"Baba ni ina son shi"
Hindu ta furta kalaman da ko a mafarki batayi tunanin zata iya gayawa Abba su ba, duk kuwa kusancin da yake tsakanin su, saboda kunya. Anty ma tun satin daya fita sai ta WhatsApp ta tura mata sakon cewa tayiwa Abba magana Hamza yace zai turo. Amman yau tura ce ta kai bango. Kiri-kiri take ganin yanda duka yan gidan suka juya mata baya kan maganar Hamza. Kuma Zaid ne, duk shi yaja da zancen binciken shi, batama ga matsalar shi akan maganar aurenta ba, yanzun ma da take tsugunne a gaban Baba idanuwanta. . .