Skip to content
Part 22 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Meenal ta saki ajiyar zuciya a falon ta dubi mijinta da kulawa, “Wai kuwa kayi magana da su Hajiyarka?”

Bai dubeta ba ya bata amsa, “Duk halin da nake ciki su Hajiya da Abba sun sani. Ina magana da su haka suna magana da ni. Abu ɗaya ya rage min shi ne inje in kai masu ke. Akwai abubuwan da nake son su kammala ne.

Shuru tayi bata sake cewa komai ba. Kore shurun ya yi yana mata magana cikin damuwa.

“Meenal ina ganinki bibbiyu a idanuna. Kina juya min wata Meenal ɗin ba Meenal ɗina ba. Me ke shirin faruwa ne? Duk lokacin da na fita babu ke, sai na ci karo da mai kama da ke. Meenal ko dai kece kike bin bayana? Faɗa min gaskiya.” Kwata-kwata kalamansa basu bata tsoro ba, haka bata ɗauki maganarsa da mahimmanci ba. Tallabo fuskarsa tayi tana murmushi,

“Meenal ɗinka ɗaya ce, daga ita babu wata Meenal da ta isa ta bayyana maka kanta a matsayin wata Meenal. Kada ka damu kaji? Ni Meenal ɗinka, ba zan taɓa wasa da hankalinka ba.”

Hannunsa yasa a ƙasan mararta yana shafawa. Ji ya yi cikinta yana motsi da ƙarfi. Cikin sauri ya kwantar da ita ya buɗe cikin. Yana nan yadda yake hakan yasa ya kai dubansa gareta.

“Meenal akwai wani abu. Kuma dole kin sani gaya min menene? Ko dai Aljanu sun shafeki ne?” Lumshe idanunta tayi, tana jin tsananin sha’awar mijinta yana shigarta. Tana son yau ya karɓi hakkinsa. Don haka ta fara wasu irin wasanni, wanda suka rikita shi, bai taɓa sanin Meenal ɗinsa da irin salon nan ba. Haka bai taɓa ganin ta cire kunya tana nuna masa irin wannan abun ba, sai yau.

Jikinta har rawa yake yi, wajen zame masa dukkan wani kaya da ya rage a jikinsa. Da kanta take son tayi kwanciyar aure da shi, ba wai shi ya yi a matsayinta na budurwa ba.

Nan da nan ya dawo hayyacinsa, ya ɗaga ta daga jikinsa yana dubanta. Baƙin ciki yasa tasa kuka, “Yayana ni na gaji gaskiya ka bani hakkina.”

Ahmad ya kasa magana sai dubanta kawai yake yi, yana son nazartar wani abu. Tsam ta miƙe ta bar ɗakin tana kuka. Sai da ya gama saƙe-saƙensa sannan ya miƙe da nufin ya je ya lallasheta.

Abin mamaki Meenal ya samu kwance tana sharar barci, a inda ya fita ya barta. Mamaki ya ishe shi. Shin wacece tayi masa oyoyo a lokacin da ya dawo? Ko dai Meenal aljana ce bai sani ba? Tashin ta ya yi, tana buɗe idanu ta ɗan turo bakin,

“Sannu da zuwa. Nayi ta jiranka ban ganka ba, har barci ya kwashe ni. Wai yaushe zaka kaini gidan Sarki ne?” Ɓoye mamakinsa ya yi ya zauna, “Sarki yana da lambobina, ba zan kai ki ba, har sai idan ya neme mu kamar yadda ya buƙata. Yanzu na gama da Mahaifina, ina son mu shirya muje su sa mana albarka.”

Shuru tayi bata son barin ƙauyen nan, tana jin daɗin zama a cikin sabon gidan su fiye da zamanta a cikin Abuja. Bata ce masa komai ba, ta miƙe kawai ta shige banɗaki.

Zama ya yi a bisa kujera yana tunanin meke shirin faruwa ne? Kai tsaye jikinsa ya bashi Hon Munnir bai daina binsa da sharri ba.

Tagumin ta cire masa, “Babu kyau yin tagumi miji na gari. Gaya min damuwarka. Tun ɗazu nake kula da yanayinka ya sauya meyasa?” Sosa kansa yayi ya ce babu komai.

A ƙasa suka fito suna ɗan takawa hannunsu a sargafe da na juna. Wannan ba baƙon al-amari bane agun mutanen ƙauyen, idan da sabo ya ci ace sun saba da ganin irin iskancin nan na riƙe hannu, a tsakanin Meenal da Ahmad.

Da idanu ya rakata, wanda ita Meenal bata kula ba, tana can ta ƙwace hannunta tayi wajen masu siyar da rake. Ahmad ya bi bayan wancan me kama da Meenal ɗin.

“Tsaya. Ki dakata nace!” Ya faɗa cikin tsawa, da ɗaga murya. Cak taja ta tsaya. “Meyasa kike bina? Menene alaƙata da ke? Waye yake dauƙar nauyinki? Ahmad bai yi kalan wanda zaki ɗinga bi kina wasa da hankalinsa ba.”
Juyowa tayi a ɗan tsorace. Ga mamakinsa sai yaga wata fuskar ce amma ba fuskar Meenal ba. Yana shirin yin magana ya ji kukan Meenal. Ƙyaleta ya yi ya wuce gun Meenal. “Me ya faru?” Hannu tasa tana goge fuskarta. “Ba kai bane ka tafi ka barni?”

“To yi hakuri taso mu tafi.”

Shi dai bai gayawa Meenal komai ba, tunda yaga ko a jikinta. Kai tsaye gurin bafullatani Lado suka nufa wanda tuni ya dawo da matarsa Larai cikin sabon gininsa.

Lado yana ganinsu ya sauya fuska, “Ni ina shonku amma ku rabu mana. Mutane Kaman shingam? Haka fa da ka kwanta kaman mushe, yarinyan nan ta ɗinga yin kuka.”

Meenal ta miƙe kaman zata yo kan Lado. Ahmad ya tare ta yana murmushi, “Idan baka daina kiran shi da mushe ba, sai na cire maka ido ɗaya.”

Lado ya ƙyalƙyace da dariya, “To idan ba maye ba, waye zai iya cire idanu? Ko da yake dama mayu ne.”

Ahmad ya miƙe yana ta murmushi ya ce, “To mu dai zamu tafi, ka gaida Larai.”

Suna miƙewa wayar Ahmad ta faɗi, ya kai hannu zai ɗauka Meenal ma ta kai hannu, dan haka ya haɗa hannun da wayar ya matse, har sai da tayi ƙara, “Wayyo Husby zai kashe Meenalinsa.”

Sakin hannun ya yi ya ci magani kamar ba shi ba. Meenal ta rarumi wani sanda ta yo kan Ahmad ya riƙe hannunta, tana faɗin ita sai ta rama. Lado ya muttsike idanu, “Wai har dukanka tana yi ne? Allah shi kyauta.”

Meenal ta yar da sandar, ta haye bayansa, ta lalubi kunnensa tayi masa magana cikin wani irin sanyi, wanda yasa ya ji wani abu ya tsirga masa tun daga saman kai har zuwa ƙasan tafin hannunsa. Gaba ɗaya ya rasa dukkan ƙarfin guiwar da yake tattare da shi. “Meenal kin kashe ni.” Ya furta a hankali. Ita kanta wani abu ne ya shiga tsakiyar kanta tayi luf a bayansa.

Juyowa suka yi suka sami Lado ya shige gidansa ya rufe ƙofa. Hannunta ya kamo suka wuce gida. Ya rigata shiga gida, dan haka ta saki jiki a tsakar gida ta hau ihu.

Alwala yake yi domin jiran a kira Sallah, bai san lokacin da ya fito ba yana dubanta,

‘Menene kuma sarkin ihu?”

Shuru tayi tana dubansa a zuciyarta tana jin haushin don me zai ce mata sarkin ihu? Sai da ta gama dubansa kamar zata yi magana kawai ta sake fasa ihu. Toshe kunnuwansa ya yi yana sake haɗa rai,

“Wai ina wasa da ke ne?”

Shuru tayi ta zuba masa idanu, kamar babu abinda ke damunta, har yayi tunanin ɗaukarta, sai kuma ya sake jin ta kwantsama ihu a dai-dai fuskarsa. Dole ya sassauta ,murya gudun kada ta fasa masa dodon kunne, “Sorry Meenalina. Nuna min abinda ya sameki.”

Taɓe baki tayi tana nuna masa ƙafarta da bai ga komai ba, “To ba cinnaka bane ya cije ni?”

Takaici yasa ya ɗan ja tsaki, ta ware idanunta tana dubansa. Da sauri ya gyara maganar sa. “Da na kama cinnakan nan babu abinda zai hana ni ban wulaƙanta shi ba. Sorry zo inɗauke ki muje kiyi alwala.”

Cak ya ɗauketa ta saƙalo hannayenta a wuyansa.

Meenal ta kammala shirya abin kari tana jiran Ahmad ya tashi daga barci shuru. Tana shiga ta rasa me zata yi masa, kawai ta zare fillon kansa ya koma kan gadon. Ya sake jawo bargo ya cigaba da barcinsa. Shuru tayi tana nazari. CD ta kunna ta ƙure ƙaran, hakan yasa ya toshe kunnuwansa. Duk abinda zata yi tayi masa amma bai tashi ba. Kawai ta ɗibo ruwan zafi ta ɗan watsa a ƙafarta, ta fasa uban ihu. A gigice ya tashi sai gashi a gabanta. Daina ihun tayi ta zuba masa idanu. Shi haka yake kullum ƙara kyau yake yi da sheƙi.
“Meenal na gaya maki bana son ihun nan? Ban faɗa maki bana son ihunki ba?”

Yadda ya ɗaure fuska yasa ta fara kuka. Miƙewa ya yi ya cigaba da tafiyarsa ko waiwayota bai yi ba. Itama kawai ta hau fushi. Har ya fito wanka tana nan zaune a inda take. Tana kallonsa da gefen ido yana karyawa ko dubanta bai yi ba. Yana gamawa ya sa kai ya fice. Ko motsawa bata yi daga gurin ba.

Sai kusan ƙarfe ɗayan rana ya shigo gidan. Ya tsorata da ganinta a inda ya barta. Lallai zai yi aiki da Meenal. Ƙarasowa kusa da ita ya yi ya sunkuya,

“Meenal. Kina fushi da mijinki? Kina son Allah ya ƙona ki? Kiyi hakuri Ahmad ɗinki bai kyauta ba, zan hukunta shi kin ji?”

Ga mamakinsa sai ta hau kuka. Gaba ɗaya ya jawota jikinsa, yasa bakinsa a kunnenta yana mata magana, cikin wani yanayi da ita kanta ba zata ce ta fahimci abinda yake cewa ba. Ahmad ya ƙware a sanin ciki da wajenta. Rungume shi tayi tana hawaye, “Ina sonka Husby. Ka yafe min idan na ɓata maka.”

“Matata bata taɓa ɓata min rai ba, ina sonta fiye da komai. Kada ki sake zubar min da hawayen nan naki.” Gyaɗa kai tayi da kansa ya bata abincin tana ci tana shige masa kamar wata mage.
Ƙarfe goman dare, agogon ya buga, suna zaune a falo suna kallo. Shafo sajensa tayi, “Husby maganin sauro ya ƙare kuma garin kamar da sauro.” Manna mata kiss ya yi a goshinta. Sun ɗauki ‘yan mintuna suna miƙawa juna saƙo, kafin ya zare kansa, a natse kamar bashi bane ya gama fitar da numfashi,

“Zauna ki jirani insiyo indawo.” Yau babu musu ta gyaɗa masa kai.
Da jallabiyarsa fara sol ya fita, sai gashi ya dawo hannunsa ɗauke da maganin sauron. Ganinta ya yi daga ita sai gajeren wando kayan sun yi mata kyau sosai. Kwalliyar ta karɓeta. Sai ƙamshi take zubawa irin ƙamshin ‘yar mutan Borno, wanda kai tsaye hakan ke nuna masa da tabbas ta haɗu da mutanen Borno ne suka ɗibar mata ƙamshin nan.

Sai dai yana ƙarasowa idanunsa suka gane gizo kawai Meenal take yi masa, yana ganin duk ranar da tayi irin shigar ba ƙaramin kyau zai yi mata ba. Dubawa ya yi ko ina bai ganta ba. Gabansa ya ɗinga faɗiwa.

Ƙwala mata kira yake yi amma shuru. Ƙofar wani ɗaki ya kaiwa kallo. Jini ke kwararowa yake fitowa daga ɗakin, ga kuma ɗakin a kulle da makulli. Cikin gigicewa yake faɗin

“Jinin Meenal?”

Ohh ni ‘yar mutan Borno. Ko sai yaushe Ahnal za su sami natsuwa? Kullum cikin damuwa suke.
Muje zuwa dai.

<< Meenal 21Meenal 23 >>

1 thought on “Meenal 22”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.