Skip to content
Part 24 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Jikinsa ya yi matuƙar sanyi hakan yasa ya faɗa banɗaki ya yi wanka. Yana fitowa ya wuce ɗakin Meenal anan ya sameta itama tayi wankan tayi shuru a gaban madubi.

“Ki shirya yau zamu wuce gida.” Juyowa tayi gaba ɗaya suna fuskantar juna. “Ina jin tsoron komawa Kano. Ina jin kamar wani abu zai faru. Don Allah mu zauna anan.”

Girgiza kansa ya yi, “Zaman mu ne anan wani abu zai iya faruwa. Don Allah ki ji tausayina nima ina son komawa cikin dangina. Mahaifiyata har kuka tana yi min a waya. Ina zargin ma duk nasarar da ake samu akanmu saboda rashin biyayya ne da bana yi masu.”

Ya riga ya kashe bakin Meenal ba zata iya sake yi masa musu ba. Kayayyakinta take haɗawa cikin kasala. Sun gama shiryawa tsaf suka ji hayaniya a ƙofar gida, hakan yasa suka fito ɗauke da jakunkunansu. Lado suka gani da jama’a yaje ya sanar masu Ahmad ya mutu, wani kuma ya ce ya ga gidansa a buɗe shiyasa suka kamo hanya.

Takaicin Lado ya kama shi. “Wai kai raina a hannunka yake ne?” Lado ya sosa kai, “Nayi zaton namun daji sun shinyeka ne.” Bai sake magana ba ya buɗe mota ya zube komai. Ya yi masu sallama zai je ganin gida ya shiga gaba Meenal ma ta shiga tuni suka fice.

Barcinta take sha a mota, lokaci zuwa lokaci yana tofa mata addu’a. Har suka iso Kano a gajiye. A lokacin Meenal ta buɗe idanunta. A hankali ta buɗe idanunta a lokacin da kunnuwanta suka ji Ahmad yana furta, “Meenal gamu a gidan iyayena.”

Gabanta yana faɗiwa suka fito daga motar. A falo aka San da dawowar Ahmad. Tuni gida ya rikice da murna da ihu. Hajiyarsa ta ƙare masa kallo cike da mamaki. “Yanzu Ahmad kaine ka koma haka? Ko dai ciwo kayi ne? Tabbas angaya min tunda ka auri mayyar can sai hakan ya faru da kai.”

Hantan cikin Meenal ne ya kaɗa ta sunkuyar da kanta. Dai-dai da fitowar Alhaji Sudais. Cikin farin ciki ya rungume ɗansa na wasu ‘yan mintuna.

Ganin Alhajin yasa suka kasa cigaba da aikawa Meenal mugun kallo. Da ita da kishiyarta Hajiya Zulai. Alhaji Sudais ya kamo Meenal yana sa mata albarka. Gaba ɗaya ta gama karaya.

Haka ko da aka kawo abinci caccaka kawai ta ɗinga yi. Ahmad yana kula da ita don haka ya dubeta cike da tausayi, “Meenali ba zaki ci abincin ba?” Sunkuyar da kanta tayi, tana son yin kuka bata son tayarwa Ahmad hankali. Yadda taga yana cikin farin cikin haɗuwa da danginsa.

Ji take ina ma ita ce take cikin farin ciki haka? Damuwarta kawai a yanzu taje taga Ummanta. Abba ya dubeta da murmushi, “Meenal ki ci abinci ki saki jikinki wannan gidan gidanku ne Ahmad ɗin ne ma baƙo.”

Sake kai kanta ƙasa tayi tana murmushi. Hajiya ta zabga mata harara a fakaice. Babu wanda bai ganta ba, amma sai kowa ya share.

Ana gama cin abincin Ahmad ya ce zai je ya watsa ruwa. Alhaji ma ya fice abinsa. Ita kaɗai aka bari a falo kamar mayya. Dawowa falon ya yi ya sunkuya abisa guiwowinta. “Meenalina tashi mu tafi ki watsa ruwan.”

Miƙewa tayi ya kama hannunta suka shige ɗakinsa. Key ya murza a ƙofar ɗaki dan jikinsa bai bashi ba. Tana fitowa daga wankan yasa tawul ya kanannaɗeta. Suna nan a tsaye yana mata magana, “Baby mahaifinki ya kaini ƙarshe dole gobe inje gunsa. Idan ya sake taɓa ki zan ɗauki mataki mummuna.”

“Ba mahaifina ne ya tura a kaini daji ba. Hasalima bai san inda muke ba. Kamar yadda na gaya maka akwai wani abu a ƙasa. Mu cigaba da addu’a komai zai zo ƙarshe. Ina shan wahala Yayana. Na gode da…”

Ɗan yatsa yasa mata abaki alamun tayi shuru baya son godiyar. Dole ta haɗiye abinda take son ƙarasa faɗi. Ƙafafunta rawa suke yi ta kwanto masa kaɗan. Da gaske itama tayi kewansa. A gadon ya shimfiɗar da ita, sai dai yadda yake ƙoƙarin karɓar hakkinsa yasa jikinta kama rawa. “Yaya ɗagani banyi Sallah…” Ya hanata ƙarasa abinda ta yi ninyar faɗa, sakamakon wani yanayi da ya sake tsomata.

“Babu abinda zanyi maki ki natsu ki kwantar da hankalinki ok?”

Ita bata amsa ba, ita bata nuna masa ta ji ba. Ƙamshin bakinsa kaɗai yakan gamsar da ita. Namiji ne me tsafta, ko ina a jikinsa sai dai kaji ƙamshi ba irin wasu mazan ba, da zarar suka buɗe baki sai ka ruga da gudu. Haka itama bakinta kullum a tsaftace yake, tana daraja gyaran baki fiye da komai. Shiyasa suke samun natsuwa a tare da juna, basu taɓa jin sun gundura da mannewa juna ba.

Bugun ƙofar da akeyi yasa ta firgita tana ƙoƙarin miƙewa. “Ki natsu ƙofa a rufe yake. Ko ba a rufe yake ba, ke matata ce ba aikin haram muke ba. Bari induba waye.”

Riƙe rigarsa tayi tana son yin kuka, “Ka tsaya insa kaya tukunna.” Babu musu ya tsaya. A wayo ya ɗan riƙe cikinsa da yake jin yana masa ciwo. Abinda Meenal ta manta akan gado vest ɗinta da ke kan gadon da suka gama yamutsawa. Yana buɗe ƙofar Hajiyarsa tana shigowa.

“Wani iskanci ne da rufe ƙofa? Ahmad yaushe ka canza daga mai kunya ko koma sahun wasu?”

Zata cigaba da magana idanunta suka sauka akan vest ɗin. Ta saki Salati da ƙarfi, “Ke amma dai wannan yarinya jarababbiya ce. Me zan gani haka? Hajiya Zulai zo ki ga abin mamaki.” Hajiya Zulai kamar jira take ta kutso kanta. Itama Salatin ta saka.

“Ahmad ka saki yarinyar nan yanzu. Hankalina bai kwanta da tarayyarku ba. Ka saketa nace ko inbaka mamaki yanzu.” Meenal ta durƙushe a ƙasa tana kuka, “Hajiya kiyi haƙuri kada ki raba ni da Yaya shi ne kaɗai gatana a yanzu.”

Hajiya ta taɓe baki, “Nima shine gatana kika raba ni da shi mai zubin mayu. Ke na tsaneki. Ina kika taɓa ganin shegiya da ɗan halas sun zauna wuri guda? Kai Ahmad cewa nayi ka saki mara kunyar nan ina falo ina jiran takardarta.”

Fuuu suka fice zuwa falon. Ahmad ya kamo ta ya mayar da ita ƙirjinsa. “Ki daina kukan nan yana taɓa ni.”

“Ka taimake ni ka kaini gidan Ummana.”

“Idan na kaiki gidan Umma ni kuma inzauna da wa?”

Shuru tayi ta kasa bashi amsa. “Zan kai ki gidan Umma amma kwana biyu kawai zaki yi mu dawo mu cigaba da rayuwar mu. Na tabbata duk inda sarki yake hankalinsa yana kanmu.

Girgiza kai tayi da ƙarfi “Ni na tsani duk wata zuri’ata. Umma ta isheni rayuwar duniya. Ko sun zo gareni ba zan amsa gayyatar su ba. Da kai da Umma kune gatana a garin Kano.”

Yasan ɓacin rai ne kawai don haka ba zai matsa mata ba. Shimfiɗar da ita ya yi ya manna mata sumba a kumatu sannan ya fice.

A falo ya same su sun harɗe kamar ba su taɓa dariya ba. “Nace ka sake ta ko?”

“Ba zai saketa ba, wacce bata san ciwon kanta ba. Har abin alfaharinki ne ace ga ɗanki can ya fara sakin aure? Yarinyar da ya kamata ki ɗauketa da mahimmanci shine kike faɗin a sake ta? To kuwa duk ranar da Ahmad ya saki matarsa babu shakka tare zaku jera wajen ficewa daga gidan nan.”

Meenal ce ta fito ta durƙushe a gaban Hajiya tana kuka, amma hakan bai sa Hajiyar ta sakko ba. Sai dai furucin Alhaji ya yi matuƙar ɗaga mata hankali. Hakan yasa ta kasa furta komai sai ƙafafu da take jijjigawa.

Ahmad ya dubi Meenal kamar ya rungumeta ya lallasheta. Sai dai ko kusa da ita yaje Hajiya zata fara cewa ta riga ta gama da shi. Miƙewa ya yi ya fice daga gidan gaba ɗaya. Yana son zuwa ya dawowa Meenal da turarenta kusan kullum sai tayi maganar turaren.

Ya jima a cikin ƙaton shagon da ya haɗa komai, yana neman turaren. Cikin ikon Allah ya samu, yana sa hannu zai ɗauka yaji hannunsa ya haɗu da wata. Zoben Meenal da ya gani ne yasa shi juyowa. “Meenal biyo ni kika yi?”

“Wacece kuma Meenal? Ni sunana ba Meena ba, sunana Amina.” A zuciyarsa ya ce “Ai duk ɗaya.” Haka yana ƙara al’ajabin faruwar hakan. Babu abinda ya bambanta su, haka jikinta yana fidda ƙamshi irin na Meenal.

“Ke mutum ce ko Aljan?”

“Mutum ce kamar kowa. Turaren nan nazo siya ka bani wannan ɗayan shi ya rage a kaf shagon nan.”

Ɗaure fuska ya yi sosai, “Wannan turaren na matata ce. Duk duniya ban ga wanda ya isa ya ɗauke shi ba.”

“Wacece matar taka? Meenal ‘yar gidan Munnir ɗan Abubakar jikan Munnir? Ƙawata ce kuma jinina ce, tare muka gama Makaranta da ita. Amma kuma zan baka mamaki akan turaren nan.”

A lokaci daya ta ambato maganganu mabambanta, ba tare da ta fitar da dalilan kowanne daga cikin su ba.

“Kin daɗe kina son bani mamaki baki sami nasara ba, haka idan har kika ce zaki biyo sahu ki sace turaren nan, sai nayi maki abinda tunda kike baki taɓa tunani ba. Daga ƙarshe ki daina bin diddigina.”

“Da zaka bani turaren nan ni kuma da na taimakeka akan abinda ke shirin faruwa nan da…”

Gani tayi ya yi gaba abinsa ba tare da ya waiwayota ba. Murmushi tayi guy ɗin yana burgeta ko don rashin tsoron da yake da shi. A tsaye yake. Da wahala ka ga razanar shi akan abu. Tunda ya riƙi Allah yake jin kansa babu wanda ya isa ya yi masa abinda Allah bai rubuta a cikin shafin rayuwarsa ba.

Ya gama biya ya fito zuciyarsa cike da saƙe-saƙe. A gaban motarsa ya ganta bayan ya barta a ciki.

“Matsa min a jikin mota.”

“Wai ni Amina Shehu. Meyasa kake tsanata?”

Muryarta sak na Meenal. Duk yadda ya ƙware wajen iya ganon Meenal jabu da Meenal tasa, wannan karon ya kasa tantancewa. Tsawa ya daka mata wanda yasa ta matsa bata sani ba.

Zai shiga motar ta riƙe masa riga yana juyowa cikin zafin rai ya wanke ta da mari lafiyayyu. Sannan ya nuna ta da yatsa, “Idan ke aljana ce nafi ki hatsabibanci. Idan ke ce matata Meenal zan koya maki hankali dan bana ɗaukar iskanci daga na ƙasa da ni. Idan kika sake taɓa riga ta sai na baki mamaki. Ki je ki cire fuskar aro ki mayar da naki fuskar zai fiye maki alkhairi.”

Tana tsaye hannunta riƙe da kumatunta tana duban Ahmad har ya ɓace mata.

Yana isa gida abin mamaki da tashin hankali ya sami fuskar Meenal hannaye shimfiɗe kamar wacce aka mara. Ya dubi kumatun ya sake juya ɗayan ɓangaren, “Meenal waye ya mareki?”

Shafa fuskarta tayi ta ce, “Ni dai naji zafi kamar anmareni amma a zahiri babu wanda ya taɓa fuskata. Sannu da zuwa.”

Bai amsa ba ya jawo hannunta suka shige ciki.”

“Meenal gaya min a ƙawayenki wacece Amina Shehu da kuka yi Makaranta tare?”

Meenal tayi dariya, “Hala ka haɗu da ita? Ƙawata ce da gaske tare muka yi Makaranta.”

“Ok gobe idan zamu je gidan Umma sai mu tsaya ki ganta kamanninku ya ɓaci.” Yana maganar yana duban fuskarta. Yatsunsa ne kwance a fuskar Meenal, wannan ya nuna aljana ya mara kenan? Kai da wahala dole dai akwai wani abu mai matuƙar mahimmanci a ƙasa.

Meenal ta zaro idanu, “Ban taɓa jin wanda ya ce ina kama da Amina Shehu ba. Ita da take gajera ni kuma doguwa? Bari dai muje zaka ganta bamu da alamun kama.”

Shuru ya yi kawai yana nazarin maganganun Amina Shehu da kuma na Meenal a yanzu.

Dare yayi akayi zaman cin abinci. Hajiya ta dubi Ahmad fuskar nan a ɗaure, “Idan kun gama sai matarka taje ta kwanta angyara mata ɗakinta.”

Meenal ta dubi Ahmad shima ita yake kallo. Duk suka yi shuru babu wanda ya ce komai. Shi kuma Alhaji yana jin su, ya tabbata zata haɗu da ‘ya’yan zamani.

Bayan anwatse ni Ahmad ya jawo hannun matarsa suka shige ɗaki suka mayar da ƙofa. Dama kafin ya ajiye turaren Meenal sai da ya tofe da addu’a gudun kada Amina ta ɗauka kamar yadda ta kira kanta.

A jikin ƙofar ya rungumeta, “Meenal kiyi haƙuri da abinda Hajiya take yi maki watarana sai…”

Hannunta tasa a bakinsa, “Idan ka bani haƙuri zan damu. Amma da ka kaini ɗakin da Hajiya ta ce.”

Girgizai ya yi, “Ba zan iya muna gida ɗaya inkwana daban da inda kike ba. Ina son ɗumin jikinki.”

Bata iya cewa komai ba, sakamakon saƙwannin da yake turo mata.

<< Meenal 23Meenal 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×