Skip to content
Part 1 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI

Shimfida

Malam Auwalu dan asalin kauyen Badume ne dake jiyar Kano. Manomi ne kuma dan kasuwa a lokaci daya da Allah ya azurta da rufin asiri. Kafin rasuwar su shida matar shi Balaraba da tsiran su duka shekara biyu ne, dan shine ya rigata rasuwa. Allah ya azurta su da yara shidda.

Da yake daga baya sun dawo cikin garin Kano da zama, hakan yasa duka yaran samun wadataccen ilimin addini dana boko. Dukkan su mazan harkar kasuwanci ta kayan abinci sukeyi da mahaifinsu ya rasu yabar su a kai, banda Aminu da son boko ya shiga ranshi sosai, dan bayan ya kammala Degree din shi ta farko a fannin siye da siyarwa, yana gama bautar kasa ya samu aiki a wani kamfani da yake Kaduna, da yayi aure ma can yaci gaba da zama. Duk da aikin shi bai hana shi cigaba da karatu ba da ya nemi izini suka kuma bashi dama da alkawarin cewar zaici gaba da aiki tare dasu dan mutum ne mai hazaka.

Lokacin daya kammala degree din shi ta biyu ya kuma sake cigaba dan yana son karatun shi yakai matakin da zai zama farfesa, ga aure daya kara rungumowa. Sai yayi dabarar bude gidajen gona har guda biyu anan garin Kaduna din. Inda yake kiwon kaji, zabi, talotalo harda kifin tarwada da a turance akafi sani da catfish. Allah ya saka mishi nasibi da yake mutum ne mai wadata iyali. Cikin wasu yan shekaru kusan duk wasu masu gasa kaji a Kaduna a wajen shi suke siye. Gidan shi daya dauki shekaru yana ginawa suka koma da yake a unguwar Barnawa nan wajen station road a garin Kaduna. Shima Allah ya azurta shi da samun yara.

Auwalu Musa – Balaraba Tukur

-Yaran su

•Mannir •Rabi’u •Humaira •Aminu •Khalil •Salim

Aminu Auwal Musa (Baba)

-Matan shi

Rashida AbdulMannir (Mama)

-Yaran ta

•Muhsin •Huzaifa •Salamatu •Halima •Khadija •Junior •Amna

Karima Sani (Anty)

-Yaran ta

•Zaid •Jafar •Hindatu •Khalil •Asma’u

Kawayen Hindatu Al’amin

•Zainab (Biebee) •Aina’u (Dimples) •Yasmin •Hajarah •Hawwa

*****

Malam Abbas bafullatani ne daga shiyar jahar Katsina, kauyen Marake. Auren da ake kira na gata shi akayiwa Abba da matar shi Amina, dan lokaci bata shige shekara sha shidda ba, shikuma yana da ashirin da uku. Haka suke rayuwar su babu yabo babu fallasa har suka sami yara biyar inda a haihuwar ta karashen, Allah yaiwa Amina rasuwa. Haka yaran sukaci gaba da tashi cikin maraicin uwa kafin su rasa mahaifi suna yawo tsakanin dangi.

Cikin hakan ne Abubakar ya shiga Kaduna ko zai sami sana’a inda ya fara aikin katakaye har Allah ya hadashi da matar shi da sadakar yalla ce da tayo gudun hijira saboda hatsaniyar da ake a yankinsu na Sudan sukayo najeriya, garin Kaduna, ita tayo Kaduna tana aikatau a wani gida, ko hausar kirki bataji lokacin. Da yake bashi da dangin da suka damu balle suyi magana akan rashin tabbaci na asalin Mariya, basu sami wata matsala ba sukayi aure ya kama haya anan unguwar Tudun Wada, sukayi zaman su yana cigaba da aikin katakayen shi ciki suke duk wata hidimar su.

Mal. Abbas – Mama Amina

-Yaran su

•Abdallah •Ahmad •Abubakar •Maryam •Rabi’atu

Abubakar Abbas (Appa) – Mariya (Anna)

-Yaran su

•Hamza •Abid •Faruk •Jamila (Auta)

Abokan Hamza Abu Abbas

•Usman Ayoob (Fodio)•Muhammad Kamal (Arafat) AbdulHafiz Ashir •Abdallah Nuhu

*****

Wani irin shiru ne mai cike da firgici da tsakiyar dare kadai kan samar, badan ta duba agogo ba, amman tana da tabbacin karfe biyun dare zata iya yi, wata walkiya akayi da ta sata sake rakubewa jikin bangon wajen saboda akwai hadarin da yake nuna alamar saukar ruwa ko wani lokaci, da babu taimakon hijabi haka zata kasance daga ita sai rigar bacci, kafin wata irin gigitacciyar tsawa ta sata dafe cikinta da yaron da yake kwance a ciki sai da ya motsa mata da alama tsoratar da tayi ta tabashi shima.

Runtsa idanuwanta tayi wasu irin hawaye masu ciwo na tsiyayo mata, batasan inda zata nufa ba a cikin tsohon daren nan. Tsayuwa ta sake gyarawa tana dafe da cikinta har lokacin, hannunta na rike da bakar leda da take a kulle da alamun wani abu a ciki. Tafi mintina talatin a tsaye bakin kofar gidanta, gidan auren ta bayan ta saurari kashedin da Hamza yaima maigadi da fadin,

“Wallahi idan ka bude mata kofar gidan nan, ba aikin ka kadai zai zo karshe ba, sai nasa an rufe mun kai, ka fadi dalilin da yasa ka bude ma wata gidana.”

Mamaki ne karshen abinda tayi, tasan Hamza kamar yunwar cikinta, sai dai batayi zaton rashin mutuncin shi yayi kamari haka ba, idan bai tausaya mata ba, zai tausaya ma halin da take ciki, ina zata nufa cikin tsohon daren a unguwar su da ko da rana saika yini bakaji motsin mutum ba, motoci ma sai jefi-jefi ta baki da akanyi a gidajen, ko kuma su mazauna unguwar. Dakyar ta iya jan jiki tana takawa ta rakube inda take tsaye a yanzun, ko takalma babu a Kafafuwan ta. Ajiyar zuciya ta sauke na kukan da takeyi har numfashin ta na tsaitsayawa, dai-dai lokacin da ruwan sama ya kece kamar da bakin kwarya. Idan Allah ya taimaka duk gidajen unguwar ana kunna generator, a haske take fayau, ba kasafai suke gane ko akwai wutar lantarki ko babu ba.

Idanuwanta Hindu ta sake runtsewa, wannan karin ajiyar zuciyar da ta sauke tafi alaka da sanyin ruwan da yake ratsa sassan jikinta, musamman da yake hade da iska mai karfin gaske. Takowa tayi ta dawo jikin gate din tana bubbugawa,

“Baba Maigadi dan Allah ka taimakamun, ka duba cikin da yake jikina…in samu wajen rakubewa idan asuba tayi ko ruwan ya tsagaita sai in tafi”

Hindu ta karasa maganar cikin matukar galabaita da rauni, tana saka hannunta dake rike da yar bakar ledar ta share hawayen da ruwa yake wankewa, jikinta na amsawa cikin kyarma da iskar da ta sake kadawa, sake bubbuga kofar take da karfi, jin alamar motsi yasata dakatawa, dattijon maigadin ne ya bude kofar yana saurin ziro kai kafin ta samu damar shiga,

“Kiyi hakuri, kinsan halin maigidan, wallahi aikin nan shine rufin asiri na….”

Wasu hawaye Hindu taji sun tsiraro mata, aure mai rufin asiri, aure kuma mai tonon asiri, kaddara na zabar inda zata jefaka batare da ta baka wani zabi ba. Yau itace a tsaye tana rokar inda zata rakube, ita Hindatu Al’amin, gaskiyar hausawa, duniya makaranta, duniya kuma juyi-juyi. Yau ta birkice da ita, asalima a shekara daya duniyar ta fara wasan cikar shekara da rayuwar ta.

“Dan Allah ka taimakamun, bansan inda zanyi a daren nan ba, ban sani ba.”

Cewar Hindu, numfashi Baba Maigadi ya sauke, tunda ya koma ciki yarinyar tai mishi tsaye a rai, amman yana tsoron abinda zaiyi sanadin aikin shi

“Sai dai ki shigo na minti kadan, in ara miki wayata inda wanda zaki kira.”

Cikin rawar murya mai alamar kuka ta amsa da fadin

“Eh ka aramun.”

Dan ta manta da wata abu waya, balle tayi tunanin tata da Hamza bai barta da natsuwar dauka ba, mutumin da ko takalma bai bari ta saka ba, ballantana kuma wata waya. Cikin gidan ta shiga da sauri, tana karasawa yar barandar dake gaban dakin baba maigadi ta tsaya tana tsiyayyar ruwa dan tayi sharkaf, kasa tayi dakyar tana dafe cikinta, wani irin sanyi ne yake ratsata har kwanya.

“Ungo….”

Baba Maigadi ya fadi yana mika mata karamar wayar shi da take daure da kyauro, hannunta na kyarma ta karba, tana kallon shi da yar lemar da yake rike da ita. Wayar ta duba, taji duniya, inka ganta batare da ka latsa ba, zaka iya rantsewa da bata aiki, gwangwan ce. Batama gwada lambar Mama ba, dan tasan kashe wayarta take da daddare, Baba ne zata kira idan ya daga, tunda shikuma ba daga bakuwar lamba yake ba, a duniyar ta lambobin mutum hudu ta haddace, ta Baba, ta Mama, tata, sai kuma ta Hamza da a yanzun babu amfanin da hakan zai mata. Lambar baba ta saka ta kira tana karawa a kunnenta, ringing din da wayar tayi alamar ta shiga na saka ajiyar zuciya kwace mata, kafin wasu hawayen su zubo, wannan karin kuka ne mai sautin alamun zafi da qunar zuciya yake zubo mata.

Har wayar ta yanke bai daga ba, sake kira tayi, sai da ta jera kira biyar tana yankewa ba’a daga ba, zuwa lokacin zuciyarta ta kara karaya, amman tasan hakura da kiran wayar na iya ja Baba Maigadi yace ta tashi ta fita tunda ba’a daga ba, kuma ruwan da ake ko alamar tsagaitawa baiyi ba, ballantana tasa ran zai dauke, inda take zaune ma feshin ruwa na samunta, ga sanyin tiles din ya kara mata sanyin da takeji, sai kyarma jikinta yake. Zazzabi ma takeji kamar ya saukar mata. Lambar ta cigaba da kira harta bace lissafi, cike da tausayawa Baba Maigadi yace mata

“Ki shiga daga ciki….”

Ganin yanda take kara takurewa da alamar sanyin da takeji, a ran shi yake tunanin yanda ba zai sake jin haushi idan mata sukai wa jinsin maza kudin goro na cewar basu da mutunci, basu da tausayi ba. Randa yaji wata ta kira abinda da namiji yayi da akuyanci, kalmar ta kwana biyu tsaye a makoshin shi, dan baiga abinda yai zafi da zata danganta jinsin shi da dabba ba, sai yanzun da kalmar ce ta farko da tazo mishi akan fassara abinda Hamza yaiwa Hindu din batare daya duba tsohon cikin da take tare dashi ba, balle yayi tunanin hadarin dake cikin fitar ko da namiji ne a tsohon daren nan, ko babu hadari, balle kuma mace.

Hindu bata jira ya sake mata magana ta biyu ba, ta mike dakyar ta tura kofar dakin tana shiga, da kafet cike da dakin, irin jan nan, sai tarkacen da batabi takan su ba, dan harda katifa irin ta yan makaranta, daga gefe bakin kofa ta zauna tana dan turo kofar, kar Hamza ya fito ya fatattake su daga ita har Baba Maigadi. Dan kadan ne cikin abinda zai iya aikatawa, ita shaida ce. Lambar Baba taci gaba da gwadawa tana karanto duk wata addu’a da tazo ranta, lokaci zuwa lokaci take saka gefen hijabinta da yake a jike tana share hawayenta da sunki daina zuba.

*****

Bacci suke su duka biyun mai nauyin gaske, da yake babu wuta, tasowar hadari da iska yasa an dauke, ga wani irin zafi da ya dira. Sun jima suna juyi, suna dan taba hira kafin bacci ya dauke su wajen sha biyu. Cikin bacci Alh. Aminu yakejin ringing din wayar daya lalubo yana dubawa da bugawar zuciya, ganin bakuwar lamba yadan nutsar da zuciyar shi

“Waye wannan….”

Ya fadi, kiran yana yankewa yaga missed calls da lambar har guda ashirin da daya

“Subhanallah”

Ya furta yana mikewa zaune gabaki daya, dan ya tabbatar ba lafiya ba, baccin na barin idanuwan shi, salatin da yayi shiya tashi matar shi Rashida da yaran gidan duka suke kira da Mama daga bacci, duhun dakin na hanata ganin shi sosai, hasken wayar shi ya tabbatar mata da a zaune yake

“Alhaji lafiya dai ko?”

Kai Alh Aminu ya girgiza ma Mama yana fadin

“Wallahi ban sani ba, wata lamba ce an kirani har sau ashirin da daya fa, bansan irin baccin da muke ba haka yau.”

Alh Aminu ya karashe yana kokarin sake mayar da kiran da yaki shiga, da alamar matsalar network. Ita kanta Mama tashi tayi zuciyarta na wata irin dokawa.

‘Inalillahi wa ina ilaihi raji’un’

Take fadi tana maimaitawa cikin ranta, bata son furta abinda zuciyarta take saka mata na camfin da hausawa suke cewar idan wani mummunan abu zai sameka sai baccin asara mai nauyi ya danne ka, dan duk yanda kaso casa’in cikin dari yake kasancewa gaskiya, yau zata kasance da kaso goman. Dan haka bayan Inalillahi jaddada ma kanta kalaman kwarin gwiwa takeyi

‘In shaa Allah babu abinda ya faru.’

Tana kallon Alh Aminu da shima hankalin shi a tashe yake, sai da gabanta ya sake mummunar faduwa da taji yace

“Hello…. Waye?”

Alamar kiran ya shiga har an daga

“Hello…”

Ya sake fadi dan bayajin abinda ake fadi, network din na rawa, amman da alamar macece, kashewa yayi ya sake kira, zufa na tsatssafo mishi, a duniya Allah ya dora mishi son ‘ya’yan shi, duk albarkar yawan su daya samu, idan yana da iko ba zai bari ko kuda yahau su ba, balle ya taba mishi su, dan sune jigon rayuwar shi, farin cikin ranshi. Akan ce tsakanin da da uwa sai Allah, kaunar su ba abu bace da za’a fassara kan mizanin kalamai, zai karyata hakan, dan kaunar da yake ma yaran shi har iyayen su mata na jinjina mata lokutta da dama.

‘Allah ka tsaremun yarana, Allah karka jarabceni ta hanyar su, Allah ka dubeni’

Alh Aminu yake fadi yana kara maimaitawa, lokacin da yaji an daga kiran, cikin wani irin raunin murya da shessheka aka ce

“Baa… Baba… Baba na”

Kafafuwan shi Alh Aminu ya sauko daga kan gadon a gigice, badan yagane muryarta ba, saboda ta fito daga kasan makoshinta a galabaice, ga network din bashida kyau, sai dan ita kadai take ce mishi ‘Baba na’ duk a cikin yaran kamar ita kadai ya haifa. Har magana sauran sukan yi akan hakan, maganar Hindu a ko da yaushe itace

‘Baba na ne, kaunar da take tsakanin mu daban da irin ta ku, nafi ku kaunar shi’

Yakan murmusa ko tuna hakan yayi, da gaske ne a cikin ‘ya’ya akwai wanda zaka fi jin kaunar shi, Hindu ta kasance itace wannan ‘yar, har kasan zuciyarshi shi yake jinta, ko digon hawaye bayason gani akan fuskarta, ko da na farin cikine

“Hindatu?”

Ya furta da shakku tattare da muryar shi yana sake fadin

“Hindu? Hindun Baban ta…”

Mama kuwa kallon shi takeyi cikin kaguwa dajin me yake faruwa, amman taga hankalin shi ya tattara wajen sauraron Hindun, fatanta dai Allah yasa komai lafiya. A wahalce yaji muryarta ta sake fita

“Baaba ya koreni, Hamza ya kore ni. Yaki hakura gari ya waye…”

Wani abu Alh Aminu yaji ya tsirga mishi daga dan yatsan kafarshi zuwa tsakiyar kan shi, kafin ya dunkule yana dawowa ya tattaru a kirjin shi hadi da danne zuciyar shi ya takurata

“Ya kore ki?”

Ya bukata yanajin dacin da baisan ta inda ya taso mishi ba a makoshi, zai rantse yaga kan da ta daga mishi, gunjin kukan da take na sauka kunnune shi cikin rashin dadin saurare

“Cikin daren nan? Cikin dare zai koreki? Kina ina yanzun?”

Yanda take maida numfashi na sashi hasashen kalar kukan da take da yake tafasa zuciyar shi, dakyar tana numfarfashi ta amsa shi da

“Dakin Ba…Baba Maigadi, shiya aramun waya… Baba kazo karya fito ya koreni…”

Zuwa yanzun Alh Aminu ya mike tsaye

“Ki tsaya nan, kina jina? Gani nan zuwa, ki tsaya nan karki fito ko ina kinji Hindu… Yanzun zan zo in shaa Allah”

Kukan da take yasan ba zata iya magana ba, haka ya jira har sai da yaji tace

“To…”

Can kasa tukunna ya kashe wayar

“Me ya faru Alhaji?”

Mama ta bukata, ko kallonta baiyi ba balle ya amsa, dan ranshi in yai dubu a bace yake, ga hankalin shi da yake a tashe. Wajen durowar kaya ya karasa ya bude, doguwar riga jallabiya ya dauka ya dora kan wandon shaddar da ya kwanta dashi sai singileti, yanayi yana kiran wayar Muhsin da taki shiga, dan haka ya kira ta Huzaifa, bugu na biyu ya daga ko sallama baiyi ba balle tunanin gaisuwa yana fadin

“Baba lafiya?”

Hankalin shi a tashe, kai Alh Aminu ya girgiza, da wani irin zafin zuciya yace

“Ka sameni gidan Hindu, ka gwada kiramun Muhsin shima”

Duk da Huzaifa yaji shi ta dayan bangaren da wani sabon tashin hankali da yake bayyane a muryar shi yace

“Me ya samun Hindun? Baba me ya sameta? Ka fadamun ko zan samu natsuwar tuki”

Numfashi mai nauyi Alh Aminu yaja yana fitarwa

“Mijin ta ya koreta cikin dare nan, cikin daren nan Huzaifa…”

Ya karasa maganar yana kashewa, da fitilar wayar yayi amfani ya lalubi mukullin motar shi, da idanuwa Mama take ta binshi dan ita din bamai yawan magana bace ba, sai da taga zai fice ne tukunna ta bi bayan shi da fadin

“Kayi tuqi a hankali dai, Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya”

Tasan halin shi, shisa bata damu ba, komawa tayi ta kwanta tana jin yanda ruwan yake kara sauka har lokacin, da tunanin barkatai a ranta, ciki harda yanda batasan gaibuba, amman ta hasoso karewar auren Hindun a haka.

*****

Tana sauke wayar daga kunnenta ta mike ta fito daga dakin Baba Maigadi da yana ganin ta ya taso, wayar ta mika mishi

“Baba nagode.”

Ta furta cikin rawar murya tana fitowa daga barandar dan ta nufi kofa

“Ina zaki je?”

Sai da ta share hawayenta, tana ta kyarmar sanyi har lokacin ga wani ruwan da ya soma dukanta

“Za’a zo a daukeni yanzun, kar ya fito in maka sanadin aikin ka”

Kai kawai Baba Maigadi ya iya jinjinawa cikin tausaya mata, shiya bude ma Hindu kofar ta fita daga gidan, jikin bango ta samu ta rakube, ruwan na cigaba da dukanta, tanajin Baba Maigadi bai rufe gidan ba har lokacin, da alama yana tsaye bakin kofa, hankalin shi sam yaki kwanciya duk da tace mishi za’a zo daukarta din. Ba zatace ga lokacin da ta dauka a tsaye a wajen ba, amman tabbas bata da lafiya, rashin lafiyar da bata da alaka da Hamza, zazzabine mai zafi yai mata rumfa, har cikin idanuwanta take jin shi da take budewa tana rufewa, ga dan cikinta da yaketa motsi kamar yana son fitowa, wannan karin har bayanta sai da taji ya amsa, tako dafe cikin tana kiran

“Yaa Rabbi….”

Wata irin azaba na ziyartar kwanyarta, kafin hasken mota ya dirkako ta, daga idanuwa tayi tana jin sabon kuka ya kwace mata da taga motar Baba ce, yanayin parking ko kashe motar baiyi ba ya fito daga ciki yana sauke idanuwan shi kan Hindu da take ta takurewa duk idan iska ta kada, tana hango shi ta fara takowa, yana ganin yanda bata da takalmi, gata rungume da tsohon ciki. Wani abu Baba yaji yana karyewa a cikin zuciyar shi, ga dacin da yai mishi tsaye a makoshi, yama kasa takawa ya karasa inda Hindu take, yayi tsaye ne kamar an dasa shi. A wahalce ta karaso wajen shi tana wani irin kuka kamar zata shide

“Baa… Baaba na”

Ta fadi muryarta na sarqewa, hannu Baba ya mika ya kama na Hindu da baya tallafe da cikinta, yanajin sanyin daya dauka kamar kankara, shi kan shi da baifi minti biyu da shiga ruwan ba yayi sharkaf, ledar dake hannun nata yake bi da kallo

“Ham… Hamza ya bani.”

Ta fadi dakyar, karbar ledar Baba yayi ya saka cikin aljihun jallabiyar shi yana taimaka ma Hindu da takejin bayanta kamar zai rabe gida biyu, numfashi ma a wahalce take jan shi tana fitarwa, Baba ji yake tamkar zai kama da wuta saboda bacin rai. Mota ya bude yana taimaka ma Hindu ta shiga, dai-dai lokacin da wata motar ta tunkaro wajen, tsaye yayi bayan ya mayar da kofar ya rufe, Muhsin ne da Huzaifa suka fito suna karasowa inda Baba yake

“Ina Hindun?”

Huzaifa ya bukata dan inba ganinta yayi ba hankalin shi ba zai kwanta ba, murfin motar Baba ya bude mishi yaganta a zaune ta jike sharkaf, numfashi Huzaifa ya sauke cike da nutsuwar da ta saukar mishi

“In dai na isa da ku bana so kayanta su kwana a gidan marar mutuncin nan”

Baba ya fada yana saka Huzaifa kallon shi cike da tashin hankali

“Baba kayi hakuri dan Allah, ka isa Wallahi har kayi yawa ma, amman yanzun dare ne, gashi ana ruwa, ba lallai a samu masu motar da zasu fito ba”

Huzaifa ya karasa maganar da sigar lallashi, yana saka Muhsin dorawa da

“Kayi hakuri Baba, gobe tunda sassafe, kaga yanzun ya kamata muje gida ta sake kayan nan kar zazzabi ya kamata”

Kai Baba ya jinjina wani abu ya tokare mishi makoshi, bai ba Hamza auren yar shi dan yagaji da ita ba, duk da burin kowanne iyaye shine suga yaransu a gidajen mazajen su, amman idan babu kwanciyar hankali da nutsuwa gara ya dinga ganin yar shi cikin gida kullum, zai fi mishi wannan bakin ciki. Dakyar ya iya bude motar ya shiga, dan shima duk ya jike, sai da ya zauna tukunna ya kalli su Huzaifa yace

“Ku wuce gida kawai, goben idan an samu motar da zata kwashe kayan ku kirani”

Wannan karin su duka suka jinjina ma Baba kai, suna tsaye har saida sukaga ya bace musu, tukunna suka koma mota, gida Huzaifa ya fara sauke Muhsin, tukunna ya wuce nashi gidan shima.

*****

Wani irin sanyi take ji yana ratsata har cikin kwakwalwar ta yana hana mata wani tunanin daya wuce na son rufa da katon bargo ko zataji dumi. Da suka karasa gidama, Baba ne ya bude mata bayan motar, amman tayi galabaitar da ta sakko kafafuwanta wajen motar, amman ta kasa raba jikinta da kujerar.

“Hindu?”

Baba ya kira ganin yanda take fitar da numfashi a wahalce yana dorawa da

“Ko mu wuce asibiti?”

Kai Hindu ta girgiza mishi, kwanciya kawai take so taji tayi, ba zata iya zaman motar ba har su sake nufar asibiti. Dakyar, hannunta daya dafe da cikinta, dayan kuma ta rike kofar motar ta raba jikinta da kujerar tana mikewa tsaye hadi da runtsa idanuwanta kafin ta sake budesu cike da gajiyar da take ji. Baba na tsaye yana kallonta zuciyar shi cike da tausayin yar tashi, a gefe daya kuma fal da bacin rai, ita ta fara yin gaba tana karasawa wajen kofar tasa hannu ta murza tana turawa ta saka kafafuwanta cikin falon. Tana karasawa kan kujera ta zauna, Baba kuma ya wuce cikin daki inda yabar Mama, ba bacci takeyi ba tun fitar shi, tana kwance ne tana tunane-tunane, ta kunna fitilar and wayarta tunda babu wuta dan ana ruwa har lokacin

Tana jin sallamar shi ta mike tana fadin

“Kun dawo? Ina Hindatun?”

Hanyar waje Baba ya nuna mata, babu shiri ta sakko da kafafuwanta. Tana daukar wayar ta wuce falon ya rufa mata baya, kallo daya taiwa Hindu taga yanda take a galabaice, tana karasawa taba fuskarta tayi zuwa wuyanta tana jin yanda zazzabi ya rufeta ruf

“Alhaji da asibiti aka wuce da ita ai, kaji zazzabin da yake jikinta?”

Mama ta fadi kafin ya amsa tana dorawa da

“Tashi muje ki cire wannan jikakkun kayan.”

Saida Hindu ta sa bayan hannunta tana goge hawayen da taji ya zubo mata, tukunna ta kama hannun Mama data riko kafadarta dan taimaka mata, ta mike, dakin Mama din suka nufa tana bata kayanta, ta sake a wajen, dan wata kunyar Mama ce karshen abinda takeji. Sake kama hannunta Mama tayi suka fito daga dakin zuwa dakin baki da yake gyare tsaf, har sauri Hindu take karawa dan so kawai takeyi tajita a kwance, har wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke data kwanta, Mama ta rufa warware katon bargon da yake dakin tana rufa mata. Gefen gadon ta zauna tana kallon Baba daya biyosu ya kasa samun nutsuwa shima ta ce,

“Kaje ka sake kayan jikinka kaima ka kwanta, zan zauna da ita zuwa safe in Allah ya kaimu.”

Dan jim yayi kamar zai musa, tukunna ya jinjina kai yana wucewa ya fita daga dakin, duk da shine karshen abinda yake so yayi. Yafi so ya samu waje ya zauna sai yaga Hindun ta warware tukunna. Da tunanin ko da Hamza ne namijin daya rage a duniya Hindu tagama auren shi har abada Baba yake sake kaya. Shi da an sami mota ma cikin daren za’a kwashe kayan, tunda shi bashida mutunci.

Mama kuwa da taga ya fita, jikin Hindu ta sake tabawa taji da zazzabi har lokacin, tana kallon duk da idanuwan Hindu din a rufe suke, hawaye ne kawai yake zubar mata yana sauka ta gefen karan hancinta zuwa kan pillow din da take kwance

“Kiyi hakuri ki daina kukan nan Hindu, kinga bake kadai bace, karki jama kanki wani ciwon kinji ko?”

Kai kawai Hindu ta daga mata badan tana da wani iko akan zubar hawayen nata ba, su suke fitowa da kansu saboda kwanciyar da tayi da dumin bargon da ya rufe jikinta ruf yaba kwakwalwar ta damar tunanin asalin halin da take ciki. Ba tayi mamaki dan Hamza ya koreta tsakiyar dare da tsohon ciki, ana kuma ruwan sama ba, tana da tabbacin yana can kwance yana baccin shi a nutse, dan babu wani abu da yake shiga tsakanin shi da baccin shi. Ya kan ce,

‘Koma meye zai iya jira, bacci na ba zai jirani ba.’

Sake runtsa idanuwanta tayi gam, har radadi suke mata da tasan kukan da tasha ne a daren, kukan da ba yanzun ta fara yin shi akan Hamza ba, bata dai san ranar karshe da zata daina ba, da gaske takeyi lokacin da tace mishi,

‘Na manta ranar karshe da hawayena suka zuba akan wani abu da ba kai ba.’

Sai takejin kamar tun tana yarinya rabon da wani abu ya sakata kuka sai bayan ta hadu da Hamza, daga ranar ta fara kukan da ya kawota inda take yanzun,

“Ko dai sai munje asibiti a daren nan?”

Mama ta tambaya cike da damuwa, dan ita kam bataso taga mai ciki a wani hali. Tunda tasan shi kanshi daukar nauyin cikin idan aka barka dashi batare da an kara maka wani ciwon ba ya isheka. Cikin disashiyar murya tace

“A’a Mama, bacci nake so inyi.”

Bawai dan tana jin baccin ba, kai Mama ta jinjina

“In kawo miki ruwa.”

Kai kawai Hindu ta iya girgiza mata da alamar a’a. Kyaleta Mama tayi a zuciyarta tana mata fatan samun sauki, ta hau kan gadon tana jan mayafi ta rufe kafafuwanta sannan ta kwanta, dan kanta harya fara ciwo, gara ko baccin kasa da awa biyune ta samu kafin asuba, fitilar wayar ta kashe tana lumshe idanuwanta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Mijin Novel 2 >>

1 thought on “Mijin Novel 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×