Skip to content
Part 15 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

Cikin sati daya, ko idanuwanta ka kalla sai kaga yanda tayi zuru-zuru. Anty da ta tambayeta haka kawai tace mata.

“Karatun ne ya kara zafi Anty.”

Jinjina kai kawai Anty tayi, da damuwa a cikin idanuwanta.

“Ki dinga hutawa dai.”

Murmushi ta tsinci kanta da yi, Anty na daya daga cikin iyayen da basu cika bayyana kaunar su a fili ba, amman a cikin duk wani motsi da zatayi sai ka karanci tsantsar kaunar da take yiwa yaranta. Su kansu suna mamakin yanda take gane wani abu yana damun su, ko ya canza a tattare dasu. Hindu ba zata iya gayawa Anty asalin abinda yake damunta ba, batasan ta inda zata fara ba ko da zata iya. Jaruman litattafan hausa kan sha gwagwarmaya a ciki labaran su, kafin su samu cimma burin su, amman sunayin hakanne tare da Samarin, suna nuna musu wata irin zazzafar kauna a duk wani motsi da zasuyi.

Samarin basu taba zama matsalarsu ba, sai dai dangi, ko wani abin daban. Amman cikin sati daya, Hamza ya zame mata matsalar da ki a mafarki bata hango faruwarta ba, ga soyayyar shi da ta samu waje tayi mata zaune. Ta dauka tana da rikici, ta dauka ta iya rigima, ta kuma dauka ta gama gane cewar shi Hamzan yana da rikici, sai a satin nan daya, tunda ya fara kiranta da budurwar shi, ko wayarta ya kira yaji busy saiya tsareta da tambayoyi akan wa take magana da shi, idan wani da ba dan uwanta bane ya fara tashin hankali kenan, wani irin kishi take gani tattare da shi daya fara bata tsoro.

Yanzun kiri-kiri yayi mata blocking din Ahmad daga Instagram har Twitter din ta, harda fadin, “Allah ya isa idan kika kara magana da shi, dan ba kya son shi baya nufin shi din baya jin wani abu a kanki, ko da bayaji ni baimun ba, bana son shi, bana so kina magana da shi.”

Ahmad din har kiranta yayi, bata daga ba saboda batasan me ma zatace mishi ba, taga text din shi.

‘Naga kinyi blocking dina Hindu, bansan ko nayi miki wani abu bane ba, na kira baki daga ba.’

Goge text din tayi saboda kunyar Ahmad din da takeji, yana da hankali da matuqar kirki, da ta gwada cewa Hamza

“Ba zai yiwu ka dinga mun blocking din mutane ba, wasu abokan karatuna ne, idan ina bukatar tambayar su wani abu fa?”

Yanda ya fadi

“Ni? Ni kike fadama ba zai yiwu ba?”

Sai da tadan raba wayar da kunnenta, kafin ta mayar tana jin shi yana cigaba da fadin

“Kome zaki tambaye su, ni ki tambayeni, ni kadai na isheki, banda yan uwanki, ni kadai ne namijin da zai kasance a rayuwar ki, gara ki saba tun yanzun”

Kafin ma ta sami fadin wata magana harya kashe wayar shi. A kwanaki bakwai rana daya ce basuyi tashin hankali da shi ba, sai ya hau Instagram dinta, ya zaqulo tsohon chat ya tisa mata rigima a kai, ba karamin tashin hankali tagani wajen shi ba, akan hirar su da ya gani da Jalil, inda yasan yanda zancen ya qare ma da bai tashi jijiyar wuya a kai ba. Ita kam tunda ya bata password din shi ta hau sau daya, bata ma sami nutsuwar da zata koma ba. Sai yanzun da batada abinda zatayi, bata da wani assignment saboda jarabawa data qarato, sai project din zangon kawai, da a hankali take bin zanen.

Da yake asabar ce, a daki ta wuni, Anty ma bata sakata aikin komai ba, dan yanda taga tayi zuru-zuru sai ta kyaleta, taji dadin hakan har ranta. Yanzun ma tunda ta idar da sallar la’asar ta koma kan gado tayi zamanta. Hamza yace mata yana da aiki, idan anyi Magriba zai zo ya ganta, tunda duk satin basu hadu ba, sai dai video call kawai da sukeyi. Yau din ma tun safe, sai text din shi bayan la’asar.

“Azkar din yamma.”

Ta amsa shi da tayi, ko tana makaranta ne haka yake mata wannan tunin, yanzun da Asuba duk baccin da yake idanuwanta in batayi karatun Qur’ani ba sai yasa ta tashi, wani lokacin video call zai kira yaga ko ta tashin, yakan ce mata,

“Ranar ki zata tafi dai-dai idan kika fara ta da sallar Asuba a kan lokaci, kiyi karatunki koya ne, kiyi azkar, sai ki rufe da sallah raka’a biyu idan rana ta fito”

In ta nemi yi mishi musu saiya ja mata ayoyin da zasu kashe mata jiki, sosai da duk rana Hamza yake kara samun waje a zuciyarta, lamurran shi kuma na bata mamaki sosai da sosai. Twitter din ta hau tana cin karo da tarin notifications da ta fara budewa, taga Mansy ce da tayi ma Hamza magana, ba gane me tace tayi ba tunda da fulatanci ne, wani irin tsaki taja, tsanar da tayi mata na dawowa farko

“Tsohuwar banza mai tallar goro.”

Ta furta a fili tana kara dorawa da wani tsakin, ta tafi DM din Hamzan ta bude, nan ma na Mansy ne a farko.

“Nawan ina kaje ne yau haka?”

Ta karanta sakon da tayi da harshen Hausa, wato munafunci ne yasa take mishi yare a bainar jama’a, anan kuma takeyin magana da wanda kowa zai iya fahimta. Shiga sakon tayi, zuciyarta nayin tsalle ta dawo makoshin ta, kafin ta koma kirjinta inda taci gaba da dokawa da wani irin ciwo da yasata yin tari, idanuwanta har yaji suke da abinda ya wuci hawayen da taji sun taru cikin su, hotunan da Mansy ta turo mishi ne tana dorawa da, “Wanne yafi kyau?”

Rigar mama ce mai hade da wani wando da Hindu takan ga turawa sun saka a bakin ruwa, bata ga dalilin da zaisa Mansy ta turo ma Hamza irin wannan hoton bane ba, ko da soyayya sukeyi abune da bai kamata ba sam-sam. Amman kamar yanda Dimples kan fadane,

“Ni banga dalilin da zaisa mata suje suna fada da yan matan mazajen su ba, ko ke budurwa da bakima shiga gidan shi ba ki fara tsanar matan da suke tare da shi ba, saboda koma me yake faruwa a tsakanin su, shi ya bada fuska.”

Amman hakan bai hanata jin kamar ta soka ma Mansy mashi ba, sama tayi tana karanta hirarrakin su da ko kadan babu kintsi a ciki, sam batasan hawaye take ba sai da taga digar su saman screen din wayarta, sosai kirjinta yake mata zafi, bata taba jin ciwon zuciya irin wanda takeji ba yanzun. Kwata-kwata tashin hankali bakonta ne, fitowa tayi daga hirar, tana cigaba da bude sakonnin sauran matan, da suke ma Hamza tallar kawunan su, sai dai amsar shi daya ce ga duk wadda ya amsa.

“Digits”

Ma’ana lambar wayar kenan, in suka ajiye kuma babu wani abu da yake sake hadasu, amman hirar su da Mansy ta gama tabbatar mata da abinda yake faruwa a tsakanin Hamza da sauran matan.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Ta tsinci kanta da furtawa tana sauke wata ajiyar zuciya saboda kukan da takeyi. Hamza na bin mata, ko baya bin sauran matan yana tare da Mansy. Wannan ba zargi takeyi ba, hirar su ce ta tabbatar mata da hakan. Wayar ta ajiye kan cikinta, tana saka tafukan hannuwanta duka biyun ta rufe fuskarta da su. Kuka takeyi da ba zata tuna ranar da tayi irin shi ba, sosai zuciyarta take ciwo kamar zata fito. Tana nan kwance, tayi kuka har fuskarta ta kumbura, kafin ta iya mikewa tana shiga bandaki, ta wanke fuskarta, tana dauro alwalar Magriba. Tana fitowa ana kiran sallah, lokacin da yayi dai-dai da shigowar Asma dakin da sallamarta da Hindu ta amsa murya a dishe.

Tana kuma yin sauri ta kabbara sallah, tana jin Asma ta shiga bandaki, tana fitowa kuma ta fice daga dakin. Tana idar da sallah, dakyar ta iya yin azkar, da ta daga hannuwanta sai ta rasa addu’ar da zatayi, tana tsaka tsakiya neman wani canjin ba Hamza ba, ko kuma nema mishi shiriya, kafin ta yanke hukuncin tsayawa a nema mishi shiriya, dan zuciyarta ta karyatata wajen tunanin cewa abinda tagani akan Hamzan ya canza abinda take ji, yana nan daram a ranta kamar komai bai faru ba.

Wayarta data fara ruri ta mika hannu ta dauka tana ganin shine, dagawa tayi ta kara a kunnen ta.

“Ina cikin gidan ku”

Ko magana batayi ba ta sauke wayar daga kunnenta, tana mikewa. Ko fuskarta bata duba a mudubi ba, hijabin jikinta kawai ta sake, tana daukar ruwan toka, da ta Asma ce ta zira a jikinta. Ba zata tsaya shafa wani abu ba, shiya sakata kuka, ya kamata yaga haka, ba zata boye mishi tana cikin yanayin damuwa ba.

*****

Komai sabone a wajen shi, inda wani a cikin abokan shi zaice mishi a shekarar nan zai kira wata yarinya da budurwar shi zai karyata. Ba zaice ga yanda akayi ya ce Hindu ta saka shi a layin samarinta ba, yafi ta’allaqa hakan akan yanda tunaninta da wani saurayin yasa shi ganin wani hadarin kishi na gilma mishi ta cikin idanuwan shi, kirjin shi har zafi yakeyi. Bayason kowanne namiji a kusa da ita banda shi, bayason wani yaji muryarta, balle yaji yana son ya riketa kamar yanda yakan ji duk idan tana magana.

Aikin daya sakko su gaba bai hana shi tunanin halin da take ciki ba, da wa tayi magana a makaranta, wayai mata magana, waya tare ta a hanya. Shi kadai sai ya tsinci kan shi da jan karamin tsaki, yanzun tunda ya shiga Instagram dinta rabon daya shiga nashi, yana kai kullum yana ganin yanda ta sake tana hira da maza da yake bala’in bata mishi rai. Yau ma duk da ya yanke hukunci ajiye komai yaje ya ganta, haka ya shiga Instagram yana dudduba sauran chats dinta, dan duk wanda ya karanta saiya goge gabaki daya, yayi blocking idan namiji ne. Matan baya bi ta kansu sam, tsaki yaja ganin wani yayi mata sallama tafi biyar.

“Wawa kawai.”

Ya fadi yana saka AbdulHafiz da yake shan shayi yana aiki a system din shi ya dago da ido ya kalle shi

“Me yasa maza basu da aji ne?”

Hamzan ya tsinci kan shi da tambaya, yana saka AbdulHafiz yin murmushi.

“Me yasa wasu mazan basu da aji zaka ce. Me ya faru?”

Tsaki Hamza ya sake ja, duk satin nan baya rabuwa da ciwon kai, akan Hindu ne kuma, ita ce sabon ciwon kan da ya shigo rayuwar shi.

“In kaga mazan da suke DM dinbHindu suna mata magana zakayi mamaki wallahi, kamar basu da wani aiki banda bin yaran mutane.”

Shayin AbdulHafiz ya kurba, sannan ya ajiye kofin a nutse, ba sosai yake saka kananun kaya ba, yanzun ma dan suna gidane, anan suke ta aikinsu tun safe, tracksuit ne a jikin shi, riga da wandonsu, yaja zif din rigar har wuyan shi a rufe yake ruf, dago da idanuwan shi yayi yana saukewa kan Hamza da yake girgiza kan shi cike da dana sanin subutar bakin da yayi akan Hindu din. Banda Fodio babu wanda yasan da maganarta, shima Fodio din ya dauka Hamza ya sami abinda yaje nema ya barta.

“DM? Screenshot ta turo maka?”

AbdulHafiz din ya fara tambaya, Hamza ya riga yasan ba zai iya kaucewa maganar ba, ya riga yayi subul da baki, kuma yanayin fuskar AbdulHafiz din ya nuna mishi ba zai bashi wannan damar ba yau, gashi su kadai ne, Arafat da su Fodio suna kamfanin su. Daga shi sai AbdulHafiz din a gidan, da saiya sake maganar, AbdulHafiz zai dauka bayason yayi a gaban su Arafat a lokacin, zai kyale shi.

Kai ya girgiza ma AbdulHafiz din.

“Da kai na nake gani.”

Shayin AbdulHafiz ya sake kurba yana ajiye kofin.

“Abu biyu zan fada maka, ban san me kakeyi a Instagram ko Twitter din ta ba, amman hakan zai saka rashin yarda a tsakanin ku, idan ka yarda da kanka, ka yarda da soyayyar da take maka, sauran mazan bai kamata su dame ka ba.”

AbdulHafiz ya fadi yana dorawa da,

“Ka zama Sarki a masarautar yarinyar da kake tare da ita, sauran mazan duk da zasu zo fadawa ne, ba su da wani muhimmanci, da kanta zata baka labari kuyi dariya. Karka fara dora alamar tambaya akan zaman ku, in bata baka dalilin yin hakan ba.”

Yana jin kalaman AbdulHafiz dinne, amman bai yarda dasu ba, badan bai yarda Hindu tana son shi ba, kawai dai yana so yaga dawa take magana ne.

“Wacce Hindu din?”

AbdulHafiz ya tambaya, tunda maganganun da yayi basa bukatar amsa, kawai saurare ne, idan Hamza yaga dama ya dauka, idan baigani ba ya rigada yayi nashi bangaren.

“Yarinyar da ka amsa a DM dina.”

Kai AbdulHafiz ya jinjina, yagane ta, yana son yaji tabbaci ne daga wajen Hamzan. Sosai ya gyara zaman shi yana tattara duka nutsuwar shi da hankalin shi akan Hamzan, dan maganar da yake son fadi na da matuqar muhimmanci a wajen shi.

“Nasan kaddara zata hadaku idan Allah ya rubuta hakan ko da ban amsata ba, kaddarar tazo da ni ne sanadi. Ka jini Hamza, saboda zan fada maka sau dayane, kamar dan uwa kake a wajena, kasan hakan, ba yau ne na farki dana fada maka ba, ina maimaita maka ne….”

Numfashi Hamza yaja yana fitarwa, tun kafin AbdulHafiz din ya karasa maganar ta tsinci kanshi da son tashi ya gudu ya bar dakin, dan ya kauce ma jin koma meye zai fada.

“Kusancin da yake tsakanin mu ba zai sa ka darsa mun kokwanto a neman lahirata ba Hamza. Kana jina, idan ba da niyyar aure kake tare da yarinyar nan ba, idan babu alkhairi a tare da niyyar ka, ka yanke koma menene a tsakanin ku, bazan zama silar baka ticket din da zaka sakata a layin matan da kabi ba. Baka isa kai mun haka ba, wallahi baka isa ba, kaji na rantse, ban isa in hanaka abinda kakeyi ba, shisa nake binka da addu’a, amman banda ita, banda Hindu….ba rokon ka nakeyi ba, fada maka nayi. Bazan yafe maka ba wallahi…”

AbdulHafiz ya karasa maganar yana so Hamza ya fahimci da gaske yake, idan ya bata musu yarinya zai yanke alaka da shi, maganar farko tayi mishi yanayi da Nabilar shi, batayi kama da matan da Hamza ya saba bi ba sam, ba zai zama sanadin da zata lalace ba. Ba zai yafe ma kan shi ba idan Hamza ya taba ta, kamar yanda ba zai yafe ma Hamzan ba. Kofin shayin shi ya dauka yana tura kujerar da yake kai baya, hadi da mikewa dan yaje ya karo wani shayin da yake kitchen cikin kettle.

Nan yabar Hamza a zaune yanajin kamar an mishi wanka da ruwan kankara. Shi bai shirya yin aure ba, sam babu wannan tsarin a rayuwar shi nan da shekaru biyu ma, ko gidan shi bai gama ba. Bai san yanda AbdulHafiz din yake so yayi ba, yanajin dai yanzun ko Hindu bata isa ta raba shi da kanta ba, balle kuma wani. Har ran shi yanzun ba zaice ga abinda yake da niyya akan ta ba, yana son kasancewa da ita, amman shi bai shirya aure ba sam. Kamar yanda bai shirya yanke alakar da take tsakanin shi da AbdulHafiz ba, zai iya hakura da Hindu ko da aurenta zai idan hakan zai shafi alakar da take tsakanin su da AbdulHafiz, yana jin shi kamar dan uwan shi, sun wuce matakin abokantaka.

Sosai kan shi yake mishi ciwo, AbdulHafiz ne ya dawo.

“Kai ba zaka sha shayin ba?”

Ya tambaya kamar bai gama hargitsa mishi dukkan lissafin shi ba, ammam AbdulHafiz ne, ya riga ya gama maganar kenan, ba zai maimaita ba. Yabar komai a hannun Hamzan, zabin nashi ne. Kai kawai ya girgiza mishi da yake jin yana kara ciwo. Su dukan su aikin da sukeyi suka cigaba. Kafin AbdulHafiz din ya fara waya da Nabila, ya saka earpiece a duka kunnuwan shi, hirar tasu na saka Hamza jin kewar Hindu da ta danne shi, tun la’asar rabon daya ji motsinta. Aikin da yakeyi yai saving yana kashe laptop din ya mike, zuwa yai yadan watsa ruwa ya dauro alwalar magriba ya fito, kaya ya sake zuwa manya, wani farin yadi daya karbi jikin shi, bakar hula da takalmi ya saka. Ya dauki mukullin mota yana fita falon.

Wayar shi ya dauka da take kan tebirin da suka ajiye daga can gefe inda suke ayyukan su, dining ne ba zama suke suci abinci ba, ya zame musu kamar Office din gida. Harya kai kofa AbdulHafiz yace, “Hamza…”

Juyawa ya yi, “Allah yasa alkhairin ka ce.”

Dan murmushi Hamza yayi yana ficewa daga gidan, wasu lokuttan AbdulHafiz kanyi mishi kamar babban Yaya, duk da watanni biyar ne tsakanin su, shisa yake kasa zagin shi kamar yanda yake zagin su Fodio. Yanayin kusancin su daban ne, kuma su dukan su yana musu kamar Yaya fiye da yanda yake aboki a wajen su. A hanya ya tsaya nan masallacin da yake station round about, yayi sallar magriba, kafin ya karasa gidan su Hindu, maigadi na bude mishi kofa ya shiga da motar shi, bai fito daga motar ba ya kira wayarta, tana dagawa yace,”Ina cikin gidan ku.”

Ba tace komai ba, shima bai jira amsarta ba, ya kashe wayar daga bangaren shi, yana ajiyeta a cikin motar. Wani irin sama-sama yake jin shi, ga kan shi da yake ciwo har lokacin, duk da wani bangare na zuciyarshi na cike da jin dadin zai ga Hindun, yau maganganun AbdulHafiz da yake ji sun dabai-baye shi sun kashe mishi jiki tsaf, a karo na farko tun daya hadu da Hindu da yazo wajenta batare da yanajin kamar inta fito bai riketa ba zai mutu.

Bai fito daga motar ba, sai da yaga Hindu da ta ajiye musu kujeru bayan motar shi, da murmushi a fuskar shi ya zagayo yana jan kujerar ya zauna. Sai dai tana zama ya sauke idanuwan shi kan fuskarta, murmushin da yakeyi ya dishe

“Hindu…”

Ya kira ganin fuskarta da take a kumbure har cikin idanuwanta, ai kamar hakan take jira taji wasu hawaye da ta kasa tarbewa sun zubo mata, yana fitowa taji kamar ta rufe shi da duka, kallon da yake mata cike da damuwa shiya karya mata zuciya yasa hawayenta zuba

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un… Me ya faru? Mene ne?”

Hamza ya fadi yana kai hannu ya riko na Hindu data fisge tana goge hawayen fuskarta

“Dan Allah kiyi mun Magana.”

Numfashi taja tana sake goge fuskarta, zuciyarta take ji tana ciwo kamar zata fado

“Me yasa kabani Password din ka?”

Ta tambaya tana tsare shi da idanuwanta da suke cike da wani yanayi da yaji bayaso

“Saboda bani da abinda zan boye miki.”

Ya fadi da dukkan gaskiyar shi.

“Har hirar ku da Mansy?”

Ta bukata tana jin kirjinta na gab da budewa, numfashi Hamza yaja, yana huro iska ta bakin shi, ya dauka wani abinne daban akayi mata, ko shi yayi mata bai sani ba. A hankali ya daga mata kai, tunda ta rigada tagani baiga dalilin da zai mata wani boye-boye ba. Cikin sanyin murya saboda kan shi da yake ciwo yace,”Me kike so ince miki?”

Dariya Hindu tayi da bata da alaka da nishadi.

“Kana da karfin halin yimun wannan tambayar Hamza? Bakasan abinda ya kamata ka ce mun ba? Akan abinda kukeyi da Mansy har kana ce mun baka da abinda zakace mun?”

Idanuwan nan nashi ya kafa mata, irin wannan dalilin na daya daga cikin dalilan da zasu saka shi kinyin aure nan kusa, ba zai yiwu ana tsare shi da tambayoyi haka ba.

“Karkiyi mun ihu, karki fara cewa zakiyi mun fada. Dana baki password dina nace ki karanta mun chats? Na aikeki karanta hirar mu da Mansy? Da kika fara karantawa kikaga ba zaki iya jurewa ba me yasa kika ci gaba?”

Bakinta a bude yake tunda ya fara magana, dariyar ta sakeyi duk da idanuwanta da suke cike taf da hawaye.

“Kana da karfin hali, wallahi kana da karfin hali Hamza.”

Daga mata gira yayi cike da masifa, kan shi ciwo yake kamar zai rabe biyu. Tana kuma kara mishi ciwon kai kan abinda ita taga zata iya karantawa, shima haka ya jure bin chats dinta da garadan duk da suke mata magana, harda Jalil, baiyi kuka ba duk yanda zuciyar shi tayi mishi ciwo, sai ita da take da hawaye a kusa zatayi amfani da su ta cuce shi, haka mata sukeyi daman ya sani, abu kadan sai su fara kuka, idan wani yagani zai baka rashin gaskiya kamar kayi musu wani babban abu.

“Na karanta hirar ku da Jalil tun daga farko har karshe, saboda bani da hawaye shine zaki fini fada.”

Kai Hindu take girgiza mishi.

“Karka hada wannan da Mansy, ni banbi Jalil ba, bakama san ya muka kare da shi ba.”

Cikin idanuwa Hamza yake kallonta.

“Zunubina ne, me yasa zai dameki?”

Mikewa tayi, ba zata iya ba, zuciyarta fadowa zatai idan taci gaba da sauraren Hamza, taci gaba da ganin yanda yake nuna zina a wajen shi ba wani babban abu bane ba. Hannunta ta kama yana janta ta koma ta zauna babu shiri, hannunta ta fisge

“Karka sake tabani, abinda ya kawoka kenan daman. Wallahi ba zaka taba samu ba, saboda ni ba Mansy bace ba, kasani dai ka cutar dani…Allah kuma ba zai barka ba.”

Hindu ta karasa wasu irin hawaye masu zafi na zubo mata, zuciyarta ciwo take har cikin makoshin ta, ga wani tsoro marar misaltuwa daya lullubeta na ma’anar kalamanta, ba ta shirya ba, bata san ya zatayi idan suka rabu ba, amman ba zatayi ma kanta karya ba wannan karin, ba zata iya ba Hamza abinda yazo nema ba.

“Ni zaki hada da Allah Hindatu?”

Hamza ya tambaya yanajin tashi zuciyar na tafasa shima, duk abinda zaiyi a rayuwar shi bayaso yaji an hada shi da Allah, yana kokarin ganin zunuban shi tsakanin shi da Ubangiji ne, bai hada da hakkin mutane ba.

“Me ma kike so ki ce mun? Bari na zakiyi?”

Ya karasa maganar muryar shi na wani irin sauka, kan shi naci gaba da sarawa, a karo na farko a tsayin lokaci a rayuwar shi da yaji tsoro ya dabai-baye shi da tunanin cewa zata bar shi.

“Ya kake so inyi? Ba zan iya ba, wallahi ba zan iya baka abinda ka zo nema ba.”

Ta karasa maganar tana rufe fuskarta da hannuwanta saboda kukan da takeyi, baisan lokacin daya kama hannuwan yana rabasu da fuskarta ba, ya dumtse su cikin nata, kai yake girgiza mata.

“Baki isa ba, wallahi baki isa ki rabani dake ba, Hindu baki isa kisa in fara sonki ba kibarni, ni ban tsara soyayya a rayuwata ba koda aure zanyi, saboda bana so in wahala, ba zaki barni ba, kina jina.”

A hankali ta zame hannuwanta daga rikon da yayi mata, dan ya fara karya mata zuciya fiye da yanda take a karye. Mikewa tayi, ta goge fuskarta sosai tana tashi, dai-dai lokacin da aka kira sallar isha’i, muryarta a dishe tace,

“Kaga an kira sallah.”

Kai Hamza ya girgiza mata, shima yana mikewa

“Dan Allah ka barni, zuciyata ciwo takeyi, in ba kasheni zakayi ba yau, kabarni haka.”

Numfashi ya sauke.

“Karki barni to, kice ba zamu rabu ba.”

Kai Hindu ta iya daga mishi, gida kawai take so ta shiga, ko zatayi kuka har sai zuciyarta ta rage mata ciwo

“Okay…. Koma menene karki barni, ina son ki.”

Ya furta kalaman na sauka kunnuwan shi da tabbaci kan abinda yakeji a kanta. Kafin tayi wani abu taji ya riketa a kirjin shi, sosai wannan karin ta ture shi

“Kagani ko? Abinda kake so kenan bani ba”

Kai Hamza ya girgiza mata, ya riketa ne dan ya rage jin tsoron da yakeji, yau ko abinda take tunanin ma bayaji sam, tashin hankalin da yake ciki ya girmi wannan

“Nasan abinda nake so, kuma duka biyun ne.”

Numfashi Hindu ta sauke, ta mika hannu taja kujerar daya tashi daga kai, ta dagota tana hadata da dayar. A wajen tabarsu tana wucewa ta shige gida, tsaye Hamza yayi a wajen, gabaki daya gwiwoyin shi sunyi sanyi. Da kyar ya iya zagayawa da nufin ya bude motar shi ya shiga, yaji an mishi sallama, juyowa yayi yana mika mishi hannu suka gaisa, ya gane hoton shi, Hindu tana yawan saka shi a status dinta, Zaid tace mishi, Yayanta ne, tace likita ne. Kare mishi kallo Zaid yakeyi, akwai inda ya taba ganin Hamzan, ya rasa ko ina ne, amman haka kawai yaji baiyi mishi ba.

“Idan kana son ta da gaske, ka turo ayi magana kafin ka sake zuwa.”

Zaid ya fadi, ko bai tuna ina ya taba ganin Hamza ba, bayason irin su a kusa da kanwar shi, sam bayaso. Idan da wata niyya yazo Zaid nada tabbacin daga yau ba zai sake dawowa ba, hakan ma zaifi mishi, dan ko turowa yayi har unguwar su zaije da kan shi yayi bincike a kan shi, ba kullum yake yankewa mutane hukunci batare da yasan labarin su ba, amman kuma zuciyar shi kanyi gaskiya akan mutane da yawa, in har yaji kamar baka da hali me kyau sai hakan ya kasance gaskiya. Wucewa yayi kafin Hamzan yace wani abu, dan karma ya samu fuskar ganin wasa yake da shi.

Motar shi Hamza ya shiga, yau dai kowa so yake ya raba shi da Hindu, harda ita da kanta, kuma zai nuna musu basu isa ba, kamar yanda yace ne, yana son ta, da a rabashi da ita gara yayi abinda bai shirya ba, duk sai su sama mishi lafiya su daina kokarin ganin sun rabasu. Hanyar da zata kai shi Tudun Wada ya nufa, gara yayi magana da Appa.

<< Mijin Novel 14Mijin Novel 16 >>

1 thought on “Mijin Novel 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×