Dr. Bakori ne zaune a tsakiyar famili ɗin na S.S Bakori. Yaso ƙwarai ayi masa faɗa kamar yadda ya zata, amma sai mahaifinsa Alhaji Sudais ya dube shi da kulawa, "Ni na haifeka, nasan halinka, nasan abinda zaka aikata. Duk da abinda kayi ya razana kowa, har yaso ya jawo taɓarɓarewar zumunci a tsakanina da ƙanina Sammani. Haka a dalilin hakan Salma ta faɗa mawuyacin hali. Nasan akwai dalili mai ƙarfi da yasa ka aikata hakan, nasan da zakayi hakan da gangar da ba zaka taɓa yarda a sanya rana ba, bare har ka. . .