Canza fuska tayi kamar zata yi kuka, tana girgiza kai, “A’a soyayya dai mijina.” Murmushi ya ƙwace masa suka miƙe dukkansu ƙafafun wandonsu a ninke yake. Kai tsaye kan kujerar me kama da lilo suka zauna. Dan rigima irin na Meenal akan jikinsa ta zauna tana fuskantarsa.
Bakinta tasa a kunnensa tana yi masa magana can ƙasan maƙoshi. Hakan yasa gaba ɗaya suka ɗauke wuta suka nemi su mance a duniyar da suke.
A guje ta fito daga cikin gidan tana ƙyalƙyaltar dariya, shi kuwa ƙwala mata kira yake yi da iya ƙarfinsa. A wani lungun cikin gidan ya samu ya kamota, dan haka ya ɗan matse ta, “Kinsan meke jikinki kuwa? Idan kika yi min asarar baby sai na cire ɗan bakin nan.”
Meenal ta zaro idanu, “Ciki? Ciki ne dama a jikina? Wallahi ni sai ancire ana mutuwa a wurin haihuwa.Ni dai Gaskiya ka cire min.”
Kuka take yi sosai, abin ya bashi mamaki dan haka ya rabu da ita kawai ya kama gabansa. A ranar kowanne fushi yake yi da ɗan uwansa. Cikin sanyinta ta gabatar masa da girkin dare ta ajiye masa kawai ta shige dakinta ta rufe. Ta gama shirin kwanciyarta tsaf! Ta haye kan gado. A karo na farko da suka raba makwanci. Damuwa ce fal zuciyarta. Dan haka ta fashe da kuka tana jin bai yi mata adalci ba. Dama ba sonta yake yi ba. Sosai ta dauki zuciya da shi. Shi kuwa ko kallon wurin abincin bai yi ba bai kuma nemeta ba shima ya shige dakinsa ya rufe.. Sai dai fa barci ya gaza ɗaukar ko da mutum ɗaya.
Meenal tana ta kukanta har barci barawo ya kwasheta. Da asuba ya fice masallaci bai sake dawowa gidan ba. Da kyar ta tashi ta yi komai, ta nufi falon. Turus! Ta yi da ta hude kwanuka taga ko tabawa bai yi ba. Wasu hawayen suka sake zubo mata. Ta kwashe ta nufi kitchen tana nazari. Dama an gaya mata a rayuwar aure zo mu zauna zo mu saba ne, amma kuma ita a wawtarta Yayanta ba zai taba yarda su sami matsala ba.
Ta zauna zaman jiransa shiru. Har ta gaji ta koma ta kwanta. Anan ta yi ta amai. Shigowarsa kenan ya ji tana ta amai. Da sauri ya karasa ya riketa sosai. Bayan ya tabbatar ta gama ya kamota ya kaita bandaki ya wanke mata baki. Da kansa ya je ya gyara wurin ya wuce kitchen ya samo mata tea. Fuskarta a murtuke kasancewar mugun haushinsa take ji.. shi ma kuma tunda ya fahimci tana jin haushinsa ya kyaleta. Ya kima ya dauko mata magani, ya hade rai ya mika mata. Dole ta karba tasha duk da ta tsani magani. Cikin dare a dakin ya kwanta saboda tsoron ciwon dare. Duk sun juyawa juna baya. Garin juye-juye suka haɗe da juna akan gadon. Yasa hannu ya rungumota jikinta na rawa ta maƙale masa. “Ka daina fushi da ni, ba zan iya ba.”
“Ki daina musu da ni Meenal, Allah zai hukunta macen da bata bin umarnin mijinta. Ki bari ni nasan abinda zan yi maki idan kin tashi haihuwa ba zaki ji zafi ba.”
Sai yanzu ta sami natsuwa ta sake maƙale masa a jiki kamar wata mage.
Abinda yake burge shi da Meenal har gobe idan ya buɗe idanunsa sai ta gaishe shi, haka bata wasa da duk wani abu da ya shafe shi. Haka bai taɓa buɗe ido bai sameta ta kammala kintsawa ba.
Washegari suka fito fes! Tana makale a gefensa hannunta daya yana cikin nasa. Kullum kaunar mijinta sake samun wurin zama yake a cikin zuciyarta. A hankali ta dago ta zura masa fararen idanunta. Yana dagowa ta daga masa gira sannan ta ce, “Ina sonka mijina.”
Ya ji dadin kalaman nan. Idan hadda take bashi ya kamata ace ya haddace su. Ya manna mata sumba sannan ya rada mata, “Ina sonki fiye da yadda nake son kaina Meenal. Farin cikina baya cika idan bahu ke a kusa da ni.” Ta lumshe idanunta tana jin tamkar ta fi dubban mata sa’ar miji. Ya saka hannunsa a cikin rigarta ya shafi cikin da ko tasowa bai yi ba ya ce, “Ina som abin da ke cikinki. Wannan ne kyauta mafi girma da Allah ya bamu a cikin wannan shekarar.”
Ta kwantar da kai a kafadarsa tana jin kaunar abin da bai fito ba, yana ratsa dukkanin sassan jikinta. Gaba daya a kasan kafet din suka zauna domin su karya. Kamar yadda suka saba ita ke ciyar da shi. Ya saki sassanyar ajiyar zuciya ya rike hannunta da take kokarin kai masa cokali mai dauke da kwai baki. Ya maido cokalin ya saka mata a bakinta. “Na yi kewarki da yawa babyna. Kada ki sake hora mini kanki wurin kaurace mini. Duk abin da na yi maki, na yarda ki sakani tsallan kwado kin ji?”
Ta tuntsure da dariya. Haka yake son ganinta, ya sumbaci hannayenta sannan ya tashi domin ficewa. Tana nan makale da shi har mota da sunan rakiya.a
*****
Yau dai a rugar su Lado suka sauka. Lado ya kafe su da ido yana al’ajabi. Zai yi magana Ahmad ya Harare shi, dole ya ja bakinsa ya yi shuru. Garin babu laifi mutane suna ta ƙara cika.
Meenal ta dubi Ahmad da kansa ke kwance a cinyarta ta ce, “Me zai hana a fitar da kuɗaɗe a tallafawa almajirai? Suna matuƙar bani tausayi. Suna buƙatar taimako.”
“Hakan yana da kyau, ki sami su Yumnah kuyi maganar yadda ya kamata. Amma wannan aikin sai kin dire min babyna tukunna.”
Abinda yake yi mata yasa ta riƙe hannunsa tana lumshe idanu. Kullum haka suke basa gundura da juna.
Haka zai jawo hannunta suyi ta tafiya a ƙasa, saboda nauyi da ta yi. Mita kuwa da karaya babu wanda bata yi masa. Hajiya Fulani ta yi juyin duniyar nan a dawo da Meenal gida wanka amma fir suka ƙi amincewa.
Yau da ciwon naƙuda ta tashi, ya ɗibo abubuwan da ya tanada, ya ce zai karɓi haihuwarta da kansa. Ta dube shi ta ce ai ita ba ta yarda ba. Bai ce mata komai ba ya koma kujera yana satan kallonta. Da abin ya ciwo ta bata san lokacin da ta barshi ba. Cikin ikon Allah ta haifi ƙatuwar ‘yarta mace.
Ahmad ya gyara ta da ita da babyn, sannan ya kira Maman Anwar ta ƙarashe ayyukan. Sai can dare ya sake shigowa ya ɗauki babyn yana sake yi mata addu’a. Meenal ta turo baki ta ce, “Ce min ka yi babu wahala.”
“Yanzu ba gashi har kin mance wahalar ba?”
Zaro idanunta ta yi, “Wallahi ba zan taɓa mancewa ba. Menene sunan Babyn?”
“Ta ci sunan Umma, Salma.”
Taji daɗin wannan kara da aka yiwa Umma dan ta cancanta.
Ta ce, “Allah ya raya Salamatu.” Ware idanunsa ya yi ya ce, “Ke! Baki da kunya ko?”
Matsowa tayi jikinsa, “Rashin kunya wani mutum ya koya min.” Murmushi kawai yayi mata, suka cigaba da kallon babyn. “Zo ki ba ta ta sha” Babu tunanin komai ta ciro tana rufe idanu. Ya kafe su da ido, hakan yasa ta ce, “Zan rufe idan baka daina ba.” Ya mike yana murmushi kawai.
Tun a washegari gidan Ahmad ya fara cika da dangi, har zuwa ranar suna. Hatta Sarki sai da ya zo ya duba baby Salma. Haka aka kawo sha tara na arziki.
Saboda farin ciki Meenal ba ta san lokacin da ta goce da kuka ba. Taso mahaifiyarta da tana raye taga wannan ranar.
Duk yadda aka so a tafi da Meenal, Ahmad yasawa idanunsa toka ya hana. Dole aka ajiye mai zama.
*****
Husband! Zo ka ga wani abin muamaki.” Fitowa ya yi yana duban tv kamar yadda yaga hankalinta yana kai. Mahaifinta ne ya fito daga gidan yari, har anzo tarbarsa. Meenal tayi shuru, haka Ahmad. Ajiyar zuciya ya ƙwace masa, “Ƙasarmu kenan. Ni nasan zai fito. Yana da kuɗi dole zai fito.”
Meenal ta rasa farin ciki zata yi kokuwa baƙin ciki? Kawai sai ta sa kuka. Rarrashinta ya dage yana yi.
Hon Munnir ya taka da ƙafafunsa yazo gaban Meenal ya sake roƙonta, a ranar tasha kuka. Haka mahaifinta ya kawo su Husna ya dinga nan nan da ita. A ƙoƙarinsa ya gyara laifukansa.
Salma dai tayi wayo, haka Meenal taso ta ɓatata da shagwaɓa sai da ya yi da gaske sannan ta koma tsawatar mata.
Cikin hukuncin Allah burinta ya cika akan almajirai ta buɗe Kamfaninta ta zuba ma’aikatan da aikin su kula da duk abubuwan da suka shafe su. Meenal ta sake cika tayi kyau, haka shima Ahmad ya sami kwanciyar hankali.
Yana zaune ya ji ana watsa masa ruwa, yana juyowa ta ruga da gudun gaske, yau zai yi maganin yarinyar nan. Ɗakin ya biyota ya mayar da ƙofa ya rufe. Zaro idanu ta yi kafin tasan abin yi ya fara aika mata saƙwanni, daga bisani ya ba ta wahalan da tun da suka yi aure bai taɓa tunanin yi mata hakan ba. Hatta ƙafafunta ba ta iya motsawa. “Idan gobe aka ce maki ina hutawa ki zo ki sake ɓata mini hutun ki ga yadda zamu ƙare.”
Tausayi ta bashi ya manneta a ƙirjinsa yana sa mata albarka. “Allah yasa a samo min ƙanwar Salma.” Hannun mara ƙarfi tasa tana dukan ƙirjinsa ya yi murmushi ya ɗauketa sai banɗaki. Gaba ɗaya suka shige cikin ruwan ɗumi, kowa da irin tunanin da yake yi.
*****
Wannan labarin gaba ɗayanta sadaukarwarka ce Mahaifina. Ka zama tamƙar abokina. Iyalanka sune abokan hirarka da shawararka. Haƙiƙa ka zama jan gwarzo. Ina alfahari da kai Daddy❤❤
Alhamdulillahi. To ga Meenal dai Allah ya nufeni da kammalawa. Ina fatan wadanda na ɓatawa akan labarin Meenal za su gafarceni ɗan adam ajizi ne. Gaba ɗayan littafin na ɗauke shi na sadaukarwa MANHAJAR BAKANDAMIYA.Ina fatan Allah ya daukaka wannan manhaja ta yaadda za ta fi kowacce manhaja a duniya. Taku ce har kullum Fatima Danborno.
Sai kun sake jina insha Allahu da sabon labari.
Alhamdulilah munagodiya Anty Fatima jinjina munanan taredake Allah ya Kara basira mun ilmantu Amman sunsha kalubaleachikin lettafin meenal
Labarin Meenal akwai kalubale kam kala-kala. Na gode kwarai. Allah yasa mu amfana da abinda ke ciki, mu watsar da abubuwan da basu da amfani.