayi ta ce, “Ajiye ni anan.” Babu musu ya ajiyeta ta fice. Kafin ya bar wurin yaga ta tare wata mota, kafin kiftawan idanu ta shige motar. Dr Bakori ya kafe motar da idanu yana jin wani irin bacin rai, wanda ya rasa dalilin yin hakan. A hankali ya ce, “Yarinyar tana da kafiya da yawa. Allah ya shiryeta.”

Kwance yake, yana ta juyi a gado. Tunani ne birjik a kwakwalwarsa. Duk yadda yaso yarinyar ta kauce masa a zuciya abin ya faskara. Bai taba ganinta da waya ba, haka bata da kawa wacce tasan komai nata. Da alama bayan kafiya da yarinyar take da ita har da zurfin ciki. Kullum ya hadu da ita sai ta tsoma shi a cikin dogon tunani, daga karshe baya iya gane komai. Meyasa zata iya kashe mahaifinta? Me ya yi mata? Bayan ciwon zuciya da Meenal take dauke da shi babu ko tantama tana fama da lalurar kwakwalwa.

Ciwon kai yana sake samun wuri a cikin kwanyarsa don haka ya bude jajayen idanunsa da kyar, ya sauke santala-santalan kafafunsa kasa tare da rike kan da karfi yana karanto duk addu’ar da tazo bakinsa.

Meenal ce kwance a wani kango tana rusa kuka, tare da rungume jikinta da take jin cizon abubuwa kala-kala. Gaba daya rayuwarta babu dadi. Fiya-fiyan da ta siyo ta bude a cikin jakarta ta kurawa ido. Tana bukatar mutuwa, amma ba ta wannan hanyar ba.

Tun bayan da akayi maganar aurenta da Sulaiman ta shiga bibiyar rayuwarsa. A karon farko ta kama kwalaban giya a dakinsa. A karo na biyu ta ji shi yana waya yana fadin ba sonta yake yi ba, yana so ne ya koya mata hankali ya nuna mata da gaske mazan da ta tsana sun fi karfinta. Shigowar da tayi yasa ya ganta, ɓacin rai yasa shi ya hau ta da duka ko ta ina. Da kyar aka kwace ta. Da aka tambaye shi abinda tayi masa sai ya karkace ya ce, “Baba don nace ina son yarinyar nan, shi ne ta shigo dakina tana zagina tana gaya min gara injanye maganar auren nan. To na hakura da ita.” Abin tsoro da firgici kowa ya goyi bayansa ba tare da antsaya anji nata bayanin ba. Ta yaya zata kaunaci maza? Yau namiji ya yi sanadiyyar barinta gida ta dawo garin da bata san kowa ba. Tana son nesanta kanta da kowa nata ta hakanne za a daina jin haushinta. Kangon ta sake duba tana me jin tsananin tsoro. Dole ta mike jiri na dibanta saboda yunwa ta fito bakin titi kawai ba tare da tasan inda zata je ba.

Wani irin birki ya ja da karfi wanda yasa ta rintse idanu tana Salati. Yana fitowa ya fizgota ya dauke ta da lafiyayyun mari ya hankadeta, “You are very stupid! Gidan uban wa zaki je a cikin daren nan da har kike shiga tsakiyar titi ba tare da kin damu da rayuwarki ba?” Yadda yake magana ya yi matukar firgitata. A karo na farko da ta ji tsoron wani Dan adam a rayuwarta. Jikinta babu inda baya rawa. A lokaci guda ta fita hayyacinta. Hannunta ya fizgo ya cilla mota, yana jin kamar ya yi ta dukanta har sai ta dawo hayyacinta. Cikin hotel din ya kaita a dakinsa. Dukkansu sun yi shuru aka rasa me karfin halin fara magana. Da kansa ya ga dacewar ya kora shurun ta hanyar dubanta, “Kuruciyarki ta tashi a banza. Kin isheni, tun ranar da kika shiga rayuwata kika dagula min duk wani shiri na. Meyasa ba zaki kyaleni inyi rayuwata ba? Kamar yadda kika tsani maza haka nima na tsani wasu matan, daga ciki kuwa har da ke.”

Mikewa tayi tana jin Karin tsanar Dr. Bakori haka tana danasanin kwanciyarta asibitin su, da bata kwanta ba da bata san shi ba. Yana zaune yana kallonta. Har ta kusan kofa jiri ya kwasheta ta zube anan. Rike ta ya yi yana jijjigata. Ga shi dai idonta a bude suke amma babu bakin magana. Hawaye kawai ke zuba daga idanunta. Har yanzu radadin marin da ya yi mata ya gaza barin ta. Haka suke maza basu da tausayi, babban burin su su ganka a cikin matsala su kara maka wata.

Ya fahimci akwai yunwa a tare da ita. Don haka ya dauko mata ragowar kaza da madara. A gabanta ya tura mata. Bata da wani zabi da ya wuce ta ceci cikinta da ke barazanar tsinka mata ‘yan hanji. Shuru ya yi yana kallon yadda take cin kazan kamar tana cin magani. ‘Yan yatsunsa ne kwance a fuskarta. A take nadamar abinda ya yi mata ya shige shi. Tana gama ci ta kalle shi ba tare da tayi magana ba. Da hannu ya nuna mata hanyar bandaki, ya kwantar da kansa a bisa kujera.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Meenal 2Meenal 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×