Skip to content
Part 8 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

A falo Baba Sani da iyalansa suka gama koke-koken su sannan suka bijiro mata da zancen aurenta da Dr. Bakori. Girgiza kai take yi cikin kuka, “Baba bana sonsa, ba zan iya rayuwa da namiji ba, ku taimakeni kada ku yi min haka, nafi son rayuwata a haka.” Cikin natsuwa suke warware mata waye Dr. Bakori, har ta samu ta rage rudun da take ciki. Ta ce kafin ta amince tana da bukatan yin Magana da Dr. Bakori. A waya suka yi Magana, ta ce masa zai sake ta idan komai ya dawo dai-dai. Da kwarin guiwa ya amsa mata.

Yana kwance yana kallon yadda ake ta shirye-shiryen bikinsa, hankalinsa ya gaza kwanciya, ya rasa dalilin da yasa sam baya farin ciki da wannan auren, gani yake yi kamar ranar bakin cikinsa ne ta zo.
Daga Office yake ya kama hanya domin zuwa ya duba Meenal, yana shiga cikin gidan, ya sami Khadija da Salma sun tasa Meenal a gaba suna ta auna mata zagi.

Suna ganinsa kowacce ta hau rawar baki, bai ce masu komai ba, ya karasa kusa da Meenal ta dago cikin jajayen idanunta tana dubansa, “Suna ta zagina akanka, sun kasa ganewa minti talatin kafin auren mu ana iya fasawa.”

Gabansa ne ya fadi da kalamanta har yasa masa rike kansa da karfi, tabbas ko mutuwa Meenal tayi sai ya ba mutane mamaki. Amma meyasa yake cikin faduwan gaba kullum? Mikewa ya yi ba tare da ya ce mata komai ba, ya fice kawai.

Wukanta ta dauko tana dubansa, “Kafin mutu dole in kashe rayuka biyu.” Halima ce ta shigo tana zare idanu,

“Meenal wa zaki kashe da wuka?” Meenal ta dubeta kawai bata yi Magana ba ta mayar da wukarta ta ajiye.

Gobe zai kasance daurin auren su, a wannan daren Dr. Bakori ne zaune a mashaya, wanda ya rasa dalilin da ya kai shi wurin. Meenal ce ta wuce, wanda babu ko tantama ita ce. A a fi minti uku ba, sai ka wata da irin shigar Meenal itama ta wuce.

Hankalin Dr. Bakori ya kai matuka a tashi. Mikewa ya yi da nufin ya bi bayanta, don yasan yanzu wancan zata yi kisa. Karshenta Meenal ta taka sahun barawo. Wancan ta fara fitowa, Ahmed ya rike ta, ta dage iya karfinta tana son ta kwace, har sarkar wuyanta ya tsinke a wurin, a lokacin ne kuma Meenal ta fito cikin sauri tana shirin ficewa. Hakan yasa ya saki wancan, ya durkusa ya dauki sarkar ya bi bayan Meenal da sauri.

Tana shirin ficewa ya damko hannunta. Tana kokarin kwacewa ya daga hannunsa ya dinga wanke ta da mari, yau yadda yake ji zai iya kakkaryata ya watsar, saboda tsabar bacin rai.

A cikin motarsa ya jefar da ita yaja suka bar wurin. Sai da yayi parking a harabar gidansu kafin ya fito ya finciko ta.

“Da alama zaki zama mace ta uku da zan fasa aurenta kafin daurawa. Ba zan iya auren mutumin da bai yarda da kaddara ba. Ke wacece da ba za a jarabceki ba? Aka jarabci Annabawa ma bare ke? Wallahi idan kika sake zuwa wurin nan, da kaina zan hukunta hukunci irin wanda zaki yi zaton babu wani wanda ya taba yi maki irin tsanar da na yi maki. Kullum sai kinje da wuka, wasu suna amfani da hakan suna zuwa suna kisa.

Akwai ranar da za ace kece kika yi kisan, kin ga kin batawa kanki suna kin batawa zuri’arku suna. Abin takaicin gobe kike shirin zama matata kuma kike irin wannan fitar. Bace min a gaba tun kafin intattaka ki.” A tsorace ta goge hawayenta, tana son yin Magana amma labbanta sunyi mata nauyi.

Bata taba ganin fushinsa irin na yau ba, haka zuciyarta ta ji babu dadi da har take kokarin kure Ahmad. A guje ta fada gida tana kuka. Tambayar duniyar nan babu wand aba ayi mata ba, amma ta kasa cewa komai. Inda ta godewa Allah har sai da ta sauya kaya sannan aka fahimci irin kukan da take yi.
Bata san meyasa bata kaunar gari ya waye ba. Sai yanzu ta fahimci dalilin da Ahmed zai kawo gobe wajen hana daura auren su.

Tunda gari ya waye take kuka. Haka Ahmad da kansa ya ce a daura auren su sha daya da rabi na safe. Sha daya dai-dai Ahmad ya karaso kofar gidan su Meenal jikinsa babu kwari. Ya rasa meke masa dadi.
Yana zaune a yaga isowar iyayensa, wanda ya yi dai-dai da wanzuwar motar ‘yan sanda agujen gaske. Dr. Bakori ya lumshe idanunsa, da suka koma jajir, “Ta faru ta kare.” Haka ya yi ta nanatawa a zuciyarsa, ba tare da ya iya koda motsa kafafunsa ba. Cikin jiri ya fito ya jingina da motarsa yana bude idanunsa da kyar.

Meenal tana cikin shiryawa, kawai ta ji hayaniya na tashi, tana fitowa, wata kakkauran mata ta damketa, Meenal ta lumshe idanu hawaye suka biyo fuskarta, ta ce “Alhamdulillahi. Allah na gode maka.”
Kanta babu dankwali aka fito da ita, Umma ta rike su da karfi tana fadin babu me tafiyar mata da ‘ya sai angaya mata abinda tayi,

“Hajiya ‘yarki tayi kisan kai, yau da safe a cikin Hotel. Ta kashe wani babban dan siyasa Hon Rabi’u.” Ita kanta Meenal wannan bayani na dan sandan ya sanyata a cikin rudani. Yaushe ta fita yau bare har ta kashe wani? Ashe su Salma da Khadija da aka fasa bikinsu a cikin minti talatin nasu me sauki ne? Ashe ita nata minti talatin din a kurkuku zata karashe shi?

Duk wani me imani idan ya kalli Meenal sai ya yi mata kuka. Tuni Umma ta zube ta sume agun. Duban Umman take yi, tana jin ko sai yaushe zata faranta mata rai? Ita kanta tausayin kanta take ji. Suna gab da shiga motar ta hango shi tsaye ya rungume hannayensa a kirji yana dubansu. Fizgewa tayi da iya karfinta, tana son taje ta roke shi ya yafe mata, tabbas da tana bin shawararsa da bata sami irin wannan tozarcin ba.

A zaton su guduwa zatayi don haka suka taka aguje domin kamo ta, tana gab da isa wurinsa, ta ji wani irin duka a fuska, wanda ya dauke ganinta na wasu ‘yan dakika. Ahmed ya rintse idanu yana jin wani abu me tsananin zafi ya tokare masa makoshi.

Tuni jini ya fara fitowa daga bakinta, duk da haka kokarinta ta karasa gare shi, hakan yasa bata dakata ba, don hakane ta sake jin saukar wani abu me kama da bugun guduma a tsakiyar kanta, wanda yasa ta fadi kwance a gabansa. Duk wani halitta dake wurin sai da ya yi kukan tausayin Meenal. Dr. Bakori ya rintse idanunsa, sai ga kwalla. Dan sandan ya cigaba da rufe ta da duka, wanda yasa duk wani hakuri na Ahmad yakau, cikin zafin nama, ya fizgo dansandan nan sai ganinsa akayi a gefe, Ahmad ya watsar da shi kamar kayan tsumma.

Hannu yasa ya dago Meenal yana girgizawa, amma ko alama bata motsi. Cikin fushi ya tashi zai sake yin kan dansandan akayi saurin rirrike shi. Idanunsa jajir yake dubansa,”Tunda ka kashe min mata ba tare da hakkinta ba, nima zan dauki mataki akanka. Haka ake bincike? Ka kamata ne da zaka yi mata irin wannan dukan?” Sosai aka rike Ahmad yana kallo suka kwasheta suka watsa a cikin Mota.

‘yan uwan Ahmad suka hau maganganu suna godewa Allah da ba a riga andaura auren ba, bare su hada iri da ita. A natse Ahmad ya dago ya karaso kusa da mahaifinsa, da ke tsaye da Baba Sani.

“Ina son a daura min aure da Meenal yanzu.” Wannan Magana ya jawo cecekuce, haka ‘yan uwan Ahmad sun ki amincewa da wannan zance na Ahmad. Alhaji Sudais ya dubi Baba Sani ya ce, “Mu karasa a daura auren.”

Kanin mahaifinsa Alhaji Sammani yasha gaban su yana huci, “Yaya ka gafarceni amma ba za a daura auren nan ba. Idan kuma ana son dole sai andaura auren sai Ahmad ya gaya min dalilin fasa auren ‘yata a ranar bikin su. Saboda ina da tabbacin babu laifin da ya kai laifin kisa a hotel. Indai wacce ta kashe rai tana da mahimmancin da za a kasa fasa aurenta, to babu ko shakka Salma tafi kowacce mace cancanta ka aureta, tunda ita ce dolenka. Idan banda kai mahaukaci ne ina kai ina auren ‘yar mace? Yarinyar da dangin uwa kadai gareta babu na uba? Dama na zuba maku idanu ne, nasan babu inda wannan abu zai je. Don haka ina nan tsaye babu me ɗaura auren nan yau.”

Zuciya ke cinsa, yana jin zai iya aikata komai akan Meenal, yana jin ko mutuwa ya yi yau dinnan sai andaura masa aure da Meenal, yana jin ko mahaifinsa ne ya aibata Meenal zai iya daukar mataki na guje masa, yana jin ko mahaifinsa ba zai iya tankwara zuciyar da ta kekakashe akan tausayin Meenal akan fasa auren nan a yanzu ba. Haka yana ji a ransa, idan ya bar kanin mahaifinsa ya tafi ya yi barci me daɗi shi da kansa zai iya mutuwa.

“Mutuncin Meenal ya fi mutuncin mutane dari. Meenal ko kiyashi ba zata iya kashewa ba. Dole za a daura min aure da Meenal, ko da kuwa ta kasance daya daga cikin marasa amfani a duniyar nan.”

Karasowa ya yi gaban kanin mahaifinsa, yana dubansa, duba irin na tsananin bacin rai,

“Tun da ka zabi ingaya maka bambancin Salma da Meenal anan to zan gaya maka. Tun da ka hana ni inrufa maka asiri kamar yadda nayi a farko, to zan bude maka. Da Meenal da Salma, da Khadija, dukka ‘yan uwana ne. Yadda na rufawa Salma asiri haka na rufawa Khadija. Ina rokon Allah idan Meenal tana da laifi Allah ya hana ni rufa mata asiri.”

Saminu ya yi saurin karasowa gaban Ahmad, yana masa magana cikin tsawa,

“To kada ka rufa mata asirin mana. Babu laifin da ya kai laifin kisa. Ya zama dole ka janye auren nan.”

Ko kallonsa Ahmad bai yi ba, babban burinsa yau ya sawa kanin mahaifinsa damuwa a cikin ransa. Don haka ya ci gaba da Magana, “Salma ta kasance macen da maza suke binta ta baya, ina son ka dangana ‘yarka Salma da asibiti domin ayi mata aikin gaggawa, idan ba haka ba, sai matsalarta ta gagareka zama inuwa daya da ita. Wannan laifin yasa na kasa aurenta, laifi ne da Meenal ba ta taɓa kwatanta aikata makamancinsa ba. Meenal ta nesanci zina, ta nesanci maza saboda kawai ta tsira da mutuncinta.”

A lokaci guda hannaye biyu suka biyo fuskar Ahmad da nufin mari, cikin zafin nama ya kaucewa hakan, yasa hannu ya shake Yayansa, shaka irin na fita hayyaci.

“Kai waye zaka kai hannu fuska na? Waye kai zaka zagi Meenal? Idan ka sake kuskuren shiga sabgata sai nasa adda na datse hannunka. Duk wanda ya sake yunkurin aibata Meenal anan zan ɗauki mataki mafi muni akansa. Idan nace akan kowa ina nufin kowa.” Ya watsar da shi gefe, idanun nan sun sake rinewa da ɓacin rai.

Tirkashi! Wannan abu ya jawo tashin hankula fiye da tunanin mutane. Shi kansa Abbansa sai da ya shiga rudu sosai. Alhaji Sammani kuwa zaman ‘yan bori ya yi yana ganin Ahmad ya gama ci masa mutunci. A natse Abba ya dubi Baba Sani da yake jinjina girman kaunar da Ahmed yake gwada wa Meenal,

“Alhaji Sani muje a daura auren nan kafin mu san abin yi anan gaba.”
Ahmad yana nan tsaye yaji sanarwar daura aurensa da Meenal, daurin auren da ya kasa tsoma shi a farin ciki, daurin auren da ya zama mafarin shigarsa matsaloli da dama. Kai tsaye ya nufi gidan iyayensa da nufin shiga daki. A gaban mutane, a tsakiyar jama’a mahaifiyarsa ta fito tana huci,

“Idan ka sake ka shiga gidan nan Allah ya isa ban yafe maka ba. Kaje kawai na sallamaka. Idan sauran basu isa da kai ba, ni na isa da kai, dan kuwa ni na kawo ka duniyar nan, ba ubanka da kake takama da shi ba.

Mace tayi kisa a cikin hotel? Kuma ka auro ta?” Farar takarda ta mika masa, wanda ga dukkan alamu tun bayan sanar da ita abin da ya faru take rike da takardar, “Gashi ka sake ta yanzu ko kuma intsine maka.”

Ahmad ya rike kansa da ƙarfi yana jin damuwarsa tana sake ninkuwa. Da yasan mahaifiyarsa zata iya fadin mummunar kalma akansa da babu abinda zai kai shi auren Meenal.

Tunda yake da mahaifiyarsa bai taba ganin fushinta irin hakan ba. Sai dai kuma aikin gama ya gama ba zai iya sakin Meenal a irin halin da take ciki ba. Kafin yasan abin cewa ya ji muryar mahaifinsa, wanda hakan yasa ya saki ajiyar zuciya me karfi, “Ba zai sake ta din ba, zo kit sine masa. Lalle shaidan ya yi aiki sosai akanki, domin wannan ba halin matata ba ce. Ina baki shawara ki daina bin zugan jama’a domin za su kai ki su baro ki. Matsa min a hanya tun kafin bacin raina ya sauka akanki.”

Babu musu ta kauce masa, sai dai har yanzu tana nan akan bakanta. Ahmed kawai ya juya ya fice daga gidan. Kai tsaye Police Station din ya nufa. Cikin ikon Allah yasan D.p.o din, don haka ya bada izinin a fitar masa da Meenal.

Yana nan zaune kansa a kasa, aka shigo da ita, ya dago idanu suka dubi juna. Gaba daya halittarta ta sauya, saboda wahala. Zata fadi kasa yasa hannu ya tarota, a hankali ya maida ta cikin kirjinsa yana sakin ajiyar zuciya. Ita kanta wani sanyi ne ta ji ya ratsa mata, wanda rabon da ta ji hakan har ta manta.

A hankali yake shafar gashinta yana sunsunar ko ina da ke jikinta, ya kasa Magana, ya rasa idan ma zai yi Magana me zai ce mata? Hawaye take zubarwa sosai, jikinta yana wani irin rawa, da alamun yunwa a tattare da ita. Dago fuskarta ya yi yasa harshensa ya ɗauke hawayen da ke zuba, daga bisani ya manna mata kiss a goshi, “Kada ki damu Allah yana tare da ke. Daga karshe andaura min aure da ke.” Sosai ta ware idanunta tana dubansa, ashe akwai maza na gari? Idan ma akwai sai dai Ahmad ne kadai. Guiwarta ta duba da yake yi mata zogi, shima duban guiwar ya yi, duk ciwo. Yarinyar tana bashi tausayi matuka.

“Waye Alhaji Rabi’u?”

“Abokin Hon Munnir ne.”

“Kin taba ganinsa?”

“Eh na taba ganinsa.”

“Waye ya kashe shi a hotel?

“Shi ne abin da ban sani ba.”

Gyada kansa ya yi.

“Ki kwantar da hankalinki insha Allahu. Allah zai kawo karshen duk wani azzalumi.”
Hannunsa ta kama tasa akanta, tana kuka, “Kaina zai fashe.” Dr. Bakori yana jin dama zai iya cire duk wata damuwa da ke kan Meenal ya dora akansa. Yana jin yadda jikinta ya yi zafi sosai.

“Bari a bani izini sai induba ki.” Yana mikewa yaga jini yana bin kafafunta, ya dubeta a dan firgice, “Jinin menene wannan?” Kankame jikinta tayi tana kuka,
“Al’adata ce ta zo.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Meenal 7Meenal 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×