Skip to content
Part 6 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Cikin abinda bai fice minti goma ba, Meenal ta fice hayyacinta. Kafin wani lokaci ciwonta ya tashi. Kanta ya langwabe jini yana fita ta baki ta hanci. Tun safe take cikin yanayin nan babu wanda ya ankara sai da yamma da me kula da ita ya zo ya budeta. A firgice ya koma ya rufe wurin saboda yadda halittar ta ta koma. A waya ya sami Hon. Munnir ya sanar masa da duk abinda ke faruwa.

Cikin gaggawa ya tura a fito da ita daga wurin aka kira likita cikin gaggawa. Shi kansa duk rashin imaninsa da ya kalli yarinyar sai da gabansa ya fad’i.

A natse yake shiryawa kamar ba shi bane zai yi tafiya me tsawo. Ya rasa dalilin da yasa ya kasa mance Meenal, bayan ta kasance macen da yafi kowa tsanarta. A gaban idanunsa ta kashe Alhaji Tasi’u. Ba zai taba mance wannan rana ba. A falo ya sami iyayensa suna zaune suna hira. Yana son ya ga ranar da shi ma zai iya zama a tsakiyar su ayi hirar da shi. Doguwar addu’a ya samu daga bakin iyayensa kafin ya kama hanya.

Sai yamma sosai ya iso garin, don haka masaukin da ya saba sauka kawai ya nufa da ninyar sai ya huta sosai cikin dare zai je ya duba Alhaji Khalid kamar yadda ya saba.

Ya jima a bandaki ruwan yana saukar masa har tsakiyar kansa. Yana son ya sami saukin radadin da kirjinsa yake masa, amma hakan ya gagara.

Tun ɗazu yake jin ana kwankwasa masa kofa, sai dai ba shi da alamun fitowa daga banɗakin bare har ya duba ya ga waye. Shi dai yasan tun da yake zuwa babu wani wanda yake zuwa ya buga masa kofa. Hakan yasa ya yi tunanin kila lambar dakin wani suke nema.

Bayan fitowarsa ne ya fiddo da turarukansa ya fesa a jiki sannan ya tada Sallah. Ya jima akan daddumar ya rasa irin addu’ar da ya kamata ya yi. Shin ya ce Allah ya jikan Meenal ne? Ko kuwa ya ce Allah ya bayyana Meenal? Wayarsa ya kafe da idanu yana duban kiran mahaifinsa.

A natse ya jawo wayar ya dauka. Babu wata magana me tsawo da ta haɗa su, suka yi Sallama tare da ajiye wayar a tare. Kwankwasa kofar aka ci gaba da yi, wanda sai yanzu hankalinsa gaba daya ya koma ga kofar. Tashi ya yi ya bude kofar yana duban mutumin da ke buga kofa. Ɗaure fuska ya yi sosai, “Lafiya?” Mutumin da ke kokarin shiga ɗakin Ahmad ya dube shi, “Oga ne ya aiko mu mu tafi da kai.” Ahmad ya dan dubi agogon hannunsa, karfe goma na dare. Ta yaya mutumin da ya saba aikowa a tafi da shi da misalin karfe goma sha biyun dare yau kuma ya sauya tunani? Kamar mutumin ya shiga zuciyarsa dan haka ya ce, “Yallaɓai ya ce yau da wuri yake bukatar a duba shi.” Babu musu ya koma ciki ya tattara kayan aikinsa ya fito suka tafi.

Tun ahanya Dr. Bakori ya shiga dogon tunani. Ya rasa dalilin da yasa ya gaza amincewa da mutumin da ya dauko shi.

Gida ne na gani na faɗa. A kalla girman gidan kadai idan ka tsaya kallo zai iya debe maka kewar duk wani abu da ya kasance ba shi da mahimmanci a tare da kai. Tun bayan saukansa daga motar ya kasa ɗaga ƙafafunsa. Mutumin ya nuna masa hanya, babu musu ya bi bayansa yana tafe yana duban manyan mazan da ke tokare a guri daban daban kowanne da irin aikin da yake yi. Ga dai shi dare ne, amma kuma zaka iya rantsewa yanzu garin ya waye.

A dai-dai wata kofa yaja ya tsaya. Babu ƙamshinta amma kuma akwai abinda yake amfani da shi wajen gane wanzuwarta agurin. Sai dai me zai kawo ta nan? Takun tafiya ya ji alamun za a fito daga ɗakin. Babu ko tantama wannan takun tafiyar Meenal ce. Cak! Ya ja ya sake tsayawa a karo na barkatai. Yana ji a jikinsa akwai abinda yake shirin faruwa. Daga cikin babban falon ya ji ana faɗin ku ƙaraso da shi mana.

Dr. Bakori sarkin zuciya, nan da nan ya hasala. Yana shiga falon ya karaso dai-dai fuskar mutumin da yake cewa a ƙaraso da shi ya yi masa wani duba, “Ya kake cewa a karaso da ni kamar na zama ɗan cikinka? Ya kamata ku dinga daraja mutanen da burin su ku sami lafiya. Ina Alhaji Khalid?” Gaba daya dakin babu wanda bai yi mamakin tsaurin ido irin na Dr. Bakori ba. Don haka Hon Munnir ya dube shi a wulakance, “Ka yi matukar sa’a kana da amfanin da zaka yi min, da ba haka ba, babu abinda zai hana ban dauke numfashinka daga duniyar nan ba.” Dr. Bakori ya matso daf da shi, “Idan ka kasance Mahallicinmu zan so ka dauke rayuwata a yanzu. Zan kuma nuna maka kudi ko mulkinka basu isa su sa ka juya ni ba. Babu mahalukin da zan taɓa da sunan duba lafiyar wani. Sai kasa bindiga ka ɗauki rayuwata a yanzu.”

Juyawa ya yi da nufin ficewa. Hankalin Hon Munnir ya kai matuka a tashi. Domin yasan Dr. Bakori ne mutum na ƙarshe da zai iya taimaka masa akan Alhaji Khalid. Yana da labarin taurin kan Ahmad sai dai ko kadan bai san taurin kansa ya kai har haka ba. Yana da buƙatar dole ya lallashi Ahmad domin yasan Alhaji Khalid bai yarda da kowa ba sai Dr. Bakori.

“Tsaya.” Dr. Bakori ya ja ya tsaya tare da kafe ɗakin nan da idanu. Baya son ko zai fita daga gidan nan ya fice ba tare da ya duba ɗakin nan ba. “Na ji zan baka wani aiki ne akan wanda kazo dubawa. Idan aikin nan ya kammala kana da riban Miliyan hamsin.” Da murmushi a fuskarsa ya dawo yana dubansu ɗaya bayan ɗaya. “Ina sauri lokacin duba Maigida ya kusa zan koma.”

Hon Munnir ya miƙe yana kaiwa da komowa. “Ina son ka yi wa Alhaji Khalid allurar guba ya mutu. Idan ka yi hakan zaka sami riban da har ka mutu ba zaka daina amfani da ita ba.”

Daga ɗakin Meenal ce a d’aure kamar mahaukaciyar da ake tsoron kada ta gudu. Tun lokacin da ta ji kamshin turarensa take kokarin rarrafowa ta fito abin ya gagara. Gaba daya bata iya tashi saboda daurin ya yi mata illa sosai. Tun da suka sake mata makwanci take wurin a zaune. Ba karamin wanda yasan Meenal ne zai iya ganinta ya gane ta ba.

“Hon zan yi maka abinda kake so. Amma dole sai anyi takatsantsar. Saboda hatsarin abinda kake buƙata a gurina. Har yanzu dai muna da sauran lokacin da zamu yi wannan aikin. Yanzu kuma zan rubuta irin allurar da ya kamata a siyo min inyi amfani da su.” Gaba daya sai suka hau kallon juna suna mamakin saurin amincewarsa. Lalle kudi babu abinda ba zai iya siya ba. Muryarta da ta disashe suka ji tana fad’in “Ruwa.” Kafin a ankare har Dr. Bakori ya tura kansa cikin dakin. Ba Hon Munnir ba hatta mutanen da ke kewaye da shi sai da suka firgita.

Wani irin jiri ke shirin kwasarsa ya yi saurin rike bango. Meenal ta riga ta zama wani sashe na jikinsa. Zai yi wahala Meenal ta shigo wuri ta fita bai gane ta shigo ba. Zai yi wahala ya ji takun tafiyar Meenal bai gane ita ce ba. Zai yi wahala ya ji muryar Meenal bai gane ita ce ba. Yasani Meenal tana raye bata mutu ba. Zai yi amfani da dukkan karfinsa wajen ganin ya kwato ta daga cikin halaka.

Sai dai tambayoyi ne cike da cikinsa, babu mai iya amsa masa sai mutane uku. Meenal Ummanta ko kuma mamallakin wannan gidan. Ba karamin namijin kokari ya yi ba wajen dakewa da nuna rashin damuwa da ganinta. Dr. Bakori ya dubi hannayensa yana jin yau idan ba su bashi Meenal ba zai iya afka masu, zai iya kashe rai domin ya taimaki Meenal. Fitowa ya yi daga dakin yana duban Hon Munnir, yana ji a jikinsa shi ne silar kawo Meenal dinsa a cikin wannan bakar azabar.

Yana ji da zai iya da ya zubar da hawayen tausayin Meenal don samun rangwamen abinda ke cikin zuciyarsa.

“Hon wannan yarinyar ba ta da amfani ne? Idan ba ta da amfani a shiryata a ba ta taimako ta dawo hayyacinta zata taimaka min kwarai wajen ganin ancimma abinda ake buƙata agun Alhaji Khalid. Domin Alhaji Khalid mutum ne me tsananin wayo da wuya ayi allurar nan ta cikin sauki.”

Gyaɗa kansa ya yi, “Doctor yarinyar can tsintota muka yi. Idan zaka iya duba lafiyarta kuma kana ganin zata iya taimakawa ai babu komai. Sai dai kuma har yaushe zata sami lafiyar da zata iya aiwatar mana da aikin mu? Lokacin ya kusa.” Dr. Bakori ya zaro wayarsa tare da kiran Alhaji Khalid ya bude muryar wayar gaba daya. “Yallabai na ƙaraso kuma bana jin dadi. Na dan boye kaina ina kulawa da kaina, ko za a daga min kafa zuwa gobe?” Allah ya kara sauki ya yi masa tare da amince masa ya kula da kansa.

Hon Munnir ya dubi Dr. Bakori cikin murmushi, “Ka burgeni matuka. Da alama bayan mutuwar Alhaji Khalid zamu ci gaba da hulɗa.” Wannan karon da ɗan jagora aka haɗa shi zuwa gun Meenal. Sunkuyawa ya yi a gabanta, ya rasa ta yadda zai fara. Ɗaga kai ya yi yana duban mutumin da ya tsaya masa akai ya ce, “Dan bamu wuri ko?” Sum-sum ya fice. Har Dr. Bakori zai kai hannu jikinta, kamar ance ya daga kansa ya hango ‘yar Camera me daukar dukkan wani abu da ke faruwa a cikin dakin. Murmushi ya yi yana sake jinjina girman wayo irin na Hon Munnir.

Tabbas da bai ga Camera din ba da babu abinda zai hana bai shiga hannun su ba. Don haka ya sauya taku, “Ke ya zama dole kiyi biyayya ga Hon Munnir, idan kina son rayuwarki ta yi kyau. Ba karamin taimakonki ya yi ba, tunda har ya kawo ki irin wannan gida. Zan duba lafiyarki zan baki kulawa, zan yi aiki da ke, da zarar mun gama zan dawo masa da ke nima in kama gabana.”

Meenal ta dube shi cikin hawaye tana son ta yi masa magana ya yi mata wata alama da tasa itama daga kanta ta dubi abinda yake son ta gani. Kawar da kanta kawai ta yi ba tare da ta iya furta komai ba. Hannayensa yasa yana kwance mata daurin a lokacinne ya sami daman yi mata magana a kunnenta, “Duk abinda nasaki ki yi idan kina son komawa ga Ummanki.” Ba ta ce komai ba har ya gama kwanceta.

Idanunsa ya ware yana duban Meenal ta zama gurguwa. Tunda yake ganin zalunci bai taɓa ganin kalar na Hon Munnir ba. Ta yaya ma har aka dauko Meenal daga Kano ta dawo Sokoto? Mikewa ya yi ya barta anan ya fito yana duban su, “Yarinyar tana bukatar kulawa sosai. Ko za a kaita masaukina?” Babu tunanin komai aka amince da miƙa Meenal cikin Hotel. Tausayinta ya kara kama shi. Ganin mazan nan za su dauke ta yasa ya dakatar da su ya dauke ta da kansa yasa a mota. Meenal ta rintse idanunta har yanzu tana nan da akidarta na tsanar duk wani jinsi da ya kasance na da namiji. Kafe Hon Munnir ta yi da idanunta da suka sauya kamanni. “Insha Allahu sai na zama ajalinka.

Hannayenta take duba da suka kumbura, ta sake sa kuka tana juya hannayen, “Da wannan hannayen nawa zan kasheka.”

Da isar su masaukin Dr. Bakori ya juya yana kallon yadda yaran Hon Munnir suka manna masa ‘yar Camera a jikin gadonsa. Bai san lokacin da murmushi ya subuce masa ba. Gaba daya suna son raina wa kansu hankali. Ya ji dadi da suka kasa yarda da shi. Suna ficewa ya cire duk wani abu da zai sa aji maganarsa da Meenal. Frij ya bude ya ciro Coke me sanyi ya fincike hancin ya kai baki. Sai da ya tabbatar makoshinsa ya gamsu sannan ya yi cilli da gwangwanin. “Meenal me ya kawo ki Sokoto? Menene alakarki da Hon Munnir? Kin shirya karbar taimako daga namiji?” Cikin kuka take girgiza kai, “Na tsane ku. Bana son taimakon ku har sai kun kashe ni.”

Daure fuska ya yi sosai yana dubanta. Kamar zai yi wani abu sai kuma ya fasa ya tashi ya fara had’a ruwan allurai. Duban kanta tayi a cikin Hotel tare da mutumin da ba muharraminta ba. Yaushe iyaye wa’inda suka san darajar ‘ya’yan su za su iya barin su a cikin hotel?

Kallonsa take yi yadda yake duba lafiyarta. Ko warin jikinta baya ji. Kura masa idanu tayi, a lokaci guda wani abu ya dinga ratsa dukkan jijiyoyin jikinta. Sai dai ita da kanta tayi kokarin ta fassara abinda hakan ke nufi abin ya gagara.

Yana son ya taimaka mata ta tsaftace jikinta ya kasa. Duk lalacewar Meenal idan har namiji zai matso kusa da ita sai ya ji yana sha’awarta. Yarinyar tana da wata baiwa a jikinta wanda ita kanta bata san da ita ba.

Ficewa ya yi ya fice zuwa harabar hotel din da tunani fal cikin ransa. Ma’aikaciyar hotel din ya kira yana rokonta ta taimaka ta biyo shi dakinsa. Cike da jin dadi ta biyo shi a zatonta sonta yake. Ganin aikin da ya nuna mata zata yi masa yasa ta dan sauya fuska. Bai damu ba ya koma ya zauna shuru yana tunanin inda ya kamata yaje ya samo mata kaya masu kyau. Yana ganin ta kama ta sun shiga band’akin kawai ya zari key ya fice.

Da kaya niki-niki ya dawo. Yana godewa mutanen Sokoto da basa rufe Shaguna da wuri. Daga ita sai karamin tawul ya sameta tana zaune shuru. Ko kallonta bai yi ba ya zaro doguwar riga ya mika mata. “Kisa wannan.” Kallon rigar tayi ta sunkuyar da kanta, “Sai dai ka kira matar nan ta sake taimaka min ba zan iya sawa ba.” Dr. Bakori ya rabo Meenal da gidan Hon Munnir ne domin ya taimaketa, yanzu kuma yana neman ya sauke ladan da yake shirin samu ta hanyar danasani.

Ba zai iya kwana daki daya da ita da wannan tawul din ba. Abincin ya tura mata tana ci tana had’a rai. “Na ko..” Ta kasa karasa maganarta sakamakon daure fuska da yayi kamar bai taba dariya ba, ” Ya kamata ki gane bani da lokaci. Kuma ya zama dole kisa kayan nan da kanki, ko da kuwa hannun zai cire ne gaba daya.” Kallonsa take yi kawai tana girgiza kai. Kuka take yi irin kukan da maraya yake yi a lokacin da ya tuna iyayensa.

Dr Bakori yana son ya dinga lallashin Meenal sai dai kuma rarrashin mace yafi komai to masa wahala. Da ace ba tausayinta yake ba da tuni ya kwakkwada mata mari sannan yasa ta ci abincin dole. “Da kike gidan Hon Munnir waye yake baki abinci?” Tambayar kawai zuwar masa ya yi ba tare da ya shirya fitowarta ba. “Da ruwan wanke-wanke nake shan ruwa, da farar shinkafa nake cin abincin rana wanda shi ke daukana har dare.”

Dr. Bakori ya kafe ta da idanu yana jin maganarta kamar a cikin mafarki. Nan da nan idanun suka sauya kala. Jikinsa har rawa yake yi saboda tsananin bacin rai, “Meenal! Wani irin laifi kika yi masa haka da har kika cancanci irin wannan izayar? Ruwan wanke-wanke fa?” Mi’kewa yayi zumbur yana dubanta, “Zan shayar da Hon Munnir ruwan mamaki.” Zai fice ya ji muryarta, “Hon Munnir zai iya kasheka idan yasan ka sanni. Kada kaje ka siyar da rayuwarka akaina. Ko na tashi mutuwa zan yi. Damuwata kada ka kashe Alhaji Khalid.”

Dawowa ya yi kusa da ita. Ya zama dole Meenal tasa kaya idan tana son hirar su ta cigaba da yin tsawo. Rigar ya dauka ya taimaka mata wajen ganin ta kare jikinta. Ita kanta sai yanzu ta fi samun natsuwa.

“Meyasa kike tausayin a kashe Alhaji Khalid a karo na farko? A sanin da nayi maki babu wani namijin da kika taba yabo bare har kiyi tunanin zai iya yi maki wata rana a cikin rayuwarki.” Sunkuyar da kanta tayi tana son share hawayen da yayi mata kaca-kaca da fuska, sai dai kamar a lokacin ake sake ingizo su. “Alhaji Khalid ya taba taimakonmu. Sai dai tsanar da nayi wa maza ya hanani tuna alkhairinsa ko sau daya. Don Allah kada ka kashe bawan Allan nan.”

“Menene alakarki da Hon Munnir?”

“Bani da alaka da shi.”

“Zan koma gida zan sami mahaifiyarki zan sanar da ita kina raye, zan gaya mata ba zan yarda ku hadu ba har sai ta gaya min wace ce ke!” Girgiza kanta ta shiga yi da karfi, “A’a kada kayi min haka. Ka taimakeni ka bar rayuwata. Bana son kowa yasan mummunar kaddarata. Bana son kowa yasan wace ce ni. Bana son duniya ta cigaba da guduna tana kyamatana. Gaba daya babu komai a cikin rayuwata face kazanta.”

“Meenal babu kazantar da zaki yi da zai sa duniya ta kyamace ki. Tunda kika yi kisa ban kyamace ki ba bana jin akwai abinda zaki aikata a duniyar nan ingujeki. Ki fad’a min ko da abu daya ne me girma da namiji ya yi maki da har kika ji ki tsani maza. Dole insan wacece ke Meenal. Duk inda nasa kafafuna sai na hadu da ke, har ta kai ina iya gane kin zo wuri ko da ban sa ki a cikin idanuna ba.”

Kukan da take yi yana ba shi tsoro matuka. A hankali ta d’ago tana dubansa, “Namiji yasa na shake wuyar mahaifiyata ina neman rayuwarta. Idan ka koma Kano ka je gida gun mahaifiyata ka dubi fuskarta zuwa wuyanta, zaka ga manyan tabbai. Namiji ya watsa wa mahaifiyata Acid! Namiji yasa na shiga gidan yari, akan abinda ban ji ba ban gani ba” Kuka take rizga kamar ranta zai fita, kuka take yi irin kukan nadama, kuka take yi bata son tana tunawa da komai da ya danganci rayuwarta. Cikin matsanancin kuka take magana, “Wannan kadan ne daga cikin abinda namiji ya yi min. Yaushe zan iya yafewa d’a namiji? Yaushe zan iya jin tausayin d’a namiji? Ta yaya zan yafewa kaina? Na cuci kaina, na cuci uwar da ta haifeni cikin kunci da bakin cikin rayuwa ta bani nononta nasha, ta yarda ta kwana da yunwa ta bani abincinta, da na tashi yi mata sakamako sai na saka mata da abinda har ta mutu ba zata taba mance ni ba. Wayyo Ummana ki yafe min.”

Dr. Bakori ya kasa yadda zai yi Meenal ta dawo hayyacinta. Ya jima bai ji tausayin wata halitta ba kamar Meenal. Tabbas ya ga fuskar mahaifiyarta. Gaba daya jikinsa ya mutu. Ba zai iya lallashinta ba dan haka kawai ya zura mata idanu yana kallon yadda take kuka. Meenal abar tausayi ce, indai har namiji ya jawowa Meenal wa’innan abubuwan da ta lissafo ya zama dole ayi mata uzuri. Mi’kewa ya yi tsaye kamar zai fice sai kuma ya waiwayo, “kiyi hakuri Meenal. Ki mayar da lamuranki ga Allah. Ki daina kukan nan kada ciwon ki ya tashi. Zan taimake ki amma sai bayan nasan wace ce ke.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Meenal 5Meenal 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×