Ba zai iya nemon makulli ba, don haka yasa ƙarfinsa bugu biyu ana ukun ƙofar tayi baya. A cikin jini ya sameta a kwance. Ya ƙarosa hankalinsa a tashe.
“Meenal! Menene waye ya yi maki haka? Ki gaya min! Idan mahaifinki ne ya sake biyo ni wannan karon da hannuna zan ɗauki mataki. Dole ko inkashe shi ko kuma shi ya kashe ni.” Har ya miƙe cikin ɓacin rai sai kuma ya yi tunanin idan ya bar Meenal a haka ai sai ta mutu.
Ga dukkan alamu sai da suka yi kokawa kafin aka ci nasarar yi mata manyan yanka fiye da uku. Ɗauketa ya yi ya shige da ita inda zai kwaso kayan aikinsa. Tsoron barinta ita kaɗai yake yi. Cikin ikon Allah ya yi mata dressing duk tana sume sai da ya gama sannan ya dawo gurin dai-daita numfashinta. A tsananin firgice ta buɗe idanu zata yi ihu taga fuskar nan babu rahama, don haka ta riƙe shi jikinta yana rawa.
“Yayana akwai mutum a gidan nan. Kuma mace. Ka ga inda muka yi kokawa ta yanke ni? Yaya ba mu biyu bane a cikin nan gidan ka ɗauke ni mu bar gidan.
Ta riga ta gigice. Shafa goshinta yake yi da yake ɗaukar zafi, “Shikenan Meenal bari ki sami sauƙi sai inɗauke ki inkai ki gidanmu. Hakan ya yi maki?” Da kai ta amsa masa. Ta riga ta tsorata ba zata sake yarda ta zauna ita ɗaya ba.
Yana son zuwa banɗaki ya yi alwala baya son tafiya ya barta. Yana gwada miƙewa ta kama kuka ita duk inda zai je ya tafi da ita. Dole ya ajiyeta a ɗaki kuma ya bar ƙofar a buɗe.
Ƙarfe biyun dare Meenal tana kwance tana shirga barci, shi kuma yana sake duba ciwonta. Yaga kamar wucewar wani abu don haka ya miƙe ya bi bayan abin. Sai da ya yi nisa ya tuna meyasa ya bar Meenal? Cikin sauri ya dawo ɗakin yana shiga ya sake ganin anfice. Girgiza kansa kawai ya yi ya shiga ya ɗauro alwala ya fito ya fara nafilfili don nemawa kansa mafita. Masifar tayi yawa. Ya ci alwashin yana komawa gida zai nemi Hon Munnir a duk inda yake.
Suratul Yusuf yake karantawa cikin Qira’arsa mai daɗi. Meenal ya gani tana ta juye-juye tare da riƙe kai da ƙarfi. Bai daina karatun ba har zuwa lokacin da ta haɗa zufa. Ta kuma koma barcin.
A hankali ya ƙaraso gurinta ya goge mata gumin ya riƙe goshinta, “Allah ya yi maki albarka Meenal. Insha Allah zaki cinye jarabawarki. ki ɗauketa me sauƙi, ki ɗauka cewa ta wasu tafi taki wahala.” Yana son zuwa kitchen yana tsoro. Ayatul Kursiyyu ya tofa mata ƙafa bakwai. Ya shafi kanta, “Na barki da kariyar Mala’iku fiye da dubu. Za su yi gadinki har indawo insameki cikin ƙoshin lafiya.”
Yana ficewa ya shiga kitchen ya ɗan samar mata da abinda zata ci. Har ya dawo bata tashi ba. Rungume ta ya yi a kunnenta yake magana cikin sanyi, “Meenal tashi kin ji? Tashi mu je ayi wankan kiyi brush sai ki ci abinci.
Buɗe ido tayi tare da miƙa sannan ta sakko ya kama ta suka shiga banɗakin. Duk abinda ya lissafo shi ya yi mata su, sannan ya sa mata doguwar riga ya kamo ta suka dawo falo. Tashin hankali babu abincin da ya dafa mata babu dalilinsa. Ancinye abincin tas. Riƙe kansa kawai ya yi ba tare da ya iya ko da ƙwaƙƙwarar motsi ba. Dafa bayansa tayi, “Menene Yaya?” Murmushi ya yi mata, “Babu komai. Ina zuwa.” Har ya sa ƙafa zai fita nema masu wani abun, sai kuma ya ji kamar wucewar mutum. Dawowa ya yi da baya. Tana kallonsa ya tofa mata addu’a sannan ya sake shiga kitchen.
Yana sane sarai so ake a tsorata shi, shi kuma bai kasance daga tsatson tsoro ba. Kowa ya san Katsinawa mutane ne marasa tsoro. Cikin gaggawa ya dafa mata indomie da ruwan tea. A gabanta ya dire. Ta ɗan dubi fuskarsa, “Na gode Yayana.” Girgiza kai ya yi, “Idan kika sake yi min godiya zamu ɓata. Kina son mu ɓata ko?”
Girgiza kai tayi tare da yin tagumi tana dubansa yadda yake ƙoƙarin dole sai Indomie ɗin ya rage zafi. Ɗagowa ya yi da nufin kai mata baki yaga kawai ta kafe shi da ido,
“Yes any problem?” Ɗaga gira tayi alamun eh. Ya ajiye cokalin ya zuba mata ido, “Gaya min.” Girgiza kai tayi tare da yi masa alamun tana sonsa. Da kai ya amsa mata ya cigaba da bata indomie.
Duk inda yayi idonta yana kansa. Wani irin sonsa ne yake sake huda dukkan jikinta.”
Kwana biyu baya iya fita ya barta. Daman jiyan wajen Nuhu ya je suka ɗan tattauna. “Yaya kaje ka siyo min fura.” Harara ya sakar mata, “Ai ko me siyar da furar ce ba zan je ko nan da can ba. Tunda kika ga na koma ina bin masallacin unguwar nan a gida ke kinsan ba zan iya fita in barki ba.
Dr. Bakori ya kasa tsaye ya kasa zaune. Tunani yake yi waye a cikin gidansa? Babu shakka Hon Munnir ya koma bin ta ƙarƙashin ƙasa, ya fara yi masu turen Aljanu. Riƙe kansa ya yi yana tunanin wannan wani irin uba ne? Meenal bata yi sa’ar uba ba.
Banɗaki ta shiga ta kuma hana shi tsayuwa akanta yana nan tsaye yana kaiwa da komowa yaji sallama. Cike da mamaki ya nufi ƙofar. Yana kallonta ta juya tana tafiya. A zatonta zai biyo bayanta ne kamar yadda ya saba. Sai kawai ya juya gurin Meenal. Har yanzu bata fito ba.
Buɗe banɗakin ya yi ya zuba mata idanu kawai. Meenal ce kwance cikin kwamin wanka ruwa ya riga ya cika tam. Bai san lokacin da ya cirota daga cikin ruwan ba. Shimfiɗar da ita ya yi a ƙasa ya ɗinga danna ƙirjinta. Ya haɗa bakinsa da nata yana zuqo ruwan.
A ƙalla ya kwashi mintuna talatin akanta. Har ya fara tunanin kai ta asibiti, ya ji tana wani irin tari ruwan yana fita. Ɗaukarta yayi ya rungume a ƙirjinsa yana godewa Allah.
“Kiyi haƙuri Meenal a cikin satin nan insha Allahu zamu koma gida. Ya zama dole inkawo ƙarshen wannan al’amari.” Yana maganar yana shafar bayanta. Ita dai gaba ɗaya jikinta babu ƙwari tayi kwanciyarta tana tuna abinda ya faru. A rikice ta sake maƙale masa ta bubbugi bayansa yana ɗagowa ta shiga nuna masa ƙofar bayi. A take ta sume.
Rintse idonsa ya yi yana jin ƙirjinsa yana zafi. Tana farfaɗowa ta sake rushewa da kuka tana magana a hankali, “Aljani na gani Yaya yana son ya kashe ni.”
“Aljani ba zai iya cutar da ke ba Meenal idan har kina addu’a. Meenal kinyi sanyi da yin nafilfili. Yanzu ɗaukar Qur’anin ma yana baki wahala. Ki daure ki ɗinga yi kin ji”
Cikin shagwaɓa ta ce, “Idan zan ɗauka sai in ji kasala.” Bai ce mata komai ba. Ya riga da ya nausa a cikin tunani.
*****
Tana zaune yana gyara mata ƙumbuna tana yi masa mita, “Wayyo ni dai gaskiya ka bini a hankali ka ga zaka ji min ciwo.” Ko kallonta bai yi ba hakan yasa ta kamo hannunsa tana girgiza masa kai, “Da zafi fa.” Oh abinda ya kamata ace ya gama a cikin mintuna goma ma, sai gashi rigimar Meenal yana son ya kaisu awa ɗaya a zaune.
“Meenal idan baki tsaya ba zan sa ki kuka.” Dariya tayi ba tare da ta kalle shi ba, “Nikam Allah na tuba a yanzu dai me zai sa ni kuka? Gaskiya babu.”
Murmushi kawai ya yi. A lokacin ne kuma suka ji Sallama. Har ta miƙe zata je duba su waye? Shima miƙewan ya yi ya ja hancinta, “Da shegen rawan kanki, da kika tashi ina zaki je?” Bata bashi amsa ba sakamakon zura idanunta a cikin lumsassun idanun nan nasa masu ɗaukar hankali.
Ƙofar ya buɗe abin mamaki Nuhu ne da Maman Anwar sai dai kuma babu Anwar a tare da su. Ahmad ya ji daɗin ziyarar bazatan nan da Nuhu ya yi masa. Suka ba juna hannu ita kuwa Meenal sai idanu ta zurawa Maman Anwar sam bata ji daɗin wannan ziyara ba. Ahmad ya kula da ita dan haka ya take mata ƙafa, alamun ya ankarar da ita. Amma sai yarinyar nan ta kwantsama masa ihu ta ce, “Yaya kana danne min ƙafafuna.” Kunya ya ɗan kama shi ya ce, “Sorry ban kula bane Bismillar ku.”
Gaba ɗaya suka shiga falon aka hau taɓa hira.
“Meenal tashi kije ki ɗora girki.” Tana jinsa sarai tayi kamar bata ji ba. Ahmad ya waiwaya ya ɗauki filo zai buga mata, abin mamaki yaga ta tashi ta zura da gudu tana ƙyalƙyaltar dariya. Nuhu da Maman Anwar suma dariyar suka yi. Maman Anwar ta miƙe tana cewa muje intayaki.
“Meenal ya kwana da yawa?” Kamar kada ta amsa sai kuma ta amsa da “lafiya.” Ga mamakinta sai taga Maman Anwar tana haɗa girki wani iri. Bata ce mata komai ba itama ta ɗora wani girkin.
“Meenal ki bari mana tunda nayi wannan gaba ɗaya.” Girgiza kai tayi ta ce, “Husby ba zai ci ba, idan ba ni nayi ba. Kema nasan mijinki hakane.”
Maman Anwar ta cigaba da aikinta tana yaƙe.
“Meenal halayyar wasu mazan yana damuna. Kowacce mace tana da matsala a gidan mijinta.”
Haushi da takaici yasa ta ɗago tana dubanta, “Ban da ni a ciki.” Maman Anwar ta karkace zata dasa daga inda ta tsaya. Meenal ta fice a kirchen ɗin ta barta a tsaye.
Abinci yana nuna kowacce ta zubawa mijinta. Nuhu yana kai baki ya ajiye plate ɗin ba tare da ya ce komai ba ya jawo kulan Ahmad ya ɗibi nasa ya cigaba da ci. Ita dai Meenal sai duban su take yi.
Har aka kira Isha’i Ahmad ya ƙi fita Nuhu ya cika da mamaki. Yaso ƙwarai su zagaya unguwar anan ma Ahmad ya ƙi fita. Suna hirar su suna kallon Film. Duban Meenal ya yi ya ce, “Ka ga Sarkin barcin nan tayi barci bare inkaita ɗaki.” Cak ya ɗauketa ya kai ɗaki. Nuhu yana kula da Maman Anwar da ke zube kamar kayan wanki tana barcin ƙarya. Magana ya yi mata cike da takaici, “Gara ma ki tashi dan Walh ba zan ɗauke ki ba.”
Tashi tayi tana ‘yan surutai. Shi kuwa yana Kaita ɗaki ya shimfiɗeta ba tare da tunanin komai ba ya fice abinsa. Da kansa ya nunawa su Nuhu inda za su kwana wanda dama anyi wurin ne saboda baqi.
Ya rasa dalilin da yake jin faɗiwar gaba. Ga shi Nuhu ya ƙi zuwa ya kwanta. Cikin damuwa ya miƙe, “Nuhu hankalina yana kan Meenal tana da yawan tsoro bari inje indubata.” Bai tsaya sauraren amsarsa ba ya shiga ɗakin gabansa yana wani irin faɗiwa.
Tana ɗauke da dogayen yatsu gashin kanta har ƙasa yake ja. Hannunta riƙe da wuƙa me sheƙi. Gaba ɗaya bata da kyan gani.
“Me zaka iya yi? Me zaka iya yi? An aikoni zuwa gurin Meenal ka hanani cika aikina. Shekaruna ɗari biyu a duniya ban taɓa kasa aiwatar da abinda aka aike ni ba sai akan Meenal. Duba ka gani yanzu zan ɗauke ta zuwa Dajin hagu. Barinta a raye zai iya ɓata abubuwa da yawa. Duba ka ganiiii…” Duban Meenal ɗin ya yi tana fitar da wani hayaƙi. Bakinsa ɗauke da addu’a ya tunkaro ta yana jin zuciyarsa ta bushe. Wani abu ta fesa mata daga ita har Meenal ɗin suka ɓace.
Ahmad ya zubawa turirin hayaƙinta idanu yana jin wani damuwa yana shigarsa. Yana jin yaushe zai iya rintse idanunsa bayan ansace Meenal ɗinsa? Fitowa falo ya yi yana bin bango yana kiran Meenal. Nuhu ya fito yana dubansa “Wacce Meenal ɗin da ka kai ɗaki?”
Ahmad yana son yin magana wani irin duhu ya gilma masa. Wannan tashin hankalin yayi masa yawa. Gara ya ga gawarta a gabansa zai fi samun natsuwa, da Meenal tayi rayuwa a cikin dajin da babu uwa babu uba. Tausayin Meenal ya yi masa yawan da ya kasa dakatar da shi daga faɗiwa zuwa sumewa. Suma mai kama da ɗaukewar numfashi gaba ɗaya.
Duk yadda Nuhu yaso isa wurinsa kafin zubewarsa ƙasa hakan bai yuwu ba dan kafin ya iso Ahmad ya yi mummunar faɗuwa.
_Ba zan gaji da sadaukar maki da komai nawa ba, Aisha Ibrahim Garba Ɗan Borno. Ki ɗin ta dabance a cikin zuciyata. Ina sonki fiye da yadda nake son kaina
21
Yana buɗe idanunsa ya ji wani irin ciwon kai yana ratsa shi. Ta ina zai fara taimakon Meenal? Nuhu ya jero masa sannu yafi a ƙirga. Ahmad ya dubi Nuhu ya ce, “Nuhu kazo ka koma gun aikinka kada ka damu zan iya kula da kaina.”
“Ina Meenal? Wai meke faruwa da ku ne?”
“Zaka sani anan gaba.” Shuru Nuhu ya yi yasan ba zai gaya masa ba. Bai yi ninyar tafiya ba amma Ahmad ya dage. Dole suka yi sallama suka wuce.
Lado ya gama gayawa Ahmad hatsarin da ke cikin dajin da ya ambata masa an kai Meenal. A hankali ya ce, “Muje ka saita ni akan hanyar zan je.” Lado ya gyaɗa kai, “shoyayya manya. Babu shegiyan da za akai dajin nan inbita koda kuwa uwatace Mandiya. Idan ka shirya kazo innuna maka.”
Har Lado ya juya yaji hannun Ahmad ya damƙo shi. Ya firgita iya firgita. Bai taɓa jin mutum me ƙarfi irin Ahmad ba. Yanzu ya yarda zai iya. Sai da ya haɗiye yamu da ƙyar sannan ya ce, “Ni me kuma nayi?”
“Muje yanzu ka nuna min.” Babu musu suka kama hanya suna tafe Lado yana tsine masa a zuciyarsa.
Sun yi tafiya me nisa kafin Lado ya ja ya tsaya. “Wannan hanyar zaka miƙa zai kaika har wurin. Allah ya baka sa’a.Sai a yafewa juna.” Har Ahmad ya kusa shiga hanyar Lado ya ce, “Tsaya. Waye zai ci gadon gidanka idan baka dawo ba?” Ahmad kawai ya ci gaba da tafiya ba tare da ya sake waiwayowa ba.
Tafiya yake yi yana zaton haɗuwa da wata halitta amma shuru kake ji. Ga ciwon kan yaƙi barinsa, ga yunwa ga ƙishi. Gaba ɗaya ya rasa meke masa daɗi. Da agogonsa yake gane lokacin Sallah ya yi, rashin ruwa yasa a dukkan salolin da yake yi taimama ce. Ko alama babu nadama a tare da shi. A bayyane ya ce, “Idan na fito kai zan fara kashewa Hon Munnir. Da hannuna zan kasheka. Babu nadamar aiwatar da hakan a tare da ni.” Duk tafiyar da Ahmad yake yi addu’a bata bar bakinsa ba. Damuwarsa kawai yaga Meenal.
Yamma ta yi sosai, baya jin komai sai ƙaran dabbobin daji. Dole ya nemi wata bishiya ya zauna shuru. Shi kansa yasan yana shan wahala. Har ya fara gyangyaɗi ya tuna bai ga Meenal ba. Hakan yasa ya miƙe ya ci gaba da tafiya a cikin dajin nan.
Idan ya gaji ya nemi wuri ya zauna ya huta. Ba shi ya nemi makwanci ba sai da sha biyun dare ta yi. Ahmad ya riga ya sadaukar da ransa a cikin dajin nan. Yana jin zai iya mutuwa idan bai nemo Meenal ba. Haka ya yi alkawarin sai dai ya mutu a cikin wurin da ya fito babu Meenal.
Da asuba ya tashi ya gabatar da Sallah. Ga mamakinsa babu wani namun dajin da ya kawo masa farmaki. Yunwa tana neman ta illata shi. Don haka ya yi ta duba ko zai ga ‘ya’yan bishiya ya ci, amma bai ga komai ba, sai mangoro. Shima ɗanye ne. Haka ya tsinka ya yi ta cinsa hakannan, har ya samu idanunsa suka buɗe.
Da yamma likis ya ga wani bukka, har zai shiga ya fasa. Ya yi nisa da bukkan jikinsa bai bashi ba. Jiki asanyaye ya dawo ya ƙurawa bukkan idanu. Girgiza kai ya yi da nufin wucewa. Sai kuma yaji kamar ana mutsu-mutsu. Hankali a tashe ya dawo ya dai san Bismillah kawai ya yi sannan ya cusa kansa.
“Meenal!” A ruɗe ya tunkarota. Anɗaureta da baki da hannu a jikin wani bishiya me cike da tashin hankali. Ko motsi bata son yi saboda azaba. Shi bai gane me take nufi ba da take girgiza masa kai.
Hannu ya kai da nufin kwanceta wani irin azaba yasa ya cire hannun yana rintse idanu. Ahmad yana jin ko zafin nan zai zama dalilin cirewar numfashinsa ne sai ya kwance Meenal. Yana sake kai hannu bai ankare bs wani maciji da bai san daga ina ya fito ba ya fasa kansa. Ahmad ya zaro ƙaramar wuƙarsa ya caka masa. Sai dai ko gezo bai yi ba. Murmushi ya saki me ciwo. Sai yanzu ya fahimci abinda ya kamata tuntuni ya yi. Addu’o’i ya yi ya tofawa macijin nan. Wani irin zabura ya yi kafin kuma ya neme shi sama ko ƙosa ya rasa.
Ahmad ya yi Hamdala. Har abada ba zai daina godewa Allah da ya yo shi a musulmi ba. Gaba ɗaya musulunci daɗi ne da kwanciyar hankali idan har ka biyo hanyar da zaka sami daɗin.”
Duban bukkan yake sake yi a waje ɗan karami ne amma a ciki girmansa ya gawurta. Sosai ya matsota yana addu’a yana tofa mata. Ya jima yana janyo doguwar addu’a sannan yaga duk wani ɗauri da aka yi mata ya kwance kansa. Kai tunda Ahmad yake bai taɓa ganin masifa irin wannan ba. Da wani ya bashi labari ba zai taɓa yarda ba.
Hannu ya miƙa mata ta kama ta faɗa jikinsa tana hawaye. Kamo ta ya yi ya ɗauketa ya fice daga bukkan ya juya hanyar da ya fito. Sun yi tafiya me nisa kafin suka nemi wuri suka zauna. Duk ta galabaita. “Ruwa, ruwa.” Kafeta ya yi da idanunsa. Idan ya ce zai je nemo mata ruwa ya tafi ya barta ƙila su sake ɗaukarta. Yanzu ina mafita? “Ki yi haƙuri Meenal muje mu duba gaba ƙila mu sami ruwa.” Haka ya ɗauketa suka cigaba da tafiya. Tana jin ƙishi amma ta kasa sake yi masa magana. Zata jure.
Cikin ikon Allah yaga wani ɗan ƙaramin kududdufi ya sauketa yaje ya tara hannunsa yana ɗibo ruwan yana tara mata hannunsa a baki. Sai da ya yi hakan sau kusan goma sannan ta gamsu da abin da tasha. Reshen bishiya ya karyo me yalwan ganye ya shimfiɗa a ƙasa ya kwantar da ita.
Ahmad ko rintsawa bai yi ba har asubahi ta yi, suka ci gaba da tafiya. Gaba ɗayan su sun galabaita. Cikin hukuncin Allah suka iso titi da rana tsaka. Ahmad ya yi shatar mota suka koma gidan su da ke rigan Fulani. Gida ya shiga ya kawo masa kuɗinsa, sannan gaba ɗaya suka nufi frij. Sai da suka kusan cinye kayan marmarin da ke cikin frij ɗin sannan kowanne ya zube a kujera. Ahmad ya riƙe kansa shuru yana tunani. Akan Meenal ya baro gatansa ya baro aikinsa ya zo dajin Allah yana rayuwa.Lokaci ya zo da zai koma garinsa.
Tashi ya yi kawai ya wuce ɗaki ba tare da ya tsaya yin wanka ba, ya shiga haɗa kayansu.
“Mahaifiyarka fa ba ta son Meenal baka tunanin wata rayuwar wahalar da zata sake shiga?”
Riƙe kansa ya yi da ƙarfi yana karanto Innalillahi. Ina mafita??
Ina matukar jin dadiin littafan ki Kuma ina karuwa sosai.