Cikin sati daya, ko idanuwanta ka kalla sai kaga yanda tayi zuru-zuru. Anty da ta tambayeta haka kawai tace mata.
"Karatun ne ya kara zafi Anty."
Jinjina kai kawai Anty tayi, da damuwa a cikin idanuwanta.
"Ki dinga hutawa dai."
Murmushi ta tsinci kanta da yi, Anty na daya daga cikin iyayen da basu cika bayyana kaunar su a fili ba, amman a cikin duk wani motsi da zatayi sai ka karanci tsantsar kaunar da take yiwa yaranta. Su kansu suna mamakin yanda take gane wani abu yana damun su, ko ya canza a tattare dasu. Hindu ba zata. . .
,,💙💙