Da safe Hajiya ta cika tayi tam. Da ƙyar ta amsa gaisuwarsu. Hakan yasa Meenal ta kimtsa kayanta yana shigowa ya samu har ta gama shiryawa. Kwanciya ya yi kamar mai jin barci, “Husby na shirya.”
“Haɗa min ruwan wanka.”
Ta dube shi, “Ai na haɗa tuntuni.” Zare idanunsa ya yi. Bai ce komai ba ya shige banɗakin ya watsa ruwa ya fito. Yana gamawa ya yi kwanciyarsa, “Husby ka tashi muje mana.”
Wai ina zamu je?”
“Gidan Ummana.”
“Ohh ai ba yau nace zamu je ba sai..” Bai kai ga ƙarasawa ba yaji saukan filo ko ta ina tana buga masa. Kuma da iya gaskiyarta take dukan.
Murmushi ya yi ya fizgota ta zube gaba ɗaya a tsakiyar ƙirjinsa, “Kin ƙosa ki tafi ki barni ko? Da wasa ta ce, “Ehmana.”
Wani abu da ya yi mata ne, yasa ta zaro idanu,”Yaya ban ƙosa inbarka ba.” Ta faɗa cikin sigar shagwaɓa. Tana zame masa hannu. Murmushi ya yi ya miƙe suka fito.
Haka da zata yi masu sallama da ƙyar suka amsa, haka suka fito jikinta babu ƙwari. Kai tsaye gidan Amina suka tsaya, ya bar Meenal ta shiga.
Ba su wani jima ba suka fito tare. Tun daga nesa yaga saɓanin abinda zuciyarsa ke gaya masa, haka ya ga abinda Meenal ke gaya masa a jiya. Cikin mutunci ta gaida Ahmad ya dubi Meenal, “Ba ita ba ce. Wancan kamanninku ɗaya.” Amina Shehu ta ce, “Ƙila wata ce wacce ba mu yi zato ba, ta ɓoye sunanta. Ko dai Aisha ce? Kinsanta da iya ɓoye suna ta ari na mutane.”
Meenal ta ɗanyi shuru can ta ce “To ai Aisha bama kama da juna.”
“Hakane kuma.” Gaba ɗaya suka ɗauki shuru na wasu ‘yan mintuna. Daga bisani Ahmad ya yi mata godiya suka bar ƙofar gidan.Ganin kamar yana cikin damuwa yasa ta kwanta a kafaɗarsa, “Wani mutum ya yi gamo.”
Bai san lokacin da ya yi murmushi ba. “Meenal gyara gyalen ki gashinki ya fito.” Da sauri ta gyara tana duban fuskarsa. “Idan ka sha mur sai inga kayi kyau, idan kayi murmushi sai ka sake yin kyau. Ban taɓa ganin kayi dariya ba. Why?”
“Ban iya dariya ba, bana son kuma inga namiji yana buɗe baki yana tuntsurar dariya ba gaira ba dalili. Yanzu dai ba wannan ba, mu fara zuwa gidan Baba Sani mu gaishe shi daga nan sai in ajiyeki a gidan Umma ni kuma zanje wani wuri.”
Da sauri ta ce, “Zan bika wani wurin.” Juyowa ya yi ya dubeta. “A’a Umma ba zata so kije ki sake fita ba. Gidan abokina zanje.” Zata yi magana taga ya yi parking, dan haka suka sauka.
Baba Sani ya ji daɗin ganin su kwarai. Sun jima a gidan, daga bisani suka miƙe zasu tafi, ya yi masu doguwar addu’a sannan suka koma hanya.
Umma da kanta ta fito dan taraiyar su. Meenal ta rungume Umma a jikinta tana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa. Hawaye kawai suke fitarwa. Ahmad da ya ga abin bana ƙarewa bane ya shiga basu haƙuri yana lallaɓa su. Haka suka shiga falon Umma yana kallonsu yadda suke hira abinsu kamar basu da damuwa. Meenal ta shaƙu da Umma, bata buɗi ido taga kowa ba sai Ummanta. Ɗaga kansa ya yi yana duban hoton Umma da Meenal da Nafisa sai Rufaida, dukkansu suna dariya. Nafisan ya kafe da ido yana jin tausayin yarinyar.
Miƙewa ya yi zai tafi, sai kuma yaga tana ƙyafta idanu. Hakan yasa ya ce masu zai dawo babu jimawa.
Har bakin mota ta raka shi, ta buɗe masa motar ya shiga, sannan ta ɗan rankwafo, “Allah ya tsare min kai mijina.” Da Amin ya amsa sannan ya ja motarsa.
Kai tsaye gidan Hon Munnir ya nufa. Kowa ya ganshi sai ya cika da mamaki. Bai jira anyi masa iso ba, haka babu wanda ya ce zai tsaida shi ɗin.
A falon ya same shi da abokansa da wata mace a kusa da shi suna kwasan dariya. Gabansu kwalabai ne har da na giya.
Dukkan su babu wanda bai firgita da ganinsa ba, musamman ma Hon Munnir. Ahmad ya ɗinga kallon su cikin jin ƙyama.
“Wai wakilanmu ne a haka. Kun fito duniya kuna gaya masu ku mutanen ƙwarai ne. Dan Allah ku tashi ku bamu wuri zamu yi magana.” Sum-sum suka miƙe suna ficewa. Ita kuwa karuwan tana zaune ta kafe Ahmad da idanu kamar tsohuwar zakanyan da take jin yunwa taga abinci. a hasale ya ce, “Malama tashi ki fita.”
Hon Munnir ya ce, “Rahama tashi ki je zan kiraki.” Ahmad ya ware idanu, “Dama musulma ce? Allah shi kyauta ya gyara mana zuri’armu.”
Babu wanda ya amsa masa ya dubi Hon Munnir, “Kayi zaton na mutu ko? Ikon Allah kenan. Nazo ne inja maka kunne, idan ka sake kawo min farmaki ko matata Meenal ni sai na yi maka mummunar illa.”
Hon Munnir ya miƙe yana duban Ahmad, “Doctor illa ɗaya zaka yi min kuma tuni an riga anyi min, shi ne a sanar da mahaifina Meenal ‘ya ta ce. A yanzu haka sarki yasan da maganar wanda nake zargin Salma Umman Meenal ko kuma abokina Alhaji Khalid. To na riga na kashe Alhaji Khalid. Kai kuma tunda aka harbeka kuka gudu. Ni yanzu idan Salma ce ma kafin ta mutu sai tayi soyayya da ni da ƙarfin tsiya kamar yadda Alheri tayi sannan inyi mata yankan wulakanci. Ba zan sararawa duk me son hanani sarautar Masarautarmu ba.”
Ahmad da ɓacin rai ya rufe shi bai san lokacin da yakai masa shaƙa ba. Ya fara magana cikin zuciya jikinsa har rawa yake yi,
“Idan ka kashe Alhaji Khalid kaci nasara Umma tafi ƙarfinka. Idan kace zaka taɓa Umma sai na yi maka kisan wulakanci. Kai wani irin uba ne wai? Mara tsoron Allah. Yarinya ƙarama tana neman ta zautaka! Don Allah ka taɓa jin imani da tausayin halin da ‘yarka take ciki? Kai ka ɗai ne a yanzu barazanar Meenal. Mahaifinka kuma da kake neman wanda ya gaya masa kayi abin kunya, ni na gaya masa. Ni na gaya masa Meenal jininsa ce a lokacin da yaje Egypt nayi masa aiki a dalilin Meenal. Ka ga shegiya mara gata tayi maka amfani, duk da kaso ya mutu ne. Don haka ya rage naka a yanzu nima kasa a kashe ni idan har ka cika kai mai kisa ne. Daga ƙarshe ba zan bar kisan da kayiwa Alhaji Khalid ba sai na ɗaukar masa fansa. Sannan ka jira shigowar Meenal cikin masarautar da kake yi wa kallo anan Aljannah take. Ni zan ɗauki Meenal inkaita da kaina, sai ka kashe kanka dan baƙin cikin shegiya ta shigo masarautarku.”
Watsar da shi ya yi ya koma kujera ya zauna. Lallai Ahmad ya firgita shi yau fiye da tunaninsa. Bai taɓa tunanin shi ne wanda ya ruguje masa shirinsa ba. Har ya kai ƙofa Hon Munnir ya sake gyara wuyansa da yake masa raɗaɗi, “Baka isa ka shigo masarautarmu da Meenal ba. Mahaifiyata har yanzu bata san da wannan zancen ba. Ina sonta fiye da komai na rayuwata, na tabbata abinda yasa Sarki bai gaya mata ba, yana tsoron yanayin da zata shiga ne. Idan kayi ƙoƙarin buɗe min abinda ya ɗaɗe yana rufe a karo na biyu, zaka sha mamakina.”
Ahmad ya juyo, “Mamakin nake son ka bani.”
A fusace ya fita. Gidansu ya koma ya haɗa dukkan wasu Record akan Hon Munnir. A yanzu ya yarda ya amince Meenal ta rasa uba. Ya amince dukkan Recording ɗin da ya ɗauka zai damƙa su ga hukuma. Ya ji mutuwar Alhaji Khalid haka ya yi mamaki da mahaifinsa bai gaya masa ba. Ba zai sanar da Meenal komai ba gudun tashin hankalinta.
Da daddare yana zaune a falon Umma sun gama hira da ita ta shige ɗakinta, Meenal tana kwance a cinyar Ahmad suna shan hira. Ƙarfe goma agogon ya buga baya son yin dare, don haka ya tashi suka fice tana taka masa.
Kamar zata yi kuka suka yi Sallama. Yana tafiya ta dawo ɗakin Umma tana sharar ƙwalla. Ta bata labarin duk abubuwan da suka faru. Umma tayi tagumi, “Shikam mahaifinki baya yin nadama ne? Kullum kamar tunzura shi ake yi? Nima ya tuhumeni da gayawa sarki maganar nan, ashe Ahmad ya faɗa masa. Allah ya kawo mana ƙarshen masifar nan. Haka aka tsinci gawan Alhaji Khalid a yashe ankashe shi. A ruɗe Meenal ta ɗago tana Salati. Mutuwar ya dake ta, kawai tashi tayi ta karɓi wayar Umma tayi ta kiran Ahmad bai ɗaga ba hakan ya sake ɗaga mata hankali.
Har Ahmad ya kai gida ya yi parking ya yi wanka yasa jallabiya, ya tuna ya bar wayarsa a gidan su Meenal, kuma da yawan shaidun da ya haɗa suna cikin wayar nan, Meenal tana iya gani ta ɗauka. Ba ma haka ba barin wayar a wani wuri akwai matsala. Don haka ya canza kaya zuwa ƙananan kaya, ya fito kawai ba tare da kowa yaga fitarsa ba. A zuciyarsa yana jin daɗin zai shiga har gurin Meenal ya yamutsata, don da gaske yake jin kewarta.
Bai ɗauki mota ba sai ya hau keke napep. Mai gadin gidan su Meenal ya yi mamakin ganinsa ya dawo babu mota gashi a lokacin sha biyu saura na dare.
Ƙofar a buɗe take hakan ya bashi mamaki matuƙa. Don haka kai tsaye wayarsa da ke silent ya ɗauka tana nan a inda ya barta. Ya cusa a cikin aljihu. Ɗakin Meenal ya nufa tana sanye da Kayan barci tayi tagumi idanun nan sunyi jaa, sai sake kiransa take. Tana jin motsi ta zaro idanu. Zata yi magana yasa hannunsa a bakinsa alamun tayi shiru.
Da sauri ta sakko ta rungume shi, “Ina ka shiga ina ta kiranka husby.”
“Wayata na mance ta a falon Umma saboda daɗin soyayya.” Ajiyar zuciya take yi da ƙarfi kamar wacce tayi tseren gudu, “Meyasa baka bari sai gobe ba, bayan kasan dare ya yi.”
Hannayensa suna lume a cikin gashin kanta ya bata amsa a shaƙe, “Saboda ina kewarki shiyasa.” Shuru tayi fara aikawa juna da saƙo ta wata siga me wahalar fassaruwa. Sai da ya tabbatar da ta gamsu sannan ya zare jikinsa.
Zai fice ta miƙe jikinta babu ƙwari, “Zan rakaka.” Dawowa da baya ya yi, ya manna mata sumba. “Ki kwanta baki da ƙwari a jiki. Gobe da safe insha Allahu zan zo akwai maganar da zamu yi.”
“Amma meyasa tun ɗazu nake ta jin motsinka har na fara tsorata.”
Dubanta ya yi, ya bata amsa,”Bana son Umma tasan na shigo ne kunya zanji. Oya go and sleep.”
Ya ƙarashe maganar a kunnenta. Hakan yasa tsigar jikinta tashi. Tana kallonsa hawaye cike da idanunta, ya fice. Gaba ɗaya ya gama ɗaureta ta yadda ta kasa ƙwaƙƙwarar motsi. Tana son Ahmad irin son da bata taɓa yiwa wani ba. Da shi da Ummanta tana jin ƙaunarsu fiye da komai.
Hayaniya take ji a falon hakan yasa ta fito a ruɗe.
Ahmad ne hannunsa riƙe da wuka ga Umma nan shimfiɗe a cikin jini, haka ga ‘yan sanda nan sun nuna shi da bindiga. Shi hankalinsa gaba ɗaya yana kan Umma da ke yashe cikin jini. Meenal ce kaɗai tashin hankalinsa.
Idanu suka haɗa jikinta yana ɓari, “Wayyo Umma ka kashe min ita ne? Me tayi maka?” Wani gigitaccen ƙara tasa tana faɗin, “Namij…. Wayyoooo Allah ka ɗauki raina inhuta ganin wannan baƙin cikin. Ummmaaaaaa.”
A take ta zube a wurin a sume. Ahmad da yaji saukar maganar Meenal har tsakiyar kansa ya ɗinga kallonta. Ya sani tashin hankali ne yasa Meenal faɗin hakan, idan kowa a duniya zai gaza fahimtarsa yasan Meenal ɗinsa ba zata taɓa gudunsa ba. Duk da irin matsayin Umma agunta. A hankali ya sauke wuƙan da ke hannunsa yana jin dama shi aka kashe aka bar baiwar Allan da bata ji ba, bata gani ba. Yana son isowa kan Meenal, amma ƙafafunsa sun gagara ɗaukarsa. Yana ji yana gani ‘yan sandan suka fice da shi. Mai gadi kuwa ya fi kowa firgita haka yayi mamakin Ahmad sosai.
Tohhh fa! Hargitsi, tashin hankali, tausayi, al’ajabi duk a cikin littafin Meenal. Kuyi haƙuri masoya Ahmad da Meenal, a duniya kowa da irin jarabawarsa. Haka kowani tsanani yana tare da sauƙi. Masoya Umma ina me baku haƙuri. Mu je zuwa, ni na hargitsa insha Allahu ni zan warware komai. Ta ku ‘yar mutan Borno.
Mahaifin Ahmad ya zagaya falonsa ya fi a ƙirga ya rasa meke masa daɗi. A lokaci guda ya kai duba ga mahaifiyar Ahmad dake rusa kuka, bayan ya kawo masu saƙon za a wuce da Ahmad kotu jibi, haka Ahmad ya ce a barshi kawai gaskiyarsa zata fito da shi.
Ransa a ɓace ya dubeta, “Duk kece silar komai. Yau da baki takurawa Meenal ba da ba zai kaita gidan Hajiya Salma har ya ɗinga biyo dare wajen isowa ga matarsa ba. Yanzu ga ɗanki yana cikin matsala.”
Hajiya ta sake rushewa da kuka ƙannansa suna taya ta. Shi kansa Yayansa kuka yake yi.