Skip to content
Part 27 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Yau satin ta biyu kenan a wurin ta rame tayi baƙi. Iya wahala Meenal ta sha shi ta gode Allah. Damuwarta a wani hali Ahmad yake ciki? Waye zai kawo masa shaidu?

Abinda bata sani ba, tun bayan da Ahmad yaga bata sake zuwa ba, jikinsa ya bashi aikin gama ya gama, Hon Munnir ya cika burinsa. Tun daga ranar ya hana kowa tunkararsa. Ya amince zai amsa shi yayi kisan don kawai yasan kashe Meenal za ayi, to idan ya fito Meenal kuma ta mutu ya yi rayuwa da wa? Gara shi ma kawai ya bita.

Ran Barr. Tajuddeen ya yi matuƙar ɓaci, haka Ashmaan har sai da ta kai su ga faɗawa juna magana, kasancewar duk ‘yan zafin rai ne. Duk shiga Kotun da ake yi babu wata ƙwaƙƙwarar shaida, don haka Alƙalin ya ce yau za a tarkata shaida ta ƙarshe kuma za a yanke hukunci.

Kan Meenal a ƙasa, bata ko son ɗago kanta saboda damuwa. Wani ya shigo yana dube-dube. Kawai ya kwance ta. “Ki zo mu je ki bada shaida akan Ahmad, yau za a yanke masa hukunci. Mijinki ya yi mana taimako a duniya ba zamu taɓa barin a cutar da shi ba. Ki karɓi wannan CD ɗin, ni na ɗauki yallaɓai a lokacin da yake bada umarnin a kashe Ummanki. Ga kuɗin mota kiyi sauri.”

Meenal ta karɓa tana rawan jiki. Ta baya ya fice da ita ta ɗinga gudu tana waige, ji take kamar za a zo a kamata. Da ƙyar ta sami abin hawa tayi gidan su Ahmad. Babu kowa a gidan sai Maigadi hakan ya tabbatar mata duk suna kotun.

Bata sami matsala da maigadin ba, dan ya ganeta. Ɗakinsa ta shiga ta kwaso dukkan abubuwan da ya gaya mata ta fice. A ƙofar kotun mutane ne cike da ƙyar ta samu ta kutsa a lokacin da shari’a tayi zafi. Kowa kuka yake yi. A tsakiyar kotun ta ce, “Ya mai girma mai shari’a nice shaida ta gaba da ake nema.” Tuni idanu suka koma kanta. Yana ɗagowa yaga ita ce ya rintse ido yana wa Allah godiya.

Tiryan-tiryan ta faro bayani. Ta cigaba da cewa, “Watarana na fito daga gida ina kuka sai naji a jikina kamar ana bina, na juya banga kowa ba. Na wuce kan bolan da na saba zuwa da zarar aka ɓata min rai, domin anan ne mahaifiyata tayi rayuwa. Sai naga wata me kama da ni sosai, na cika da mamaki. Kai tsaye ta gaya min ita Aljana ce. Nayi matuƙar tsorata naso ingudu ta dakatar da ni, ta gaya min tana tare da ni tun ina jaririya a cikin gidan nan.

Ban yi zaton da gaske ne ba sai da ta fara bin mijina tana zuwar masa a cikin siffofina. Tun yana iya bambance mu har ya zamana baya iya tantancewa.

Hon Munnir yasha turawa a kashe ni sai ta zo a matsayin nice su sassareta. Ranar da suka zo kashe ni ita kuma ta ɗaukeni gaba ɗaya ta kai ni daji. Ni kuma nasa rigima mijina nake son gani hakan ya hasala ta ta ɗaureni a cikin ɗan bukkan da kazo ka same ni.

Ita ta hanani inyiwa Mijina bayaninta a matsayin Aljanah. Duk yadda take taimakona hakan baya hanata idan na ɓata mata rai ta hukunta ni.

Mahaifina ya tsane ni ne saboda na kasance ƙazantacciya mara gata. Nasha wahala a hannun mahaifina, bai taɓa tausayina ba.” A cikin kotu mutane da yawa sai da suka yi kukan tausayin rayuwar Meenal. Kowa faɗi yake wani irin uba ne haka?

Hon Munnir da suke zaune suna jiran hukuncin Ahmad sai abu ya juye kansu. Hankalinsa idan yayi dubu to ya tashi dan haka ya shiga zare idanu. Meenal duk ta gabatar da shaidu. Umma suka gani a tsakiyar wurin angungurota. Farin ciki yasa Meenal zubar da hawaye. Umma da Dr. Aslaf ya ɓoyeta sai yanzu kowa ke ganewa ashe matacciyar tana raye a ƙarƙashin kulawan Dr. Asaf.

Umma ta fara magana, “A ranar da daddare ina leƙe ta windo saboda naji alamun shigowar mutum bansan waye ba, dan haka na yaye labule, sai naga Ahmad. Dariya nayi na koma ciki saboda nasan soyayyarsa da Meenal a gaban kowa yinta suke. Can sai na fito ina shirin ce masa ai na ganshi. Shine naji ansokeni da wuƙa, a lokacin Ahmad ya fito kawai sai aka turani jikin Ahmad ya zaro wuƙan cikin firgici, daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba, sai a gadon asibiti.”

“Kotu tana son ganin Hon Munnir idan baya kusa aje a zo da shi.”

Babu musu Hon Munnir ya taso ya je gaban kotu. Tun kafin kotu ta faɗa abinda take son ji ya fara bayani, “Sunana Munnir Abubakar. Ni ne mahaifin Meenal.” Daga Meenal har Ahmad shi suke kallo da mamaki, da yau ya kira kansa da mahaifin Meenal, ba tare da irin ɓacin ran da yake shiga ba.

“A gaskiya na wahalar da Meenal, haka naso inkashe ta, saboda yadda idanuna suka rufe. Tabbas ni na tura a kashe Hajiya Salma. Ina roƙon kotu da tayi min sassuci.”

Meenal ta fashe da kuka tana jin duniyar tayi mata ƙunci a lokacin da take jiyo alƙali yana yankewa Hon Munnir ɗaurin shekaru talatin a gidan yari, tare da taran miliyan talatin domin baiwa su Meenal suyi jinyar kansu. Haka kotu ta wanke Ahmad da laifin da ake zarginsa.

Meenal ta ƙarasa ta rungume Ahmad tana kuka, sai dai kukan da take yi yasa Ahmad kafe ta da idanu, ba kuka bane irin na farin ciki. Kuka ne irin na tana cikin tashin hankali.

Hannunta ya jawo ya kaita har gaban Hon Munnir. A karo na farko da ya yi mata kallon Rahama. Cikin son dakewa ta fara magana, “Zanje innemo wani uban, amma ba kai ba.”

Juyawa tayi zata wuce ta ji Muryarsa tana rawa, “Allah ya yi maki albarka Meenal. Na gode ‘yata. Don Allah ko sau ɗaya ne ki ambace ni da sunan Abba, zan riƙe hakan ya zamar min abin alfahari.”

Duk irin wahalar da ya bata, tana jin sonsa yana ratsa ta, amma meyasa shi bai taɓa ji ba? Kuka take yi tana girgiza kanta, Ahmad ta kalla cikin kuka. Murmushi ya yi ya gyaɗa mata kai, haka ta juyo tana kallon Umma. Itama gyaɗa mata kan tayi. A hankali ta ƙaraso kusa da shi, “Abba… Meyasa baka taɓa jin tausayina ba? Meyasa Abbana?”

“Ina jin tausayinki, nasha zama ni ɗaya inyi kuka akan abinda nake yi maki, sai dai nima ba laifina bane, umarni nake samu daga gun bokana akan lamarin mulkina. Ki yafe min nayi kuskure.”

Meenal ta ɗinga girgiza kai kawai ta faɗa jikin Ahmad tana kuka. Tana ji tana gani aka tafi da mahaifinta da mutanansa.

Tana fitowa ta rungume hannu kawai tana kallon kowa. Kowanne da ɗan uwansa kusan ma anmance da ita. ‘Yan uwan Ahmad ƙoƙari suke su sanya shi a mota. Haka ‘yan uwan Umma.

Umman ta juyo ta ce, “Meenal zo mu je gida.” Girgiza mata kai tayi, “Ban cancanci insake zama a gidan kowa ba. Shi kansa auren a yau zan datse shi. Zan je inyi rayuwa a inda mahaifiyata ta rene ni.”

Ahmad da ya ji maganarta a sama kawai ya juyo yana kallonta. Sam taƙi yarda ta haɗa idanu da shi. Baba Sani ya ce, “Meenal kina jin haushin dan na koreki akan Ahmad ne? Ban yi haka dan tozarci ba, ki ɗauka a ranki ke ce akayiwa ƙanwarki haka, dole zaki so ɗaukar mataki.”

“Hakane Baba. Ku tafi kawai yanzu ma zan koma ne in shigar da ƙarar Lukman da Ruƙayya, idan ba abi min hakkina ba ni zan bi wa kaina.”

Baba Sani ya girgiza kai, “Lukman da Ruƙayya sun yi hatsari suna can a asibiti babu me bin ta kansu. Idan kika gansu za ki so da mutuwa suka yi da sun huta.”

Ahmad ya ƙaraso har gabansu ya miƙa hannu, tana son ƙin binsa soyayyarsa tana ingizata. Dole ta miƙa masa hannun, “Baba ku je gida zan kawo maku ita insha Allahu.”

Babu musu kowa ya kama gabansa, shima ya shige da Meenalinsa a kwance a gefensa. Har yanzu tunanin mahaifinta ne fal a cikin ranta, har yanzu soyayyar mahaifinta yana damunta, har yanzu tana jin dama tayi rayuwa me tsawo da shi.

Gaba ɗaya a falo aka zube Hajiya ta ɗinga neman afuwan Meenal ita dai sai kuka babu magana. Ahmad yasan shi kaɗai zai iya mayar da kukan nan dariya. Don haka ya ƙosa su shiga ɗaki.

A can ƙarshen gadon ta maƙale tana kuka. Hannu yasa ya jawota ya manne da jikinsa, “Bari ingasa maki jikinki.” Idanunta a ritse, ta ji ta a kwamin wanka, ta saki ajiyar zuciya me ƙarfi. Ya jima yana wanke ta da sabulan wankansa sannan ya kwantar da ita shima ya shiga ya yi. Kafin ya fito har ta tayar da Sallah. Don haka shima ya tada.

Shuru dukkan su suka yi a cikin ƙaton bargon, kowa da irin tunanin da yake yi, “Meenal ashe me kama da ke aljana ce? Na jima ina wannan tunanin, sai dai rashin hujja yasa na kasa maganar.”

Shuru tayi bata bashi amsa ba, saboda wani kukan da ya taho mata. Hannu yasa ya jawota jikinsa, “Zan baki sarautar masu kuka. Kina so?” Nan ma shuru tayi masa. Sai da taji hannunsa a cikin rigarta, magana yake mata amma sam bata gane komai, sai faman girgiza masa kai take yi alamun ya daina bata so. Ya jima yana yamutsa ta, sannan ya janye jikinsa ya rintse ido. Yana ji a jikinsa ya kusan mayar da ita cikakkiyar mace. Luf tayi ta daina kukan, amma bata daina tunanin mahaifinta ba. Tana jin bai yi wa ƙannanta adalci ba.

A sati guda aka shirya har da Umma domin amsa gayyatar Sarkin Gombe kamar yadda ya buƙata. Ahmad ya ce ba zai je ba, su tafi kawai. Hakan yasa Meenal ta ce itama ta fasa zuwa. Dole ya shirya aka tafi da shi.

Sun sami tarba irin wanda dama sun yi zaton hakan. A wani ƙayataccen ƙaton falo me kama da fadan sarki aka ajiye su. Bayan angabatar masu da kayan ciye-ciye haka maza sun je sunyi Sallah tare da mai martaba matan ma sun yi a cikin gida.

Meenal tana zaune a takure mutane suka shigo amma ta kasa ɗaga kai ta kalli kowa. Mai martaba ya ƙaraso ya ɗago kafaɗunta ya kaita gaban wata dattijuwa, “Meenal wannan ita ce kakarki ita ta haifi mahaifinki sunanta Amina, takwaranki. Meenal ta ɗago kawai sai suka rungume juna. Hajiya Amina ta ɗinga bubbuga bayanta, “Yi shiru Aminatu. Da angaya min komai da wuri da da kaina zan zo inɗaukoki. Ke ce cikakkiyar jikan da zanyi alfahari da ita.”

Haka Hajiya Fulani ta raba Meenal da jikinta ta kaita gaban Pastor Samuel ta ce “Meenal wannan shine kakanki. Bayan dawowar sarki yasa aka nemo shi. Shi kansa ya nemi ‘yarsa Alheri har ya ji babu daɗi. Ga matarsa Zugwai.” Pastor ya rungume Meenal a lokacin da ta saki wani irin ajiyar zuciya. Ta jima a jikinsu tana zubar da hawaye, sannan aka sake nuna mata ƙannenta su Husna da kuma matar Babanta. Sosai suka karɓeta da farin cikin ganinta. Meenal ta ɗago jajayen idanunta ta ce, “To mu zamu koma. Ba zan iya kwana a cikinku ba. Bayan da ranku da lafiyarku kuka bar min mahaifiyata a cikin tsananin wahala. Ni yanzu Ummana da Yaya Ahmad sun isheni rayuwa.”

A guje ta tashi ta shiga inda bata san inane ba. Tana kuka me ban tausayi. Kowa a ɗakin Ahmad ya kalla hakan yasa ya gane me suke nufi.

Tashi ya yi ya sameta ya ɗago ta zuwa ƙirjinsa, “Meeenal irin godiyar da zaki yi wa Allah kenan? Wasu shegun da aka haife su zubar da su akayi a titi suna nan har gobe ba su san ma su waye iyayen su ba.

Bare ke da Allah ya yi maki gata. Ki gode masa ta hanyar da ta dace ba ta wannan hanyar ba. Kije ki kwana a cikin danginki, zan kasance da ke idan hakan zai faranta maki rai.”

Meenal ta dube shi, “Komai kace min inyi amsar zata kasance eh ne kawai. Bana fatan inriski ranar da zan zama silar ɓata maka rai. Ba zan taɓa mance karamci irin naka ba. Kayi alƙawarin dawo min da farin cikina, a tunanina hakan ba zai yuwu ba, ashe ina raye zanga wannan ranar. Me kake son inbaka ka gane kai kaɗai ne a cikin zuciyata?” Hannu ya kai bisa ƙahon zuciyarta ya ce, “Ki bani wannan kin gama min komai. Sai kuma nan wurin da nake buƙata a yanzu.” Kunya tasa ta rufe fuskarta daga bisani ta biyo shi tana kai masa duka yana kaucewa. Basu ankara ba sai ganinsu a gaban iyayensu suka yi. Ahmad ya ɗan sosa kai, gaba ɗaya akayi dariya. Cikin shagwaɓa ta dubi matar Babanta ta ce, “Yanzu anti me kuke yi wa dariya?” Nan ma aka sake yin dariyan ta zagaya bayan Hajiya Fulani ta ɓoye fuska.

Kwanan su biyar suna zaga dangi. Hajiya Fulani ta dubi Umma ta ce, “Wai inbanda kafirci ma masifa ne, wai harda wani suna kamar ta matsafa wai Zugwai? Wannan suna ya tsaya min a rai. Allah ka dube mu kasa su dawo addinimu, addinin gaskiya.”

Umma tayi dariya ta ce, “Ai zaki ji sunaye kala-kala.Kuma kinga sun riga sunyi nisa. Sai dai addu’a da dabara dai. Ko da yake tunda Meenal tana dariyarta, dukkansu ta miƙa masu hannu suka tafa, “Su Kaka sun karɓi musulunci da taimakon Gwarzo Ahmad.”

Tuni ɗaki ya ƙaure da murna. Haƙiƙa Ahmad ya zama gwarzon da samunsa zai zama da wahala. Sarki ya jinjina masa haka anyi masa tayin sarauta ya ce Allah ya tsare shi. Haka Sarki ya dage ya musuluntar da Pastor da matarsa Zugwai wacce ta koma Zulaihat, shi kuma ya ci sunan Musa.

Ahmad yana dawowa da matarsa ya amsa tayin asibitin da suke ta nemansa a Abuja. Don haka yana fara aiki da su ya sami natsuwa ya ɗauke Meenal zuwa gidansu. Gida mai dumbin tarihi.

Sun sami Nuhu da matarsa cikin ƙoshin lafiya.

Yanayin garin yau da ruwan sama aka tashi, don hakane yammacin tazo da wani irin sanyi da iska mai daɗi. Ahmad yana tsaye shuru a waje ya ƙurawa wani shuka idanu. Meenal ta ƙaraso ta fasa ledan da ta hura, ya bada wani irin ƙara.

Jawo ta ya yi jikinsa, “Angaya maki kowa matsoraci ne kamarki?” Dariya tayi ta ce zo muje ka ɗora ni akan wancan dakalin. Ido ya zaro, “Ai yanzu kin fi ni nauyi. Ba zan iya ba.” Turo baki tayi alamun fushi. Yau dai yana ji a ransa zai sauke dukkan abinda ke damunsa. Ita kanta yadda taga yana lumshe idanu tasha jinin jikinta.

A daddafe suka yi Sallar Isha’i ya haye gado ya ce bai da lafiya. Hakan yasa duk ta ruɗe daman haka yake so.

Wani irin wasa suka yi me gigita ƙwaƙwalwa, kafin sannu a hankali ya gangara asalin wurin. A hankali yake bi da ita wanda ya ci nasarar tsinka abinda aka tanaje shi domin shi. Ba ta yi masa raki ba, tayi juriya haka tasha albarka. Jin kansa yake kamar babu wanda ya kai shi sa’a. Tana ɗan yi masa ‘yan koke koken shagwaba, garin lallashi aka sake komawa cikin aiki.

Da asuba jikinta ya yi tsami sosai, dole ya taimaka mata ta samu tayi wankan. Daga nan kuma sai zazzaɓi. Shi ya haɗa Break ya kawo mata ta ci kaɗan ya bata magani.

Yau gidan su Dr Aslaf zai kaita saboda yau group din su na manyan mata suke gabatar da meeting ɗin su. Don haka ya ce Nuhu ya raka su, Maman Anwar ma ta ce zata je.

Hankalin Meenal ya yi matuƙar tashi domin taga wayewarsu ma ba irin nata bane. Don haka ta kasa sakin jiki a cikin su. Islam ta dubeta da murmushi a fuskarta, “Kina da tsoro Meenal, ki saki jikinki duk ɗaya muke.” Ita kuwa Maman Anwar tuni suka tsaneta saboda abubuwanta da halayyarta.
Bayan buɗe taro da addu’a sai kuma kowacce tana faɗin irin matsalar da take fuskanta a gidan miji. Wata ta ce ya cika masifa, wata kuma yana da riƙo, wata kuwa uwar miji ta sanyata a gaba, wata kuma mijin ne yake da neman mata. Karima ta ɗan ja tsaki, “Yumnah ni chatting ɗin da Suraj ya ragu sosai. Musamman da na bi hanyar da kika gaya min, akan idan yana chat inzuro kaina? Walh yanzu ya daina. Ina ganin ya ɗauki waya zan dawo kusa da sh inmaƙale masa, sai ki ga ya ajiye.”
Islam ta taɓe baki, “Ni fitan daren nan da yake yi yana damuna ya kasa bari.”
Yumnah ta ce to mu biyo masu ta hanyar magunguna da kuma kayan ƙamshi masu riƙe jiki. Bari inkira ‘yar mutan Borno mu ji inda take haɗo nata, kayan ƙamshin jikin, da sabulai masu kyau da gyaran fata. Cikin abin da bai fi minti biyar ba Yumnah ta gama wayar suna zaman jiran number.
Gaba ɗaya suka kafa kai suna kwafar lambar. 0703 888 2560 sunansa Jafar Gidan Kamshi. Yana nan a sabon garin Zaria. Duk turarukan Fatima Danborno a can take saya. Hatta kayan gyaran jiki a wurinsa take siya. Nima kuma duk sirrin gyaran da nake yi a wurinsa ne. Ku dinma ku jaraba ku gani. Sai kuma nau’ikan abincin da nake yi kala-kala wannan kam BAKANDAMIYA ce Sirrin. Ina da Account da su, dan haka acan nake sami kalolin abinci nake yi masa yana ci yana santi.” Maman Anwar ta ce “Me ne ne kuma Bakandamiya?” Yumnah suka yi dariya suka tafa da Islam. “Lallai an dade ana barinku a baya. Waye bai da manhajar Bakandamiya a yanzu? Gaskiya bana jin akwai wanda zai ce bai san Bakandamiya ba. Komai kike nema in dai kika shiga , ina tabbatar maki kin samu kin gama. Ga sanya nishadi. Littafai kuwa sai kin zaba kin dirje a dari biyar dinki kacal!”
A take duk suka bude suna al’ajabi. Hatta nau’ikan su drinks sun gani a wurin. Hanyoyin da ake sarrafa dankalin turawa har nau’ika goma. Bayan sun natsa ne sai kuma Maman Anwar ta karkace ta gaya masu matsalarta. Yadda ta ga suna dubanta duk sai jikinta ya yi sanyi. Yumnah ta fara magana, “Kema me zai kai ki sakin jiki haka? Haihuwa ɗaya? Kuma me zai sa zaki je gun miji zaki fesa turare me ƙarfi? Ni kin ganni nan akwai wani mai da nake haɗawa kina shafawa zaki yi zaton humra ce da ita kadai nake amfani bayan na gama turara jikina.
Maman Anwar ta yi matuƙar ƙaruwa akan abubuwan gyaran jiki, zuwa na kai. Hatta man gyaran baki sai da suka sanar da ita, sannan aka koma fagen girke-girke.
Sai wajen yamma sosai suka rabu suna kewar kowa. Yau dai so take ta cire kunya ta faranta ran mijinta. Wanka ta tsala ta fito ɗaure da tawul. Duk abubuwan da Yumnah ta bata sai da tayi amfani da su. Ta kunna kaskonta ta turara tun daga can ƙasanta har zuwa cikin jikinta. Turare ne ɗan gaske daga Maiduguri. Tana jin yadda hayaƙin ke shigarta. Tana gamawa ta shafe jikinta da man da Yumnah ta bata a matsayin humra. Ƙamshin ya ratsa ta yasa ta ajiyar zuciyar da bata shirya ba.
‘Yan ƙananan kayanta ta sanya, ta fito falon yana zaune yana sauya tasha. Ta baya ta saƙalo hannayensa ta zuba a wuyansa, yasa hannu ya zagayo da ita. Sosai yake dubanta. Gaba ɗaya sai ta sauya masa, kamar wacce zata je party.
Rungumeta ya yi tsam a jikinsa yana shinshinar ƙamshin da suka susuta shi. Tun suna iya fahimtar Abin suke aikatawa har suka ɗebi kansu zuwa wani garin da ba za su iya kiran sunan garin ba.
Ƙafafunta suna cikin ruwa shima haka, gaba ɗayan su suna cikin nishaɗi, ya ɗan dubeta, “Wai naga ban sake ganin me kama da ke bane.”
Meenal ta ce, “Ni mafarki nayi wai ta ce ta tafi ba zata sake dawowa ba, daman ta tsaya ne saboda tana tausayina, yanzu kuma ta ga wanda yafi ta jin tausayin nawa.”
Tana gama maganar tasa kanta a ƙirjinsa. Ɗago haɓarta ya yi suna duban juna, “Tabbas mahaifiyarki ce kaɗai zata nuna min tausayinki. Amma daga ita babu wani na biyunta sai ni.”
Hannu tasa ta jawo hancinsa, “Haka nima babu macen da zata nuna min sonka, sai Hajiya da ta kawo ka duniya. Ina sonka Husby, irin son da bansan ta yadda akayi na fara ba. Zan cigaba da sonka har in koma ga Mahaliccina.”
Kafeta ya yi da ido, don haka tasa hannu ta ɗibo ruwan ta watsa masa, ya yi firgigit. “Mugunta ko Meenal?”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Meenal 26Meenal 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×