Skip to content
Part 26 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Kukan da suke yi ya fi komai sake dagula masa lissafi. Sai dai har gobe har jibi ba zai daina kallon Hajiya a matsayin silar cilla danta a matsala. Ita kuwa Hajiya ta yi danasani, ta kuma tsani kanta.

Ahmad yana zaune ya hada kansa da guiwa. Kalaman Meenal suna ci gaba da dukansa. Babbar tashin hankalinsa a duniya shi ne tunanin a wani hali Meenal take yanzu. Yana da tabbacin idan kowa zai juya masa baya, Meenal ba za ta taba juya masa baya ba. Wata zuciya ta ce da shi, “Umma ce fa. Umma ita ce gatan Meenal. Meenal tafi kaunar Umma akan kowa. Ya runtse idanunsa yana hasko Umma kwance a cikin jini. Radadin zuciyarsa ta karu. Yana son Umma, yana kaunarta. Ta ya ya zai iya kasheta? Yanzu shi kenan Umma ta mutu? Ya dunkule hannunsa jikinsa babu ta in da baya karkarwa. Yana da tabbacin Meenal ce za ta zo ta yi shaidarsa akan ba shi da alaka da mutuwar Umma.

Ware idanunsa ya yi da sauri. Meenal ce tsaye akansa cikin kuka mai ratsa zuciya. Ya kasa ko motsi, tausayinta ya cig aba da ratsa dukkan ilahirin jikinsa. Yana jin da za a bude shi da ya jawota jikinsa ya lallasheta. Cikin shesshekar kuka ta fara maganar da ta jawo daukewar numfashi na wucin gadi daga zuciyarsa,

“Ba zan taba yafe maka ba. Duk irin kaunar da Umma ta nuna maka,ka rasa da irin abin da za ka saka mata sai kisa? Me ta yi maka da har ta cancanci kisa? Wallahi sai na tabbatar an hukuntaka daidai da laifinka. Da zan sami dama da da kaina zan kasheka da hannayena. Ahmad na tsaneka! Na tsaneka!!! Na tsaneka!!! Azzalumi macuci. Na yi danasanin amincewa da kai. Ka cuceni ka rabani da farin cikina.” Ta juya tana kuka mai taba zuciyar mai saurare. Ahmad ya runtse idanunsa yana ji a zuciyarsa shikenan ya rasa kaso mai girma a cikin wacce yake ganin ita ce shaidarsa. Idan haka ne me ne ne amfanin rayuwarsa? Gara ya amsa kawai shi ya kasheta da ya zauna a duniyar da Meenal take yi masa kallon wani azzalumi. Sunansa da ta kira kai tsaye ta fi komai bashi mamaki. Bai taba sanin akwai ranar da Meenal za ta bayyana a gabansa da irin wadannan kalaman ba. Tunda aka kawo shi ya kasa hadiyar daidai da ruwa. A zuciyarsa kuma yana sake jinjina girma da matsayin Umma a zuciyar Meenal wanda ta cancanci Meenal ta juyawa kowa baya akanta. Amma kuma bai tsammaci Meenal za ta yarda cewa shin e zai kashe Umma ba.

*****

Meenal tana kwance ana yi mata karin ruwa. Tunda aka kawota asibitin bata farfado ba sai yanzu. Ta bude idanunta tana kallon dakin da take. Sannu a hankali abubuwan da suka faru suka dinga dawo mata cikin kanta. Ta fashe da kuka tana cewa, “Umma kada ki yi mini haka, kada ki tafi ki barni. Umma ke ce kadai farin cikina.” Tana kuka da iya karfinta. Ji take yi kamar za ta mutu saboda radadi da azabar da zuciyarta take yi. Baba Sani ya ce,”Kin dai ga abin da mijinki ya aikatawa Ummanki? Dama ni ba yarda na yi da shi ba. Yanzu ga shi ya dauke mana ita. Wallahi ba zamu taba yafewa Ahmad ba.”
Sulaiman ya ce, “Wallahi sai ya san ya kasheta. Yanzu kin ga abin da wanda kike takamar yana sonki ya aikatawa Umma ko?”

Meenal ta dago cikin hawaye tana dubansu, “Tayaya zai iya kashe Umma? Kaima yanzu Baba ka yarda shi zai iya kashe Ummana? Wallahi ko bakin bindiga aka dora a kirjina ba zan taba yarda mijina zai iya kisa ba. Duk in da aka kaishi ni zan je in bayar da shaidar bai kasheta ba.”

Gaba daya sai suka hau kallon kallo. Ran Baba Sani idan ya yi dubu ya baci. Ya dubeta yana huci, “Kin bani mamaki Meenal. Irin sakamakon da za ki yi wa wacce ta reneki kenan? Ta zabeki akan kowa? Yau kin girma kin nunawa duniya mijinki ya fita.”

“Ka yi hakuri Baba. Duk wanda ya kashe Umma ko wanene ba zan taba barinsa ba. Amma ka yarda da nib a mijina ne ya kashe Umma ba.”

“Rufe mini baki mutuniyar banza! Dama tsintacciyar mage bata mage. Idan kika fita daga asibitin nan kisan gidan uban da za ki koma ba cikin zuri’armu ba. Shashasha wacce batasan halacci ba.”

Tana kallo suka fice suna tsine mata. Da kanta ta cire karin ruwan bata da wani buri da ya wuce ta ganta a gaban mijinta. Za ta kwantar masa da hankali. Za ta gaya masa ba shi ne ya yi kisan nan ba. Tana tafe babu ko kwandala batasan in da ta nufa ba. Duk wanda ya ganta sai ya sake kallo. Ta tari napep ta nufi gidan kawarta. Anan ta matsa mata sai ta ci abinci. Tana cuccusawa tana hawaye tana cewa “Wallahi ba zai kashe Umma ba.” Da ta tuna mijinta yana can bai ci abinci ba, ta ture abincin ta ce ta zuba mata a kula, tana da tabbacin bai ci abinci ba. Ta zuba mata tana jin tausayinta yana ratsata. Ita ta bata kudin mota tana tsaye har mai napep ya ja suka wuce police station. Cikin kuka ta fado police station din. Wani ya dubeta ya ce, “Wai ke me ya da kike damunmu ne? Dazu kika zo nan yanzu kuma kin sake dawowa. Ki wuce ki bamu wuri ba za ki ganshi ba.” Meenal ta fasa kuka ta zube tana yi masu magiya. A lokacin d.p.o din ya fito daga office. Ya dubeta sosai cike da tausayawa ya ce, “Ku je ku fito mata da shi, ku kai shi office din Sadau, domin ta ga mijinta. Tashi ki daina kukan hakannan.”
Da sauri aka aiwatar da umarninsa. Suka sanyata ta ci abincin tukun. Tana zaune a ofishin hawaye kawai ke zuba a cikin idanunta. Aka shigo da shi kafafunsa daure cikin ankwa. Ta mike zumbur! Tana tunawa da kwanaki biyu iwar haka suna cikin farin ciki da Umma. Da sauri ta karaso ta rungumeshi tsam ta sake fashewa da kuka tana cewa, “Sun kashe mini Ummana. Kai kuma sun sanyaka a cikin masifa. Baba Sani ya koreni daga gidansa akan na ki amincewa kai ka kashe Umma.”

Bai san lokacin da ya saki gauron ajiyar zuciya ba. Ya mayar da hannayensa ya rungumeta.

“Idan kin yarda da ni, bana neman yardar kowa. Ina da shaidu akan abubuwan mahaifinki wanda zai taimaka mini a kotu, Sun shirya hakanne domin su rabani da ke. Allah ya jikan Umma. Ki daina kuka zan gaya maki in da abubuwan da na boye suke sai ki je ki kwaso. Kada ki damkawa kowa sai a kotu. Insha Allahu zamu tsallake wannan jarabawar.”

Meenal ta kwantar da kai tana sauraren kalaman Ahmad masu tsuma zuciya. Hawaye kawai ke zuba daga idanunta. Mahaifinta ya dade yana cuzguna masu. Amma kuma insha Allahu za su kawo karshen komai. Tunda take jin kiyayya bata taba jin labarin irin na mahaifinta ba. Gaba daya suka zauna a kasa, ta bude abincin tana diba tana bashi a baki. Baya jin dadin komai, amma haka yake karba domin ya faranta mata. Sosai ta bashi abincin, sannan ta ce, “Yanzu zan wuce gida in kwaso abubuwan. Wai da gaske Ummana ta rasu? Shikenan na rasa gata.” Ta fashe da kuka. Ya kafeta da idanunsa kawai. Yana ta lallashinta har ya gaya mata zuwan da ta yi ta gaggaya masa magana. Ta girgiza kai ta ce, “Ban dade da farfadawo ba. Ban zo wurin nan ba sai yanzu.”

Duk suka yi ta jimami. Daga karshe suka rabu akan zata wuce gidan. Haka take tafiya kamar mahaukaciya. Ji ta yi an fizgota cikin mota. Tana ihu suka toshe mata baki. Wani gida suka kaita suka jefar da ita sannan suka rufe ruf! Ko tafin hannunta bata gani, bayan sun daureta. Kwanaki biyu ta yi har ta fara shidewa. Taga an bude kofar. “Ruwa-ruwa.”

Abin da take iya furtawa kenan. Mahaifinta ta gani a gabanta yana dariyar mugunta. Ya dubi mutanensa ya ce, “Ku kawo mata ruwan wanke-wanken tasha sannan ku bata kanzon tuwo. Su ne abincinta. A gabansa aka kawo ruwan wanke-wanke aka bata. Dan haka washe gari ta dan sami karfi saboda kanzon da take samu tana cis au biyu a rana.

Hon Munnir ya shigo yana kallon Meenal cike da nishadi.
Meenal ta ɗago cikin bushewar zuciya tana yiwa mahaifinta mugun kallo, “Kaji kunya! Ka ji kunya tunda abin duniya ya rufe maka idanu. Kuma ban yarda kai ne mahaifina ba, don Allah ka ƙaryata hakan. Ba zan bar wanda ya kashe min Ummana ba. Haka mutumin da kake zaton zai wulaƙanta insha Allahu zai fito.”

Hon Munnir ya saki murmushi ya matso kusa da ita, “Don ‘yar da aka haifa a titi ta iya gayawa Babba irin wannan furucin ai ba abin mamaki bane. Pastor ne kakanki fa, meye abin mamakin rashin kunya agun jikan Pastor?”

Cikin dakewa ta ce, “Haka kuma jikan Sarkin Gombe.” Ɗauke ta ya yi da mari yana dubanta, “Kaf zuri’armu babu shegu. Ke kinsan yadda na tsaneki? Ji nake kamar inshaƙeki kawai ki mutu kowa ya huta.”

Bakinta na rawa, hawaye na zuba har cikin bakinta ta ce, “Ka kashe ni Abba.. Don Allah Abba ka kashe ni inhuta.”

Tunda Hon Munnir yake, bai taɓa jin mutuwar jiki kamar yanzu ba. Sunan da Meenal ta kira shi ya shigar masa har cikin jikinsa. Jikinsa ya yi matuƙar sanyi. Amma da ya tuna abubuwan da yake buƙatan tunkara zamanta a duniya ya toshe masa, sai yasa ƙafafu ya yi fatali da tausayin.

“Zan cigaba da baki wahala anan, har sai ankashe wancan ɗan iskan me shegen taurin kai, ana kashe shi sai kema ki bi bayansa.”

Meenal ta furta, “Alhamdulillahi. Allah na gode maka da zaka sake haɗa mu cikin ƙaramin lokaci.

Hon Munnir ya dubeta yana mamakin ƙarfin zuciya irin na Meenal.

“Zaki cigaba da shan ruwan wanke-wanke.”

“Babu damuwa na shiryawa dukkan wani izayarka. Kuma kai ba Allah bane, ka daina tunanin duk abin da kake yi mini wayonka ne ko dabararka. Idan kuma kana ganin wayonka ne dan girmar Allah ka kasheni yanzu in daina ganinka a matsayin wanda ya yi dalilin zuwana duniya.”

Ya yi kamar zai sake kai hannu bisa fuskarta, sai kuma ya janye ya nunata da yatsa,
“Ba zan kasheki ba, har sai na mantar da ke alakar da kike kokarin shimfidawa a tsakaninmu. Sai izayata ta saka da kanki kin yakice jinina a cikin jininki. A duk lokacin da kika dangantani da ke, ji nake ina ma in saka bakin bindiga in dauke numfashin da kike shaka har kike samun damar kallon halastacce kike manna min haramtacciyar jininki a cikin nawa.

Ficewa suka yi suka barta baki a bushe. Kuka take yi, tana jin wani imani yana sake shigarta. Ta sani duk wani tsanani yana tare da sauƙi.

<< Meenal 25Meenal 27 >>

1 thought on “Meenal 26”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×